← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 145

Sashe 77

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai Iluh naxo muyi magana".

'Dagowa Iluh yai ganin Asabe yasa da sauri ya du'ka yana cewa "ashe babah ce sannu da zuwa ina kwana"? Ya gaida ita amsawa tai da fara'ar mugunta a fuskarta ta kalli gabas ta kalli yamma babu kowa a layin d'an kasa tai da murya tana cewa.

"Kasan me nake so dakai yanzu a yau d'in nan basai gobe ba kayi shiri maza ka koma garin ku gobe ka bugo sammako kaida iyayenka wajen neman auren Indo nayi maka alkawari zanyi ruwa nayi tsaki a baka ita kaji"? .

Kai Iluh ya d'aga cike da murna dan shima dama a matse yake ya aureta a yanxu dan tun ranar da yaje gurin ta sau daya ya harbu da sonta da sha'awar ta musamman da yaga tana da kayan aiki😳🙈 (Innalillahi wallh fans ba ruwana🤭).

"Ka jini ai ko"?.

Kai ya d'aga yana cewa "eh babah insha Allahu ayau kuwa zan tafi gobe innata da baffana zasu zo" yana rufe baki Asabe tace "yauwa d'an albarka maza tashi kayi shiri ka tafi nima bari na koma na sanarwa ubanta cewa zaka turo" tana fad'in haka tabar gurin yayin da Iluh ya mi'ke yana shiga shagon ya soma d'ura kayansa a leda da mai wanki da marar wanki ko wanka baiyi ba 'kafarsa duk kasa haka ya fito yana shigar da baron cikin gidan malam Garba yai musu sallama ya d'au hanya su kansu sun d'anji mamakin tafiyarsa amma babu wanda ya tambayeshi".

Batun Asabe bata koma gida ba sai dare kusan karfe goma a kofar d'aki ta samu Balarabe yana zaune gurun ya zuba tagumi tsaye tai a kansa tana shewa wanda yasa a firgice ya d'ago yana kallon ta itama shi take kallo cikin hasken farin wata tace.

"A lallai Balarabe akan lamarin wannan shegiyar 'yar taka Indo shine kake neman hana kanka sukuni? hummm nayi maganin abun gobe karkaje ko'ina ka tsaya a gida ka shirya tarar ba'ki".

Muryar Balarabe kamar yana mura sakamakon dad'ewa dayai bai magana ba yace "su waye zasu zo"?.

'Daki Asabe ta wuce tana cewa "iyayen Iluh d'an garuwa naje na sameshi d'azu nice nasashi yaje gida ya turo su nan da karshen watan nan a gama komai" tana rufe baki Balarabe ya dafe kirjinshi sakamakon jin bazatar datai masa gabansa ya fad'i harsai da ya saki salati zuciyarsa na harbawa baice mata komai ba ya share wani d'an 'karamin hawaye daya zubo masa wanda baisan na meye ba sai yanzu yake jin takaicin kansa da haushin kansa da yakai tallar 'yarsa a masallaci baisan meya sameshi ba yana son 'yarsa amma bashi da wani iko a kanta kome zai mata na muniya bada son ransa bane abun na damunsa a raisa ya rasa ta inda matsalar take sannan haka nan yaji baya kaunar baiwa Indo wannan d'an garuwar fatansa Allah yasa Dauda yaji yazo ya samu Asabe dan yasan shi kad'ai ne zai iya taka mata burki a yanxu ya mike da'kyar yana shiga d'aki.

Washe gari asubar fari ko haske bai gama wayewa ba Iluh ya dira a gidan Balarabe tare da iyayen sa😔 tare dasu akai abun kari😲 farin ciki da murna a gurin Asabe kamar ta xubar ruwa a kasa tasha dan dad'i haka nan akai komai jikin Balarabe a mace kamar mara laka yace a fad'owa Dalah mahaifiyar tace tana da alhakin sani haka Asabe ta hana babu yadda ya iya taya labari ya jewa Dauda a tsegumin gari suna zaune ana tattaunawa sai ganinsa sukai shida Dalah sun shigo gidan zaro ido Asabe tai a ranta tace "to shi kuma wannan yaron uban waye ya fad'a masa har yazo".

