← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 145

Sashe 67

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Biki yayi biki haske ya gama haskawa a wajen kid'ane mai mugun 'karfi yatshi kamar kunnen mutum zai fice tsabar 'karar tai yawa Amatu da su Maryam suna gurin harda su Aisha Asma'u da Jamila sun zo balle iyaye 'kirjin biki su Safiyah da Aunty umma su maman Asraf sune akan gaba suna rawa 'ya'yansu sunai🤭 Binta dai dasu A'i suna gefe suna kallon abinda yafi karfinsu suna mamaki su abun saiya zama sabo a gurin su anyi bajinta an raba kyautuka na fad'a a gurin humm Safiyah tayi kokari.

Har dare yai sosai ba'a basu ankara motoci da yawa sun tafi wasu ma babu mutane ga guri ya d'au duhu hankali tashe Amatu tace.

"Maryam wai me muka tsaya yine kalli fa babu kowa daga mu sai masu dije kuma suma tafiya zasuyi dan Allah ki Kira ys Ahmad idan bazai samu damar zuwa ya d'auke muba ya turo mana mota".

Shiru Maryam tai cikin tunani da rashin madafa tana kallon su tace "kuzo muje" ta juya zata fara tafiya Amatu ta dakatar da it's "muje ina Maryam date nefa"? Amsa Maryam ta bata suna kokarin fita tace "eh aina sani zan Kira ya Ahmad amma gara mubar wajajen nan haka baki gani ba masu dijen kamar marasa gaskiya sai kallonmu su d'ayan harda murmushi suna fitowa ta dialing numbar wayar Ahmad tana kiransa yana d'agawa tace.

"Ya Ahmad an baro mu acan fa babu mota ka turo a d'auke mu".

Daga can 'bangaren cikin fad'a Ahmad yace "azo a d'auke ku duk da uban me kuka tsaya yi har aka watse"?.

Kallon Amatu Maryam tai kamar zatai kuka "tace dan Allah yanxu ba lokacin tambaya bane la rufa mana asiri kazo ka d'auke mu daga baya saikayi mana fad'an" tana rufe baki d'ittt taji ya kashe kiran kallon su tai jiki a sanyaye tace.

"Bazai zoba gara mu tafi da wannan tsaiwar tamu anan bamu sani ba ko wani ya fake yana kallon su da asara gara gidadanci da zaman banza gara aikin kishiya ko zata zagi uwarka🤪😠 ku muje mubar wannan" aiko tana rufe baki suka d'eba a guje suka bar gurin tun suna tafiya da sauri har suka gaji suka dawo tafiya a hankali da azaba tai azaba duk cire takalman kafarsu masu tsini👠 sukai suna rikeshi a hannu sunaci gaba da tafiya gashin sun fahimci kamar binsu ake motar bayansu kamar daga gurin event din domin mai motar yaiwa Amatu magana bata kulashi yaiwa Ikram ita kuwa harda ashar ta sakar masa dama saida ya jinjina kai kafin yabar gurin da suke a modeling din daga haka basu sake ganin wulginsa ba Nabilah tsabar wuya tayi wuya har kuka take dayake dama ita raguwa ce ga shagwa'ba bata juri wuya ba.

"Haba ke kuwa Nabilah wannan kukan ba magani zai miki ba abinda yafi sau'ki kiyi shiru insha Allahu babu abinda zai samemu har muje gida" Amatu tai maganar tana ri'ko hannunta tare da kar'bar takalman data ri'ke da jaka duk dan ta rage mata kaya ko tayi shiru hatta gyalenta da d'an kwalin kanta suna hannu duk tabi ta burkice ganin motar tayi kusa dasu yasa ta kara fashewa da kuka tana cewa.

"Wayyo Abbana ka taimake mu zai kashe mu".

A fusace Maryam ta juyo tana cewa "wai ke Nabilah kinyi hauka ne ubanwa kike fad'awa anan d'in kin wangame baki sai kuka kike 'yar tselan uwa kawai wallahi idan baki rufa min baki ba saina fasa shi".

