← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 145

Sashe 38

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da yaje gidan Adama tace masa ta bar gidan tun d'azu nan fa yaji ya susuce da sauri cikin azama ya juyo yana kalle kallen inda zai ganta can ya hangota tana cikin yaran anguwa suna wasa karasawa yai yana cewa "Indo na me kike yi anan zo mu tafi gida" d'agowa Indo tayi ganin ubanta yasa da gudu ta mi'ke tana zuwa ta d'afe shi tana cewa "baba" daukarta Balarabe yayi yana cewa "me kika zo yi nan"? Tana washe baki tace "wasa" "wasan kuma har nan? Indo na muje gida kinji" to tace tana rike hannunsa yana tafe tana masa zance suka zo wucewa ta gefen wata mace dake zaune tana sakin 'kosai a wani kofar gida kana ganinta kaga 'yar duniya dan hatta bakinta yayi bakin busa haya'ki taje tayi rayuwa a gurare daban daban tasan harka har ta had'u da wani mutum alhaji me kud'i ya aureta ta haifi yarinyar gud'a d'aya Bahijjah kamar gaske suna zama cikin lumana rana daya ta aika shi lahira ta washe dukiyarsa tayo awon gaba da ita da yake ta haram ce tuni tasa tagaba ta 'kurmushe kamar yadda wuta ke cin audiga ta wajen inda take sana'arta Balarabe ya biyo daidai zai wuce cikin shishshigi ta d'ebi 'kosan a leda tana cewa.

" 'yan mata ga kosai".

"A'a ta gode kibar kayan ki" Balarabe ya fad'a batare daya kalli inda take ba kara matsowa tai tana cewa "haba kai kuwa ba kyau maida hannun kyauta baya dan Allah ka bari ta kar'ba" dakatawa Balarabe yai cikin jin haushin ta da sauri ta mi'kewa Indo ledar tana cewa "ki gaida mamanki" to Indo tace kafin ta sake magana fuuu Balarabe ya bar gurin da kallo ta bishi tana cewa wacce ke zaune kusa da ita.

"Ke Meroh kinsan wannan mutumin? A ina yake"?.

Dariya Meroh tayi tana gyara daurin kwalin kanta ta soke shi a gaban goshi tana cewa "meya faru kike tambaya"?.

Daidai Balarabe yasha kwana ya 'bacewa ganin ta tace "ba komai kawai kallo d'aya nayi masa naji ina son sa" zaro ido waje Meroh tayi "kai 'kawata kin d'ebo da zafi kinsan waye wannan har kikace kina son shi bazai ta'ba aurenki ba".

Jiki a sanyaye tace "meyasa kika ce haka"?.

Kai Meroh ta rausaya "saboda ba mata a gaban sa matar sa daya ce kamar rai sunanta Dalah yana matukar kaunar ta ita da wannan yarinyar da kika gani a hannunsa dan haka gara tun wuri ki saukewa kanki wahala".

Kai ta girgiza tana sake kallon hanyar daya bi tace "Meroh bazan iya ba ina son sa kuma dole saina aure shi ta dad'i kota akasin haka da yardarsa koda 'kinsa da amincewar sa ko da karfin hatsi nidai saina aure shi Meroh kiban shawara tun bayan rasuwar baban Bahijjah ban kara ganin Wanda ya kwanta min a rai ba sai shi yanzu ya zanyi"?.

Ta'be baki Meroh tayi "ya zakiyi kuwa Asabe bayan hakuri kece 'bakuwar zaman garin nan amma mu da bamuje ko'ina ba munsan waye balarabe ba mutum ne mai wargi ba baya daukar raini ki taka a sannu".

Shiru Asabe tai na d'an lokaci tana tunani kafin ta d'ago tana kallon Meroh tace "to amma kawata babu wata hanya da zanbi ya soni ko mu 'kulla mu'amala daga nan na samu kusanci dashi"?.

Zaro ido Meroh tai "ki samu kusanci da wa"? Lallai kam Asabe kice mu tanadi geron waina dan wallahi kinji na rantse miki idan kikai kokarin cusa kanki da masa shishshigi tofa maganar gaskiya wata rana saidai ki jiki a kabari dan balarabe mutum ne mai zafi".

