Sashe 41
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🚨 GARGA'DI DA TUNATARWA🚨
Ban yarda a juyi ko kwafin wani bangare daga cikin wannan littafin nawa ba domin hakki na ne mallaka ta da gumi na basira ta na 'kir'kira na rubuta kada mutum ya min satar koda kalma daya ce idan kuma ba haka ba mutum zaiga sakamako kada ace na yanke hukunci ba sanarwa shiyasa na fad'a sai a kiyaye idan kunne 👂👂 yaji?.....................😠😡.
🙈'YAR MUSA JIKAR ABUBAKAR MUHAMMAD TA KOWA CE👌.
Nayi kewar ku kwana biyu yan uwa fatan kuna lafiya ku fito mu warwasa zamu shiga duniyar nishad'i🤣😂😅.
Bani da haushin kowa nifa i haven't girman kai if you are fushi dani to wallahi you are just 'batawa kan k lokaci 🙃🤑.
TYPING 📲 {WEND 13/24 8:10AM}💐💐💐💐💐💐💐💐💐
💎Me kamar sarki 💎
💫Annuri writer's association 💫 home of hospitality and harmony gidan karba hannu biyu da zaman lafiya.
Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty mai tambarin YMA dutse Jigawa new world new life and new style 👌. sabuwar duniya kuzo ku kallo dad'i yana Jigawa 😜 ga garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa.
29~AL-ADAL
The utterly just
30~AL-LATIF
The Gentle
15~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mustagfirina.
🐦🕊️YUSRAHMS ABUBAKAR
🦋[email protected].
🌄 UNCARING ND TRAGEDY🌄
Episode 29_30
Juyi Salamatu tayi cikin barci taji murya ana kiranta a firgice ta bud'e idonta ganin wani 'katon ba'kin abu tai a samanta yana yawo gashi bata ga alamar d'akin da take ciki a kwance ba "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda take maimaitawa 'kara matsowa abun yake taga yayi wani juyi wurrr ya rufo kanta da sauri ta tashi a guje ya sauka akan gadon sai kuma ya 'bace jitai kanta yana juyawa lokaci guda taji hajijiya na dibanta ko ganin gabanta batai ta kama hanyar fita daga gidan babu ko d'an kwali akanta.
Daidai Rakiya matar Sabi'u ta fito da buta a hannunta ganin inuwar mutum yana tafiya yasa a tsorace taja da baya tana cewa "a'uzubillahi minal shaidanur rajim" jikinta na 'bari ta haska da fitila cikin salati ganin wacce take shirin fita yasa tace "Babah ina zakije a wannan tsohon dare kanki fa ko d'an kwali babu"?.
Ganin tayi banza da ita yasa da sauri ta koma d'aki tana taso Sabi'u a gigice ya fito bai tsaya sa takalmi ba aguje ya fita waje can ya hango tayi nisa sai tafiya take ga karnuka na mata haushi cikin azama yaje yasha gabanta yana haki yace "Babah ina zakije"? Bata bashi amsa ba kuma bata kalleshi ba ganin haka yasa ya sake cewa "meya sameki ne ko baki da lafiya"?.
Namma shiru tayi masa kanta kuma yana kallon 'kasa ta'ki d'agowa mamaki ne ya kama shi sosai har ya kasa ce mata wani abu sai hannunta daya ri'ke yana janta don ya mayarta gida amma sai yaji ta tirje kamar yaja irin kafaffiyar bishiyar nan juyowa yai yana kallon ta tare da zaro ido waje jin 'karfi a jikinta kamar doki zaiyi magana kawai yaji ta kwashe da wata iriyar dariya da sauri ya saketa yana ja da baya dariya take sosai kamar zararriya d'ifff kuma yaji tayi shiru tare da dafe kanta ta kurma ihu tana yanke jiki ta fad'i 'kasa, da gudu Sabi'u yazo yana durkusawa a gabanta girgiza ta ya soma yi amma shiru mi'kewa yai cikin jarumta ya d'agata yana sa'bata a kafad'a yai gida da ita saida ya kaita har daki ya kwantar kafin ya fito yana mamakin ina Rakiya tayi ne nasu d'akin ya shiga can ya hangota saman gado ta lullu'ba sai kakkarwa take karasawa yai yana janye bargon yace.