Cikin jin haushi da gajiya Ikram tace "Maryam 'kyale 'yar bura uba ta zauna anan d'in Abban yazo ya ceceta kinga nan da kwana uku sai muci waina aikin banza kawai mstttt haba dan masifa kin dame mu da kuka keba jaririya ba waye bai gaji ba ya danne saike ce fallalliya harda kiran Abba ai mu kuma daga sama muka fad'o bamu da uba shiyasa bamu kirashi yazo ya cecemu ba saike ko na sake jin bakin nan".

"Haba dan Allah kuwa wannan tai mata wannan tai mata dame zataji da gajiya koda jarabarku"?.

Harara Ikram ta sakarwa Amatu tana cewa "to uwar iyayi ban sako dake ba bana son shishshigi ga da wacce nake idan kuma bazata iya yin shiru ba saidai mu raba tafiya tunda duk wani harkar 'kauyanci ta iya".

"Baza'a raba tafiya ba amma dai ku 'kyale ta gaskiya takurar taku tai yawa irin haka da a gida d'aya kuke wannan ai saiku sa ta rame keda Maryam hum'um".

"Ke rufe min baki ina ruwanki ne a tunani da Nabilah nake magana ta bada ke ba dan haka karki sake shiga ciki" Ikram na rufe baki Amatu tace "idan kinyi da ita kamar kinyi dani ne domin yar uwata ce kuma jini na ke bari fa kiji baki isa kice zaki fad'a min magana na 'kyale kiba never in history kin gane"? Cikin 'bacin rai Ikram ta kalli Amatu tana shirin magana sukaga hasken motar ya haske musu idanu tuni suka manta da abinda suke kowa ta rud'e ciki ya d'uri ruwa ri'ke hannun Nabilah Amatu tai cikin jarumta tace "kada kiji babu abinda zai same mu insha Allahu zamu koma gida lafiya" janta tai suka cigaba da tafiya yayin da Maryam da kuma Ikram suka tsaya guri d'aya sun kasa gaba ganin har Amatu tai nisa yasa Maryam d'aga murya tace.

"A'a Amatu kada kibi tanan bakisan waye ba kizo mu canza hanya".

Amatu bata tsaya da tafiyar da take ba kuma bata juyo ba tace "wallahi Maryam bazan canza hanya ba tanan zanbi babu wani mutum da yake da ikon da zai cutar da d'an uwansa sai Allah yaso idan kuna iyawa ku taho mu tafi idan bakwa iyawa ku tsaya anan d'in ko ku canza hanyar mukam mun wuce".

A rikice Maryam tace "a'a Amatu kada kije kizo mubi tanan".

Ko juyowa Amatu batai ba suka yi gaba sunje daidai motar suka tsaya su Maryam na tsaye daga nesa jiki na'bari suna kallonsu suga abinda zai faru a mamakin su gani sukai sun shiga motar tabar gurin ihu Maryam tayi tana cewa "na shiga uku na lalace idan na koma gida ba tare dasu ba me zance waye wannan ya d'auke su kar suje a kashesu" ta'be baki Ikram tai tana cewa "a kashe sun mana uban waye ya kaisu ba kinyi musu magana ba sukai kunnen uwar shegu dake Allah yasa kidnapping d'insu akai naga ta tsiya" harara Maryam ta zafga mata "ba amain ba mai bakin tsiya insha Allahu babu abinda zai samesu" tsaki Ikram taja daidai wani mai keke napep yazo wucewa suka tsayar dashi suna ce masa Mopal-Base sannan suka shiga babu kud'i a hannunsu saida suka sauka Maryam ta kar'bo ta kawo masa a gajiye suka shiga bedroom turus suka tsaya suna 'kare musu kallon mamaki dama gida suka zo d'agowa Nabilah tai tana kallon su ganin yadda sukai yasa ta kwashe da dariya tana cewa.

