← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 145

Sashe 34

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawo da hankalin sa yai kansu jin Ramatu na cewa ",dauko mana kan mu wanke Ilyah".

Kaiya girgiza "waye zai ci wannan kan ko shi maye ne an riga an jefa a kwata saidai mu ha'kura".

"Mu ha'kura kuma shikenan munyi asara"?.

"Eh ya riga yai mana ba'kin ciki ya jefa a inda bazai gyaru ba".

Kallon kan Ramatu keyi cikin takaici gaci ga kwanan yunwa ta juya saitin habu tana cewa "saika biya idan kuma ba haka ba cikin ragunan ka na kewaye nasa mahauci ya yanka daya".

'Dakin Baffah Habu ya shiga batare dayai magana ba ya dauko kud'i a inda Baffah yai masa kwatance saida ya fito zai fita ya kalli Ramatu yana cewa "idan tsautsayi yasa kika ta'ba min dabbobi yau saikin gane Allah da girma yake wallahi saina balla miki kafa sannan ki biya ni kud'in abinda kika min" yana fadin haka yai waje da kallo Ramatu ta bishi tana cewa "Allah ya isa ban yafe ba".

Ganin Ilyah zai fita tace "so'ko'kon banza shashasha kana jina da wannan mara kunya har yana zancen 'balla min'kafa amma bakace masa komai ba" juyowa Ilyah yai yana cewa "to me zance kece kika tsokane shi tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ke duka" yana fad'in haka ya fice abinsa kallon kan ragon tai tana cewa "bazan ha'kura ba saina gyara ragon nan ai kwatar gidanmu ce bata gidan uban kowa ba😲🤣.

Habu na komawa asibitin yaga iya Salamatu ba Sabi'u zama yai yana kallon ta yace "ina yaya Sabi'un yaje"?.

Tana kallon hanyar da Sabi'u yabi tace "likita ya kira shi tun d'azu bai fito ba".

Mi'kewa Habu yai yana cewa "to bari nabi bayansa naji meyake faruwa" da yake yasan office din doctor din kusan karo sukai da Sabi'u shi yana shirin fitowa shi kuma yana shirin shiga da sauri yace.

"Yaya Sabi'u lafiya me doctor yace maka fatan ba akan ciwon Baffah bane"?.

Sauke ajiyar zuciya Sabi'u yai yana cewa "eh yace tun jiya yayi batun za'ai masa gwajin jini ya bamu takarda kuma baiji ance komai ba har yanzu shine nace yayi hakuri kaje gida amso kud'i ne yace da ka dawo muji ayi masa".

Kai Habu ya d'aga "to yaya Sabi'u muje ga kud'in can na dauko mudai fatan mu Allah ya bashi lafiya".

Juyawa sukai suna komawa gurin Salamatu ganin yasa tace "meya faru kuma"?.

'Daukar kud'in Habu yai yana cewa "zamuje gurin gwajin jini da Baffah ne".

"To innalillahi Allah ka baiwa bawan nan naka lafiya" Salamatu ta fad'a cikin jimami tana rafka tagumi numfashi Habu ya sauke batare da yace komai ba ya d'an kalli Sabi'u yana masa alamar suje wucewa sukai yayin da suka bar Salamatu tana share hawaye.

Kusan awarsu gud'a kafin ta hangosu tafe suna rike shi girgiza kai tayi cikin tausayawa da takaici ta wani bangaren musamman halayen Ilyah da mahaifiyar sa Ramatu sam basa kyautawa...........................

"Babah ya kamata kije gida kinga rana tayi sosai" muryar Habu ya katseta.

D'agowa tayi cikin sauke ajiyar zuciya tace "bazan iya tafiya kamar jikin malam babu dad'i Habubakar anan zan tsaya na wuni" zama kusa da ita sukai Sabi'u na cewa "shikenan fatan mu dai Allah ya bashi lafiya koda Baffah ya rasu Ilyah ne sila ba sunan kowa a bakinsa sai shi ya matukar damuwa darashin biyayyar sa bansan meke damun Ilyah ba a iya sani na Baffah ya mana kokarin da ba kowanne ubane zai iya ba ya bamu kyakkyawar tarbiyya to matsalar daga ina take"?.

Habu da ransa ya sosu jin abinda Sabi'u yace akan Ilyah wanda ya tabbata gaskiya ne tsaki yaja yana cewa "matsalar tana gurin babah Ramatu duk tsiya data jajirce ta nuna masa matsayin Baffah tana ankarar dashi ai duk haka bazai faru to amma a gabansa zataiwa Baffah tas ba dole ya mayar dashi ba komai ba".

"To Habubakar ya muka d'iba muka iya da ranmu gidan Baffah ba haka yake ba ada idan kaxo gidan kafin ya auro Ramatu zakasha mamaki bata yabon kai ba har a waje sha'awar zamana dashi akeyi amma da yake 'kaddara tariga fata Saida Ramatu ta shigo cikin rayuwar sa ta gur'bata mana zama".

"Ai dama nasan haka zata faru badan karna kauce hanya ba da nace meyasa Baffah ya aureta" Habu ya fad'a yana kallon Salamatu.

