← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 145

Sashe 138

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka a bangaren su Tanko ma duniya tayi zafi duk yawan dukiyar su a yanzu babu ko tsinke sannan kome suka ta'ba saiya narke masifa goma da asirin ta samesu ga wata irin jinya ta manya manyan 'kuraje data fito musu a jiki ko'ina ruwa yake babu kud'in yin magani haka suka dawo ana gudunsu a gari har majalisa da sunzo za'a kama toshe hanci ana mi'kewa d'aya bayan d'aya mutane na barin gurin a fashe a barsu sun zama abin gudu d'oyi suke fitarwa na 'kin kari haka rayuwarsu ta dagule qarshe garin neman waraka suka karasa hallaka kansu sun sauya gurin wani boka wai ya bincika musu idan malam Habu ne yayi musu asiri a maida kansa boka yace musu ba shi bane saidai a basu magani shi yanzu rayuwarsa yake a wadace cikin farin ciki jin haka yasa Tanko yace a sake maida Malam Habu gidan jiya ya rasa komai bai kamata Malam Habu yaji dad'i ba cikin qunci suke so ya qare rayuwar sa boka ya basu magani yace su bari sai dare su fito suyi aikin idan suka sake wani ya gansu da akwai mugujejiyar matsala.

Yarda sukai suka amshi magani dare nayi kowa ya baro gidansa suka had'o a inda zasuyi suna cikin hada tsafikan sun kusa kammalawa suka ji surutai a bayansu a firgice suka tashi wasu samarine da suke farauta duk dare sun dawo suka biyo ta wurin humm tun basuga abinda suke yiba Tanko ya fasa qara mai karfi yana fisge fisge haka Mudi tuni suka she'ka a guje cikin gari suna ihu ga dare yayi sosai mutane suka fito aka cika layi ana mamakin miye ya samesu kuka kowanne su keyi babu wanda yake cikin hayyacinsa balle su rufawa kansu asiri a gaban kowa da kowa suke fad'ar duk abinda sukaiwa Malam Habu tun daga lokacin daya gano sune silar mutuwar qanwarsu Lami zuwa gidan yarin da sukai na shekara ashirin da biyar bayan Tanko ya fito suka had'a makirci suka fara zuwa gurin boka Hambuwa yayi musu asiri a malam Habu ya talauce tsiya iri iri ta ri'ka samunsa komai saida suka fad'a har xuwa yau humm kowa shiru yai jikin mutane yayi sanyi sai tausayin Malam Habu daya shiga rayukansu Allah sarki bawan Allah ashe bada banza ba anata ganin laifinsa ga munanan baka'ken munafikai babu wanda ya nuna taimakonsu haka aka bursu a gurin kowanne yana ta birgima a kasa suna mututuwa da ife-ife har gari ya waye suna gurin a kwance maimakon da suka farka su tashi a hankalinsu ina suna kallon juna sai dariya da kiran yeee wallahi mune mune silar komai mune muka sa Malam Habu a damuwa daga nan suna mi'kewa sai cikin bola suka fara tsintar ledoji suna d'aurawa a jiki alama hankali ya gushe hauka ya samu.
HUM KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE.
DUK ABINDA KA SHUKA SHI ZAKA GIRBA.

Su Hassan sun dawo gida haka suka sayi fili kusa da gidansu suka famfa gida mai kyan gaske kamar a cikin gari suka fitar da hanyar da matansu zasu ri'ka shigowa su Bara'atu basai kullum suna zagaye fitowa da komawa ba sannan suka matsawa Ilyah lamba sai yaje Cameroon ya kai musu ro'kon arziki dole ya shirya shi da Bara'atu da Maimuna suka je hum su Hassan fa yayan mai kud'i suka taro sosai dan ko kansa Ilyah zai sayar bai isa ya taro mahaifinsu kud'i ba tarba Mai kyau suka samu ba kunya suka bararraje suka share duk yawan kayan da aka kawo musu aiko sun sha gori a gurinsu Hassan musamman Bara'atu ya tuna mata cewa ita gashi yanzu tazo gidan su ta shirgi abinci har da'kyar take tashi amma su kuma da sukaje gurin kwana ma ta basu ta'ki Bara'atu batace musu qala sai hararar su da take tana musu wani kallo wato a gidan mutane sai sun nuna halinsu ta inda Allah ya rufa asiri ma iya sune a bangaren ba'ki ba kowa.

