← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 145

Sashe 134

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asab baiyi magana ba ya mi'kawa Isham box din yana cewa "duba'' kar'ba Isham yayi ya bud'e yana kallon yawan dollars d'in takardar kai ya d'auka yana karantawa shima baisan sanda ya zabura ba yana cewa.

"Kenan zargi na ya tabbata Clarah ce ta sayar da ita wa wata kasar kan bala'i amma gaskiya ta raina ma mutane wayo" rufe akwatin Isham yai yana kallon Asad yace...

"Buddy yanxu a ina zamu sameta karma ace tasan mun san itace ta gudu ta ruwan sanyi zakai mata magana ka boye fushin ka".

Cije lips Asad yai zuciyarsa ta cika tayi dam tsananin fushi ne kawai bayyane a fuskarsa da'kyar Isham ya shawo kansa ya d'aga waya ya kira Clarah farko bata d'aga ba sai a na biyu ta d'aga muryarshi normal ya tambayeta inda take tazo yanzu zasuyi magana yana so zata lura da Amatu ne jin abinda yace yasa murna ta rufata hankalinta ya kwanta ta d'auka ko ganewa yai itace Sir David ta kalla tana cewa.

"Muje kar na'ki zuwa yayi zargin wani abu ina so nabi a huce wajen kashe Amatu yadda zanga ya Asad zaiyi idan aka wayi gari babu ita".

Murmushi Sir David yai yana mi'kewa yace "dole zai ha'kura ya zaiyi gashi ke kuma kinyi masa nisa kinga auren mu gobe zamuje a d'aura shi in an jima zamuje mu bugo invitation card mu raba amma kafin nan yanxu idan munje ki fad'awa Asad da baki kina gayyatarshi muga ya zaiyi"?...

Dariya Clarah tai suna shiga mota sukaje hospital d'in ta tambayi wani soja Mayesh Boun yace mata Asad baya nan mamaki ne ya kamata ta sake kiransa cewa yana Ina ne yace tazo gidanta yana harabar gidan gabanta ne ya fad'i jikinta yad'au rawa da'kyar ta samu ta shiga motar suka tafi gidan yana tsaye a harabar gidan da sauri ta fito cikin tashin hankali ganin murfin kofar parlonta a 6alle ga Isham acan gefe shima ya kasa ya tsare yasa muryarta na rawa tace.

"As asd Asad lafiya meyasa faru"?..

Takardar hannunsa ya d'ago mata cikin tsantsan fushi da 6acin rai yace "I said no to you so many times Clarah did I wrong you in any way akan nace bazan aureki ba shine kike kokarin kasheta kika sayar da ita fad'a na dake ne bada ita ba I think ni nace bazan aureki ba kuma ba itace ta hana ni ba ra'ayina ne Clarah baki cancanti zama matata ba gaba da baya ni Asad da matsoraci bana had'a tafiya shiyasa koda lokacina bana baki kin jahilci kanki kin yaudari kanki kin cuci kanki kin rud'i kanki sannan kin wahalar da kanki karshe kece da fad'uwa zaki tashi a tutar babu''?.

D'ora hannu Clarah tayi aka jin abinda yace ta shiga uku ya akai ya sani waye ya fad'a masa tasan yau kasheta ne Asad kawai bazai ba a Marshalls islands.

"Asad dan Allah ka saurare ni banyi haka dan na 'bata ran..........

Zazzafan marin daya kifa mata ne ya hanata karasa maganar da take 'kara ta saki me qarfi cike da azaba ta gigice bata ganin komai sai duhu baya tai wurrr zata fad'i ya fisgota yana sake wanketa da wani marin a zafafe yace.

"You messed with everything and in the end with righteousness too? no one else must face the injustice that was meted out to you bayan duk abinda kika aikata yanzu kike tunanin zan yi miki uziri"?.

Sha'ke mata wuya yayi yana kallon cikin idanuwanta da sukai ja suka fiffito babu ko d'igon tausayinta a ransa har jini ke fitowa ta hancinta wata irin hankad'a yayi mata wacce ya wullata can gefe kamar iska ce ta kaita hucin tsananin 6acin raine yake fitowa daga zuciyarshi yana kallon yadda ta yun'kura da'kyar ta mi'ke tsaye tana dafe kanta ga hawaye yanata gudu muryarta na fita qasa qasa tace.

"Asad kayi hakuri abinda ya faru wallhi kishin kane yasa na jahilci kaina Amatu batai min komai na fansar da ita nasan nayi kuskure ka bani dama na gyara na cuci kaina"?.

Cikin tsawa yace "Righteousness may be devoured by evil😡 but it will prevail in the end🔫" yana rufe baki ya sakar mata bullet ya harbeta.🙊

Ihu mai 'karfin gaske Sir David yayi yana kallon Clarah data fad'i 'kasa ko motsi batai ba da gudu yaje yana girgiza ta ganin bata numfashi ta mutu yasa a fusace ya d'ago yana huci ya mi'ke yana cewa "Asad meka aikata kenan ka kasheta fa akan wanne dalili taya? Bayan sharrin dakai mata haka bai isheka saita kasa tabar rayuwar dan mugunta kayi bincike ne kafin ka zartar da hukunci wallahi Asad bazan yarda saina daukar mata fansa daga jin wannan maganar taka shiryawa kai dan kawai ka tsaneta kayi mata haka".

