← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 145

Sashe 125

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kullum da kalar training d'in da yake bata kuma tana da kokari sosai har a ransa yana yabawa da karfin zuciya da jarumtaka irin tata domin baiyi tunanin zata iya jurewa ba sai yaga tabashi mamaki wata biyu yayi full yana bata kyakkyawan horo na musamman haka da aka zo 6angaren koyon harbi farko saidai ta ri'ke bindigar shi kuma ya tsaya ta bayanta ya d'ora hannunsa akan nata ya saita mata abinda zata harba daga baya data fara koya ita kad'ai zai jera mata balloons🎈 da yawa ta ri'ka saitasu tana harbarsu d'aya bayan d'aya yazo ya koya mata saita abu daga nesa ka harba da koyon hawa dutse ta igiya da tafiya a cikin ruwa tafiya mai nisa a ruf da ciki kawai abinda ya rage mata shine ta iya saukowa daga jirgi ta igiya da saukowa daga sama a jikin saukar lema wannan kuma yasa a ransa idan sunje Marshall islands ya koya mata acan domin bazai tafi batare da ita ba tunda dole akwai taimakon da zatai masa bayan haka ga muradin ta na zama soja itama.

Har gurin Mami yaje akan tafiya da ita domin yana so zai koma duk da dama ya kira sir murtih Jonah yayi masa bayanin abunda ya tsayar dashi shiyasa ma aka bashi lokaci harya dad'e haka suna zaune su biyu daga shi sai Mami yake ce mata.

"Mami mun gama magana da wannan yarinyar tare da ita zan tafi dan ta cika burinta kuma Nima zatai min amfani sosai".

Kallonsa tai cikin rashin gamsuwa da zancen sa tace "gaskiya Asad bazan bari ka tafi da yarinyar mutane har wata kasar ba ka sata aikin soja sannan kace baza taje gida tayi sallama da mahaifanta ba akan me? Me kake nufi"?.

"Mami ba wani abu nake nufi da hakan ba kawai dai nace baza taje bane haka na yanke".

"Aiko indai haka ne baza taje tayi sallama da mahaifanta ba saidai kaima cikin biyu ka za'bi d'aya"?.

"Me kenan Mami"?.

Gyara zama Mami tai tana fuskantar sa sosai tace "na farko zan amince ka tafi da ita ne idan ka bari taje tayi sallama da 'yan gidan su, ko kuma bazataje sallama ba zata bika kamar yadda kake so amma saidai tana matsayin matarka za'bi d'aya"?.

Da sauri Asad ya girgiza mata kai yana cewa "a'a Mami wannan hukuncin yayi min tsauri dan Allah ki janye wannan maganar baza taje gidansu ba sannan ni kuma babu mace a raina babu ita a cikin tsarina idan xanyi aure sai nayi retire maybe dan girman Allah Mami kar kice a'a nayi miki alkawari babu abinda zai sameta zan kula da ita kamar yadda na tafi da ita zan bata komai take bu'kata bazan bari ta shiga wani hali ba ina tare da ita zanyi mata irin ri'kon da yaya yake yiwa 'kanwarsa Mami please ki amince min na tafi da ita matsayin 'kanwa gareni zaifi zaman lafiya a wajenmu gabadaya dan Allah"?.

Shiru Mami tai tana kallon sa da mamaki fal ranta wai matsayin 'kanwa? 'kanwa fa? Humm Asad yana da tsattsauran ra'ayi tasan tunda ya kafe a 'kanwar nan saidai suje a haka...........

"Mami bakice komai ba kin amince"?.

Kaita girgiza tana d'agowa ta kalleshi kafin tace ''ita jewel d'in kunyi magana da ita ta amince zata bika ne"?.

"Eh ra'ayin tane kuma ki tambaye ta ba tilasta mata nayi ba".

"Shikenan Asad ba damuwa Allah ya tsare Allah ya bada sa'a kawai shine fatana a gareku".

"Amin Mami".

