← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 145

Sashe 55

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da mamaki Halimi ta sake kallon shi jin abinda yace kodai 'bacin ran da ya shiga ya ta'ba masa 'kwa'kwalwata ne sake duban sa tai sosai taga dai har lokacin idansa yana li'ke kamar tsohon makaho😂😁 tace "wacece batace ka bud'e ido ba wai alhaji kana lafiya kuwa"? Jin yana neman yin 'barna yasa da sauri ya bud'e ido a gigice yana kallon ta tuna cewa idan yai kuskure harda shi za'a 'batar jin ta sake jefo masa tambaya "Alhaji ina ta magana ka share ni wai ina kaje ne tun shekaran jiya baka dawo ba sai yau"

Cike da tsananin mamaki ya juya yanai mata kallon baki da hankali ne yace "shekaran jiya kuma? Wannan wanne irin hauka ne na fita d'azu kice wani kwana biyu bana gida saboda ga wanda baisan abinda yake ba ko sai nabar kwana a gida kawai tsabar kin mayar dani gaula"? Baki bud'e Halima take kallon sa anya bai fita hankalin sa ba da gaske take yau kwana biyu baya gida ganin ya mi'ke zaibar gurin tace.

"Amma alhaji da wasa kake ko"? Dakatawa yai "da wasa nake me"? "Da wasa kake dan kaji me zance ne shiyasa ko Australia d'in kaje...............

"HALIMA ya ishe ki bansan shirmen banza Italia naje ko California ba Australia ba zancen iska ke wai mahauci kika mayar dani ne inace d'azu na fita taya zanyi tafiya kwana biyu ban sanar miki ba"? Shiru tai kawai ta zuba masa ido ta kasa cewa komai yaci gaba "ko kina tunanin naje mun had'u da baby ne tunda naga yanzu zargi ya shiga tsakaninmu Halima ki shiga hankalin kifa kafin na saita miki shi............ shiru yayi yana kallon TV ganin ana haska gawar Gwamna da kuma Commissioner cewa sun rasu daren shekaran jiya zuwa safiyar yau zaro ido Halima tai tana kallon Prof wanda ya zubawa TV ido yana sakin murmushi d'ora hannu tai aka tana cewa.

"Nashiga uku Alhaji mezan gani haka badai kaine kayi wannan aikin ba karkace min da hannunka ko had'in bakin ka? Wata irin dariya ya saki wanda ta tsorata Halima yana cewa "eh mune muka kashe su nine na bayar da jininsu a 'kungiyarmu kuma ba kinji na fad'a miki ba duk wanda kika fad'awa wallahi zaki mutu ranar kwanan 'kabari zaki ni yanzu na zama had'ararran mutum ki bini a hankali Halima kinji dai na fad'a miki idan kunne👂 yaji"? Ya karasa maganar yana ri'ke kunnen sa Halima dai kasa magana tai duk jikinta rawa yake.

Yace "ina Hudayyah zan kaita wani wuri yanzu duk ma inda kika kaita kafin na shiga na fito ki dawo min da 'yata" muryar Halima na rawa tace "ina zaka kaita Alhaji na rokeka kada ka d'ora ta akan gur'batacciyar hanya kaima inai maka fatan shiriya please alhaji badan niba karka sanya yarinyar nan cikin wani mummunan bala'i dan naga ka matukar 'bata a halin yanzu ka fita haske ka shiga duhu kayi nisa Alhaji bakajin kira".

"HALIMA ki kiyaye nifa idan kika cika tambaya zaki hallaka saiki kame bakin ki" yana kaiwa nan yayi gaba d'ora hannu Halima tai aka tana binsa da kallo harya shiga part dinsa ya banko kofa toshe kunne tai tana sake kai dubanta kan TV jikinta na tsuma tabbas da gaske Gwamna ne da commissioner ana musu sutura hawaye ne taji ya cika mata ido yana zuba shar shar daidai ya sake fitowa Hudayyah na binsa a baya zasu fita Halima da kuka yaci 'karfin ta tace.

"Hudayyah karki je ko'ina idan na isa dake ki dawo idan kin d'auke ni mahaifiya wacce zan fad'a miki kiji".

