← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 145

Sashe 21

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me gari na kallon Ramatu data mi'ke yace "ke kuma gobe ki kwana cikin shiri da zuwan sammaci domin na gaji da kashe shari'arki gara na kaiki gaba inda za'a saita miki zama" shewa da gud'a ta saki tana cewa "ai kayi ta banza meyasa zaka bari sai gobe ka kaini a yau mana me gemun wofi" tana fadin haka ta karkad'e masa 'kura tai gaba tana yiwa Lami masifa "kema dan ubanki meyasa baki fad'a min wanda yace miki jahilar ba kika 'kyale gashi kin jawo min zuwa gurin yan sanda" muryar Lami da damuwa tace "kiyi hakuri dan Allah bada sona bane" "shikenan koma gurin tallar ki bari nabi ta gidan su Balkin itama naci uwarta ta fad'a tana kama hanyar anguwar da kallo Lami tabi bayanta tare da sauke ajiyar zuciya ta share hawayen daya zubo mata ko kadan bata farin ciki da kasancewar Ramatu uwa a gareta kowanne d'a zaiyi tunkaho ya nuna uwarsa a ko'ina amma banda ita juyawa tai ta nufi dandali tun daga nesa taga yadda ake nunata ana 'kus 'kus amma ba yadda ta iya haka ta daure ta karasa ta samu guri kawai ta zauna tare da sunkuyar dakai kasa ta rafka tagumi kunyar kowa take ji abinda Ramatu take aikatawa a garin indai yaro ya d'ago yakai shekara hud'u zuwa biyar to yasan Ramatu saboda bala'in ta.

✍️MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘😘.

Sai Allah ya kaimu gobe zamu d'ora maman little Zaran aunty.

Kai jama'a Ramatu mai zamani Ramatu Ramatu tuwaiye Ramatu Ramatu me kike dafawa kan awakai kiyi ki dafa ki bani nawa zani ba takai ba ko kano ne kije ki dawo ai na Sara miki Ramatu dole na wake ki tab muje zuwa readers yanzu aka fara.

IN ANA BATUN JIRGI ME AKE DA MOTA AHMAD BIN MUHAMMAD DA GA NANA BINTA A CIKIN WALIYYAI KAINE KAKE SARAUTA JIKAN MA'AIKI INA MI'KO GAISUWA TA.

Rayuwar da ba annabi ba rayuwa ba dakai naffake rasulullah ban fake da kowa ba na kirayi sunan Allah mamallaki mai mulkin dukkan halittu marashin mataimaki auwalu akiru zahiru badinu ya madaukaki ka karar dubun basira badan halina ba🌹💞.

YUSRAH 🌹 MUSA ABUBAKAR MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY 💃.

TYPING 📲 💎ME KAMAR SARKI 💎🌃 EMPIRE DAULA.
🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
🏘️ Home of 🤝 hospitality and 🌹💞💃🌄 harmony gidan karba hannu biyu da zaman lafiya.

💻✍️ Yusrah yar Musa jikar Abubakar Muhammad ta kowa ce 😜 ku fito mu warwasa yau zamu shiga duniyar nishadi mu Debi nishadi yadda ya kamata🐧 ga ayu ma yazo taya mu.

17~AR-RAZZAK
The provider
18~AL-FATTAHU
The victory giver

9~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Salihina.

🌄 REMEMBER ND ABSENT MINDED🌄
Episode 17&18
Washe gari tun asuba Baffah vya tashi 'ya'yan sa sukai sallah zasu tafi gona kowa da fartanya a hannun sa suna shirin fita gani su biyu ne yace "ah kai Sabi'u ina Ilyah ba nace ka tashe shiba"? Amsa ya bashi "eh Baffah na tashe shi yaje masallaci sallah tare muka dawo yana d'aki" "au yana d'aki yai shiru? Kai Iliyasu kana ina"? Jin ba'a amsa ba yasa Baffah aje ledar buhun dake hannunsa ya je kofar d'akin su ya d'aga labule cikin mamaki yagan shi kwance idonsa tar cikin nashi.

