← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 145

Sashe 71

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akwai wani mutum munafiki sunansa Haliru a cikin ma'aikatan gurin yana da zagon kasa sosai yake jin haushin su malam Habu duba da cewa sunzo sama takai Allah ya bashi farin jini sun d'aukaka agun mafi yawan ma'aikata sun sansu kuma suna yi dasu hakan yana 'kona ran Haliru a 'bangare guda ga yaron alhaji Idris (komai da ruwanka) zama masinjoji dasu malam Habu ba karamin firgitashi yaiba saboda yanzu duk wani kud'i da Alhaji Idrisu zai bayar a rabawa mutane harda su a ciki suna tsaye zai rabawa mutane sisi bai isa ya tafi dashi ba sun kafa sun tsare ba'kin ciki ya gama isarsa ya tsanesu ji take kamar ya kashesu da ransu shiyasa Sam basa shiri ko hannu suka bashi da sunan gaisuwa baya kar'ba sai harara sai zagi haka kud'i yana gama rabawa zai wulla musu jakar yana hucin takaici yabar gurin har dariya yake basu saidai sunyi alkawarin har subar Cameroon kamar yadda suka cewa alhaji Idrisun bazasu ci amanarsa ba zasu ri'ke komai tsakani da Allah Malam komai da ruwanka yaso su had'a baki su ri'ka cutar alhaji Idrisu zasu koma Nigeria da ma'kudan kud'i su kuma suka a'a shikenan ya d'aura gaba dasu kome ya had'o su sai zage da hantara.

😘MRS AL-AMEEN AHMAD CE😘

KAI WASH ALLAH NA TYPING 📲 AKWAI WUYA😣 KUYI HAKURI FANS YAU BA YAWA NA GAJI NE ANAN ZAMU TSAYA MU KWANA SAI MAI DUKKA YA BAMU ARON RAI ZUWA GOBE INSHA ALLAHU ZAMU D'ORA LITTAFIN ME KAMAR SARKI 👑 INDA MUKA TSAYA👌.

See you next time we will meet again tanks for ur support Allah ya d'aukaka ku fans d'ina ina yinku babu adadi😘🌹.

💋YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋

BARKAN MU DA KWANA MASOYA YAN GROUP DIN ANNURI WRITER'S ASS💫 DA SAFREEYYAH FANS GROUP🍇👌 DA MR HAUSA EBOOKS AND VIP WOMEN 24TV NOVELS INA MIKO GAISUWA MAI TARIN YAWA GAREKU FATAN RAHMAR ALLAH TA TABBATA A GAREKU.

TYPING 📲 Fri, Jul, 19/24 03:43PM (+_+)(+_+) Little Zaran Aunty💃.

💞ME KAMAR SARKI💞

____________________
____________________________
___________________________________

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫
🏠Home of 🤗hospitality and 🌲harmony🤙gidan kar'ba hannu biyu da zaman lafiya🙅.

STORY AND WRITTEN
✍️Yusrah Musa Abubakar
MRS ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD CÊ😘

Wannan page naku ne 'yarana ta kaina Allah ya rayaku kan tafarki madaukaki akan hanya ta shiriya da turba ta musulunci Amin.
💞FATIMA ZARAH (ILHAM)
💞HABEEBAT (IKRAM).

51-~AL-HAQQU
The Truth
52~AL-WAKILU
The trustee

25~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil 'Dayyibina.

🌄INSIST ND JEER🌄
Episode 51&52
Kamar yadda Asabe ta umarci Balarabe cewa yayiwa liman magana idan akwai wanda zai auri Indo sadaka haka yayi da asuba bayan anyi sallah a masallaci liman yace kada kowa ya fita akwai sanarwa saida yayi addu'a aka shafa sannan ya juyo yana fuskantar mutane da Sallama a bakinsa bayansun amsa ya fara bayani kamar haka.

