Sashe 2
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida Amatu ta kuma sauke numfashi kafin a hankali ta soma magana "Fatima mafarki nai wai gani a wani irin guri mai shuke shuke da kyan gani abin kwatance gurine daya wadatu da furanni kala kala ina sanye da alkyabba fara tarr nasha lalle kafa ta takalmi ne mai kyau da tsada wuya na da sar'ka ta gwal fuska ta da kwalliya a gefe da gefe na akwai bayi a baya na akwai bayi sun tsaya tun kafin na shigo gurin shi kuma tsaye yake a gaban wani guri wanda ruwa yake 'bubbuga an zagaye gurin da fulawoyi masu kyan launi a hankali na isa gareshi ta bayansa batare daya sani ba na taka wani dutse ina son nakai daidai tsayinsa daga bayansa nasa hannuna na rufe masa idanu wanda inajin sautin murmushin daya sakar min kafin ya rike hannuwa na yana bude idanuwansa ya juyo gare ni yana d'aga ni sama daga kan dutsen bai ajiye ni ko'ina ba sai a wani gurin shimfidadden carpet mai taushi wanda ya 'kawatu da kayan 'kawa na ado da abubuwan sha iri daban wanda ban ta'ba gani ba zama mukai yana rungume dani da muryar sa mai za'ki yace 'ina tsakanin sonki mata na banda kamar ki ina fata mu kasance tare' murmushi nai wanda yaja hankalin sa har ya shafo beauty points dinta daya lotsa sakamakon murmushin da nai bude baki nai zanyi magana ya sunkuyo yana d'ora bakinsa akan nawa kawai daga haka naji umma tana tashi na ban cigaba ba har bacci na koma bayan sallar asuba ko zan dora daga inda na tsaya amma a banza banyi mafarkin komai ba kinji abinda yasani farin ciki kuma ni kaina bansan dalili ba".
Sauke ajiyar zuciya Fatima tai kafin ta fara dariya tana cewa "gaskiya ne "kawata kenan mafarkin yarima d'an sarki kikai kuna tare kin zama matar sa"? Kai Amatu ta d'aga tana cewa "eh" cigaba Fatima tai "kai ai mafarki yana da abin mamaki sai kikaji dama gaske ne amma bamu sani ba ko zai zama gasken nan gaba" kai Amatu ta girgiza "taya zai zama gaskiya Fatima wannan gurin har na 'kare rayuwa ta bazan ta'ba ganin saba" cikin tsokana Fatima tace "to kika sani ko Sa'adu d'an gidan mai gari zaki aura" hade rai Amatu tai "kinga ki daina hada ni dashi kin manta kwanan baya uwarsa har gida taje ta tsiyata umma ai ko d'an gwal ne Sa'adu bazan aure Shiba" dariya Fatima tai tana cewa "nima da wasa nake Sa'adu da ba ganin girman manya yake ba kuma ba abun kunya bane ya ci mutuncin ki ubansa ya sani amma ya dauke kai da d'an wani ne da kinji bakinsa na shela 'kauyukan kusa damu ma sai sunji labari" tabe baki Amatu tai tana cewa "yabi dai a hankali duniya ta ishi kowa riga da wando wanda bai zota bama jiran sa take balle wanda yake cikin ta".
Tare suka shiga gidan daya kasance da mata uku Kowacce da aikin da take matar dake bakin rijiya tana jan ruwa ne ta juyo tana cewa "Ke Amatu ya na ganki ke kadai ina sauran a ina kika baro su Jamilan ga tallar abinci na jiran su"? Aje kwanon hannunta Amatu tai tana d'an kallon wacce tai mata maganar kafin tace "suna can basu gama aikin ba" sakin gugan A'i tai tana rike kugu tace "kuturun ubancan lallai malam da wargi yake wato ke da yake mai ido da kwalli ce kina kai abinci kika dawo amma tawa 'yar da yake bata da gata tana can rana na gasa mata baya wallahi bazai yiwu ba bari na dauko hijab na na bisu gonar na taho da 'yata da kaina" d'aki ta nufa tana bala'i "wannan muguntar har ina 'ya'ya mata ba maza ba a dauke ku aikin garada cikin rana ba wani amfanin arziki za'a samu ba dandani haukaci kafin shekara ya kare sai dai aune za a kashe min 'ya da aiki to wallahi bazata sa'bo ba".
Ganin ta saki gugar ta fad'a ga babu mai ruwa a gidan yasa Saude data fito daga d'aki tace "haba A'i amma dai baki adalci ba bafa mune mukai miki laifi kika saki guga ta fad'a yanzu dame zamu debi ruwan"? Cikin masifa A'i tace "oho miki ban sani ba damuwar kice kina da ruwa ko baki dashi bai shafe ni wannan ba matsala ta bace taki ce" cikin 'bacin rai Saude ta shako hijab din A'i nan suka fara dambe wanda ya riga ya zame musu jiki idan da sabo sun saba da sauri wata mace ta fito daga wani wuri dake fitar da hayaki tana cewa "haba ku kuwa dan Allah kullum kuna cikin fad'a ko karnuka basa abinda kuke gashi abin takaicin babu ruwan ku da wai yaranku suna gurin suna kallonku kada ku zama haka wata rana zakuji kunya" ganin ko sauraron ta basayi yasa ta shigq tsakanin su tana raba su amma ina Saude ta gama tukuikuye hijab din A'i tana cewa "babu ruwan ki Binta ki kyale ni naci uwarta" a hasale A'i tace "kici uwar ki dai dan wallahi baki isa ki zage ni na kyale kiba saina zubar miki da wadannan rubabbun hakoran" a fusace Saude ta kuma shako A'i sai saukar duka kakeji tim tim suna dambe wanda gabadaya sun gama luguiguice Binta wacce take kokarin raba su amma ta kasa tsawa suka ji ta bayansu.
