Sashe 97
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka raba komai d'ai d'ai buta cokali plate sai tukunya ita kuma duk wanda shine da girki ya dora aiko a take faka-faka suka d'ebi 'bantaran bulo suka kafa murfi A'i sai murna ake anzo birni za'a fara shan shurba bakinta kamar zai yage😂 sai kallon shinkafar da ake gyarawa take tana hasko yadda za'ai mata cin wulakanci na an dad'e ba'a had'u ba😃 ga kayan miya🍅🌶️ a gefe abinka da maison bajinta harda d'an nama🥩 kad'an ya sayo asa cikin miyar samayar da mugun yawu na shekara da shekaru.
Satin su Malam Habu d'aya da zuwa Kano Alhaji Musa ya sameshi akan yayi karatun boko ya kawo masa takardarsa ya bashi aiki a companyn sa yace a'a baiyi boko ba sai iya ta arabic yayi amma 'yarsa guda d'aya tayi makaranta sosai kwanan nan ta karasa karatunta saidai bangaren aikin soja ne ko zai taimaka mata ta cika burinta Alhaji Musa yayi mamakin jin wannan furuci wato a cikin yaransa yan mata akwai wacce take son yin aikin soja ya jinjinawa jarumtarta saidai gaskiya bashi da hanya dan haka yacewa malam Habu bashi da wata kofa dazai taimaka mata amma zai jarraba kokarin sa a kanta wacce irin sana'a Malam Habun yake sonyi yace masa kowacce amma banda mai kud'ad'e da yawa saboda yana tsoron ta'ba kayan mutane sakamakon anyi masa baiji dad'i ba jin haka yasa Alhaji Musa ya d'auki adaidaita cikin wacce yake bada haya ya bashi tare da sharad'in duk wata zai ri'ka bashi dubu ashirin Malam Habu yayi murna sosai ya kuma yi masa godiya haka ya dawo gida fara'a fal fuskarsa haka iyalansa nasa ma sukaita binsa da addu'a ta gari da fatan arziki Allah ya d'agashi a ranar daya fara fita yawon haya a ranar ya sayo asusu wanda za'a rika sa kud'in idan ya dawo daga hayar an cire na abinci sauran saiya saka a ciki.
Kullum haka yakeyi kuma alhamdulillah yana samu sosai tuni suka fara murmurewa kuwa domin suna samun komai akai akai yanzu babu abinda suka rasa wanda rabon da suga haka tun kusan shekara ashirin baya😥 sai yanzu aiko haka suka tashi a tsaye suka dage masa da addu'a abu d'aya suka tambaye shi yace a'a wato suna son suyi sana'a wai ta wanke wanke a gidajen masu kud'i shikuma ya nuna bai amince ba tunda yanzu yana da yadda zaiyi ya ciyar dasu ya tufatar dasu babu wacce zatai dole suka ha'kura amma sun so ya barsu domin zasuyi samuwa.
Saidai kuma ana cikin haka ne Alhaji Musa yazo masa da bukatar dan Allah a cikin yaranshi ya bashi d'aya kullum zata ri'ka zuwa tana taya matarsa girki da 'yan abubuwa domin 'yar aikinta tayi aure ya d'auko mata wata ita kuma bata da hali sata take musu suka koreta gashi aikin gidan Hajia ita kad'ai zai mata yawa kuma tana zuwa office.
Jin uzirin da Alhaji Musa ya kawo masa yasa malam Habu ya amince tilas badan yaso ba saidan halaccin dayai masa amma baya kaunar yaga yaransa a waje musamman da suka kasance mata ga gari ba nasu ba 'katon birni mai girma sosai da fad'i.
A ranar daya amince tun daga ranar yace Asma'u ta fara zuwa amma bai yarda tana zuwa ita kad'ai ba ta dauki Jamila ko Aisha ko Amatu wani ya rakata duk da suma yanzu sunada abunyi domin basu daina d'inkin hula ba kowa tana tsantsara d'inki kamar inji ne yake bugata ba hannu ba.
