← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 145

Sashe 113

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maida Irfan yai cikin katifarsu ta yara ya zuge masa zip din saboda sauro kada ya shiga ya cijeshi kafin ya juyo gurinta yana cewa.

"Aha ina jinki meya faru"?.

Gyara zama Indo tai tana fatan ya amince da abinda zata fad'a dan shima wani san baya abinda ba shine yayi ra'ayi ba tace.

"Dama batu ne akan tafiya gida naga mun shekara harda wani abu amma baka zancen muje mu ganosu dan Allah ina so muje ko bamu dad'e ba".

"Oh akan haka ne dama kikasa na daina wasa da yarona ashe shirme zaki fad'a min"?.

A shagwa'be Indo tace "Allah a'a yaya Dauda wannan ba shirme bane da gaske nake".

"Ok shikenan zamu je amma sai watan gobe kada kiyi magana domin ko tari kikai saina mayar dashi watan jibi kin gane" jin abinda yace yasa Indo rufe baki da hannu tana dariya qasa qasa dan tasan ba qaramin aikinsa bane yace sai watan jibin da tayi masa kuskure dole tayi taka tsantsan kada ta jawa kanta tana murnar zata gida ya qara jan tafiya.

🏙️KANO🏙️
_______Yau da gobe tafi qarfin wasa tun Amatu na shasshare Ajeeb idan ya kirata a waya har zuciyarta ta karkata kansa kamar bata ja masa aji ba sai tsintar kanta tayi dumu-dumu a cikin soyayyar sa kuma koda wasa bai ta'ba fad'a mata daga inda yake ba wai yace shi d'an sarki ne ko wani abu dazai nuna mata ainishin waye shi duk ya 6oye saida abu yayi nisa zuwansa ya yawaita Malam Habu ya sameta akan idan taji zuciyarta ta amince dashi zata iya zama dashi tayi masa magana yaga manyansa a gidan nan domin saurayin Aisha ma ya gama komai indai itama nata da gasken yake ya turo a had'a su ayi bikin kamar yadda akai na Asma'u da Jamila.

A ranar da Ajeeb yazo da dare ta fad'a masa kuma yayi mata alkawarin za'a daga gidansu domin shima yau da niyyar maganar data kawo shi gurinta kenan sai kuma ta rigashi furtawa amma tana ganin idan taga waye shi ko ya bayyana mata kansa zata amince ta aureshi ta nuna ko shakka babu mezai hana aishi take so ba komai ba.

Humm amma fa bayan wucewa kwanaki da mai girma Alhussain yazo su malam Habu sun girgiza kuma sun tsorata dama wannan saurayin dake zuwa dan sarki ne? Cafff gaskiya bazasu iya d'aukar 'ya suna matsayin talakawa a talakawan ma fakirai irinsu duk da yanxu alhamdulillah Allah yayi musu rufin asiri sosai domin har Jamila dake Canada tana turo musu da kud'i su sai abinci bangare guda ga Alhaji Musa gakuma uwa uba Malam Habu da baya son qasawa ko gazawa jajirtaccen mutum mai 'kwazo.

Abu d'aya ne ya tsaya a ran Malam Habu ganin mai girma Alhussain dayai ya tuna masa wancan had'uwar da akai karfa ace wannan d'an matashin ne da suka had'u a kofar shiga makaranta shekarun baya tun Amatu tana shekara shida harya bata kyautar rigarsa kodai da gaske abun daga Allah ne uhmmm bashi da ikon hanawa ko jayayya yabar za'bi a gurin mai duka domin kunyar mai girma Alhussain yasa dole ya kar'bi maganar baya da manyan mutane duk da sune suke nema a gurinsa itakam Amatu harda kukanta domin da tasan a masarauta yake bazata amince masa ba ita da ba jinin sarauta ba haka kawai taje ta cud'anya dasu gashi ta riga ta gama ji'kewa da soyayya dashi tayi zurfi a kansa haka ta gama kukanta ta share malam Habu yana kwantar mata da hankali cewa tayi fatan abinda zai zama alkairi a rayuwarta idan babu alkhairin a tsakanin su Allah ya raba abun ta ruwan sanyi amma yanada yaqinin afkuwar alkhairin domin abunda ya faru a baya.

GIDAN NURAIN
Su Mimih na zaune a parlor suka jiyo 'ka'karin amai daga part d'in Nafisa a guje suka mi'ke suna yin part d'in su ganewa idonsu miyake faruwa suna shiga suka tarar Nafisa dur'kushe tana she'ka amai duk ta 6ata jikinta zaro ido Mimih tai tana kallon ta tace .

"Ke aman uban me kike badai ciki ne dake ba"?.

Nafisa bata iya d'ago kanta ba balle harta bata amsa sai murd'e murd'e take ta'be baki Meelat tai tana cewa "kya tsaya tambayarta wai ciki ne da ita meye wannan inba cikin ba kalli fa yadda tayi wani fari kuma fuskarta ta kumbura kallo d'aya zaki Mata kisan wannan akuyar akwai ciki a jikinta".

Meelat na rufe baki mimih tace "tabdijan kan bala'i wallahi baki isa ki haifa mana baby a gidan nan ba familyn mu bazai ta'ba hada jini da bagidajiyar qauye irin ki ba".

Wata irin harara Meenah ta sakar mata na tsantsan 'baci ran ganinta da cikin wanda take so take fatan ya aureta ya'ki sauraron ta saboda Nafisan tace "Humm barni shegiyar Mimih saita haifi cikin nan a yanzu ko na 6arar dashi wai a haka iyayenta nada kud'i sune masu arzikin qauye".

