← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 145

Sashe 72

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sauke ajiyar zuciya Balarabe yai yana cewa "to shine yazo nan yasa akai sallama dani akan yazo nemar auren ki kamar yadda na bada sanarwa a masallaci duk mai son sadaka tun ba'aje ko'ina ba gashi kin samu miji da kina ja'be a cikin gida baki da motsi daga d'aki sai band'aki kin daiji abinda nace ko Iluh ba'kon d'an garuwa na gidan malam Garbah mai sa'a yazo tambayar aurenki kuma na bashi dan haka zai koma gida yaje ya turo iyayensa ayi magana d'an wajen Wudil ne kuma saura tsautsayi yasa ki bari Dalah da 'yan uwanta suji wannan labarin saina kusa kasheki".

Fitowa Asabe tai ta riski karshen zancen da suke caraf ta cafe da fad'in "yo malam tsoron me kake ta fad'a man Dalan banza ta isa hanaka abinda kai niyya 'yarka ce Indo ka fita mu'kami da ganin dama dole sai yadda kace ko abinda ka yanke shine suke kai".

Kai Balarabe ya jinjina "to aini kinsan wanda nake tsoro malam Sa'idu yayan Dalan kinsan tsinannen mutum ne akwai masifa yanzu yana jin wannan labarin sai kinga tsiyar da zamu kwasa dashi".

Ta'be baki Asabe tana cewa "shid'in banza ya isa jada ni? Kaga kabar min komai ahannu na ni kuma nayi maka alkawarin sai Indo ta auri wannan d'an garuwar nan da 'yan kwanaki".

Kai Balarabe ya d'aga "to shikenan na baki wu'ka da nama dama kai da kaya mallakar wuya ne sai yadda kikace".

Murmushin mugunta Asabe tai tana cewa "Yayi ina so zan fita in anjima idan na dawo zamu karasa maganar".

Da alamar tambaya Balarabe yace "zuwa ina"?.

"Zuwa oho tunda so kake sai nace ga inda zanje wai Balarabe zargine ya fara shiga tsakanin mu ko kuwa me?".

"A'a kiyi hakuri niba zarginki nake b...................

"Kai dallacan gafara kaban guri zan fita duk inda nake so a lokacin da naga dama kuma kai baka isa ka hana ba dan Naga yanxu wani sabon raini kake ji dashi🙊 fad'a min uban waye yake hure ma kunne a waje cewa idan ka dawo gida ka wulakanta ni? Kazo tsayar da idonka cikin nawa saboda ga sa'arka tana magana ko"?.

Jikin Balarabe na rawar tsoro yace "kiyi hakuri ni ban d'auka da wata munufa ba" fad'in haka ya juya yana fita a gidan da harara Asabe ta rakashi tana jan tsaki sannan ta juyo da kallonta kan Indo tana cewa "ke kuma mujiya mai ba'kin hali kinji abinda ran'kwal'kwalin😔 uban naki yace sai kad'au shiri ki nemi kayan d'aki dan ko cokali bazai saya miki ba wallahi saina hana saidai daga gidansu Dalah akai miki ko tabarmace" tana kaiwa nan ta shige cikin d'aki" sunkuyar dakai Indo tai tana goge hawayen da yake zubo mata cikin razani da rashin samun madafa saidai da wannan rayuwar 'kuncin ta gwammaci zama da Iluh d'an garuwa ko hakan zai zama sanadin ba'kin cikinta ta za'bi zama cikin bare akan zaman gidansu.

GIDAN MALAM HABU
A'i tana zaune gaban murhu tana dama kunnu ita kad'ai sai magana take "oh ni Aishatu naga ta kaina wannan masifa har ina? Ace yau kimanin kwanakin malam ashirin da biyar da tafiya ace babu ko waiwaye ba d'an aike na tabbata duk tsiya za'a samu wanda zaiyo nan haka nifa shiyasa ban yarda nadau kud'ina na bashi ba da yanzu ya dira ni dan nasan muzai bari a wahala wa yasani ma ko guduwa yai ya barmu ba yanzu zai dawo ba koma har abada bazai dawo garin ba ba'kin ciki ne ya koreshi".