Da fad'a Baffah yace "dama kana jina ina magana kayi shiru kaifa muke jira zamu tafi gona kaso ka sake sabon kwanciya" banza Ilyah yai kamar da dutse Baffah ke magana ba mutum ba, "dakai fa nake Iliyasu"? Tsaki Ilyah yai yana juyawa Baffah baya yace "bazanje ba ko dole ne"? "Baza kaje ba Ilyasu"? "Eh Baffah haka nace bazan je ba na gaji" "meke damunka Iliyasu yau ni kake cewa baza kaje ba kamar kana magana da abokin ka"? Maimakon ya tashi saiya kuma jan bargo yana rufe jikinsa.

Abu Baffah yaji ya tsirga masa har saida ya dafe saitin Zuciyar shi yana bin Ilyah dake lullu'be cikin bargo da kallo kafin muryarsa a sar'ke yace "Iliyasu ni mahaifin ka yau kake cewa wai baza kaje ba har abin nake yakai haka? Allah ya shirye ba bazan maka baki domin kai d'ana ne bana so ka shiga wani hali amma indai kaci gaba da fand'are min zamu raba hanya dakai".

Baffah na rufe baki yaji ance "to saime dan kun raba hanya dama wani abun arziki kake bashi saidai shi idan ya samu ka ri'ka zizzilla ido kamar 'bera a ragaya kana jiran a baka kullum hannun ka a bud'e kamar ganyen rogo bari kaji maganar gaskiya Iliyasu daga yau ya daina yi maka wahala wadannan din dai suje su karata inma kashe su zakai amma banda d'ana" sosai Baffah ke kallon Ramatu ya ma kasa magana ga juyawa da kansa keyi duhu ya fara gani da sauri ya dafe bango jin zai fad'i ya soma karanto addu'a zuwa wani lokaci daya ji sauki ya kalli sauran yaran nasa yana cewa "Sabi'u kuma ku zauna ku huta yau gobe sai kuje kaji" kai Sabi'u ya girgiza cikin damuwa da jin zafin abinda Ramatu tayi da rashin biyayyar Ilyah ga Baffah yana jin tsoron kada wata Rana a wayi gari sun kashe shi da ba'kin cikin da suke kunsa masa tunda a yanzu ma hawan jini ya kama shi ance ya daina yawan tunani da tuna abinda ya bata masa rai.

Yace "a'a Baffah zamuje nida Habubakar mu karasa noman ka zauna a gida basai kaje ba zamuji da komai" ya fad'a yana rike Baffan ya mayar shi d'aki ya dauki maganin shi ya bashi kafin ya fito suka wuce.

Kwana biyu a tsakani Baffah na zaune a kofar d'akinsa yana rubutun allo yaji sallama yana d'aga kai yayi murmushi saboda ganin wanda ya shigo fuskarsa da fara'a yace "Musbahu sannu da zuwa yanzu kake tafe 'karaso shimfida maza ka zauna kee Salamatu munyi ba'ko kawo masa ruwa" zama Musbahu yai cikin farin cikin zuwansa da ganin Baffah domin rabonsu da juna harya manta gaida shi yayi daidai Salamatu ta aje kofin ruwa a gaban sa ya gaishe da ita amsawa tayi tana tambaya sa "Musbahu mutanen birni ya iyalin suke"? "Wallahi suna lafiya Innah ina Sabi'u habu da Ilyah"? "Ayya suna gona amma kila yanzu zaka sun dawo yau ne ma naga sun danyi jinkiri ko maye ya tsayar dasu"? Ta fad'a tana mikewa ta tafi d'ebo masa abinci daidai fitowar Lami daga d'aki zata fita talle ganin sa yasa ta karaso har kasa ta durkusa ta gaida shi amsawa yai cikin mamaki bayan ta fita ya dubi Baffah dake faman rubutu yace.

