Sashe 135
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To gashi dai ka gani ba'a ta'ba kawo masa army ya barshi darai ba dukkan su allurar mutuwa yake musu waye ya sani sai yanzu da asirin sa ya tonu zaiwa Amatu".
"Hum yayi fatan kar mu had'u dashi dan saiya fuskanci u'kuba".
Daidai sun tsaya a kofar gate din wani gida Isham yace "wannan shine gidansa".
Da mamaki Asad yace "dama ka sani"? Kaiya d'aga "eh sau d'aya ba lokaci mai tsawo daya wuce lokacin da wannan had'ararriyar matsafiyar ta ri'ka mana 'barnar jami'an mu".
"Ok waye wancan a zaune"?.
"Me gadinsa ne".
"Da kyau muje" 'karasawa sukai suna tambayar sa ya tabbatar musu da yana nan ya dawo gida tun d'azu dan haka suka umarce shi daya shiga yayo musu magana dashi amsa musu yai yana shiga ya ganshi ya fito daga bedroom a firgice yana sake le'ka window ganin su Asad tsaye yasa ya soma tattara kaya gashi bada asalin fuskar daya sanshi ba har yayi tunanin bashi bane amma kuma yasan ba kowa a cikin gidan sai shi fad'a masa yai cewa wasu mutum biyu a waje suna son ganin sa jin abinda mai gadin yace yasa ya zaro ido waje jikinsa na rawa yace.
"Kace musu bana nan idan ka fita" yana fad'in haka ya d'aura doguwar igiya a jikin 'karfen window ya kama zai fita daga gidan.
Ganin haka yasa da gudu mai gadin ya fita yana fad'a musu abinda yake faruwa hankali tashe Isham yace "Buddy ya ka tsaya ya kamata muje mu tare sa guduwa fa zaiyi" Asad baiyi magana ba sai mai gadin daya kalla yana cewa.
"Shekararka nawa kanai masa gadi"?.
Jikin mai gadi na rawa yace "shekara ta biyar" kai Asad ya jinjina "kasan wani abu a tare dashi kada ka 'boye min ka fad'a min gaskiya saboda ya dad'e yana 'barna".
Kai mai gadi ya d'aga "eh nasan wani abu sunansa Mr badman daga yankin yurof yazo kasar nan wai a matsayin likita saidai maganar gaskiya fuska yake sawa ta wani babban likitan sojoji da akai da suka kashe shi sannan suka dau kwafin fuskarsa da bayan an nuna a TV cewa ya mutu har gurin jana'izar sa daga baya sai wannan munafikin ya bayyana da fuskarsa matsayin shine bai mutu ba sharri ne akai masa yaci gaba da likitancin 'karya yana kashe sojoji dayi musu allurar guba".
Yana kaiwa nan Asad ya dakatar dashi yana kallon Isham yace "muje" shiga mota sukai suna bin bayansa wanda suna yin nisa sosai suka fara hangoshi yana gudu sakamakon shi a 'kafa yake tsayar da motar Isham yai suna fita suma suka rufa masa baya da mugun gudu hankalin sa inyai dubu ya tashi a gigice yake furmutsawa cikin daji yana kuma waigowa ya kallesu sun kusa cimmasa yana shan wata kwana yaso 'bace musu saidai ba hali domin 'katon tabkeken kogi ya gani a gabansa mai ambaliya babu gurin wucewa ruwan har tsiri🌊🌊yake yana mummurd'ewa da kumfa ga manya manyan duwatsu a gurin dawurwuri yake yayi nan yayi can har suka 'karaso inda yake ganin idan ya bari suka kamashi zaisha bakar azaba wacce ba'ai tsammani ba sai kawai ya jefar da jakar dake goye a bayansa ya juya a guje yana zuwa yai tsalle ya fad'a kogin ya gwammaci ya mutu cikin ruwa da ya yarda su kamashi daidai sun karaso suma basu tsaya kallon wani yawan ruwa ko ambaliyar da yake ba suka afka ciki suna nemansa shikam ya fara shid'ewa bai iya ruwa ba amma a ransa ya ayyana gara ya mutu a ruwan da ya yarda su kamashi.
