← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 145

Sashe 23

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin masifa Ramatu tace "bazan jeba dan malafar ubansa wallahi babu inda zanje hauka ma kenan yadda ya dauka min 'ya har gida haka zai dawo min da ita mara mutunci maye kawai ana gudun ka kai kana li'kewa aikin banza nasan malam da hadin bakin ya tafi da ita to sanka 'kanin 'kafarka kaje koma ina ne ka kar'bo min 'yata ehe wannan muguntar har ina"?.

'Daki Baffah ya shiga yana cewa "nidai na fad'a miki kada ki kuskura na sake jin wani batu" kuka Ramatu ta kama bayan wucewar Baffah d'aki "wai a dake ka a hanaka kuka nida 'yata a cuce ni amin mulkin mallaka na rantse da Allah sainaje har wudil din na dauko ta" ta karasa maganar tana face hanci da hucinta ta shige d'aki.

Sun isa wudil lafiya yayin da Musbahu ya kaita gidansa tare da dan'ka amanarta a hannun matarsa Halima tana yara guda biyu Naja'atu da Yusuf sunyi mamakin ganin Lami lokacin da suka dawo daga makaranta cikin alamun tambaya Yusuf yace "maman mu wannan daga ina tazo"? "Oh Yusuf kwai tambaya daga shigowa ko hutawa bakai ba"? "To ai maman mu naga ban santa ba ban ta'ba ganin taba"? "Eh haka ne Abban kune yazo da ita 'yar uwarku ce a makaranta zai sata zatai karatu saura naji wani yaro ance ya nuna mata wani bambanci kunsan Allah ko saina ma d'a shegen duka kuna jina"? Hada baki sukai "eh mama" "yauwa ku wuce maza ku shirya saiku dawo muci abinci" to suka ce suna wucewa.

Mrs Al'ameen Ahmad ce 😘 😘.

ZAMU KWANA ANAN SAI ALLAH YA KAIMU GOBE DA RAI ZAMU D'ORA.

Ina godiya 💖💕👏🤝 sosai reader's da addu'ar ku gare ni Allah ya barmu tare amin.

Wannan page din naka ne dan uwa rabain jiki CPT. SALISU KOLI ABDULLAHI mai tambarin no going back⚔️🗡️👊💣🔫💥🦁.

#VOTE
#SHARE
#COMMENTS
#FALLOW.

[email protected] MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY 💃👌👍.

*Writer*
1👉Yarima Abdul-maleek
2👉 Rayuwa biyu
3👉 Safreeyyah
4👉 d'an millionaire
5👉 Royalty
6👉 Husnah ko Badiyat
7👉Haskena sauban
8👉 Minah-Umer
9👉 Kowacce'kwarya
10👉 Zuciyar Aliyu
11👉 Dama kece
12👉 Me kamar sarki
Loading A GIDAN TALAKA

Ga wanda yake bukata wadannan litattafan kofa a bud'e take kai tsaye ayi min magana tanan👇.
08160983083
Chat with me 💻📱🖥️.

19~ AL-ALIM
The all knowing
20~AL-QABID
The Restrainer.

10~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Raki'inah.

