← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 145

Sashe 117

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Please Ajeeb maganar ta isa haka dan Allah na fahimce ka kayi shiru basai ka sake cewa komai ba" murmushi Ajeeb yai "shikenan Asad ni kwanciya ma zanyi na shiga kwana duk jikina ciwo yake good night" yana fadin haka ya haye gado tare da jan bargo Asad na zaune yai shiru cikin dagulewar lissafi ya kasa gane inda maganganun Ajeeb suka dosa balle ya fahimci abinda yake nufi saidai ya jira zuwa asuba idan sun dawo daga masallaci ya sake tambayarsa maybe lokacin ya sake dawowa cikin nutsuwar shi dan gani yake kamar baya cikin hayyacinsa yake masa magana d'azu, jin saukar numfashinsa yasa shi kallonsa har bacci ya d'auke shi fuskarsa ya zubawa ido ya kasa daukewa haka kawai ya gaza bambance wanne irin yanayi ya shiga meke damunsa haka ya 'bata lokaci a zaune yana tunane tunane iri iri har kusan karfe uku na dare ya kasa runtsawa karshe sai mi'kewa yai yayo alwala yazo ya fara nafilfilu bayan ya idarma zama yai yaci gaba dayi a gurin har akai kiran farko akai assalatu sannan ya tashi Ajeeb yayo alwala suka wuce masallaci bayan an idar tare suka dawo idanuwan Asad sunyi ja sakamakon rashin barcin da baiyi ba saboda baya son yawan tambaya yasa suna dawowa ya fad'a gado wanda Ajeeb ya kwanta a kusa dashi yana ja musu bedsheet.

Har gari ya waye sosai rana ta fito Ajeeb ya tashi haryai wanka amma Asad baya ko motsi bai tashe shiba bayan ya shirya ya fita zuwa 'bangaren mai martaba da gurin Mami dan ya gaishe dasu.

Kusan sha biyu na rana shiru Asad bai farka ba dawowar Ajeeb yazo yana d'an babbuga filon dayai matashin kai dashi yana kiran sunansa da'kyar Asad ya bud'e idonsa yayi ja ya kalli Ajeeb daya dafa kafarsa daya akan bed din daya tana kasan carpet da murya barci yace "lafiya meya faru"? Zama Ajeeb yai yana aje masa jakan dake hannunsa yace "lafiya kawai naga karfe sha biyu tayi kuma baka tashi ba kamar ka manta yau daurin aurena dana Ameer shiyasa na tashe ka" Asad baice komai ba yake shirin komawa ya kwanta cikin magiya Ajeeb yace.

"Please karka koma dan Allah"👏.

Dafe kai Asad yai jin har lokacin bai daina masa ciwo ba kuma rashin barcin da bai samu yayi da dare bane yasa gashi Ajeeb ya hana shi komawa yasan duk abinda zai fad'a masa yanzu bazai fahimce ba.

"Asad ka tashi man dan Allah yaufa ranar d'an uwanka Ajeeb ce ya kamata ka tashi ka taya ni d'iban nishad'i yau zanyi mata" Ajeeb ya karasa maganar yana murmushi kallon sa Asad yai kamar zaice wani abu ganin ya bud'a baki Ajeeb ya girgiza kai yana cewa "ga kaya nan wanda zaka sa idan zamuje wajen daurin auren ankon mune duka su Ameer da Annur duk iri d'aya ne baza'a bambance angon ba a cikin mu musamman nida kai tunda fuskan mu iri d'aya ka shirya a hankali akwai sauran lokaci sai 'karfe uku da rabi zamu tafi" kai Asad ya d'aga baiyi magana ba yayin da Ajeeb ya juya yana fita komawa Asad yai yana sake sabuwar kwanciya tare da sake jan bargo ya rufe idonsa dan gaskiya indai bai rama barcin nan ba tofa bazai iya samun nutsuwa ba a yau balle har yaje wani d'aurin aure.