Tsaki Asabe tai tana cewa "duk zafinsa yayi ta banza akwai inda zan kai shi a gama min dashi wanda sai yadda naga dama zan juya shi kamar yadda ake diban ruwa a randa yayin da ake jujjuyata yadda ake so kin gane".

Dariya Meroh tayi "humm Asaballiye tawa na gane mana wato akwai wani abu da kike shirin yi ko akwai wata muguntar da kike son had'awa".

Kai Asabe ta jinjina tana cewa "tabbas Meroh ina son wannan mutumin kuma duk rintsi saina aureshi kota tsiya kota arziki ko yana so ko baya so dan ban ta'ba ganin abu ina so na rasa ba kuma bazan fara akan sa ba a yau din nan basai gobe ba zan fara shiri na domin cika buri na idan naga dama nan da sati sai an daura mana aure dashi" sauke ajiyar zuciya Meroh tayi tana cewa "shikenan 'kawalliye romon gwada mukam 'yan rakiya ne idan abun ya tabbata" "ai ko zai tabbata Meroh ki zuba ido saina baki mamaki kinsan Marka aminiyata ce tasan lungu da sa'kon bokaye ita zan nema" Asabe ta karasa maganar tana sake kallon hanyar da balarabe yabi ha'ki'ka tana kaunar sa bazata cuci kanta ba zata samu mafita ita dai Meroh kallon Asabe kawai take tana tausayawa matarsa domin tasan wace Asabe indai ta 'kwallafa ranta akan balarabe bazata kyale shiba saita samu ta aureshi.

Ganin yadda gabadaya lamarin Ilyah ya cakud'e yasa hankalin Ramatu yai matukar tashi kuma ta kasa gane alhaki ke bin Ilyan na rashin biyayyar da yaiwa Baffah sai kawai ta fara zaton ko Salamatu ce tayi wa Ilyah siddabu dan haka ta dauri niyya ta tafi gurin boka da akai mata kwatance yana cikin wani ba'kin daji abun tsoro tafiya miliyon kasiran kafin ta isko inda yake.
Tsoro ne ya mamaye Ramatu jin wani irin 'kugi da gurnani kamar ta shiga tsakiyar dajin da namun dawa suke rayuwa jikinta ne ya fara rawa jin an daka mata tsawa yasa taci wani uban tuntu'be ji kake kifff tass ta kifa kasa wata tsawar aka kuma sakar mata wanda a wannan karon Ramatu yanke jiki tai tana fad'uwa kasa a sume wata ba'kar mahaukaciyar dariya aka saki saiga wani irin abu me dubu ya dira a gaban Ramatu tare da fara gewaya ta zuwa wani lokaci saiga Ramatu an d'aga ta sama ana jijjiga ta wanda wahala tasa tilas ta farka tana bud'e idonta ganin ta a sama ana majujuwa da ita yasa ta fara ihu tana kururuwa lokaci guda kuma tai tsit ta kame guri daya jin an daina juyata kasa ta le'ko taga shakka babu tayi nesa da 'kasa yanzu ya ita ya zatai tana cikin wannan tunanin taji an fisgota da mugun 'karfi yuuuuu tayo kasa ji kake tim ta daki 'kasa 'kara ta saki tana kiran "wayyo Allah na shikenan na mutu na lalace........................

"Rufa mana baki!!! Me ya kawo ki nan"?.

Jikin Ramatu nata kakkarwa ta mi'ke da sauri tana shirin zubawa a guje aka kuma jawota baya 'kiiiii tasss ta kuma kifawa nan guri ya kaure da kukan jirajirai zuwa wani lokaci kuma aka daina kukan sai dariya tuni Ramatu ta yada kwalin kanta dan gyale da takalmi tuni sun dad'e da fad'uwa.

"Ku kamotaaa ku ri'ko ta yau zamu sha jinin ta ku tatsilo mana ruwan idonta ku zu'ke kwakwalwarta😲🤣".