Juyowa Hudayyah tai tana kallon ta tace "haba dan Allah mum yanzu fa zamu dawo Daddy yace zan raka shi sahat ne me zan taho miki dashi"?.

Halima data gama rudewa jin abinda Hudayyah tace yasa ta kalli Prof da alamar tambaya a fuskarta na mamakin 'karyar daya shimfid'a mata wato 'yarsa ma saiya yaudare ta jin bud'e 'kofa yasa ta kallon kofar harsun fita da gudu ta bisu compound d'in gidan ya bud'e mata mota ta shiga Halima fuskarta fal da tsananin fushi tace.

"Hudayyah nace karki je ki fito a motar nan"?.

Tsaki Prof yaja yana ri'ke da murfin motar ya zafgawa Halima wata ba'kar harara yana cewa "ta fito taje miki gidan uban wa? Halima kibar sakun ido yanzu idan ba haka ba zamu kwashi damben tsiya dake wallahi kinji na rantse".

Takaici ne ya rufe Halima tana kallon sa ta jinjina kai tana cewa "shikenan Alhaji kayi komai lokacin kane akwai ranar dana sani tana nan zuwa abinda ka shuka shi zaka girba ba'a shuka gyad'a dawa ta fito kabi a sannu kabi a sannu Alhaji ina gargad'in ka cewa ka dawo hanya ka tuba tun kana da sauran lokaci kafin duniya ta juya maka baya" banza yai mata yana had'e rai maida hankalin ta tai kan Hudayyah data sa earpiece a kunne sai kad'a kai take tace.

"Ke kuma tunda kin za'bi kibi makauniyar hanya babu ruwa na idan kikaje ban yafe miki ba".

"Sai mai dan baki yafe mata ba dama albarkar ki wata tsiyar zata amfana mata kije ki ri'ke rashin yafiyarki mukam munyi gaba" yana kaiwa nan ya shiga yana tada mota tana tsaye Rabe mai gadi ya bud'e musu kofar gate suka fita ji tayi 'kafafun ta sun kasa tafiya sunyi sanyi kamar bazasu iya d'aukar taba dafe kanta tai tana juyawa ta koma parlor cikin wani irin yanayi wanda bazata iya fassara shiba.

MRS AL-AMEEN AHMAD CE😘.

SEE YOU NEXT TIME🤞 NA GODE😂😍🤩.

TYPING 📲 SUN, JUN 23/24 9:34PM YUSRAH MUSA ABUBAKAR MUHAMMAD 💋🤟💔💗💞💕💓🤙.

👑MË KÃMÃR SÁRKÏ 👑

WhatsApp no:234 816 098 3083.

Bismilllahir rahmanur rahim in the name of Allah the must benefits and the must merciful we love our nabi peace be upon him Amin 🤲👏🙏.

A*WA
💫ÀÑÑÙRÌ WRÌTÉR'S ÃSSÕÇÌÅTÍÔÑ 💫
----------------------------------------------------
__________________________
--------------------------------

Maman little Zaran aunty💃💃💃
🌺M🌺U🌺H🌺A🌺M🌺M🌺A🌺D🌺U🌺S🌺A🌺W🌺
🌺Y🌺U🌺S🌺R🌺A🌺H🌺
🌺M🌺U🌺S🌺A🌺H🌺
🌺A🌺B🌺U🌺B🌺
🌺A🌺K🌺A🌺
🌺R🌺Y🌺
🌺M🌺
🌺A DUTSE NEW WORLD 🌏 NEW LIFE 🌌 NEW STYLE 👌 SABUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DADI YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN JIGAWA 🍇🏞️🗻.

🕌🕋🕌
It's Friday don't forget to recite suratul Al-khaf may Allah open the door of success 4 all of u Muslims Amin 🤲👏🙏.

HÃPPY JÚMÃ'ÂT MÜBÅRÄK
🍇🍉🍎🥥🍒🍏🍓🥝🍍🍌🍊🥕

Dedicated to
📚Mr Hausa Ebooks ceo faunder of taskar hausa novels.
🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

#YUSRAHMS#
🐦🐦🐦🐦🐦🐦

39~AL-MUQIT
The Nourisher
40~AL-HASIB
The bringer of judgement

19~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Zakirinah.