'Karfe biyu daidai Ajeeb yazo ya matsa masa lamba dole ba yadda ya iya haka ya ha'kura ya tashi gashi ko breakfast bai ba amma wannan ba shine a gabansaba ba shine matsalar saba wanka kawai yayi ya shirya cikin manyan kayan hausawa shakwara da jamfa ga hula wai wai wai tabdijan sai kun ganshi FANS🤡 subahanallahi akwai dirarriyar halitta mai kyau anan abun baya fad'uwa fitowa yai sai nad'e babbar rigar yake ya wurga tanan ya jawota nan ya rasa yadda zaiyi yana shigowa falon Mami Aunty Fadilah ta kama dariya tana kallon sa cikin tsokana tace.

"Asad ya haka? Innalillahi ji yadda kake tu'kuikuye kayan zasuyi squeezing tun daga nan dan Allah kalli yadda ka wani soke hula a gaban goshi baka saba sawa bane ko kuma duk cikin style d'in ne😂"?.

Had'e rai yai yana d'an karkata kallonsa gurin Mami dake kallon sa itama tana murmushi tace "Asad kayi kyau sosai haka Fadilatinka ke nufi taga maradar kyau ta yaba" rufe baki Fadilah tai tana dariya tace "waye yaga madarar kyan? Uhm uhm nikam ban yaba ba jira nake ango Ajeeb ya shigo na saki gud'ar ban girma nai masa kirari yau ai bata Asad ake ba ana batun masu aure wayake sako tuzurai 😂" dariya Mami tai tana cewa "ayya saurin me kike lokaci ne shima wata rana zaiyi".

Shigowa Ajeeb yai shima ya d'au wankan ala tsine uwar me 'karya🙉 sai tashin 'kamshi yake fuskarsa da wadataccen murmushi ai kamar yadda Fadilah ta fad'a zazzafar gud'a ta sakar masa a satin kunne tana masa wata daddad'ar wa'kar ango cikin harshen larabci sauran suna tafi da salon wa'kar suna amsa mata Mami tace.

"Fadilah irin wannan bege haka"? Dariya aunty Fadilah tai tana nuna Ajeeb tace "ai dole mu kod'a ango mu yabeshi dan tuzurai suji haushi🤣 ko suma sa dage suyi" had'e rai Asad yai dan yasan dashi take kamar bazai tanka ba sai kuma yace "Aunty Fadilaty kin ganni nan ni Asad babu aure yanzu a tsarina bana tunani aikina kad'ai na sani kuma koda ma ace zanyi auren gaskiya ba kwana kusa ba me nisan kwana ne zai gani don sai nayi ritaya🙊" zaro ido Fadilaty tai "sai kayi ritaya kuma Asad subahanallahi gaskiya bamu amince ba sannan ai ka zama tsoro wazai aure ka"?.

"Mai sona"🙅 duk tsufa na ko na zama kwallafiya ne".

"Tabd'i wacce budurwar ce zata yarda ta aureka ka zama kwallafiya ka fara gigi".

"No aini ba irin wannan tsufan zanyi ba".

"Oh da gaske taya ka sani"? "Na sani mana alamar 'karfi"? Ya fad'a yana kallon ta rufe baki Fadilah tai tana dariya tace "tana ga mai 'kiba ai shikenan Allah yaja kwanan mu zuwa lokacin bikin tsofaffi ko ba haka ba" shiru Asad yai Ajeeb da suke tattaunawa da Mami daidai sun gama ya juyo yana cewa "Asad muje ko lokaci yayi" yana rufe baki kiran mai martaba ya shigo wayarsa da sauri ya d'aga cikin ladabi yace "hello Abba kayi hakuri gamu nan" sauke wayar yai yana kallon Asad yace "mu tafi Mami auntis mun tafi ku mana addu'ar dawowa lafiya".

"Ok Ajeeb sai kun dawo Allah ya tsare hanya ya sanya alkhairi" Amin yace suna fita daga part d'in Mami gabadaya gidan fal yake ya cika dam ta ko'ina da mutane manyan ba'ki masu mu'kami su hud'un duka mota daya suka shiga sakamakon Shaukiyyah da Ameer su na gida ne dukka sai aka bari a d'aura a guri d'aya idan anje na Ajeeb d'in.

