Sashe 137
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Tofa amma Asad maganar kamar bata dad'i bace naga kamar hankalin ka a tashe? Kaga zonan zauna kusa dani ka samu nutsuwa" ta fad'a tare da kamo hannunshi kamar yaro ta zaunar dashi kusa da ita tana shafa gashin kansa tare da karanta masa addu'a zuwa wani lokaci ta kalleshi.
"Asad me ya faru kamin bayani yanzu".
Bai kallo saitin inda Amatu take zaune ba ya ri'ko hannun ta a firgice Amatu ta kalleshi Sam ba ita yake kallo ba mamaki ne ya kama Mami lokacin da Asad din yasa hannun Amatu cikin nata muryarshi da saukin fushi yace "Mami duba min hannunta".
Kallon mamaki Mami ta sake masa tana cewa "Asad kana lafiya babu komai a hannunta kalli kaga" kai ya girgiza yana sake kama d'ayan hannun Amatun yace "Mami duba min zaki tana da ciki" ba Amatu ba hatta mami saida ta zabura tana zaro ido tace "ciki dai na haihuwa Asad kake nufi"? Kai ya d'aga jikinsa na saki na tunanin taya Amatu zata samu ciki a ina shikam ya yarda da ita d'ari bisa d'ari kuma bazai iya zarginta ba".
Fuskar Mami fal da fara'a ta ja Amatu jikinta tana rungumeta tace "allhdllhi bi ni"imatihi kai masha Allah babyn Mami kace na kusa samun jika daga gareka aure yayi kyau"? Shidai Asad shiru yai yayin da Amatu ta samu kanta cikin tsananin tashin hankali muryarta na rawa tace.
"Ciki wai na haihuwa" dariya Mami tai "eh mana jewel cikin haihuwa ko kema da yake jikin ki bakisan kina dashi ba"?.
Tab Amatu jitai hankalin ta ya sake tashi fiye da d'azu kawai sai hawaye shar shar da mamaki Mami tace "jewel bakya son haihuwa"? Kai Amatu ke girgizawa cikin kuka tace "wallahi mami bani da ciki" dubanta Mami keyi sama da kasa tace "kamar ya baki da ciki bayan gashi Asad ya fad'a" har lokacin Amatu kuka take tace "wallahi bani da ciki Mami bansan waye ya fad'a masa ba" maida kallonta kan Asad Mami tai "to waye ya fad'a maka"?.
"Ajeeb ne".
Baki bud'e Mami tace "Ajeeb dai shi taya ya sani daga dawowarku harzai fara"?.
"Cewa yai wai shi doctor ne kallo d'aya ya mata ya fahimci tana da cikin wata uku".
Idon Amatu kamar zai fito waje ta dora hannu akan cikinta da yake shafe ta kuma fashewa da kuka cikin lallahi mami tace "kinga jewel kiyi shiru bari Ajeeb din ya dawo muji meye gaskiya daga saukar ku ya daga muku hankali.
"Mami nifa abinda na kasa ganewa yadda nayi miki alkawarin zan tafi da ita matsayin 'kanwa haka ne ban ta'ba bari zuciya ta rinjaye ni na karya alkawarin dana dauka ba amma Ajeeb muna zuwa yace min haka ai abin da mamaki".
Tofa itama mami a wannan lokacin data fahimci mai Asad din ke nufi ta gane cewa dai babu wani abu daya ta'ba shiga tsakanin su ya akai Amatu ta samu ciki harna tsawon wata uku innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zabure mami tace "subahanallahi Asad me kake son cewa ne wai wani abu bai shiga tsakanin ku matsayin ma'aurata ba"? Kai ya d'aga mata alamar eh tashin hankali ne ya sake lullu'be Mami tana kallon Amatu tace "jewel meke faruwa ne meye gaskiyar al'amari"?.
