← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 145

Sashe 101

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🥕OSUN🥕
Indo tana zaune a d'aki suna zancensu da angoriyenta Dauda shi yana kwance yayi matashin kai da cinyarta sai dariya suke abinsu cikin nishad'i sukaji anyi sallama da sauri Indo ta janye kansa tana tashi tsaye ta koma kan kujera ta zauna harda d'an zaro ido.

'Dan harararta Dauda yai yana cewa "bismilllah kasaso maman Niseh shigo ciki muna nan

Dariya Maman Niseh tai tana shigowa tace "aina dauka bacine kuna yi nace ina salama shiru ashe kana gida yau baka fita ba dama nace bari nazo naga amaryar ka ne".

Maman Niseh bayerabiya ce a mokoftansu take suna mutunci sosai da Dauda tunda dad'ewa ko gida idan zai tafi ita yake barwa ajiyar mashin d'insa.

Tashi zaune Dauda yai yana kallon yadda Indo ta kame guri d'aya kamar zaiyi dariya yace "wallahi maman Niseh kin ganta nan cousin d'ina ce".

Zaro ido maman Niseh tai da irin surprise d'in nan tace "to abun nan na irin gida kukayi dama da gaske ne kanayi da kace min kana son yar uwa naka zaka aureta"?.

Kallon Indo Dauda yayi daidai itama ta d'ago da mamakin dama yana sonta ne gira ya d'age mata yana kashe ido kafin yacewa maman Niseh.

"Eh itace tayi ko na iya za'be"?.

Kai maman Niseh ta d'aga tana murmushi tace "walay Doda ka iya zabe sosefa wannan beauty Ale bada zeman lafiya nima yanxu na samu makociya zaki rika shiga min muna hirako"?.

"Kai Indo ta d'aga "eh zan shigo miki insha Allah".

"Yewa ameryan Doda ashe wayeya ce ka iya zabe bari na tafi na baro yan makade a gidan kuma Niseh bata nen Ikki ma bata nen sun tafi school" ta fad'a tana mi'kewa.

"To maman Niseh ki gaida gida mun gode sosai saita shigo miki" Dauda ya fad'a yana kallon Indo data mi'ke tsaye yace.

"Wato shine dan kinji sallama harda ture min kai ko"?.

Shiru Indo tai tana turo baki tace "to ai nayi tunanin shigowa zatai kai tsaye.

"Haka kawai saita shigowa mutane d'aki kai tsaye kamar wata mara hankali kedai kice har yanzu qauyanci ne bai barki ba kamar baki dad'e a nan d'in ba".

Jin abinda yace yasa Indo ta had'e rai zatai magana yace "zo nan" gumm tai da bakinta tana d'an matsawa wajen kofar fita ganin guduwa take shirin yi yasa ya mi'ke wuf tayi zatai waje ya dam'kota yana dawowa da ita cikin d'akin ya rungumeta ta baya kenan suka ga an d'aga musu labule wata yarinya ta shigo a d'ayan d'akin suke haya da sauri ya saketa yana matsawa baya ya koma kan katifa ya zauna dariya Indo tai tana kallon sa ganin ya harareta yasa ta rufe baki cike da tsokana tayi masa magana da ido kai ya jinjina irin bari yarinyar ta fita zasu had'u ne zaro ido tayi tana masa gwalo kafin ta mayar da hankalinta kan yarinyar tana cewa.

"Amrat me ya faru"?.

Itakam yarinya da ba abinda suke ne a gabanta ba tace "wai gashi inji momyna mun dawo daga anguwa da daddy ya sayo min a hanya shine tace na kawo miki".

Kar'bar kwanon Indo tai kayan marmari ne a ciki a wankesu tas tace "yauwa Amrat kicewa mamanki na gode" ta tace har zata fita ganin kanta an fara tsefewa maybe a anguwar da sukaje ne ta'ki aka 'kyale ta dama da lallami Indon take mata tazar ko a gida dan haka tace.

"Amrat kukan taza kikai"?.

Kaita d'aga "eh wata ce acan wai saita yimin kitso ni kuwa inata kuka".

Ri'ko hannunta Indo tai tana cewa "oh ayya sannu Amrat d'ina yi ha'kuri ta ja miki kai ko rabu da ita zo zauna na karasa miki a hankali" ta fad'a tana zaunar da ita zaro ido Dauda yai dan ya fahimci inda Indo d'in ta dosa amma saiya shareta yana yin qwafa kafin ya mike yana d'aukar key d'in mashin ya fice yana cewa.

"Huyim yarinya gama zille zillenki zamu had'u ne".

Ita dai Indo dariya tai bayan fitarsa tace "oho dai kafin mu had'un aina huta ko haba wallahi ya Dauda akwai cuta ni bari ya dawo ma naga mangoro ya nuna a gidan maman Niseh d'in nan muje ya tsinko min raina ya biya🤔" ta karasa maganar tana fara gyarawa yarinyar gashinta daidai maman Amrat tazo bakin kofar tana cewa.

"Assalamu alaikum ke kad'ai dan Naga takalma biyu"?.

"Eh ni kad'ai ce maman Amrat shigo da d'ayan ya fita" shigowa tai ganin yadda Amrat ta zauna ake mata taza hankali kwance tace.

"Lallai yarinyar wato mukaje dake Ummi tana so ta miki kitson three babies kika 'ki amma da yake mun dawo gida har falli ana miki tazar kina zance ai shikenan zan Kira ummin na fad'a Mata nace duk ranar da kuka had'u kikai mata kaud'i ta zane ki" ita dai Amrat batai magana ba sai Indo datai dariya tana cewa.

"Ai babu inda zata koma balle ta daketa ranar da zaku tafi a gurina zata zauna kuje ku dawo ko Amrat"?.