D'an shiru Mami tai cikin tunani can tace "kuma kaje kunyi magana da mai nasara ne ko kuma kawai gaban kanka kakeyi''?.

"No Mami dashi na fara yin magana kafin nazo gurin ki kuma shima ya amince".

"Ok shikenan to Asad Allah yayi muku jagora".

"Amin".

"Yaushe ne tafiyan"?.

"Yau".

Zaro ido Mami tai ''haba Asad yau kuma ka bari ta gama shiri mana".

"Mami me zata shirya"?.

"Kayan sawarta".

"No baifi kala biyar zuwa shida ba inta d'iba zaiyi mata shima ba lallai tayi amfani dasu ba tunda aiki kadai zamuyi".

"Eh duk da haka ta tafi dasu dai Asad ai mutum bazai dauwama yana aiki ba ko agogo batirin yana sanyi"?.

"Ok kisa mata guda biyar d'in ta shirya yanzu zuwa karfe biyar na yamma zamu wuce"?.

Kai Mami ta d'aga "ok shikenan to Allah y tsare".

Amin yace yana mi'kewa ya fita itama Mamin tashi tayi tana shiga part d'in da Amatu take a zaune ta sameta a falo da laptop a gabanta uhm carborn copy d'in Asad ce wannan yarinyar bata gajiya da aikin itama ganin Mami ta shigo yasa ta daina abinda take tana rufe laptop d'in zama Mami tai tana kallonta tace.

"Jewel kinyi magana da Asad akan tare zaku tafi ko"?.

Kai Amatu ta d'aga " eh Mami ai yau nema".

"Eh na sani da amincewar kine"?.

"Eh nice na amince domin har za'bi ya bani cewa idan naga bazan iya ba na zauna a gida kawai babu komai nikuma nace a'a zan iya".

"Ok shikenan jewel Allah ya kiyaye ki tashi ki za'bi kayan da zaki tafi dasu kamar kala shida kada ki d'ebi masu nauyi sosai tunda naji yana maganar sunfi zama da uniform".

"To Mami aini na gama had'a kaya tun d'azu ma".

D'an zaro ido Mami tai tana kallon ta da murmushi tace "oh kice har koyi zafin kamar yadda yace wato har kin gama shiri to indai haka ne zuwa anjima ki shirya zan kaiki part d'in Sultana Fatima kiyi mata sallama da gurin mai nasara sai muje part d'in Sultan Alhussain shima kiyi musu sallama kafin lokacin tafiyar naku yayi".

Cikin ladabi Amatu tace "to Mami na gode Allah ya saka da alkhairi".

"Amin jewel kici gaba da aikin ki karki damu aike 'yata ce halak malak kedasu Ajeeb duk d'aya ne kinji ko bana ta'ba banbamta ku".

Cikin girmamawa da so Amatu take kallon Mami tana matukar sonta ta d'auketa tamkar 'yar data haifa kulawar da take nuna mata ko mahaifanta iyakaci kenan takai maqura.............

Mi'kewa Mami tai tana cewa "ok jewel kici gaba da aikinki ni bari na tafi".

"To Mami nagode".
Fita Mami tai yayin da Amatu ta mi'ke tana shiga bedroom domin ta sake shisshiryawa kar sai anzo tafiya ta tsaya neman wani abu.

Yadda Mami ta fad'a mata karfi hud'u bayan sallar la'asar ta shirya ta rakata ko'ina suka bita da fatan alkairi banda Makiyyah data shiga d'aki ta rufe kanta tana kukan ba'kin ciki da tashin hankali ganin har Asad ya gama burkicewarsa akan auren ya sauko da da itan aka d'aura ma zai ha'kura ya kar'be ta gashi zaiyi nisa zai tafi tare da Amatun mezai iya faruwa kafin su dawo itakam ta shiga uku kila mutuwa zatai.
K'arfe biyar suka bar masarautar zuwa iya airport Mami bata bari sun tafi ba Saida ta ri'ke hannun Amatu tasa a cikin na Asad ta jaddada masa ga amanarta ya ri'keta da gaskiya karya cutar da ita sau uku tana maimaita masa sannan ta bisu da fatan alkhairi.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE😘.
💦See you next time nagode.