"Kaiiiii kaiii meye hakan"!!!!? Basu saki juna ba kowa na huci suka juya suna kallonshi rai bace ya karaso yana cewa "wannan wanne irin shashanci ne wai filin ya'ki kuka maida min gida da kullum sai kunyi fad'a kamar karnuka to wallahi bazai yiwu ba tun wuri ku gyara halayen ku kafin na dau mataki har yanzu bakusan waye malam Habu ba inaga saina tuna muku watakila kun manta bana son hauka da d'anyen kai".
Sakin A'i Saude tai tana huci tace "wai malam dan kawai nace............katse ta malam Habu yai "na tambaye kine meye abinda ya faru tsakanin ku na gaji da halin ku bana son jin komai yanzu kam ya isa haka ni ba shashashan mai gida bane dole ku canza nafi karfin gidana kusa tunanin ku guri daya".
Gud'a da shewa A'i ta rafka kamar zata cire hanci tana cewa "ayyuririiiii ayyuri yuriiiiii kai jama'a ikon Allah sai kallo wato kai a hakan daukar ka kake kafi karfin gidanka ko malam Habu mai carbi? To wallahi bari kaji tin wuri garama ka daina fad'a domin idan yan kauyen nan sukaji zasuyi maka dariya a baki ne kafi karfin gidanka wajen zakwad'i da zance amma ai ba wata tsiyar kake bamu ba zama 'kalli 'kalular da saidai mu ciyar da kanmu sisi kana bamu ne saidai ka zuro ido kana nema a gurin anji jiki wallahi anyi asara" ta karasa maganar tana shigewa daki tacigaba da masifa iri iri yayin da tabar malam Habu tsaye guri daya kamar an dasa shi dan bakin cikin maganganun data fad'a masa.
Kuka Amatu ta fashe dashi tana shigewa d'aki a duniya ta tsani jin ana cin mutuncin mahaifin ta zata dau Kowacce irin magana amma banda wannan A'i daga cikin d'aki tace "Jamila kizo ki fita da abincin nan kada muyi kwashe dama kune zanbi na taho dake wannan tsinanniyar ta tare ni akan na jefa guga a rijiya" sak Jamila tai cikin kunyar maganganun da A'i keyi tana kallon su Aisha da Asma'u a hankali tace "Aisha dan Allah kuyi hakuri" murmushin dole Aisha tai tana cewa "karki damu babu komai" dundu mai zafi Jamila taji a bayan ta a firgice ta juya A'i ta gani tana huci kafin ta bud'e baki tai magana ta rufe ta da duka tana cewa "suyi hakurin uban ki shegiya wacce kare ya lashewa kurwa nidai ba gado na kikayo ba mitsiyaciya" da gudu Binta ta fito jin dukan bana karewa bane tazo tana janye A'i dake d'irkar Jamila kamar ta samu jaka tace "haba A'i dan Allah yanzu wannan dukan da kike mata bakya tsoro ki tara mata jini a ciki me tai miki baki barta da yunwa da gajiyar aiki ba kinzo kina sake dora mata wani ciwon" hura hanci A'i keyi tana hararar Jamila dake kuka kamar ranta zai fita tace "wallahi kadan kika gani indai juninki a saranci zakici na jaki a guri na sarai kinsan hali na" ta karasa maganar tana kai mata wani dukan da sauri Binta ta tare cikin takaici tace "wai dan Allah A'i meye hakan"? Hannu A'i ta d'aga "kinga Binta ba ruwan ki ina ce 'yata ce koma me nai mata ki 'kyale ni" shiru Binta tai tana kallon A'i cikin mamaki kafin tace "Allah ya huci Zuciyar ki" d'ago Jamila tai tana cewa "kinga Jamila daina kuka maza dauki baho akwai ruwa a randa ta jeki diba kiyi wanka kinji" kai Jamila ta d'aga tana goge hawayen fuskarta kafin ta wuce Binta ma barin gurin tai yayin da A'i taja kujera ta zauna tana masifa wanda har makwafta suna jiyo ta.
Wucewa d'akin sa malam habu yai bai kuma furta wata kalma ba suma su Aisha d'akin su suka shiga domin su huta gajiyar su ganin yau Saude batai musu abincin saidawa ba haka Jamila ta shirya tadau abincin saidawa ta fita har lokacin bata daina share hawaye ba Wanda saida ta sake shan matsa a d'aki A'i tana mata gargadin karta sake ta dawo mata da kwashen abinci.
Da sallama Binta ta shiga d'akin malam Habu Wanda yake kwance akan wata gajiyayyiyar 'yar katifa mai yanayi da tabarma ya rufe ido kamar mai bacci jin sallama yasa shi budewa tare da tashi zaune yai shiru kana ganinsa kasan cewa yana cikin matsananciyar damuwa ko ba'a fad'a maka ba aje kwanon hannunta Binta tai tana zama a gefensa tace "malam ga abinci" ganin yai shiru bai amsa mata ba tace "malam dan Allah kayi hakuri ka daina sa damuwa a ranka kada hawan jini ya kama ka arziki da talauci duka na Allah ba wanda aka haife shi da kud'i kowa a duniya ya samu a duniya zai barshi mai rai baya fidda rai da rabo".