Tsaki Mimah tai tana cewa "Matsiyatan qauye dai au wai dama a hakan ubanta nada kud'i aini duk zato na irin d'iban bolar nan yake da naga ya kawota dan rashin zuciya ba ko cokali babu tsabar rashin zuciya" Mimah ta karasa maganar tana d'aga waya ta Kira Zainab domin ta riga ta tafi hospital tana d'agawa Mimah tace.

"Hello Aunty zee ki dawo gida yanzu ba lafiya kiyi sauri dan Allah".

A rud'e Zainab tace "meya faru Mimah wani abun ne"?.

"Eh wani abu ne Aunty zee ki taho da allurar zubda ciki domin bamu ankara wannan banzar yarinyar ashe ciki gareta yanzun nan kin ganmu a kanta sai amai take".

Cike da kishi Zainab ta dafe 'kirji tana cewa "ciki kuma Mimah? ciki dai na haihuwa wanda na sani shi take dashi"?.

"Kwarai Aunty zee kiyi sauri kada tsautsayi yasa ya Nurain ya dawo komai ya 6aci".

Jiki na rawa Zainab tace "ok ku tsaya a kanta kada ku bar gurin karta kira my choice ta fad'a masa gani nan zuwa yanzu".

"Ok Aunty zee" Mimah ta fad'a tana sau'ke wayar.

Hankalin Nafisa in yayi dubu ya tashi jin suna neman zubar mata da cikin data 'kwallafa rai a kansa take murna su Bara'atu ma suke yi yau ta shiga uku idan suka rabata da cikin nan sun cuceta yun'kuwa tai da sauri batare dasun ankara ba ta fice dsgudu domin ta tsira daga hannunsu a guje suka rufa mata baya tana xuwa main parlor Zainab na bud'o kofa suka ritsata a tsakiya hannu ta d'ora aka tana fashewa da kuka wani irin kallo Mimih tai mata tana cewa.

''Oh da kike shirin guduwa gidan ubanki zaki tafi ko qauyen zaki tafi idan kin haihu kya dawo 'yar gidadawa".

Zainab da ranta ya riga ya gama tashi da ganin yanayin Nafisan tabbas cikine da ita domin ita likita ce tasan mace juna ranta na turiri tace "ku ri'ke min ita yau saikin gane kurenki".

Ri'kewa sukai tana ihu da qarfi Zainab tayi mata allura sannan tana huci tace "ku d'auke ta ku mayar da ita part d'inta ku samun ido a kanta lokaci zuwa lokaci har sanda cikin zai fita ku kirani a waya ku sanar min na koma hospital" tana fad'in haka ta dauki handbag d'inta ta fice.

Kallon Nafisa dake kwance tana kuka Mimih tai tace "kuka yanzu kika fara wallahi kuma bari kiji idan ya Nurain ya dawo tsautsayi yasa kikace mune sanadin zubewar cikin ki hummmm basai na karasa ba kinsan gamon mu dake baya miki dad'i" kallon sauran tai tana cewa ''ku jamin ita na kaita wawwaran part d'inta data gama lalatawa da qauyanci" ta fad'a tana firgar Nafisan har saida hannunta yai qara kuka Nafisa keyi suna janta kiiii a kasa saida sukai kaita har bedroom sannan suka barta suna ficewa rasa inda zata sanya kanta tayi ta shiga uku yanzu me zatacewa su Bara'atu bayan d'azun nan tayi musu albishir tana ciki gashi wadannan azzaluman yan matan sun zubar mata dashi haka ta wuni a daki tana kuka kamar ranta xai fita musamman yadda taga jini yana zuba a jikinta ta tabbata yanzu kam cikin ya fice daga jikinta har zazza'bin tashin hankalin ta yadda zata kare kanta idan Nurain ya dawo take yi tasan zasuyi mata sharrin itace ta zubar da kanta batasan wanne irin mataki zai d'auka a kanta ba.

🌃MARSHALL ISLANDS🌃
____"____Asad yana zaune tare da Isham yana fad'a masa zaije gida ne bikin 'yan uwansa Ameer da Ajeeb saidai bazai wuce kwana uku ba suna cikin magana Clarah taxo ta riski zancen nasu da sauri ta zauna tamkar wani zai rigata tana kallon Asad tace.

"Asad zan bika muje tare tunda ba dad'ewa zakai ba nima ina so na gano family d'inka su sanni na sansu kaga dama tunda nake ban ta'ba zuwa Nigeria ba saidai daga baya idan munyi aure zanje na fara shiri yanzu ko"?.

"No".

Shine abinda kawai yace mata batare daya kalli koda wajen inda take zaune ba kuma fuskarsa bataga alamar wasa ba dan kada tayi masa magiya amma sai tace.

"Asad meyasa baka so naje naga familyn ka wannan shine karo na uku Ina tambayar ka baka amincewa a tunani na akwai yarda mai karfi a tsakanin mu amma har yanzu gani nake kamar hankalin ka bai kwanta dani ba why Asad? dan Allah ka fahimci halin kad'aici da gararin da xuciya take fama a kanka ka tausaya mini kona samu salama".

Banza yayi da ita tamkar ba dashi take ba ganin haka yasa Clarah mayar da hankalinta kan Isham tana cewa.

"Isham ka taimaka min ka fahimtar da Asad ya gane cewa wallahi ina son shi shine matsala ta a yanzu wannan shariyar da yake min babbar ciwo ne ga zuciyata kace masa wani abu please".
Chapter 113 · 0% Book details