"Dawa kikai shawara kike shirin yi mata auren dole saidai kiba da 'yarki Bahijjah domin itace kike da iko a kanta" Dauda ya fad'a yana zaro mata girman idonsa kallon Balarabe Asabe tai wanda ya girgiza kai yana cewa.

"Ahh ya kike kallona? ba nine wanda na gayyatosu ba".

Kai Dalah ta d'aga tana murmushi tace "eh mana babu wanda ya gayyato mu nan".

Sa'kwa'kwa Asabe tai tana kallon ta tace "mene babu wanda ya gayyato ku"?.

"eh a bisa ra'ayin kanmu muka zo".

"Me kenan"?.

"Au ke mekike inace kar'bar auren 'yata kika bararraje kinayi to muma shi mukazo yi saidai kin makara ki sani baki isa ba wallahi lokacin dana d'au cikin ta da wahalhalu baki sani ba na raineta dan haka baki da wani iko a kanta ganin dama tace nace ga wanda zata aura dan haka bari kiji ban amince da wannan za'bin naki ba".

Dariya Asabe tai tana cewa "dama kinji nace ki amince da za'bi na ai na riga na gama magana na basu aurenta nasa rana karshen watan nan maganar na isa ko ina da iko ya wuce aure kuma dole".

Kai Dalah ta jinjina tana cewa "au haba auren Bahijjah zaki ashe to Allah ya bada zaman lafiya idan ankai mana minti zamu zo musha biki mu shari taushe" sannan ta mayar da hankalinta kan Balarabe tana kallon sa shima ita yake kallo zatai magana a bazata taji yace.

"Dalah na dawo dake😲".

Zaro ido Dalah tai tana sake kallonsa da mamaki tace "me kace Balarabe"?.

Da gefen ido Balarabe ya kalli Asabe cikin tsoro da raunin murya yace "na dawo dake d'akin ki kizo kiyi bikin 'yarki da kanki".

A zabure Asabe tace "meee maimaita abinda kace Balarabe dan banji sosai ba ka dawo da ita ina"?.

Dariya Dalah tai tana cewa "ai dama bazaki fahimta ba amma idan kika ganni a cikin gidan na dawo zaki fahimta" maida hankalin ta kan iyayen Iluh tai tana cigaba "ku kuma kunga gaskiya dai ba 'yarta bace zura ku tai a kwalba dan taci kud'inku nice mahaifiyar yarinya bata shawarce niba bansan da wata maganar aure ba asali ma bansan d'anku ba saifa yanzu dana ganshi ni 'yata nayi mata miji dan Allah kuyi ha'kuri fatan ranku bai 'baci ba".

Murmushin ya'ke innar Iluh tai tana kallon Dalah cikin girmamawa tace "ayya karki damu mun fahimce ki wallahi babu komai ai d'a na kowa ne Allah ya bada zaman lafiya yasa gidan zama ne shi kuma Allah ya bashi wata".

Amin Dalah tace tana mayar da hankalinta kan Balarabe tace "to na gode amma kasan nayi iddah fa dole sabon aure za'ai da sadaki na da kayan lefe duk zakai ko kuwa a'a"?.

Kai Balarabe ya d'aga "eh duk zanyi nan da sati zan had'a komai sannan maganar Dauda da Indo d'in ki turo min Malam Balah muyi maganar".

Kai Dalah ta d'aga "to malam nagode Allah ya saka da alkairi ni zan koma ba'ki ku gaida gida Asabe a huta lafiya" tana fad'in haka ta juya suka fita itada Dauda wata ba'kar d'anyar ashar Asabe ta saki tana kallon Balarabe tace.