Numfashin Amatu har sama yake yana sauka da'kyar tace "wallahi Mami ku yarda dani nima ban sani ba" kan Mami ne ya d'aure Asad yace babu wani abu tsakaninsu ita tace bata sani ba ya abun yake ganin ba mafita yasa ta d'aga waya tana kiran Ajeeb cewa koma me yake a hospital din ya dawo gida yanzu tana nemansa.
Suna zaune da kamar minti talatiin ya shigo ganin su kawai yadda kowa yayi da fuska ya fara dariya wata uwar harara Mami ta sakar masa tana cewa "taya kasan jewel nada ciki harka fad'awa Asad kasa sun rud'e alama ka gani ko kuwa me maza yanzun nan ka gwada ta mu gani"?.
Murmushi Ajeeb yai yana kallon Asad daya zuba masa ido kafin yace "kiyi hakuri Mami nifa da wasa nake masa tsokanarsa nake wallahi bata da ciki" wani kallo Asad yai masa yayin da Mami ta jawoshi kusa da ita tana rike masa kunne tace "kace da wasa kake tsokanarsa kake amma ta irin wannan hanyar kasa sun bar nutsuwar su daga dawowa maraban kenan"?.
"To Mami Asad d'in ne da rainin hankali daga nayi masa magana saiya shareni wai suna hakan an dad'e ba'a had'u ba maimakon yai farin ciki daya ganni saiya had'e gira bakiga yadda yayi da fuskarsa ba kamar biri yasha lemon🍋 tsami shiyasa nace masa haka nima na rama".
"Hum to ai ka kyauta saika tashi ka koma hospital d'in dama dalilin kiran kenan" mi'kewa Ajeeb yai yana kallon Asad yace "bari na dawo zamu karasa maganar mu Asad" ko kulashi Asad baiyi ba Ajeeb da yake shirin fita yace "Mami kinga irin shariyar tasa da nake fad'a miki ko"?.
"To mezance Ajeeb kayi tafiyarka dan Allah ka barsu su huta" murmushi Ajeeb yai yana fita sai sannan hankalin kowa a cikinsu ya kwanta mi'kewa Asad yai shima ya fita domin yaje ya gaisar da Mai Martaba da kuma me girma Alhussain acan fad'ar ya samu yaran Ameer 'yan biyu kamarsu d'aya Hassan ana ce masa Aman Hussain suna ce masa Aiman yaran har sunfi shekara zama yayi yana gaishe dasu harma ya kar'bi yaran ya jima kafin ya tashi ya fita daga nan part d'insa ya wuce domin ya huta.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE
Thanks so much really appreciate it godiya sosai sosai godiya.
TYPING📲 THURSDAY SEP5/24 YUSRAH MUSA ABUBAKAR.
👑ME KAMAR SÄRKÌ👑
ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASSOCIATION 💫 Home of hospitality and harmony🤙.
Gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya🙅🏼♀️.
75~AZZAHIR
The Manifest
76~AL-BADIN
The Hidden.
02-Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mujahidina.
🌄AFFRONT ND DISTASTEFUL🌄
Episode 75&76
🏕️'KAUYE🏕️
_____Ganin lokaci yana ta kurewa shekara ba d'aya ba har yanzu Adamu bai samu ya karasa gyaran gidansa ba yasa Ilyah zuwa kofar gidansu akai masa sallama da mahaifinsa ya fito ganin Ilyah yasan kwanan zancen dan haka suna gaisawa yace.
"Dan Allah ka qara ha'kuri ya kusa kammalawa saura qarashe ne ya rage masa baranda ce zaiyi yayi filasta shikenan ya gama".
Tsaki Ilyah yai yana cewa "kallum saidai a qara masa lokaci dan jaraba har yanzu ace bai qarasa abinda yake ba wallahi ka jini nan bar ganin kun kai komai zan iya dawo muku da tsiyarku dama wata uwar kuka kaimin na rasa uban me Salma ta gano a gidan nan naku take son shigowa kuba arziki ba ba kyakkyawar sutura ba amma ta li'ke sai Adamu ban sani ba ki asiri kukai mata domin idan na mutu ku samu dukiya ta 6angaren ta"?.