"Rakiya meya sameki, baki da lafiya ne"?.
Jin muryar sa yasa ta bud'e ido tana cewa "a'a ina lafiya ihu naji da dariya daidai nasa hijab na fita zanbi bayanka shine tsoro ya kama ni na dawo gida ina Baban take ka ganta"?.
"Eh tana d'aki jira nake gari ya waye muje asibiti ni abun ne da tsoro kamar ciwon hauka ne ya kamata saboda ganin abunda takeyi itace fa me wannan ihun da dariyar kamar zata fasa gari" zaro ido Rakiya tai "itace kuma innalillahi wayyo Allah na meya samu Babah ne ban ta'ba ganin irin haka ba".
Zama yai yana sauke ajiyar zuciya yace "ni kaina Rakiya ban ta'ba gani ba sai yau Allah yasa dai ba aljanu ta had'u dasu ba" Amin Rakiya tace tana tashi zaune daga tashi tai tana le'ko kofar d'akin da Salamatu take ciki tana cewa "nifa ina jin tsoron karta 'kara fitowa bamu sani ba tayi waje ka taso muje gurin ta gara mu tsaya zuwa wayewar gari a gurin ta" mi'kewa yai yana cewa "shikenan muje" fita sukai suna shiga d'akinta a 'kan'kame suka sameta ta 'ka'k'kafe idanuwanta sun juye babu ko d'igon ba'ki sai fari tana wata irin jijjiga abin tsoro.
Rakiya dake kan gaba da sauri ta koma baya tana salati jikinta na rawa ganin abinda yafi 'karfin ta kuka ta kama cikin tashin hankali tana cewa "ta ya zamu bari sai gobe baban hajiya gaskiya musan yadda zamuyi a daren nan kalli fa abinda takeyi sai nad'ewa guri d'aya take kamar taya dan Allah kayi wani abu".
"To mezanyi wanda ya wuce addu'a ina zamuje dare ya riga ya raba mu ba asibiti ne damu a gari ba saidai muyi hakuri mu jira wayewar gari".
Goge hawaye Rakiya tai tana cewa "shikenan Allah ya kaimu Allah ya bata lafiya" amin yace tare da fara karanta mata addu'a haka suka kwana cur basuyi barci ba saida akai sallar asuba sannan ya samu wani d'an ma'koftansu mai mashin ya nemi alfarmar yakai su asibiti amma dayaje gida ba damar da zata iya hawa mashin dan tana nan a san'kare guri d'aya hatta yatsarta baya tan'kwasuwa balle ga'bo'bin jikinta rasa mafita Sabi'u yai dole karshe sai mashin d'in ya kar'bi aro yana fita wajen garinsu ya samo motar haya da'kyar suka fito da ita kamar itace haka suka sata a mota suka nufi asibiti.
Habu bai sani ba sakamakon baya gari ya tafi cikin Kano sarin kaya sai bayan ya dawo yaji labari ko hutawa baiyi ba ya tafi asibitin a zaune ya samu Sabi'u da Rakiya sunyi shiru cikin damuwa yace.
"Yaya Sabi'u dama Babah bata da lafiya? Wallahi ban sani ba dawowa ta kenan yanzu Binta take fad'a min ya jikin nata fatan da sauki"?.
Numfashi Sabi'u ya sauke tare da girgiza kai yace "Habubakar ban sani ba abun da tsoro tun safe muka zo amma har yanzu babu likitan daya fito balle muji wani labari da zaisa muji d'an dama dama".
"To meya sameta ne"?.
