Sashe 70
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya Ameer yai yana cewa "tofa me zakai masa karfa ka jawo mana tashin hankali a gida idan kace dole yazo nasan zai iya yazo d'in kuma ya aikata abinda yace ya kasheta kasan Asad daya hauro zaku ri'ka uban dambe kamar wasu 'yan wrestling dan ma yanzu hankali yazo an girma an rage wasu abubuwan"?.
"Ba wani tashin hankali kawai kayi shiru kai kam Allah ya kaimu lokaci ya dawo wallahi saina bashi mamaki zan firgitashi idan yana jin kansa shi Aliyu Asad ne to zaisan nima Aliyu Ajeeb ba kanwar lasa bane😡 zan nuna masa isa da mallaka zai gane Allah da girma yake".
Murmushi Ameer yai yana girgiza kai yace "Uhm Ajeeb bansan meyasa ka zafafa al'amarin Khimiyyah ba bayan bakasan komai ba to kodai sonta kake"? Ameer ya karasa maganar yana kau dakai ya soma dariya.
'Dan bugarsa a baya Ajeeb yai yana cewa "so dai wanda na sani da zakacewa budurwa ina son ki shi kake nufi"?.
Kallonsa Ameer yai "eh shi nake nufi man".
Kai Ajeeb ya girgiza yana cewa "inaaa ko d'aya babu so tsakani na da ita saina 'yan uwankmtaka amma badai maganar aure ba kawai ina fad'a ne dason 'kwata mata hakkinta dan kaf cikinsu babu wacce tai min indai a matar aure ne bazanyi auren had'i ba".
"Humm mukwa kaga shi zamuyi".
Da mamaki Ajeeb ya kalleshi "da gaske kake amma wace a ciki"?.
"Kai wace kaga ta dace dani"?.
Shiru Ajeeb yai cikin tunani yace "a'a ai bansan abinda ke ranka ba kasan ra'ayi riga".
"Eh haka ne amma na baka za'bi banda Khimiyyah ka fitar min d'aya a cikinsu uku sai ayi tuwona maina ga abu a gida ai bazamu fita waje mu auro ba ko ya kace"?.
Kai Ajeeb ya jinjina "eh kun kyauta saidai gaskiya a cikin su kamar ina ganin Shaukiyyah tafi dacewa dakai".
Dakatawa Ameer yai yana cewa "da gaske tafi dacewa dani"?.
Kai Ajeeb ya d'aga "eh a nawa ganin ba".
"Ok Ajeeb dakata ka bud'e idonka ka kalleni dakyau ka za'ba min"?.
"Allah da gaske nake Shaukiyyah tafi saidai kai bansan wacce kake hari ba Makiyyah ce ko Khaldiyyah"?.
"A'a nima ta takan gaskiya dama tun tuni a raina Shaukiyyah na za'ba saidai na sake baka za'bi ne saboda ko zakaga wacce tafi dacewa dani sannan nifa ba sosai nake bambancewa tsakanin ta da Makiyyah ba tunda kaga kamar su d'aya".
"No akwai hanyar ganesu mana ai Makiyyah tafi Shaukiyyah fad'in fuska sannan ita kuma Shaukiyyah tafi Makiyyah haske da dogon hanci kai baka ta'ba lura ba"?.
Kai Ameer ya d'aga "eh gaskiya ban ta'ba ba saidai yanzu na tsaya na ganeta kar wata rana naji kunya garin kiran Shaukiyyah na kira Makiyyah".
Murmushi Ajeeb yai "idan ka kirata ba matsala ranar sai ayi hirar da ita a maimakon Shaukiyyan".
Kai Ameer ya jinjina yana cewa "to amma kai babu wacce tai maka a cikinsu ka za'bi Makiyyan shikenan tunda kaga ita Khaldiyyah Annur takewa naci dan ya'ki ne".