"Sai yanzu kuka 'karaso? sannunku da hanya".

A fusace Ikram tace "ke dawa kike uban wa kikewa sannu"?.

Shiru Nabilah tai bata, bata amsa ba sai mi'kewa datai tabar d'akin tsaki Ikram taja tana cewa "zanci ubanki ne Nabilah kafin nabar gidan nan maza cigaba da shiga safgata jikin kine zaiyi tsami" kallon ta Amatu tai baki bud'e dariya na kamata tasan duk cikin jin haushin su taho sun barsu ne ga gajiya maida hankalin ta tai kan Maryam data cire kayan tana sauke numfashi tace.

"Sannunku da zuwa abinda bakwa so d'in dai zan fada sai yanzun kuka karaso"?.

A masife Ikram tace "oho miki kema ba'a sani ba".

"Kada Allah yasa ki sani idan ke nake tambaya" mutsssssss Amatu taja tsaki tana kallon Maryam tace "amma a abin hawa kuka zo dan naga da 'yar tafiya kuma kunyi saurin zuwa"? Kai Maryam ta d'aga "eh d'an napep muka tara badon haka ba ai da yanzu muna can a hanya to amma ke Amatu waye mai motar daya kawo ku"? Dariya Amatu tai cikin tsokana tace "wannan saurayin ne dayai min magana ban kula Shiba ya koma kan Nabilah itama ta share shi to shine ya d'auko mu" zaro ido Maryam tai "haba dai dan Allah da gaske bakuji tsoron ya sace kuba"?.

Kai Amatu ta d'aga "eh man ba wani sace mu dazaiyi bayan tare suke da ya Ahmad".

Da mamaki Maryam tace "kai dan Allah harda ya Ahmad amma baki mana magana kawai kuka shiga kuka tahowarku"?.

"Eh shine yace na 'kyaleku ku taho da sayyadarku ('kafa)".

"Humm ai shikenan ya Ahmad ya kyauta kuma wallahi tunda haka ne gobe bazanje G9 (jinayin) gidansa ba na kara shan wahala balle yana zumud'in amarya ko ta kanmu bazai bi ba".

Dariya Amatu tai "kai Maryam kema dai wallahi aiko zuwa gidan sa ya zama dole gobe 'karfe hud'u da rabi na asuba zaki tashi ki musu breakfast kuma kikai idan da dama sai kinyi seving d'insu kin jira sunci sannan ki wanke kayan ki mata shara sai ki dawo😂" ta karasa maganar tana kanne mata ido😜.

Ta'be baki Maryam tai tana cewa "tab wallahi ba inda zanje saidai driver yakai".

"Umm kuma idan momy ce tace kije fa ya zakiyi"?.

"Insha Allahu ma bazatace ba ki daina min fata".

"To ai shikenan bari nikam naje gurin umma na nasan yanxu batai barci ba" tana fad'in haka ta fice mi'kewa Maryam tai bayan fitar Amatu ta shiga wanka Ikram dake zaune akan stool tana chat ta ta'be baki tare da kunna voice tana dannar ashar iri iri ta tura fitowar Maryam ta kalleta da mamaki tace.

"Haba Ikki dawa kike wannan zagin haka kamar ba musulma ba dan Allah ki rage zafin zuciyar nan karki manta kefa mace ce wata rana gidan wani zakije".

Tsuka Ikram taja tana cewa "rabu dani Maryam wannan akwai tsinanne baki san halinsa bane shiyasa kike ganin laifi na amma mugun tantiri ne dan raini hankali jiya kina gani lokacin da kukaje gidan nayi masa hidima na kashe kud'i amma yace bazai samu damar xuwa ba baya gari tafiyar ujila ce ta kamashi yau kuma wani wai ya kira ni d'azu muna modeling dan ban d'aga ba shine yake min masifa da 'korafi aikin banza".
Chapter 67 · 0% Book details