"Humm habu Habubakar to me zance na kasa ganewa 'kwa'kwalwata bazata dauka ba irin abubuwan da take da dare ya bani tsoro baka gani ba yadda take sandarewa kamar busashshen ice harda ihu".
Zaro ido Habu yai "innalillahi meya faru haka ko aljanu ne"?.
"Ban sani ba Habubakar Allah yasa dai ba wani mummunan abu ne ya sameta ba" Amin Habu yace yana samun guri ya zauna suna jiran tsamani kafin likitan daya kar'bi Salamatun ya fito.
GIDAN BALARABE
Dalah na zaune a kofar d'aki tana tajewa Indo gashi taji an rafka sallama tana d'aga kai taga mace ta shigo mamaki ne ya kama ta ganin Asabe a ranta tace ita kuma wannan lafiya ba dangin iya ba na baba katse mata tunani tai da cewa.
"Ke haka ake kar'bar ba'kuwa kin barni a tsaye kamar bishiya"?.
Da sabon mamaki Dalah ta kuma kallonta tana cewa "sannu da zuwa 'karaso bismilllah ga kujera ki zauna".
Zama Asabe tai tana 'karewa gidan kallo kamar wacce tazo duban tsafta zuwa wani lokaci tace humm tare da ta'be baki tana yiwa Dalah kallon uku saura sisi takaici ne ya gama cika Dalah ganin mace tazo mata har gida zata raina mata wayo tace.
"Wai meya faru ne kinzo bakice komai ba lafiya"?.
Gyara daurin kwalin kanta Asabe tai tana soke shi a gaban goshi tareda dauko cingum daga cikin Jakarta tasa a baki tana taunawa sannan ta soma magana "humm Hajiya Dalansi dama nasan zaki mamakin zuwa na saidai da baki wahalar da kanki ba domin ba wani abu ya kawo niba kawai nazo ne mu gaisa naji ya d'iya ta take".
Baki bud'e Dalah take duban Asabe jin abinda take cewa tace "kinzo ne mu gaisa kiji yadda lafiyar d'iyarki take"?.
Gira Asabe ta d'age "eh haka nace ranar baki ga tazo miki da 'kosai ba? Ai nice na bata har nake cewa idan tazo tace ina gaida ke ko bata fad'a miki ba"?.
"Eh bata fad'a min ba mun gode".
Karya kai Asabe tai cikin yanga zatai magana taji gyaran muryar Balarabe alamar ya shigo gidan cikin tane taji yana hautsinawa na shakku da tsoro tuna abinda 'kawarta Meroh tace mata akan Balaraben mi'kewa tai tana susa kamar me ciwon 'kazuwa tana rarraba ido tare da satar kallon Balarabe da yake tsaye ganin ta a gidansa muryarta na d'an rawa tace.
"Barka da gida ina yini"?.
Wani kallo ya mata yana d'auke kai bai amsa ba sai tambaya daya jefo mata "meya kawo ki gidana me kikazo yi shin kinyi ajiya ne"?.
Kallonsa Asabe keyi ganin yadda yai mugun had'e rai yasa jiki a sanyaye tace "kayi hakuri dan Allah yanzu zan tafi dama nazo ne mu gaisa".
Da yake mutum ne mai fad'a a hasale yai kanta yana cewa "da uban wa zaku gaisa dama kina zuwa min gida ne? Karki sake na sake ganin ki a gidannan idan ba haka ba zaki bayani saikin yabawa aya za'kin ta fita min a gida nacee" ya karasa maganar cikin tsawa yana nuna mata hanyar 'kofar fita jiki na 'bari Asabe tai waje kamar zata kifa tsabar sauri tana haki.
Juyawa yai cikin fad'a yana kallon Dalah yace "kece kika bud'e mata kofa kika bata lasisin shigowa gidana ko kuwa duniyanci ne ya kawo ta fad'a min naji"? Cikin shakku Dalah tace "kayi hakuri wallahi bansan komai ba kawai ganinta nai ta shigo wai tazo mu gaisa taga d'iyarta".