👑EMPIRE/PALACE👑
_____Mami tana zaune Asad ya shigo yana zama ya gaida ita sannan yace "Mami dama ina so zamuyi magana dake ne akan wannan yarinyar".

Gyara zama Mami tai tana fuskantar sa sosai tace "lafiya Asad wani abu ne ya faru"?.

"No Mami babu abinda ya faru kawai ina son ta koma part d'ina da zama saboda na samu saukin aiki basai kullum ina cewa taje ba".

"Kamar ya Asad taya zata koma part d'inka da zama haka kawai dan aiki ban gamsu ba matsayin me kenan zata zauna ma a part"?.

"Mata".

Zaro ido Mami tai lokaci d'aya murmushi na su6uce mata ta rufe baki tana sake bud'e idonta a kansa tace "Asad wai da gaske kake ka kar'bi auren ne ka yarda yanzun ita matarka ce ko kuma saboda aikin kace haka"?.

"No badan aiki bane Mami dama tun a can nayi accepted d'inta matsayin wife jarumtarta ce ta ja hankalina itace irin macen da nake son zama da ita but saboda na riga nayi miki alkawarin a kanwa na tafi da ita yasa na ri'ke amanar da kika bani''.

Sauke numfashi Mami tai tana cewa "alhamdulillahi alhamdulillahi gaskiya naji dad'i sosai Asad dama zanga wannan ranar? Uhm masha Allah, Allah ya sanya albarka a zamanku".

Shigowa Ajeeb yai yana zama ya kalli Asad d'in cikin mamakin furucin sa wai yana son a bashi matarsa tabd'ijan nesa tazo kusa abun nema ya samu sake d'agowa yai yana kallon sa yace.

"Aida na d'auka zaka rabu da itane bazaka kar'bi auren ba sai kayi retire kamar yadda ka fad'a ko ya akai lokaci guda ka canza"?.

Had'e rai Asad yai yana cewa "Eh da nace haka amma yanzu kam nace na fasa ko zaka hana"?.

Murmushi Ajeeb yai yana cewa "Ina saidai na taya ka murna dakyau wani ya fara dawowa kan hanya".

"Dama ni akan hanya nake malam".

Harararsa Ajeeb yai yana cewa "au haba? Aiko karya kake yi da ratse kake bi wannan yarinyar daka raina itace ta dawo dakai kan hanya cikin shekara biyu ka gane gaskiya idonka ya bud'e daga makantar daka sashi da".

Tsuka Asad yai "malam kafa ishe ni zaka iya rufe baki".

"Bazan rufe ba gaskiya ce baka so kuma dole na fad'a ko zaka harbeni nasan ta'kamarka kenan bazai wuce bindiga ba kuma kome zakai saina maganu bawa da bakinsa baka isa ka hana ni surutu ba"

"Yayi kyau kaci gaba da surutun da alama tsohon dole kake son zama dan in kayi wasa saina zubar maka da ha'kora".

Dariya Ajeeb yai yana kallon sa yace "wai da gaske"?.

"A'a da qarya".

"Hum aiko yaro da anyi rushe rushen ha'kora dan baka isa ba na kusa aure zanyi sabuwar amarya tazo taga bakina da window ba".😂

"To shikenan zaka gani kaci gaba da shiga safgata zan baka mamaki".