🌄TENSITY ND QUARREL🌄
Episode 19&20
Kwana uku da tafiyar Lami misalin 'karfe sha biyu rana akaji jiniyar motar yan sanda 🚔 ta danno kai garin batai fakin a ko'ina ba sai a kofar gidan Baffah Mamman na gaban motar yace "yalla'bai ga gidan nan" akwai mace yar sanda a cikin su saboda an fad'a musu mace ce za'a kama dan haka itace ta shiga gidan wanda Ramatu najin jiniya ta 'barka danga ko takalmi babu balle hijab ta fita da gudu sallama yar sandar tayi Salamatu dake shara ta amsa mata "akwai Ramatu a gidan nan"? Kai Salamatu ta d'aga "eh akwai amma ta 'barka danga ta fita tanan yanzu" "ok shikenan" ta fad'a tana fita da sauri tace "sir tada mota matar bata gidan wai ta fita da gudu ta bayan gida" tab 360 suka koma cikin motar da mugun gudu suka bi bayanta da yake damuna ce tuni ta 'bace musu sauka sukai a motar suna barbazuwa ko'ina dan binciko ta da wani yaro suka had'u yace "wata mata kuke nema? Gata can tabi wannan 'karamar hanyar tana gudu babu kwali a kanta" basu tsaya jin karashen zancen yaron ba suka bi hanyar tuni sukai mata kofar rago suka ritsata a tsakiya turus tai ta tsaya tana huci yar sanda da aka zo da ita ce ta karasa tare da danko ta dayar tasa mata ankwa kokawa suka fara sai harbe harbe Ramatu take da 'kafa tana burgima da fisge fisge "ku sake ni azzalumai mugayen banza" make mata baki 'yar sandan tai wanda yasa Ramatu sakin kara tana cewa "wayyo Allah na zaluncin yan sanda Allah ya isa ban yafe ba tsinanniya kin make uwark............ Sake make mata baki tai saiga jini cikin tsawa tace "rufe mana wannan ru'babben bakin zaki bayani yau saikin gane Allah da girma yake wallahi bari mu karasa bayan kantar zaki yabawa aya za'kin ta" har lokacin bakin Ramatu bai mutu ba ta harari yar sandan tana cewa "babu abinda kika isa kimin harda bari muje bayan kanta idan kin cika yar halak idan an kulle ni ki dau dan mubud'in kije ki jefa shi a kogi mai ambaliya kaina fito har abada" "shikenan zaki gani zuwa jimawa saikin manta inda kike wahala sai tasa kinje suma kin dawo" yar sandan na fadin haka ta jawota zuwa inda motar su take guri ya cika dam sai nuna ta ake ana gulmar Mamman ne ya d'ebo mata 'yan sanda wulla ta sukai a mota suka tafi sai ihu da tsine tsine take wani d'an sanda yana shirin bugarta da kulke ogonsu ya hana shi cewa ya bari idan sunje can wuya zatasa tai shiru.

Duk abinda ake Ilyah na ji yai banza a cewarsa itace ta jawo rigima ba inda zaije belinta kud'in sa ko biyar bazai ciwon kaiba saidai a sayar da tumakinta a belota amma indai dan ta shine tai ta zaune a bayan kanta😲😦.

Aiko suna zuwa suka hau jibgarta ihu kamar zata fasa ofishin cikin tsawa suka ce "rufa mana baki tunda ke kin zama annoba zamuyi maganinki a garin nan ba me gari shugaban ku ba amma kin raina shi bakya ganin girmansa bari yazo zaki bayani ba ke tantiriya ba"? Ramatu na haki ga gumi jikin ta ya ji'ke tace "a'a wallahi yalla'bai ban raina mai gari ba dan Allah kuyi hakuri na tuba" cigaba suka da tambararta zuwan ogansu yasa suka dakata kallon ta yayi yana Jinjina kai kafin yace "ku 'kyale ta haka ku fito nayi magana da me garin yace gobe zasu zo da mutanen da suke 'kararta" fita sukai suna rufeta Ramatu dake kwance da'kyar ta tashi zaune tana cewa "Allah ya isa na mugaye ban yafe muku ba wallahi kuma halina na nan babu abinda za'a fasa rashin mutunci bakuga komai ba yanzu na fara" ta fad'a tare da gyara zama tana kalle kallen gurin babu komai sai 'kura da datti haushi ne ya kamata ta sake 'kudura a ranta bazata yarda ba saita rama duk shegen dayai silar zuwanta nan.