'Dan kallonta Binta tai ganin duk sauran yaran sun zubowa A'in ido suna kallonta tasan ciwon maganar sukaji har Jamilan dan sun tabbata ubansu mutum ne na 'kwarai bazai ta'ba guduwa ya barsu ba ya damu dasu fiye da tunanin mai tunani kafin Binta tayi magana Saude tace.

"Aike A'i yanxu na daina saki a sahun nasu hankali dan da kinsan abinda kike fad'a kodan kunyar 'ya'yansa kya raga masa wani abu malam mijinki ne ba abokin wasanki ba amma duk kalar shashashar maganar da tazo bakinki babu taunawa babu tunani babu ruwanki da 'ya'yansa suna gun tsabar rashin hankali saiki furta a tunaninki kina wa kanki adalci ko kina neman kima da martaba a idonsu? Gaskiya magana ta domin Allah ki canza halinki A'i malam ya mana komai a rayuwa kuma mukam bamu zama butulu masu manta kyautar jiya gareshi ba addu'ar mu a kullum Allah ya rufa masa asiri ya d'auke nauyinmu kamar yadda yake fata sannan matukar baki canza ba ina mai tabbatar miki a gaba zaki nadama".

Wani karkataccen kallo A'i taiwa Saude tana ta'be baki tace "wallahi 'karya kike babu ranar da zata fito wacce zanyi nadama a cikin ta bafa wata uwar nake d'auka ba a gidan nan ba sai wahalar rayuwa jira ma nake Allah ya dawo da malam d'in yasan yadda zaiyi Dani dan na gaji da zaman kitiko-koko kukan jakin matsiyaci kullum baci gaba sai tauyewa nake niba leda ba zai dawo ai nikam bazanci gaba da zama dashi ba sallamata zaiyi gara na koma rayuwa gidanmu tunda ga 'kanina Rabi'u yayi aure kuma Saminu ma zaiyi ko a jikinsu na laru nasan kwanuka biyu dai zan 'koshi kuma ace safe da rana da dare Allah ya dawo dashi daga tafiyar idan kuwa nan da 'karshen watan nan naji shiru zan had'a 'yan kayayyaki na nabar gidan tunda zaman ba dole bane ku da ya zame muku farilla sai kuci gaba da zaman jegon jaka".

Kai Saude ta girgiza tana kallon A'i tace "ai shikenan Allah ya rufa mana asiri mukam muda malam mutu ka raba kome ya zama baza mu gujeshi ba" .

"Hum kada Allah yasa ku gujeshi man waiku 'ya'yan masoya ko? Uhm kuje ku 'karata nikam kad'an nake jira bazan iya ba" A'i na rufe baki Dijeh ta shigo gidan da sallama kamar an jefota tazo taiwa A'i tsaye aka tana mi'ko mata hannu tace"

"A'i bani kud'ina zan tafi kasuwa"?.

Kallonta A'i tai tasan yau bata zo da mutunci ba tunda bata bari an gaisaba ta tambayi kud'i katse mata tunani tai "A'i nace ki bani kud'i na"?.

Mi'kewa A'i tai tana shiga d'aki ta dauko ba magana ta bata 'kirgawa Dijeh tai ganin bai cika ba tace "ya haka ina sauran"? 'Dan tsaki A'i taja cikin takaici tace "bani dashi iya abinda ke gareni kenan d'aka da waje na d'auko miki bani da ciko nima yana gurin mutane" ri'ke kugu Dijeh tana cewa "Ina ruwana da wasu mutane dama nace ki basu bashine a hannunki nasan kud'i dan haka malama ciko min zan tafi"? Harara A'i ta sakar mata tana kau dakai tace "nace miki bani dashi sata kike so nayi na biyaki kome"? .