"Hum ai kasan Annur d'in sai a hankali muskili ne halinsu daya da Asad ko yana sonta bazai nuna ba saiya wahalar da ita Makiyyah kuma saidai ta auri wani a waje ita da Khimiyyah dan nikam wallahi bazan auri 'yar gida ba ba wacce taimin a cikin su".
Dariya Ameer yai "tofa wacece a wajen kake so"?.
Kafad'a Ajeeb ya d'aga "oho nima ban santa ba sai ranar da Allah ya had'amu".
"Ok baka da garanti tsayayya"?.
"Eh banda ita".
"Amma Asad fa"?.
Zaro ido Ajeeb yai "tab wannan mara hankali ubanwa zai d"au 'ya ya bashi😂 indai uban ba tsanar ta yaiba saidai ya had'ota da likafani dan maybe dukan dazai mata sai yafi na Khimiyyah itakam washe gari zai waye matane a 'kabari".
Da mamaki Ameer yace "meyasa kace haka"?.
"Ameer dubawa nai Asad d'an damuwa ne fiye da tunanin mai tunani shiyasa nace haka dan wallahi na tabbata duk yarinyar da tsautsayi ya afka kanta ta aureshi tofa ta kad'e har ganyenta dan abinda na lura Asad ko yana son mace ya aureta uhmm balle ace ta cushe ce me kake tunani zai faru shifa Asad babu aure a tsarinsa ya dad'e da fad'a min wannan"?.
Dariya Ameer yai yana kallon Ajeeb dayai masa magana da serious face yace "babu abinda zai faru sai alkhairi kasan da muna tunanin tsaurin sa zai iya bamu mamaki yayi sanyi".
"Me? Yayi sanyi fa kace Asad d'in tab gaskiya abunfa da kamar wuya a yadda Asad yake ace babu neman shawararshi babu sanar masa kawai yaji an d'aura masa aure subahanallahi ranar kuwa da anga tashin hankali wanda ba'ai zato ba iri-iri Asad Asad uhmm Allah ya kiyaye" Ajeeb na rufe baki Ameer ya kama dariya wato yana jin dad'in gidan su drama bata karewa.
"Kai Ajeeb da alama dai Asad yayi zafi da yawa yanzu dai mubar wannan maganar ya kake gani Shaukiyyah ce taimin meye shawararka"?
"Ok indai haka ne kad'au Shaukiyyan kunfi dacewa".
"Shikenan Ajeeb na gode amma dan Allah karka fad'a mata so nake sai an gama case din Asad da Khimiyyah hankali ya kwanta kafin zan bayyana kowa ya sani".
"Ok babu damuwa Ameer muje dare ya fara nisa kuma Mami da Annur nasan suna can suna jiranmu tunda ga abinda likitan yace idan Allah ya kaimu gobe darai sai mu Kira abba ansan abin yi".
Wucewa sukai babu wanda ya kara cewa wani abu har suka koma a zaune suka samu Mami tare da Annur suna hira zama sukai Ajeeb daya kasa durtsuwa abin nacin ransa yace.
"Wai Mami yanzu tsakani da Allah bazakiwa Asad magana yazo ya duba yarinyar nan ba idan fa ana ta 'barawo ayita mabi sau koda ace laifin Khimiyyah ne tunda Asad yake nuna halin ko in kula akanta dole mahaifiyarta taga kamar shine mara gaskiya kuma ko mahaifin ta kara yake da yake cewa koda ace kasheta yai haka za'ai shiru laifin d'an uwa daud'ar gora ne duk da haka ba dad'i yadda ya d'aukaki Asad a cikinmu tun muna yara komai yace d'an gidana komai d'an gidana bai kamata ya saka masa ta wannan hanyarba haba koni da muke uwa d'aya uba d'aya Asad yaiwa haka zanji haushi".
Kallonsa Mami tai tana cewa "zauna ka nutsu Ajeeb yanzun wani abune ya faru"?.