Cikin takaicin irin maganar wulakancin da Ilyah yake fad'a masa ya d'ago yana kallon sa a ace Adamu zaiji shawararsa to daya ha'kura da yarinyar nan kodan wulakancin mahaifin ta ba ita kad'ai bace budurwa a qauyen nan.....................
Katse masa tunani Ilyah yayi da cewa "kayi shiru ina magana nifa bari kaji dama bason had'a zuri'a nake daku ba saboda gudun shafar talauci ina tsoron talakan mutum talaka? Humm abin gudu ne🤔 shiyasa tun farko nayi baya da Habubakar kaga kuwa tunda na gujeshi uban waye bazan gudaba? bazan amanna 'yata ta shiga wani hali ba dan haka ka gargad'i dan'ka ya tabbata komai zai ri'ka dire Mata bangaren kayan abinci basai ta nema ba ko rana d'aya taje neman abinci gidana saina d'ebo masa 'yan sanda kaji dakyau na fad'a maka sa'kona zuwa gareshi".
Kai mahaifin Adamu ya jinjina yana duban Ilyah da mamaki saidai yasan zaiyi fin haka ma saboda kamar wanda yake kud'in ganye yanzu haka kud'ad'e suke shigo masa ta ko'ina ba 'kak'kautawa shiyasa yake ganin yafi karfin komai amma yana tsorace masa duniya sanda zata juya masa baya a lokacin ne zai gane yayi kuskure amma yanzu kome za'a ce masa bazai ta'ba fahimta ba sauke numfashi yayi domin marar abu baya zuciya tunda Adamu nason yarinyar babu yadda zaice kowanne wulakanci zaiyi masa haka zai shanye tunda shi yake nema a gunsa.
"Kayi hakuri Ilyasu zan kira Adamun zanyi masa magana duk abinda muka tattauna dashi zan sameka saina sanar maka".
Ilyah yana hura hanci irin ba mutuncin nan yace "Kai na soke maganar auren nan dama dan'ka ba sa'an auren 'yata bane ka gane me za'ai da talauci dan masifa na baku lokaci fin shekara biyu amma ya garara had'a gyara gida kamar wanda yake gyara gari guda mtswwww to wallahi zan sake baku dama daya itace ta karshe kacewa dan'ka ya dawo idan ya'ki zan d'aura da wani aikin banza sai kace a kanku aka qare talauci kamar kune Habubakar gidan fatara to nidai na fad'a maka kuma zan sake fad'a maka ka kira danka ka sanar masa sa'ko na idan ka'ki saidai kuji d'aurin auren Salma da wani amma dai ba Adamu ba wad'anda su Hassan suke neman auren 'ya'yansu ma sai suga kamar bamu da kud'i shiyasa muke musu yawo da hankali munata d'aga ranar biki ta 6angaren mu baza kusa naji kunya ba ka gane lallai ka shedawa dan'ka abinda nace maka in yaga dama ya dawo in yaga dama yaci gaba da zama acan" Ilyah yana kaiwa nan yayi gaba sai masifa yake shiru baban Adamu yayi cikin takaici wato indai baka dashi a rayuwa ka shiga uku a gurin masu shin indai haka ne kuwa zai kira Adamu yace masa ya fasa auren Salma domin wannan yadda Ilyah yake furta musu kalmar talauci kamar shi ya baiwa kansa arzikin yasan koda ace anyi auren bazai barta ta zauna ba zaice za'a kashe masa 'ya a saketa bari ya shiga gida kawai ya kirashi ya dakatar dashi hankalin kowa zaifi kwanciya.
Uhm su Indo 'yan Osun ana can an koma Irfan yayi girma abinsa shekara uku ya iya magana Dauda sabuwar rayuwa ys bud'e musu acan suke zuba soyayyar su yanzu ma qaramin ciki ne da ita tun yana wata uku Dauda ya fara tara abubuwa a gurin maman niseh batare da sanin Indo ba so yake yayi mata bazata.