Wani kallo Asad ya masa mai firgitarwa ba tare da yace masa 'kala ba ya juya yana kallon Isham daya taho da sauri ganin Clarah a kwance ta mutu ga alamar harbi nan a cikinta yasa ya fahimci Asad ne ya kasheta domin Isham ba'a gabansa akai komai ba ya shiga gidan yana sake bincike ganin yadda Sir David ya gigice yana girgiza Clarah wacce itakam ta riga ta mutu bai nuna alamar komai ba ya mi'kawa asad wani file yana cewa "kalli da idonka" kar'ba Asad yai yana dubawa cike da tsananin mamaki ya kalli Isham wanda ya masa alama da ido cewa eh haka ne abinda ka gani wani irin juyi Asad yai cikin bad temper ya dam'ki wuyan Sir David dake tsaye yana kallon file din da Isham ya kawo jikinsa na rawa saboda a hannun doctor su na 'karya da suka d'auko daga wani asibitin sirri da sunan shine docton sojoji wanda zaiwa Amatu allura yake amma ya akai yazo hannunsu kenan yanzu Asad zai fahimci harda shi a cikin masu son kashe Amatun yana cikin wannan tunanin yaji Asad ya dam'ke shi ya matse masa wuya da mugun 'karfi tsakanin fushi da 'bacin rai dan'kare a fuskarsa Isham yana tsaye ya hard'e hannu yana kallon yadda idanuwan Sir David suka fito waje sukai jaa sai 'ko'karin 'kwatar kanshi yake ya kasa tun yana da sauran kuzari har jikinsa yai laushi ya luuu alamar zai fad'i hankad'a shi Asad yai yana yar'bar dashi a 'kasa kusa da inda Clarah take kwance sannan ya d'aga bindiga ya sakar masa bullet shima ya bita domin maci amana baida amfani soja irinsu masu zagon kasa basu da wani muhimmanci maimakon a had'u a ya'ki abokan gaba saidai su fuskanci yan uwansu suna neman rage jami'ansu akan su nemi a kawo zaman lafiya sauyi da lumana saidai su nemi fitina".

Juyawa Asad yai yana kallon Isham sai sannan ya samu damar magana "what condition is she now fatan baka bari ya mata allurar ba"?.

Kai Isham ya girgiza yana cewa "sorry buddy, she is in critical condition na baro Mayesh Boun acan yanzu ya kamata kazo muje".

Yana gama rufe baki Asad da sauri yabar gurin domin ya duba halin da Amatu take ciki doctors ne da yawa a kanta suna iya bakin kokarin su dafe kansa dake sara masa yai tare da juyowa yana kallon Isham daya karaso ya sake bashi wani file d'in mai photon Clarah qato a jiki.

Wani gurgu da yazo wucewa me qafa daya ganin photon yasa ya tsaya yana cewa "yalla'bai wannan ita ce".

Da alamar tambaya Isham yace "ita ce me ka santa ne"?.

Kai ya d'aga yana kallon yankakkiyar qafarsa yace ''itace shekarun baya tazo da mota ta buge wata soja da zata shiga airport nima garin ta juya ta gudu ta bugeni".

Da mamaki Isham yace "Subahanallahi kenan Clarah ce ta kashe Yusairat ma saboda kai"? Ya karasa maganar yana kallon Asad wanda yai shiru baice komai ba kai Isham ya jinjina yana cewa.

"Gaskiya Clarah taci amana sosai kuma ta cancanti hukuncin da ka yimata muje mu samu wannan shegen doctor d'in shima yaci uwarsa".

Kai Asad ya girgiza "no Isham bazan je ko'ina".

"Amma Asad akwai Mayesh a gurin insha Allahu zai kula babu abinda zai sameta taho muje" bai magana ba kawai ya wuce suka tafi suna nemansa guri guri amma babu ko alamar sa a hospital din ga dukkan alamu ya gudu kai Asad ya jinjina yana cewa "Isham baya nan fa ya gudu idan ba muyi da gaske ba bazamu sameshi ba".

"Ok buddy muje to" Isham ya fad'a yana d'auko key din mota a aljihunshi shiga sukai suna fita a hospital din to amma ina zasuje ta ina zasu fara shiru Asad yai cikin tunani kafin ya d'auko wata yar karamar abu daya d'auka lokacin da Clarah ta fad'i abun ya kalla yana bud'ewa ya d'auko wata yar na'ura a ciki kallon sa Isham yai "na meye wannan"? Kai Asad ya girgiza "i don't know a wurin Clarah na sameshi but koma meye ai zan gani" had'a shi yai da na'urar motar yana kunnawa da mamaki yaga dukkan abubuwan da suka faru komai da duk wani plan d'insu kallon Isham yai wanda shima Isham d'in shi yake kallo da surprise a fuskarsa yace "me hakan ke nufi Clara tasan wannan 'kungiyar dama"? Kallon sar'kar Asad yai dakyau oh wato wannan ce sar'kar da Amatu take fad'a masa zasuyi Clarah ma tabbas tana tare da qungiyar kai ya jinjina yana "gashi dai ka gani na sake samun 'kwakkwarar hujjar bayyanawa kowa ita wacece ba jami'ar soja bace 'yar 'kunan ba'kin wake ce bata cikin sojojin mu ashe duk zaman da ake da ita zagon kasa kawai take da had'in bakinta ake kashe jami'an mu".

"Gaskiya ne buddy yanzu ka adana wannan nà'urar zuwa lokacin da Amatu zata farfad'o daga nan kowa yasan ka kashe Clarah da babban dalili ka rage iri ne".

"Eh haka ne Isham amma yanzu damuwa ta bai wuce na kama wannan tsinannan doctor ba kace kasan gidan saba"?.

"Eh can zamuje kenan"?.

Kai Asad ya d'aga "muje wallahi shima bazan barshi darai ba shima ba likita bane bai cancanti rayuwa ba likitan bogi ne suka d'ora ashe duk sojojin mu da yake dubawa kashesu yake"?.
Chapter 134 · 0% Book details