Yan uwa mu dage never stop learning because life never stop teaching.

Y~M~A MŪHÅMMÃD CE maman little Zaran Aunty.

TYPING 📲 Fri, Sep 2/24 8:20AM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋.

👑Me kamar sarki👑

💫ANNURI WRITER'S ASS💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya🙅🏼‍♀️ ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai 'ya'yan ta.

STORY AND WRITTEN👇🏼
✍️ Yusrah Musa Abubakar Mrs Al'ameen Ahmad ce.

DEDICATED TO MR HÂUSÅ EBOOKS📚🤝 Shuraihu Usman CEO Faunder of taskar novels.

Ya cikar cikakku alhamdu ka d'ayantu kai kad'ai Allah yake so ANNABI s*a*w..
🌹Baya goya marayu mai kai dakai ya rayu dakai kan kowa ya wayu dan kai ka koyar da gayu abin da bai yuwu ya yuwa da an gano ka za'a ji ana so ANNABI s a w.
💓Annabi ka had'u had'add'e uban had'add'u mai bada kyau take a had'u mai qara doki ya dad'u mai dad'a wada ya dad'u yama za'ai ka fad'u sunanka ne kyau kai muke so ANNABI s a w....

💓 💖 💓 💖 💓 💖 💓 💖
💖 💓 💖 💓
💓 💖 💖
💖 💓
💓 💜ANNABI💜 💖
💖 💛S*A*W💛 💓
💓 💖
💖 💓
💓 💖
💖 💓
💓 💖
💓
🕌🕋🕌
HÄPPY JÜMÄ'ÄT MÜBÄRÄK
To all Muslims in the world it's Friday don't forget to recite suratul Al-khaf, I am so blessed to be a Muslim alhamdulillah.

Manzon Allah (*(saw)*) u're unique first nd last u're the answer of every question u're the mirror of our life u're the light of every darkness u have no limits ya rasulullah🥀🌷 S A W.
Annabin mu saw yayi mana nasiha cewa👇🏻
1️⃣MUSO JUNA
2️⃣MU RI'KE GASKIYA
3️⃣DA AMANA
4️⃣ MU RAYA ZUMUNCI
Hanya ne na ALJANNAH ma'kiyin zumunci bazai kusanci ceto ba😞😔🤦🏻‍♀️.

71~AL-MUQADDIM
The Expediter
72~AL-MU'AKKHIR
He who puts far away.

35~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin wa ala jami'il ambiya'i wal mursalina wa ala mala'ikatul mukarrabina wa ala ibadallahis Salihina min ahlil samawati wa ahlil ardina wa alaina ma'ahumu ajma'ina bi rahmatika ya arrahman rahimina wa sallallahu ala sayyidina muhammadin wa ala alihi wa sahabihi wa sallaman ajma'ina.

🌄 STRUGGLE🌄
Episode 71&72
_____Marshall islands jirgin su yana sauka suka fara fitowa Clarah wacce ke tsaye tad'au wanka tana jiran Asad dan da'kyar tai barci tsabar zumud'i da farin cikin zai dawo haka ta kwana rungume da fulo tana murmushi hango Asad tai tafe cikin taku yasha ado yasa glass gashin kansa sai kad'awa yake sakamakon iskar ta akeyi cike da tsantsar zallar 'kaunar da take masa ta tareshi bakin ta ya'ki rufuwa tun bai iso inda take ba ta gaggauta su had'u da sauri ta karasa hannu ta bashi tana cewa.

"U're welcome Asad barka da sauka ya hanya ina mom nd dad d'ina suke ina sisters and brothers fatan ka barosu lafiya"?.
Chapter 125 · 0% Book details