Alhamdulillah Malam Habu ma yasha kwalliyar tsadaddiyar shaddarsa mai kyau sosai lokacin da suka je har an d'aura auren Aisha da Safwan sai su ake jira a d'aura na Amatun suna zuwa babu 6ata lokaci aka fara abubuwa da addu'o'i an d'aura auren Aliyu Alhassan Aliyudeen akan sadaki wanda ake neman albarkar aure uhmm Allah yayi Shaukiyyah Alhussain Aliyudeen yau buri ya cika itama an d'aura musu aure da Aliyu Alhassan Aliyudeen (Ameer) akan sadaki kai tsaya da wancan.

Bayan an kammala komai mai martaba suka gaisa da Malam Habu yayi masa godiya cikin mutuntawa sannan su Ajeeb suka shiga cikin gidansu Amatu gaisuwar iyaye kowa kallonsu yake su hud'u kaya iri d'aya biyu kama d'aya biyu ma kama d'aya 'ya'yan sarkin gari guda.

Sai bayan karfe biyar suka koma gida Asad yayi mugun gajiya ko part din Mami bai samu ya koma gurin su Aunty Fadilah ba suna parking ya wuce part d'insa bai tsaya huta ba ya shiga toilet yai wanka ya d'auro alwala domin lokaci kad'an ya rage a kira sallah saida ya shirya ya wuce masallaci da akai sallar magriba ma bai fita masallacin ba saida akai isha sannan ya koma part d'insa shifa a yau ma baici komai ba ko ruwa bai sha amma maimakon yayi kokarin cin abinci sai kawai ya zauna a parlonsa ya bud'e laptop ya fara aiki.

Jin karar doorbell yasa yad'au remote ya bud'e kofar duk zatonsa Aunty Fadilah ce amma sai yaga Ajeeb ya shigo yana kare masa kallo kafin yace.

"Asad wai kaci abincine a yau ko haka kake zaune"?.

"Mene damuwarka in naci in banci ba"?.

"Dole na damu saboda ni d'an uwanka ne kome zakai wai Asad dan jaraba baka gajiya da aiki kamar agogo"?.

Batare da Asad ya d'ago ba yace "to ko agogon ne"?.

"Oho waya sani amma da alama shi d'in ne tunda naga rashin hankalin naka yayi yawa".

"Ajeeb fice min anan".

"Bazan fita ba kasa a fitar dani" daina aikin Asad yai ya d'ago yana kallon sa zaiyi magana wayarsa tai kara bai kulashi ya d'aga ganin kiran Mai martaba ne magana yai masa wanda kawai amsa ya bashi da cewa to sannan ya rufe laptop d'in ko inda Ajeeb yake bai kalla ba ya fice dariya Ajeeb yai yana bin bayansa yace "wato yaron nan ka gama raina ni ko? Humm zan kama kane" shidai Asad bai sake nuna dashi yake ba kawai suka wuce 6angaren mai martaba kamar yadda ya bukaci suje.

Shaukiyyah tana bedroom d'insu a zaune taci wanka tayi kyau sosai Khaldiyyah Makiyyah harda Khimiyyah suna gefenta da sauran yan Mata a dangin Sultana Shafi'ah da suka zo kallonta Khaldiyyah keyi tana daukar ta a photo cike da burgewa tace.

"Shaukiyyah na taya ki murna Allah ya sanya alkairi burinki ya cika kin auri prince Ameer nima Allah ya taimakeni ya karkato min da hankalin Annur kaina ko na daina shan wahalar soyayya".

Murmushi Shaukiyyah tai tana kallon ta tace ''karki damu Khaldiyyah kamar yau ne insha Allahu zaki auri prince Annur".

"To Allah yasa Shaukiyyah amma ni gabadaya na karaya da lamarinsa ne kullum kara nesanta kansa da soyayya yake saidai banace ba ko hakan wata manufar ce dabam amma nikam gaskiya maganar Allah ina matukar son prince Annur har cikin raina".
Chapter 117 · 0% Book details