"Assamu alaikum jama'a kunji nace ku dakata ko? To ba wani abu bane dama sa'ko ne zan fad'a na sauke nauyi daga Malam Balarabe yace a sanar muku cewa 'yarsa Indo ta kawo mizanin aure hartana neman wuce iyaka amma babu wanda ya ta'ba zuwa kofar gidansa da sunan yana sonta shiyasa ya gaji ya kawo tallar sadakarta masallaci idan Allah yasa akwai wanda baida karfin yin aure ga mace sadaka bayan mun fita zaka iya zuwa gidan malam Ka sameshi saiku tattauna Allah yasa mu dace assalamu alaikum" ya karasa maganar yana mi'kewa ya fita sannan sauran mutane suma suka tashi suna rufa masa baya kowa mamaki ya rufeshi na wannan irin tagayyara da Balarabe yazo yaiwa 'yarsa yana yayata asirin gidansa ai saiya jawowa 'yar gori daga baya ko yasa ta zama 'karamar bazawara.

Malam Balarabe yana shiga gida Indo tana shara buguzun buguzun kamar zaibi ta kanta haka ya wuce fuuuu yana shiga d'akinsa da kallo Indo ta bishi hawaye shakaf a fuskarta ta gaza gane mene ainishin abinda dake damun Balarabe yau kusan wata uku da sakin Dalah ya hana taje ko sau d'aya ta ganota ga takura da tsinuwa iri iri da take kar'ba a gurin su shida Asabe ga bahijjah da take jin kanta tafi kowa gwalli da takura mata saita 'karawa Balarabe zagi 'kuyal yana ji tari bazai iya ba huuuuuhsh kawai ta sauke numfashi tana aje tsintsiyar zata shiga d'aki taji tsawar Asabe.

"Kee kee da'ki'kiya gidan uban wa zakije baki gama min aiki ba matsiyaciya mai ba'kin hali wato dama tun d'azu ashe shara kike da nace kiyi sauri ki hura min wuta shine kikai kunnen uwar shegu dani aiko yau sai naci uwar data haifi uwarki bankad'add'iya kawai".

Had'e rai Indo tai cikin takaici ta kalli Asabe duk da zuciyarta na bugawa ta dake domin abubuwan da take mata ya gama isarta gara ta fara mayar mata kota 'kwaci 'yancinta a gidan ubanta tasan itama 'yace ba tsintota akai ba tasan ko 'yar tsintuwa baza'ai mata irin wannan wulakancin da cin fuskar da ake mata ba......................

"Ke Indo dan uwar uwarki ba dake nake magana ba shine kika tsaya kallona saboda ga sa'ar gyatumarki ko nayi miki kama da mummunar tsohuwarki Dalah kome kike kallo idan kuma ke mayya ce nafi 'karfin ki".

Ba zato Asabe taji saukar muryar Indo tace "kada ki sake zagar min uwa".

Da sauri Asabe ta dubeta da tsananin mamaki ta zaro ido waje tana cewa "maimaita abinda kikace Indo ta yuwu ko kunne na ya fara samun matsala mema kika ce"?.

A fusace Indo tace "cewa nai kada ki sake zagar min uwa".

Baki Asabe ta bud'e tana kallon ta sama da 'kasa tace "karna sake zagar miki uwa?.

"Eh haka nace".

"Ohhh lallai yau kuwa saina nuna miki cewa kinyi kuskure kuma har kibar gidan nan wallahi bazan sake sassauta miki ba wahala da damuwa yanzu kika fara sha".

Kai Indo ta girgiza tana cewa "kece a wahale bani ba domin ni bana dauke da alhakin kowa a kaina amma kefa kin cuci mahaifana kin lalata musu zama kin zama ba'kar ashana ba'kar mace mai ba'kin hali Allah wadaren mata irinki Asabe kuma insha Allahu zakiga 'karshen ki ina mai tabbatar miki bazai kyau ba dole ki girbi abinda kika shuka zaki dana sani a lokacin da baida amfani"...............

"YA ISHEKI INDO" Asabe ta fad'a cikin tsawa tana kai mata sha'ka taci gaba "bari kiji ko uwarki Dalah bata isa fad'i in fad'a dani ba balle ke 'karamar alhaki yaushe har kikai bakin da zaki iya kallona kina magana? Heyyyyy yau ake yinta kan bala'i tabd'ijan BALARABE kai BALARABE kana ina? fito yau saina ci burar uban wannan tsinanniyar 'yar taka daga kai har ita sai kun yabawa aya za'kin ta" jin shiru yasa tace "kana ina ne munafiki gidan ubanwa ka shige ina magana kai burus wato ga wacce aka kunto daga turu ko"?.