Kai Amrat ta d'aga "eh Aunty Indo bazan koma gurin Aunty Ummi ba tunda ta zageni".

"Kaikaikai lalala harda zagi ah gaskiya bazaki koma mata ba ehe kinyi fushi sai tazo biko har gida sannan zaki sauko" murmushi maman Amrat tai suna gaisawa da Indo domin yau wuni guda basa gidan sai yanxu suka dawo haka suke idan mazajen su basa nan saisu had'u a d'akin mutum d'aya suyita hira abinsu kamar yan uwan juna.

👑EMIRATE👑
______Zaune Khimiyyah take a d'aki ita kad'ai tana waya da Hudayyah tana fad'a Mata wasu abubuwan da akai bata nan sannan tana tambayarta Ina ta shige tsawon lokaci anan take fada mata wani bros d'inta ne ya mata dukan mutuwa domin ta shigar masa d'akin sirri ta goge sa'kon da Prof Jibril ya turawa Danual Chai kuma aka samu akasi bayanan da sunan 'kungiyar network ya hankad'osu cikin laptop d'in Asad baro baro ya gani ita kuma lokacin karfe hud'u na asuba idonta biyu da waya a hannunta ta fahimci komai kuma taga komai a tata wayar shine Mr Famous ya kirata yace Lallai tasan yadda zatai ta shiga ta goge komai idan ta bari asirin su ya tonu sakacin tane shine ta bari ya tafi masallaci ta shiga tana gama gogewa yazo ya ritsata yai mata mummunan duka.

Tana rufe baki Hudayyah ta she'ke da dariya tana cewa "kuturun ubancan amma wallahi yayi min daidai kai har naji ya burgeni tabd'ijan irinsu nake so jarumai masu tsantsan karfi kinsan wannan gayen dalilin da yasa na barshi kenan ban bari su Daddy sun kashe shiba sabida shima jarumi ne amma yana da taurin kan tsiya har yanxu maganar da nake miki ya'ki ya amince ya kar'bi soyayya ta".

Zaro ido Khimiyyan tai "ke wai da gaske kenan yaya zakiyi idan ya'ki kar'ba dan banga alamar zai kar'ba ba tunda har aka zo yanxu"?.

Ta'be baki Hudayyah tai "sai nasa a kasheshi duk da sonsa ya riga ya shige min 'bargo da jijiya gara na kashe shi maybe idan na bud'e ido na daina ganinsa zan ha'kura dashi".

Kai Khimiyyah ta girgiza "a'a Hudayyah kar kiyi haka da ki kashe shi alhalin kina sonsa gara a d'aura muku aure dashi tilas ko yana so ko baya so Ina ganin zaifi akan abinda zuciyarki ta baki shawara ko"?.

Kai Hudayyah ta d'aga "eh kuma fa haka wallahi Khimiyyah kin iya kawo shawara shiyasa wallahi nayi ba'kin cikin rashin ki lokaci mai tsawo abubuwa da yawa sun 'bace min kila da kina nan da yanzu na aureshi amma na gagara bakiga irin azabar da nasa ake d'an'dana masa ba amma a banza yanzu yaushe zaki zo mu had'u"?.

Kai Khimiyyah ta girgiza "babu rana Hudayyah domin kinsan yanzu ba irin da bane na riga nasa likita ya nuna cewa ciwona zai ri'ka tashi lokaci zuwa lokaci kinga baza'a barni na ri'ka fita ni kad'ai ba hatta school fa saida guard nake zuwa suna ankare dani ana tashi zan shigo mota mu dawo masarauta nikam nata banji dad'i ba amma zansan yadda zanyi yanxu idan kin koma gida ki had'ani da Daddyn ki".

"Ok Ina kusa dashi ma bari na bashi sai kuyi magana" mi'ka masa Hudayyah tai kar'ba yayi da murmushin banza a fuskarsa ya kara a kunne yana cewa "hello ours ya ake ciki miye labari kwana da yawa".

Kai Khimiyyah ta d'aga "eh Daddy na dawo bayan lokaci mai tsawo amma fa yanxu an samu matsala an zuba min tsaro sosai Daddy kuma abun tsafi yanxu babu ko d'aya a hannuna haka nake hatta sar'kar wuyana wacce da ita nake da damar zuwa dajin siddabaru yanxu ta 'bata ban ganta bansan ta yadda zan ri'ka zuwa ana komai dani ba Daddy ya zanyi"?.

Dariya Prof yai yana cewa "ok kada ki damu Hudayyah zata kawo miki komai a yau amma ki tabbata ba'a gane ba kicewa mahaifanki zakiyi bakuwa su bari ki fito ki tareta da kanki Dan kada a hanata shiga a garin bincike suga wani abu yau zaki dawo duniyar shan jini idan kin fito kin tareta".

Da sauri Khimiyyah tace "to shikenan Daddy zanyi zan fito na tareta bari naje yanzu na fad'awa ummana domin nasan itace xata fahimce ni saina samu na fito na tareta" ok Prof yace yana sau'ke wayar kafin ya kalli Hudayyah dake ri'ke da photon Muheed tana kallon yace.

"Daughter ki rage yawan tunani a kansa tunda Khimiyyah ta dawo komai yazo karshe yarinya mai hikida da basira ta farfad'o yanxu aka fara wasan kada ki damu kin sameshi muje" yana rufe baki ya murza wani zoben💍 tsafi dake hannunsa suka 'bace daidai Halima ta fito taga sunyi 'bat a idonta a firgice ta fasa qara tana zubewa a gurin ta suma tsabar razani domin batai tunanin masifar da suka debowa kansu har takai haka su ri'ka 'bacewa ba.
Chapter 101 · 0% Book details