"Yo Ina ruwana kiyo satar ki biyani kayana meye damuwa ta"?.

Wani kallo A'i tai mata "nayo sata na biyaki kud'i? Saboda ga wacce batasan ciwon kanta ba ko to ki bari watan tsoron naki bai kamaba dan wallahi bazan takura kaina ba sai ranar dana samu zan biya da uban wa yace ki raba mana bashin"?.

"Au haka kika ce jimin tsinanniyar mace ni zaki jefa da sharri wato nai miki dare kinmin rana na rufa miki asiri ni kin bankad'a nawa na lullu'be ki lokacin da kike jin sanyi shine yanxu kin bud'e rufar zaki jefani a uku dama yarda da mutumin daya fito daga gidansu mai guga (baban A'i🤫) shirmen banza ne"

A fusace A'i ta mi'ke tana cewa "a'a kada ran kada han kada mai gani ya taka makaho Dijalle kinzo inda hankali na bazai dauka ba me kike nufi da cewa yarda da wanda ya fito daga gidanmu shirmen banza ne kina son nunawa duniya mu maciya amana ne kome"?.

A masife Dijeh tace "ashe kin gane abinda nake nufi shine dan gulma kike tada ha'kur'kura da jijiyoyin wuya a gaban kishiyoyinki dan karsu miki dariya to wallahi A'i bari kiji saikin biyani kud'i na".

Itama A'i cikin d'aga murya tace "wallahi bazan biya ba sai sanda na samu aikin banza aikin wofi matsiyaciyar mata kinzo kin dameni da masifa ki barni da abinda ke damu na".

"Kece babbar matsiyaciya bani ba tsinanniya wacce batasan halacci ba daga yau tayi kai bazan sake baki kayana ba".

"To kuma ni sai akace miki zan sake kar'ba saboda ga wacce kare ya lashewa zuciya tirrr da kayanki dama can 'kaddara ce tasa na d'auki bashin a gurin ki ga mutane nan da yawa masu daukowa saina canza she'ka".

"Ki canza man bai dameni ba nidai kawai kud'ina nake bu'kata kiban zan wuce kina 'bata min lokaci".

"Au ina 'bata miki lokaci danai me? Dama na ri'ke kine kalli ki gani ba tike nai a gun na d'aure kiba zaki iya tafiya".

"Wallahi tallahi kinji rantsuwa ko A'i bazan bar gidan nanba saikin bani cikon kudina ko kiga tsiya".

Ja A'i tai ta ture tana gyara daurin zani tace "wallahi bazan biya ba sai ranar dana samu a shirye nake mu dambu mu juya mu fidda raini dama na dad'e banyi fad'a ba jini na a daskare yake yau saiya tsinka shi".

"Kika ce bazaki biya ba"?.

"Eh bazan biya ba haka nace ko akwai wani abu da kika isayi"?.

"Niko nake da abunyi tunda ni 'yar kasuwa ce bana rasa abinyi" tana rufe baki ta fad'a d'akin A'i tana d'auko sabuwar tunkuya lamba sha biyar data sayo ta dafa abincin saidawarta tayo waje da ita zata fita a guje A'i taje tana kamata da kokawa ganin zata tafi mata da kayan kud'i tace.

"Gidan uban wa zaki kaimin tunkuya ajiye tunda ba tsofinki ne suka saimun ba" A'i na rufe baki taji saukar mari tasss a fuskarta 'kara ta saki dan batai zato ba kawai zafin marin taji kokawa suka fara sosai suna dambe-dambe da dake-dake baji ba gani da sauri Saude ta Binta suka zo suna rabasu sai fisge-fisge A'i tana da kururuwa "ku barni in rama akan me zata mareni na 'kyale ta wallahi saina fasa mata baki" huci Dijeh keyi tana kallon ta tace "dan Allah ku saketa naga da yadda zata fasa min bakin wallahi yau da saina targad'aki saidai ki kwana a asibiti".
Chapter 72 · 0% Book details