Fitowa Balarabe yai da sauri yana cewa "lafiya meya faru"?.

Wata uwar harara Asabe ta sakar mata "oh abinda ya faru kake tambaya sabida ka zama tsohon kwantukwan ko? Nuna Indo tai da yatsa tana cewa "to wallahi wannan yarinyar yau saina kusan kasheta a gidan nan da hankali na ya kwanta".

A rikice Balarabe yace "metai miki"?.

"Au bakasan metai min ba kana cikin d'aki kanajin yadda take aiko min zagi tana tsiyatani sannan kace bakaji komai ba" ?.

Zaro ido Balarabe yai jiki na rawa yace "Indo d'ince ta zage ki"?.

A fusace Asabe tace "a'a ba ita bace ai kasan na saba 'karya shiyasa har zaka tsaya ja'inja dani wannan 'yar ba lallai jininka bace da jininka ce bazan ta'ba fad'a mata magana ta mayar min ba ka dau mataki yanzu ko nasa bahijjah ta kira 'kawayen ta su nad'a mata na jaki su mata kisan kawo wu'ka".

Tsaye Balarabe yai kamar bishiya yana kallon ta a tsawace Asabe tace "wai ubanme kake kallo ko yau ka ta'ba ganina d'an gidadawa nace ka mata shegen duka sannan hankalina ya kwanta kuma bada bulala ba kaga wancan iccen? Ta fad'a tana nuna masa wani sanda "to dashi zakai mata d'an ala tsinan duka wanda zaisa ta kama zazza'bin wuya.............,................

Katse mata magana wani yaro yai da cewa "salama alekum wai malam Balarabe yazo a kofar gida".

Kafin Balarabe yai magana da sauri Asabe cikin zumud'i tace "kai inji waye"?.

Juyawa yaron yai yana cewa "inji Iluh d'an garuwa wanda yake kwana a shagon gidan mu".

Wata irin gud'a Asabe ta saki tana cewa "ahayye nanaye ayuririiiiii nesa tazo kusa kwanan nan zan rabu da 'kaya na yada mangoro na huta da 'kuda masifa ta kusa barmin gida malam kayi sauri kaje man karya fusata ya tafi nasan kila sadakar dakai magana zaka bada wannan asararriyar ne yasashi zuwa idan ba haka ba muda ba ruwa muke saya ba mezai kawoshi"?.

Shiru Malam Balarabe yai kawai ya tsaya tsam yana tunani ba zato yaji Asabe ta hankad'a shi kamar baro ta tura shi hanyar kofar gida tana cewa "uban me ka tsaya kallo ne kaje saiya tafi aikin banxa d'an sakalai kawai" Balarabe baice mata 'kala ba ya fita a gidan kan Indo ta mayar da hankalinta wacce take wanke kwanuka kamar bataji abinda suke cewa ba dariya tai tana jan 'kwafa tace "hummm d'auke kai dakyau lokaci yayi ubanki zaki ci wallahi dan bazan 'kyale kiba har a gidan auren ki bazan bari kiji dad'i ba ai Indo tunda kika shigo hannu na kin shiga uku" banza Indo tai mata bata sake magana ba ta baiwa iska ajiyarta wucewa Asabe tai tana zage-zage ta shiga d'aki murmushi Indo tai tana cewa "humm akwai ranar nadama zata zo a lokacin da bazan saurari d'aya daga cikinku ba keda baba bazan iya yafe cutar dani da kike ba kisa ya dakeni ya zageni ya munana min kamar ba shine ya haife niba hummm babu komai wata rana sai labari Allah yasa 'karshen wahala tane yazo nima nayi matukar damuwa dason barin gidan nan kodan na samu canji nayi rayuwa mai kyau da 'yanci kamar kowanne d'an Adam yake yi.

Shigowar Balarabe yasa ta d'ago tana kallon sa shima itan ya zubawa ido nadan lokaci kafin yace.

"Ina fata kinsan Iluh ba'kon d'an bulani mai turin baro na gidan malam Garbah mai sa'a"?.

Kai Indo ta d'aga jiki a sanyaye tace "eh na sanshi"?.
Chapter 71 · 0% Book details