Amatu da Aisha basu jure raka Asma'u wajen aikinta ba Jamila tafi rakata har itama ta samu Hajiya tace tana wanke wanke da moping Asma'u aikin abinci a wata tana biyansu kud'i mai d'an kauri babu laifi tunda itama tana dashi mijinta nadashi gashi basu ta'ba haihuwa ba tunda suke basu da d'a sai d'an ri'ko saurayi gud'a daya yana can a Canada yana karatun likitanci sunansa Saleem (d'an lelensu🤭) d'an gidan 'kanin Alhaji Musan ne domin Alhaji Musa ba yaro bane zaikai sa'an Malam Habu saidai sakamakon shi jikinsa ba wahala babu damuwa da tashin hankali ya tashi cikin kud'i yayi girman kud'i idan ka kalleshi ka kalli malam Habu xaka rantse da Allah Malam Habu ya bashi shekara goma.
Matarsa ma haka Hajiya Aisha zatai sa'ar Binta ko A'i amma batafi Saude ba kuma mace ce mai sakin fuska wayayyiya tana da kirki kuma tana sakewa su Asma'u idan sunzo haka zasuyi ta hira harda dariya kamar 'ya'yanta tana sha'awar taga ta samu d'an kanta amma shiru harta ha'kura ma sunyi yawo kasashe iri dabam dabam domin a bincika musu lafiyarsu ita da Alhaji Musa kuma abinda ya basu mamaki ko'ina sukaje abinda likitan waccan kasar ya fad'a musu to wannan likitan ma shi zaice sunyi tunanin basa haihuwa ne amma bincike ya nuna a'a suna haihuwa basuda wata matsala kawai Allah ne bai basu ba su kara ha'kuri yana sane dasu shiyasa suka kwantar da hankalin su tun daga yaye da suka amshi Saleem shikenan suka rikeshi basu mayar dashi ba suma iyayensa basu damu ba tunda suna da wasu yayan sai suka bar musu shi ya taso cikin daula da gata sosai ga shagwa'ba kamar mace.
Su Asma'u suna morewa a gurin Hajiya Aisha kuma suna jin dad'in zama da ita koda ace bata nan yanzu ta amince musu suje gidan su Mata aiki hatta mai gadin gidan yasan da zamansu sannan koda ma ace bata nan yadda ta saba idan sun gama aiki zasu taho 'ka'ida ne saita ciko musu kuula kullum da abinci sun taho dashi to koda bata nan zasu d'iba su kimtsa mata komai sannan su dawo gida.
Umm😊 sosai ahlin gidan malam Habu sukai 'bul-'bul har wani d'an glowing sukeyi balle dama gasu sun biyoshi sunfi kama dashi haka suke farare tarrr kamarshi babu wacce tai kama da uwarta a cikinsu duk siffarsa ce dasu gashi sunzo birni yanzu sun fara wayewa su fara sanin abubuwa wanda ada ko zaman shi a duniya basu sani ba ga kuma d'an shafe shafen mayuka irin masu sa kyan jiki wanda zai gyara musu fata sunayi harda su Binta🙃 tun tuni dama sunyi tashin komad'a kowa ya ciko ba wata rama ba damuwa ba kwanan fargaba.
Sunfa zo Kano a sa'a domin bayan duk wannan alkhairin yanzu Alhaji Musa ya sai musu makaranta da yake ya tambayi malam Habu ko sunyi karatu yace eh iya Junior suka tsaya d'aya ce tayi karatu sosai bayan Senior ma ta d'ora wata shiyasa yace su barshi haka tunda a qauye suke ba damuwa akai da karatu ba a haka ma yasha maganganu.