Yayi can kasa su kuma suna ta sama suna yawo ganin basu ganshi ba yasa suka fito suna sake shiri suka 'kara nutsawa can can 'kasan suma hangoshi sukai kusa da wani 'katon shark🦈 kallon juna sukai Asad ya masa magana cewa su far masa domin babban kifi ne sosai irin wanda yake had'iyar mutum but idan suka tsaya fad'a da kifin kuma shi wannan badman d'in zai iya mutuwa Isham ne ya cicci'beshi ya fitar dashi a ruwan sannan ya dawo saboda shark din amma dama badan shi suka zo ba sunyi tunanin zai kawo musu farmaki ne dan haka kawai suka fita daga ruwan.
Yana kwance sharkaf kamar gawa a 'kasa Asad ya duka yana danna masa cikinsa ruwa yana fita kamar bakin famfo🌬️ sannan ya bashi numfashi har ya d'an farfad'o ya fara motsi wani uban naushi Asad ya sakar masa wanda azaba tasa ya bud'e ido jikinsa na rawa ya kasa magana kuma dama mezai fad'a musu sunsan komai basu da lokacin sa kawai gwangwazarsa suka ri'ka yi suna tumurmusa shi a gurin d'auko jakar Isham yai yana zuge zif d'in ya zazzage kayan dake ciki zallar allurai💉💉💉 ne kawai a ciki iri iri kallon Asad yai yana cewa.
"Kalla duka allurai ne masu had'ari ya d'eba zai tafi dasu yaje yaci gaba da cutar da sojoji irin mu me ya kamata muyi masa"? Ya karasa maganar yana duban Asad.
Asad baiyi magana ba sai dukawa dayai ya fara cika 💉sirinjin da ruwan allurar yana ajewa saida ya gama ya kalli Isham yace "a jikinsa zai tafi yaji abinda suke ji" yana rufe baki ya fara d'auka yana soka masa a jiki sai 'karfen ya 'kule sannan zai matse ruwan kuma bazai cire sirinjin ba kawai zai barshi a haka yadau wani ya danna masa haka Isham saida suka soke masa jiki da sirinji kusan hamsin babu wanda suka cire sai ihu yake yana 'ka'kaji dan yasan ko a haka suka barshi bazai sake rayuwa ba kinkimarsa sukai suna cillashi a ruwan da yake ruwa tarr yake suna kallon sanda wannan kifin ya bud'e baki ya had'iyeshi numfashi Asad ya sau'ke yana cewa.
"Muje".
Juyawa sukai suna barin wurin suka koma inda Isham ya parker motar suka shiga zuwa hospital daga nan kai tsaye gurin Sir Jalalunddeen suka nufa tare da yi masa bayanin dukkan abinda ya faru da wannan likitan bogin da kuma Clarah ba Jami'ar soja bace ita 'yar le'ken asiri ce ga abubuwan daya samu a wajenta da kuma abinda ta aikatawa Amatu tare da had'in bakin David Sir Jalalunddeen da Sir murtih Jonah da sauran manyan shuganin soldiers d'in masu fad'a aji suka had'u guri d'aya dole akai meeting akan abinda ya faru sannan sun matukar jinjinawa wadannan zaratan mazan guda biyu (Isham Asad) sakamakon namijin kokarin da sukai wajen gano surrikan dake 'boye da kuma wannan likitan bogin badman.