Jin haka yasa Ramatu wage baki cike da tsoro zata kurma ihu aka daka mata tsawa "durkusa anan ki sunkuyar da kanki kasa ki rufe ido idan kikai kuskure zaki hallaka" jiki na 'bari Ramatu ta durkusa tana runtse idonta da 'karfi.

'Dif taji gun yayi shiru kamar babu halitta mai rai daga baya taji iska da guguwa mai karfin bala'i tana kad'awa sai kuma taji saukar abu kusa da ita timmm ga tafiya diff diff anayi jikinta rawa yake sosai zuciyarta na bugawa tana nadama da danasanin zuwan tanan.

"Bud'e idonki kiyi kalloo👻".

Da sauri Ramatu ta bud'e idonta ganin wasu kalar ba'ka'ken halittu tai suna yawo jikinsu duk gashi idanuwan su jawur ga babbansu zaune kamar dutse a kafe kato dashi ya gwalalo mata ido ha'koran sa za'ko za'ko.

WASH ALLAH NA GASKIYA FANS NA GAJI 😞 TYPING 📲 DA WUYA GA AZUMI SAI ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH ZAN DORA MUKU INSHA ALLAHU.

Mrs Al'ameen Ahmad ce mai tambarin yma dutse Jigawa new world new life and new style 👌 sabuwar duniya kuzo ku kallo dad'i yana Jigawa garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa 😜.

MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

TYPING 📲 {sat, Apr12 11:59AM}
YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

💎ME KAMAR SARKI 💎

WhatsApp no:+234 8160983083

MRS AL'AMEEN AHMAD CE MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY 💃.

🍇 ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU 'YAN UWANA MUSULMAI BARKAN MU DA SHAN RUWA🥛 FATAN ANYI SALLAH LAFIYA🍇🌹.

*****
KAMAR YADDA NA ALKAWARTA CEWA IN ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH DA RAI DA LFY ZAMU D'ORA LITTAFIN ME KAMAR SARKI 👑 ALLAH YA KAWO MU DAN HAKA KU MATSO MU TAFI TARE DAN YAU ZAMU SHIGA DUNIYAR NISHADI ZAMU KWASHI FARIN CIKI YADDA YA KAMATA 😂🙈😁.

Wannan page din naka ne d'an uwa rabi jiki inai maka barka da sallah fatan alkairin Allah ya kai maka duk inda kake kaida ahlinka d'an mutan kanawa.
YUSUF KING__SKEEBOY👑👑🎧🎧 SHATAN RAPPER🎶🎶 REAGEA RP RAP DA KUMA HAUSA HIP HOP YAYAN ZAINAB (KALAR CAMERA) 📸 DA NA'IM.
🎤🎼🎙️🎧🎹🎵🎸🎶🎷🥁🎻🎺 )(*(*()*)*)( 🌹 )(*(*()*)*)(

27~AL-BASIR
The all seeing
28~AL-HAKAM
The judge

14~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mutta'kinah.

🌄 CARICATURE ND WREAK🌄
Episode 27_28
Kuka Ramatu keyi kamar ranta zai fita cikin wahala da gajiya ga wani masifaffan tsoro daya gama cikata na ganin wannan baka'ken halittun da'kyar take sauke numfashi tayi zaman dirshan a kasa.

"Ku kamotaaa naceeeeh".

Jin abinda wannan mummunan ba'kin dodan ke cewa yasa Ramatu zunbur ta mi'ke a gigice ta fita da gudu a gurin ko waiwaye babu a tunaninta suna binta sai datai nisa sosai ta fita daga dajin kafin ta waigo ganin babu kowa yasa taja burki tana haki ta tsaya tare da goge gumi ta kalli gabas ta kalli yamma har yanzu tana cikin dajin amma tasan duk tsiya ta tsira domin ta baro wajajen wadannan halittun.

Ganin abu tai ya dira gabanta tare dayin girgiza sai taga wannan katon dodon nan muryar shi kamar saukar tsawa yace.

"Hummm saiii yanzunn kika karaso? Barka da zuwa nan ma fadar muceeeeh".
Chapter 38 · 0% Book details