"Me zan gani haka Balarabe wacce irin asara ce ta sameka ka dawo da Dalah gidan nan naji kana cewa? Tabbb heyyyy jama'a kuzo ku tayani figa uwar kishiya ta zama kaza😲😁 wallahi baka isa ka dawo da itaba ko zaka mutu harda wani li'ke hanci na dawo dake d'akin ki kizo kiyi bikin 'yarki da kanki to kar naji karna gani ka gane? Aikin banza aikin wofi uban meye abinso a jikin Dalah mace kimmm haka babu fasali ku kuma sai ku d'ebi tsummokan ku kuyi gaba tunda wannan matsiyatan suka sani baza ai auren ba" mikewa tai tana shiga d'aki sai bala'i take.

Shiru Balarabe yai ba um ba um um ya rasa abinda ke masa dad'i kallonsa baffan Iluh yai yana cewa "to mun gode da karramawa malam mu zamu koma Allah ya 'kaddara saduwarmu".

Harsun mi'ke Innah tace "amma wani anzari ba gudu dan Allah Malam Balarabe naga ai kamar da akwai wata budurwar a gidan nan bayan ita yarinyar da mukaxo neman auren ta ko za'a bashi itan dan Allah"🙊😳.

TAB INNAH KIN 'DEBO DA ZAFI☕ ANYA ASABE ZATA BAIWA 'DANKI ILUH AUREN BAHIJJAH KUWA???🤔🤔🤔 HHUMM GABA-GABA DAI MUJE ZUWA ME HANKALI YA HAU KURA🐆🐵.

Tun Balarabe baiyi magana ba Asabe ta fito daga d'aki da gudu tana cewa "me kike cewa na baiwa Iluh auren Bahijjah? Dama am fad'a miki daga turu aka kunto ni ko mazan duniya sun kare me Bahijjah zatai da wannan duguzunzumin 'kazamin d'an naki wanda baya wanka balle wanki kalli fa kayan jikinsa da sumar kansa fatarsa har mai'ko take da kirci tsabar daud'a amma tsabar kanki ya kwance kike had'a Bahijjah dashi tabdijan Allah ya suturi bu'kwi inji kishiyar 'konanna tafi 'karfin auren irinsa gaba da baya wallahi kuje can da tsiyarku yaje ya nemi irinsa kucaka ya aura".

Duk su ukun da kallo suka bita banda Balarabe wanda shi dama already yana da tabbacin zatai fin haka ma tsananin mamaki ne ya kama su har suna kallon juna jiki ba 'kwari Innah tace "haba ke kuwa baiwar Allah idan ma bazaki bashi 'yarki ba ai magana mai dad'i ma sadaka ce amma irin wannan cin mutumci haka koba komai ance ka girmama ba'konka ke a ganinki kinyi daidai kena................

Bata karasa ba a tsawace Asabe ta d'aga mata hannu tana cewa "Kee dalla gafara can rufa min baki ke harkin isa nai tsari dake 'karama 'yace nace bazan bayar ba dan haka ku tattara ya naku ya naku ku 'kara gaba domin marabarku babu ita anan sannan bugu da 'kari akanka ne kai Iluh zan ja maka kunne da gargad'i daf da duk wallahi tun garin nan gurin zamanka ne kada tsautsayi yasa naji labari yazo min kayiwa Bahijjah magana saidai hukuma ta rabamu domin ba sa'ar aurenka bace ka gane kaje ka nemi jaka 'karama marar aji irinka ka aura zaku iya tashi ku 'bace min dan na gaji da ganin wad'annan munanan fuskokin naku🙊 aikin banza kawai" tana gama fad'in haka ta sa'bi gyale a kafad'a dan ko aka bata d'ora shiba tai waje tana tsine tsine.

Sukam sak sukai kamar ruwan 'kan'kara ya ji'kesu suna bin hanyar da Asabe ta fita da kallo suna kuma jinjinawa rashin mutunci da daraja d'an Adam irin nata Iluh da jikinsa ke tsuma saboda 'bacin rai dama mafarauci ne mi'kewa yai a fusace yana cewa .
Chapter 77 · 0% Book details