Sati uku da faruwar haka yanzu jikin Amatu alhamdulillah yayi sauki tana amsa sannu kuma tana d'an magana sai sauran ciwuka kadan suka rage suma su warke tana zaune akan gadon marasa lafiya ta jingina bayanta da karfen gadon kafarta daya ta zurota kasa d'ayar ta tan'kwashe ta tayi shiru kamar me tunani Asad ya bud'o kofa ya shigo tare da Isham ganin ta a zaune yasa suka karaso Isham yana mata sannu maimakon ta amsa sai ta d'auke kai tana mayar da hankalinta kan Asad tace.
"Kace ya fice daga nan".
Da mamaki Asad yace "waye zai fice"?.
Da yatsa ta nuna Isham tana cewa "bana son ganinsa".
Kallon juna Isham sukai da tsantsan mamaki har Asad a ransa yana tunanin ko Amatun bata cikin hayyacinta amma bari ya gwada ta zama yai akan kujerar kusa da gadon patient yana sake qarewa mata kallo yace.
"Isham nefa ko baki gane shiba"?.
Kaita girgiza "na gane shi amma ai harda shi a wadanda sukai min haka".
Tun kafin Asad yai magana Isham yace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un Amatullahi ni Isham d'in kike magana akai ko wani ne dabam"?.
Had'e rai tayi "kai man harda had'in bakin ka Clarah tai min".
Sake zaro ido Isham yai zaiyi magana Asad yace "meyasa kika ce harda shi kin ganshi ne a wurin"?.
Kai ta girgiza tana cewa "a'a ban ganshi ba amma ai shine ya kira Clarah yace mata wai ambush ya ritsa dakai a dajin duk sojojin su dawo an samesu amma banda kai na shirya mun fita ya sake kiranta muna cikin dajin yace ba'a ganka ba mu tsananta bincike ko nayi qarya ba had'in bakinka"? Amatu ta karasa maganar tana kallon Isham wanda mamaki ya hana shi yace komai.
Tambaya Asad ya jefo mata "taya kika tabbatar da Isham Clarah take waya"?.
"Saboda sunansa ta ambata".
"No Amatu karki dau wannan matsayin hujja ba da Isham tayi waya ba da David ne shine ya kirata bayan sun hada plan d'in zata jaki ta kaiki wannan dajin amma Isham a ranar bana gari tare dashi muka tafi Canary islands kuma a wunin Isham baiyi waya da kowa ba aiki mukai acan bamu dawo Marshalls islands ba sai karfe goma na dare naje gurin Clarah a lokacin ina nemanki tace a yau bata ganki ba sannan Isham baisan ma kin 6ata ba saida na kirashi tare dashi muka shiga dajin muka sameki d'aure a gurin wasu yan ta'addar American suna shirin harbeki muka bud'e musu wuta a gurin su shida muka kashesu tare da Isham muka kawo ki asibiti tare dashi mukai binciken komai har muka gano Clarah ta sayar dake a gun wadancan mutanen da likitan karyar da suka d'auko zaiyi miki allurar guba duka shirin tane ita da David babu ruwan Isham a ciki haba Amatu ko kowa zai cutar dake a Marshalls islands na tabbata Isham zai kareki ina kika bar hankalinki da wayonki har kike nema da'ki'kai su rinjaye ki nasan ba haka kike ba keme zurfin tunani ce mai hikima kada ki bari ma'kiyan ki suyi nasara a kanki su had'aki takun sa'ka da masoyinki kin gane na yarda da Isham na amince dashi fiye da tunanin me tunani kuma kema ina so ki yarda dashi".
Sauke ajiyar zuciya Amatu tai cikin rashin jin dad'in gurguwar fahimtar datai masa tace ''dan Allah kayi hakuri na zargeka akan abinda ba haka yake ba".
Kai Isham ya girgiza "no vex Amatu karki damu ya wuce".
Kallon Asad ta kuma yi tana cewa "yanzu ina Claran take"?.
"Tana lahira".
Asad ya bata amsa kai tsaye d'an dubansa tai da mamaki tace "kamar ya tana lahira? Wai lahira dai wacce na sani mutum ya mutu"?.
"Eh na harbeta".