"Hum Asad mamaki iya wanda ka bani yanzu ma ya ishe ni dama ai na fad'a maka wata rana zakai sanyi ka fuskanci mace kace a'a wai kai 'kwarin kai sai kayi wata uwa retire tab zamu sha kallo sai gaba ma sanda zaka tsinci kanka cikin soyayya dumu dumu sannan ne zakai bayani zama ka zauce a so.

Had'e rai Asad yai "malam ka rufe min baki ya isa haka''.

"Bai isa ba Asad dole saina fad'a ko baka so duk ji da kanka ka sau'ke hum da fa yaron nan yadda kasan tururuwa🐜 haka kake jin girman kai yanzu kuma ka had'u da 'yar baiwa nutsattsiyar yarinya ka susuce......................

"Ajeeb enough for you, Mami ki masa magana babu ruwansa da abinda ya shafi harkar rayuwata ina nine nace sai nayi retire, ba sani akai ba yanzu kuma na fasa meye ruwansa anan kice masa ya janye idanuwansa daga kan samun ido ya rufe min baki"

Mi'kewa Ajeeb yai yana cewa "shikenan jarabatu innaka mayyatun sai kaje ka 'karata ni tafiya hospital ma zanyi sannan abu na qarshe please Asad kar kace a'a dan Allah Amatu zata d'inka mana hular angwanci nida Annur"?.

Ajeeb na rufe baki Asad yace "wallahi baxa tayi ba babu wanda zata d'inkawa hula a cikinku saidai kuje gurin daurin auren da kanku babu hula".

Dariya Ajeeb yai yana cewa "sauri nake amma bari na dawo mu karasa maganar nasan da wasa kake dole ka bari ta d'inka mana yana fad'in haka yayi waje bai jira me Asad d'in zaice ba.

Mayar da kallonsa kan Mami yai yana cewa "me kika ce Mami"?.

"Ka sameta da kanka man Asad a tunani na matarka ce badan tun farko kaika nuna bakayi ba ai jewel baza ta'ki ba naga sabo da sha'kuwa a tsakanin ku.

"Mami bayan haka akwai wani rufaffan abu a tare da ita yarinyar nan Mami da taimakon ta nakai wannan matakin nasarar da nake kai yanzu bayan ke babu wacce nake jin tana da muhimmanci ada amma yanzu daga ke sai ita Mami.

Murmushi Mami tai domin itakam har yanzu mamaki take wai Asad ne mai cewa matarsa ta koma part d'insa bayan idan da dane ko kallo balle ya bada amsa,,, fitowa Amatu tai tana waya da ummanta a wayar malam Habu ta zauna bayan ta sauke wayar tana kallon Mami tace.

"Mami yaushe zanje gida"?.

Jin tambayar datai mata yasa Mami kallon Asad tunda iko na hannunsa shi kuma Amatun ya kalla yana cewa.

"Ba yanzu ba".

Shagwa'be fuska tai tana cewa "dan Allah ka bari naje gobe sati daya kawai zanyi na dawo"?.

Wani kallo tasa yayi mata jin abinda tace yasa yace "sati daya yayi kad'an saidai kiyi biyu".

Cike da murna Amatu ta mi'ke da sauri tana yin hanyar bedroom tace "yauwa nagode bari naje na hada kayana''.

Kai Asad ya jinjina daidai Mami tace "dawo jewel zo kiji".

Dawowa Amatu tai tana zama gabadaya farin ciki ne bayyane a fuskarta tace "gani Mami".

"A'a jewel ba wani abu bane Ina nufin ki bari kuyi magana da mijinki ki tantance kwana nawa zakiyi".

Kallon Asad tayi tana cewa "to kwana nawa zanyi idan naje domin yau zan tafi idan kuma naji ka bani kwanan da yawa saina tafi gobe dason samu nema nayi kamar wata na huta sosai yadda na dad'e bamu had'u ba.

Cije lips yayi hankalin sa nakan waya yace "ba yanzu zaki je ba sai nan gaba".
Chapter 138 · 0% Book details