Shikam Alhaji Musa bai tsaya 'bata lokaci ba yacewa Malam Habu ainan birni ne babu wanda ya damu da wani kowa rayuwarsa yake cikin 'yanci zaman yaran haka bai kamata ba gara kowa ta kara karatu koda kad'an ne kafin Allah ya kawo musu mazajen aure Malam Habu har rasa bakin dazai godewa Alhaji Musa yai su Binta ma har gidansa sukaje sukai masa godiya haka ya yanka musu forms suka fara karatu a Legal su uku Amatu da yake ta zarcesu kuma karatun ta ba irin nasu bane yasa tata makarantar dabam take ta kud'i da yawa ce amma haka Alhaji Musa ya biya musu kamar 'ya'yan daya haifa haka yake jinsu.
TOOFAA😲 ANA WATA GA WATA🤨 WANI ABU YA DANNO KAI😮 FANS MU LE'KA MU GANI👀 MENENE🤔¿¿¿??? ME YAKE SHIRIN FARUWA NE¿‽😟😑.
Ranar wata litinin da dare wajen sha biyu malam Habu yayi dare da haya wasu samari suka tareshi suka hau adaidaitar cewa ya kaisu gaida ashe sunsha sun 'kwale shi kuma baisan 'yan 'kwaya bane ya d'auke su harya kusa kaisu suka dakatar dashi ya d'auka fita zasuyi sai ji yayi sunce ya fice ya basu adaidaitar su tafi da ita ko su kashe shi da mamaki ya juya zaiyi musu magana amma sai yaga d'aya ri'ke da wu'ka d'ayan kuma bindiga ga sauran biyun sun zare masa ido tare da d'ora yatsunsu a baki alamar shiru🤫 kada yayi ko tari idan ba haka ba hummmmm yana ji yana gani suka turo shi waje suka fece da adedetar😵 jiyai hajijiya na d'ibansa yana ganin duhu da'kyar ya samu ya zauna yana kifa kansa zuwa wani lokaci jin ya dawo daidai ya mi'ke cikin wani irin yanayi yanzu daya zai kalli Alhaji Musa mutumin dayai masa halacci ya mayar dashi tamkar d'an uwansa na jini ya bashi komai ya yarda dashi fiye da yadda ake zato innalillahi wa Inna ilaihi raji'un😭 tsabar ba'kin cikin daya tsinci kanshi a ciki baisan sanda ya fara tafiya da kafa ba yana gani biyu-uku hudu-biyar idansa yayi dishi-dishi haka ya dawo gida jiki a mace ya tarar kowa idonsa biyu babu wanda yayi barci sakamakon rashin ganin dawowarsa kan lokacin daya saba amma a yadda ya shigo musu yasa duk suka mi'ke a rud'e suna tambayar sa lafiya basu sake gigicewa sun shiga d'imuwa ba sai lokacin da yace musu ya had'u da 'barayi su kar'be masa adedetar harzai taho gida suka tareshi ya kaisu Gaida ashe silar mashin din ya fita daga rabo ne.
Tabdijan sunyi salati sunyi sallallami harda masu kuka a ranar basu iya runtsawa ba kowa ya shiga d'aki dai kawai amma suna zazzaune akan taburmi ne har asuba sukai sallah gari ya waye ganin shiru bai dawo musu ba yasa sukai tunanin ko ya tafi gurin Alhaji Musa ne ya fad'a masa halin da ake ciki.
Batun malam Habu kam yaje kofar gidan Alhaji Musa yasa mai gadi yayi masa sallama dashi amma shima Alhaji Musan a yadda ya ganshi yasan ba lafiya shi har yayi zaton ko wani ne ya rasu a cikin iyalansa da sauri ya tareshi da tambaya.
"Malam Habu ina fata dai lafiya na ganka sassafe haka ga wani yanayi a tattare dakai meyake faruwa ne"?...
Sauke kai malam Habu yai cike da kunya da takaicin ta Ina zai fara fad'a masa ga abinda ya faru da adedetar sa zaiga sakensa bazai iya fuskantar sa da maganar ba har saida ya sake tambayar sa sannan da'kyar ya iya fad'a masa abinda ya faru har hawaye na taruwa a idonsa wajen bayani.