Washe gari mai gari da sauran wadanda sukai 'karar Ramatu sukaje ofishin fito da Ramatu akai duk ta jigata harda kumbura a fuskarta na dukan da sukai mata jiya kallon su take daya bayan daya kafin ta zauna tana cewa "munafikai matsiyatan banza me kuma ya kawo ku ai na dauka zakusa su kashe ni ne ashe iya duka ne" kallon ta da mamaki mai gari yayi yana cewa "amma wallahi ke dai Ramatu kin shiga uku ke wacce irin mace ce wato kawo kin ma da akai baki risina ba"? Wani irin kallo Ramatu ta wurga masa "au dama kun kawo ni a koya min ladabi to Babu abinda zai sauya ko yanzu na koma gida wani bankad'adden ya ta'bo ni sai naci 'kashin uban sa" kai me gari ya jinjina "bari ofisan yazo tunda kin zama shed'aniya" "eh fad'i ka 'kara idan kace shed'aniya ai ka 'bata daya kenan saidai kace shed'aniyas kaga da yawa kenan" "zan sanar masa duk abinda kike aikata mana a gari" "ka dade baka fada masa ba ofisan banza ofisan wofi yazo man tsoron sa nakeji nafi karfin wulakanci ni roba ce ina daidai da 'kugun kowanne shege....................

Jin tafiyar ofisa yasa sukai shiru zama yai ransa a had'e yace "ina jinka malam Rabi'u meya faru tsakaninka da wannan matar"?.

Gyara zama mai gari yayi yana cewa "ofisa kaga wannan matar da kake gani a rayuwar ta bata son zaman lafiya ta hana kowa yaji dad'in zaman garin ta addabe mu ranar kawai daga kawo min ita shari'a saida tai min zagin 'kare dangi sannan ta tozarta yan majalisa ta su Isubu tayi musu zagi na tsamar nama" mi'kewa Ramatu tai "to yau nake ganin sabon salon sharri me gari ni zakaiwa sharri amma Allah ya isa tsakani na dakai" tsawa officer ya daka mata yana cewa ta koma ta zauna zama tai jiki na 'bari.

Kallon sauran officer yai yana cewa "ku kuma meye tsakanin ku da ita"? Mamman ne ya soma magana "ranka ya dad'e ni kuma haka kawai wannan matar taje har gidana ta rufe yarana da duka babu dalili ta zagi mata ta" kallon d'ayan ofisa 'kai kuma meya faru"? "Ranka ya dad'e ni ma zuwa tayi har gida ta daki Balki yata ta 'kare min zagi tas" "ni kuma kud'i nake binta dubu goma sha biyar ta hana ni kusan wata shida" "nima yalla'bai kud'i nake binta ta hana ni" kowa da abinda yake cewa duk guri ya kaure d'aga musu hannu ofisa yayi yana cewa "ke kinji abinda suka ce haka ne"?.

Kai Ramatu ta girgiza "a'a ba haka bane ni babu wanda yake bina kud'i nuna mamamn tai "sannan shi wannan munafikin ba a banza na d'aki yarsa ba kullum 'ya'yansa sai sun tare 'yata Lami sunce mata jahila kuma saini dan na dake su aga zafi na saboda 'yata bata da gata su kuma 'ya'yan gwal ko"?.

"Kinga da Allah saurara bana son shashanci dama halin kine ba sau daya aka kawo ki ofishin nan ba kin zama kamar kwastoma dan haka duk abinda sukace zaki iya aikatawa dan haka bazaki koma garinku ba saikin biya kud'in da ake binki da kud'in belin da tarar dukan da kikaiwa 'ya'yan wannan mutumin".

Zaro ido Ramatu tai tana cewa "kan dambun uban nan wallahi ba wanda zan biya ko sisi ofisa baka da adalci ko kadan" mi'kewa ofisa yai yana cewa "zaku iya tafiya na gama magana idan an samu mai zuwa belinta saiku dawo" suma mi'kewa sukai yayin da aka tisa 'keyar Ramatu aka mayar da ita bayan kanta su me gari suka koma gida suna mamakin wato babu inda bakin Ramatu zai mutu ba.
Chapter 23 · 0% Book details