🌄 JOURNEY ND DISCONTENT🌄
Episode 39&40
Kamar yadda Alhussain ya fad'a haka ne ya faru sati d'aya Asad da aboki sa Abdul-kareem suka wuce Marshall islands saidai ba zama yayi ba yana kammala abinda ya kai shi ya tattaro ya dawo amma bai baro 'kasar ba saida ya tabbata ya bada Asad a kyakkyawan hannu inda za'a kula dashi ta hannu wata babbar ma'aikaciya tsohuwar soja ce sunata Deranah Enouch Jonson tayi ritaya sai yaronta zasuyi kusan sa'anni da Asad d'in sunan sa jayesh Jonson asalinsu 'yan Canada ne a yankin corner brook na ha'ki'ka kuma ba musulmai bane amma ita 'yar American ce sun koma can sakamakon aikinta da komai nasu har mahaifin Jay ya samar da Abubuwan al'ajabi na zamani wanda hakan ya zama sabon abu a gurin su d'an lokacin kad'an ya sanu a 'kasar yai suna aka sanshi ya bun'kasa hanyar arzikin sa ta bud'e ya kafa babbar masana'anta wacce babu kamarta Had'uwar Jay da Asad yayi masa amfani domin yaso shiga musulunci da d'abia mai kyau amma mahaifiyarsa tace masa bata amince yabar addinin saba Jay yayi kuka yayi ba'kin ciki Asad ya nuna masa cewa indai da rabo wata rana burinsa zai cika haka ne kuwa ya faru ba'ai wata shida ba Deranah Enouch ta mutu bayan an kammala bikin mutuwarta an gama Jay ya musulunta yayin daya za'bi suna Muhid.
Jay suna abota sosai da Asad suna matukar son junansu komai tare suke yi an basu hora da koya musu harbi da juriya a kowacce kalar azaba ce ta samesu har lokaci ya mi'ka zuwan Asad Marshall islands da shekara biyar aka sake kawo sababbin masu d'aukar darasi a wannan yanayin ne komai ya sake sauyawa sakamakon harda mata a cikinsu masu yawa Asad baya d'aukar raini baya son wargi saidai duk da haka dalilin abokin sa Muheed yasa ya koyi wani abu har ya d'an sake kadan yana abota da wata budurwa gud'a daya kuma musulma sunanta Yusairat itama dai soja ce tazo daga Bangkok hankalin ta da nutsuwar ta yasa Asad amincewa ta zama friend d'insa koda yaushe suna tare haka a 'bangaren Muheed shima akwai wacce yake friend da ita sunanta Clarah tun daga ranar datai ido biyu da Asad ta kasa nutsuwa ta tattare dukkan soyayyar ta ta baiwa Asad batare da sanin kowa ba harshi Asad d'in saidai yawan shishshige masa da take ta kuma take taken ta akan wasu abubuwan yasa kowa ya fahimta a bangaren Asad shirmen ta take ita kad'ai domin bata ita yake ba aikinsa yasa gaba sa'banin ita bata mayar da hankali ba kuma ta fiya tsoro yawanci bata amincewa tayi nisa da barek duk rintsi koda kowa baya nan idan kaje zaka sameta bata iya cika alkawarin data dauka na cewa zata kare rayukan al-umma ba wannan dalilin yasa Asad bai sake mata ba baya bata fuska sosai ba kamar Yusairat ba domin shi kanshi ya yabeta cewa jaruma ce duk tsanani a komai tana biye duk inda za'a je koda bazata dawo a raye ba bata ta'ba nuna gazawarta ba.

Suna zaune su biyu a harabar 'bangaren su suna hira Asad da Muheed suka shigo cikin shirin ko a dawo da rai ko a mace kallo d'aya Asad ya musu yana d'auke kaibai karaso ba Muheed ne kad'ai yazo inda suke yana kallon su yace.

"Har yanxu me kuke baku shirya ba? Tafiya ce ta kama kusan sati zamuyi fa a daji Amri yanzu ya kirani a waya cewa muyi sauri an kusa gamawa da sojojin mu suna bukatar agaji sai kuma na ganku a haka".

Had'e rai Asad yai yana cewa "maybe babu su cikin tafiyar yawan sha'katawa suka zo 🙄"?.
Chapter 55 · 0% Book details