Zama Ajeeb yana sake kallon numbar Asad d'in kamar zai Kira sai kuma ya fasa yana mayar da hanakalinsa kan Mami yace "na kirashi yanzu bayan mun fito daga gurin doctor nace masa yazo ya duba Khimiyyah amma yana fad'a min wani bazai zoba idan kuma na matsa yazo saiya kasheta dama ba ha'kura yaiba tilas ya barta saboda ke kiji shi Mami".
Tashi sukai zasu tafi masaukinsu Mami tace "Ajeeb kaima kasan waye Asad basai na tuna maka ba dama da mai nasara yace a 'kyale shi daka barshi domin idan kace dole ta 'karfi zakabi shi Asad bazai bi umarninka ba".
"Amma Mami saina zuba masa ido har yana maganar ko yanzu suka had'u saiya kashe ta".
"Eh ya fad'a ne kawai babu abinda zai sake had'asu insha Allahu Ina fata yarinyar nan ta tashi kuma ta dawo cikin hayyacinta ayi komai a gama wannan tashin hankalin ya isheni Sultana Hadizah ba mace ce mai kara ba kuma ko ba haka ba ta ta'ba cewa mighty Alhussain yafi sonku saboda ku maza ne akan su Khimiyyah".
"Amma Mami wannan sa'banin fahimta ne ba haka abin yake ba".
Itakam haka ta dauka haka ne, Asad yasan abinda yake baya aiki babu lissafi saidai nayi mamakin miye ya had'asu nima bazance ba Asad ne yake da gaskiya ba dan yana d'ana fatana ta farfad'o kawai".
"Humm Mami Asad ai yasan baiyi daidai ba amma kana masa magana zai hayayya'ko kanka da fad'a kamar zai rufe ka da duka wallahi kwanan baya Mami da ina masa magana cewa yai zai saitani da bindiga daga inda yake ya harbeni".
Murmushi Mami tai "shi Asad d'in ne yace haka? Harbi fa"?.
"Kwarai Mami haka yace saboda yana gadarar shi soja ne yana da makami harda min barazana".
"Amma Ajeeb naga harbi a hannunsa ranar da abinda ya faru waye ya harbeshi ko Khimiyyan ce"?.
"No Mami ba Khimiyyah bace nine".
"Kaine ka harbeshi amma meyasa kasan abinda ya had'asu ne ko kana part d'in"?.
"A'a ban sani ba kawai Ameer ya tambaye inda yake nace rabona dashi tun a wajen sallar asuba amma bari naje part dinsa na gano zuwan danai na tarar yana dukanta kamar yana dukan 'karfe ko itace ya zage da dukkan 'karfinsa ya sha'ke mata wuya shine fa naje kiranku bansan meya had'o suba yanzu iya lallahi da magana mai dad'i nayi akan ya fad'a min laifin da tai masa ya'ki ki gwada kiransa ko zamuyi sa'a ya fad'a miki Mami nikam in son sanin gaskiyar abinda ya had'asu".
"Ai Asad bazai ta'ba fad'a maka ba komai zakai kuma dama u're highness yace min na 'kyale shi harsai Khimiyyah ta farfad'o shi kuma ya dawo dan haka abinda nake so dakai idan ka kirashi a waya ka daina masa wannan maganar tunda mai nasara yace a bari ta samu lafiya".
"To shikenan Mami Allah ya bata lafiya".
"Amin Ajeeb" sauran ta kalla tana cewa "Ameer Annur kuxo mu tafi Allah ya rufa asiri" mi'kewa sukai suna fita a hospital din zuwa hotel din da suka kama.
CAMEROON
Alhamdulillah yanzu kam alhaji Idris ya baiwa su malam Habu aikin majinsa a wani karamin ofishin dattawa kuma babu laifi ana biyansu albashi mai d'an tsoka har sun fara tara kud'i a gurin hajiya mammah mai abinci.