"Baffah wai wannan yarinyar naka ce har tayi girma haka? Lallai abun da mamaki gaskiya na dad'e rabona da wajajen nan haka tun batafi shekara biyar ba fa ko Baffah"? Murmushi Baffah yai "eh haka ne Musbahu yanzu kuma shekarar ta sha biyar kaga kai kuma shekara goma kenan baka zo ba" kai Musbahu ya jinjina yana cewa "amma Baffah badan talla al'adarku bace yarinyar nan da kun sata a makaranta ilimi shine gaba da komai" kai Baffah ya girgiza "Musbahu matsalar ba'a ni bane ko yarinyar a uwarta ne bazata barta tayi karatun ba amma da yanzu ta dau wani matsayi ni kaina abun na damu na dashi nake kwana nake tashi balle ita yarinyar duk komai nata da 'kwallafa ranta akan karatu amma har yau burinta bai cika ina ba'kin ciki matsayi na na uba gareta ace na kasa biya mata hakkinta da ina da gurin dazan kai Lami tayi karatu da yanzu na kaita na dauketa daga wannan damuwar".

Shiru Musbahu yayi yana tunani zuwa wani lokaci yace "to Baffah da zaka amince sai na tafi da ita ta zauna a hannun matata tayi karatu rayuwar ta tayi inganci" da sauri Baffah ya d'ago yana kallon Musbahu yace "da gaske zaka rike min ita tayi karatu ta cika burinta"? "Eh Baffah alkawari ne bazan ci amana ba duba da irin zaman arzikin da kukai da mahaifina gashi sai ala'kar ta zama alkairi nima har yanzu ban yada ba" "shikenan Musbahu na amince ku tafi da Lami wudil ta zauna a hannun ka tayi karatu mai zurfi kuma karka dawo da ita kwana kusa..................

Kamar anyi wani abu na firgici ko tashin hankali haka suka ji muryar Ramatu tana rafka salati "la'ilaha illallahu kaito na, na lalace ni za'a munafinta? To Allah ya tonu asirin ku naji komai kuma wallahi tallahi babu inda Lami zata je talla nai niyya tayi ba karatu ba" nuna Musbahu take da yatsa tace "kai kuma daka d'ebo gemu kamar bunsuru da gurma gurman ido baka isa raba ni da 'yata ba munafiki d'an mafiya hatsabibi kawai harda wani ya amince maka ku tafi tare sai naga idan kaine ka haifa min 'yar..........

"RAMATU"!!! Baffah ya fad'a cikin tsawa da nuna bacin rai rike kugu tayi tana kallon yadda Baffah ke huci tace "malam dallacan ka rufe min baki fad'i Ramatu ka kara da babbar murya suna na kenan Lami ce kuma nace babu inda zataje babu shegen da zata bi ko'ina idan lokacin auren nata yazo shi munafikin naka mai zugaka tayi karatu zai siya maka gado ne ko kana tunanin zai taimake ka to ba dani za'ai rakiyar asara ba kaji dai na fad'a maka sai abar maganar Lami ku kama wata tashar na yanke hukunci".

"Amma ke kam Ramatu bansan wacce irin mace bace ke sam kin girma amma baki da hankali ko bakisan Musbahu baza kimin haka a gabansa balle kinsan d'an gidan amini na ne munyi kyakkyawan zama da mahaifinsa".

Ta'be baki Ramatu tai tana cewa "af daga baya kenan anyi sadaka da karuwa yo malam tsakani da Allah bazan fad'i gaskiya ina gani a cuce ni d'an yana d'an gidan amininka kawai saika dauki yarda ka bashi a wannan zamanin ba lallai mutumin arziki bane kana ganin idonsa kaga ri'kekken d'an tasha wanda yasan duniya yake jujjuyata".
Chapter 21 · 0% Book details