"Kaita girgiza "to habu kaddarace rubutacciya matar mutum kabarin ba yadda ya iya shiyasa kuma rabon haihuwar Ilyah ne da yarinyar nan Lami, addu'ar mu dai Allah ya tashi kafad'unsa mu koma gida insha Allahu Baffah bazai sake shiga damuwa ko ba'kin ciki akan su Ilyah ba duk hanyar da zamu bi musashi farin ciki koda mu zamu shiga 'kunci to matukar hakan zai faranta ransa zamubi wannan hanyar".

"Gaskiya Habu gaskiya ne tabbas zamu kokarta" Sabi'u yai maganar kallon duka su biyun Salamatu keyi tana da ya'kinin da ace babu Ramatu da Ilyah a rayuwar Baffah bazai ta'ba shiga yanayi kamar wanda suka sashi ba.

Sai bayan sallar isha sosai Salamatu ta tafi gida tabarsu da niyyar gobe tadawo.

Kusan kwana goma sukai a asibitin suna fama kafin jikin Baffah ya warware aka basu sallama tsayawa sukai suka had'a masa kayan gina jiki dasa lafiya sannan suka dauki hayar mota har gida nan 'yan gari suka fara zuwa dubiya.

Abun mamaki Ramatu dake gidan tari batai ba balle tace ya jiki haka Ilyah inya shigo saidai ya kauda kai ya wuce inzai fita ma haka ganin Baffah ya damu yasa habu kaiwa zuciyarsa nesa gudun 'bacin rai kawai ya 'kyale shi baiyi masa magana ba ya zuba masa ido yaga iya gudun ruwan sa.

Gadoji na zaune gefenta 'yarta ce da tsohon ciki Jamila matar Tanko suna d'an hira sukaji an rafka sallama wa zasu gani cikin mamaki suka ga Deluh ta shigo hade rai Jamila tai tana kawar dakai dan ta tsani ahlin su da tasan haka Tanko yake d'an iska Allah ya rufa asiri ta yarda har takai su ga aure gashi abin ba'kin ciki harda rabo tsakanin su.

Ba yabo babu fallasa Gadoji tace "maraba Delu karaso ga tabarma kece kike tafe yanzu"?.

Zama Delu tai tana kallon Jamila da da d'an ya'ke a fuskarta tace tace "wallhi nice ina kwana ya me jikin"?.

"Lafiya kalau gata nan jiki yayi sauki ya abinda ya faru"?.

Huuuuuuh Delu ta sauke ajiyar zuciya tana cewa "hummm sai godiya ya zamuyi kaddara ce".

"To Allah ya 'kara rufa asiri".

Cikin takaici Delu tace "um Amin dai ai yaron nan ya cuce ni Tanko bansan ba mutumin arziki bane".

Jin zancen da suka soko yasa Jamila tabe baki cikin halin ko in kula tana shirin barin gurin da'kyar tace "ina kwana"?.

Kallonta Delu tai "lafiya Jamilatu zauna dan Allah magana nazo muyi".

Jitai kamar ta fashe da kuka tsabar takaici ta koma tana zama tare dayin 'kasa da kanta.

Cikin lallahi Delu ta soma magana "Jamila dan Allah kiyi hakuri abinda ya faru ki koma d'akin mijinki ki haihu acan na sani Tanko bai kyauta ba kada ki dubi halinsa ki tausaya min ki bini mu tafi".

Ba arziki Jamila ta d'ago tana kallon Delu muryarta cikin kuka tace "wallahi bazan koma gidan Tanko ba ni dashi har abada bazan ta'ba yafe masa ba sai Allah ya saka min dama yasan haka halayensa suke ya cuceni ya aureni tsabar mugunta harda ciki babu ni babu Tanko idan kin samu dama zuwa gurin sa kice ya sakeni kuma ko haihuwa nai a ranar dana haihu zan kawo muku dan'ku ko 'yarku bazan raineta ba" ta karasa maganar da kuka sosai na tsantsan tsanar tanko.

Ita kanta Delun kukan take ta kasa cewa komai sai kallon Jamila da take ganin ta mi'ke tabar gurin yasa tace "Gadoji dan girman Allah kiba Jamila hakuri tazo mu tafi wanda tai yajin dominsa baya nan a shekarun da aka yanke masa ko daya bai dauka ba gashi ta silarsa yaja mutuwar malam Balah ubansa zan iya rantse miki a cikin mu babu wanda yasan me Tanko yake aikatawa Saida asirin sa ya tonu akan yarinyar nan ashe duk fayd'en da akewa yan matan garin nan dana kewaye shine da Mudi har ran malam ya fita bai daina tsinewa Tanko ba".

Shiru itakam Gadoji tai domin itama a tana bangaren ta kudura cewa Jamila ta baro gidan Tanko har abada kuma tana fatan kada Allah yasa yaron da zata haifa yazo darai dan kada su samu ba'kin iri cikin danginsu babu wanda zaiyi alfahari da d'a mai mummunar d'abi'a irin tanko........................

Maganar da Deluh tai ne ya dawo da Gadoji daga duniyar tunanin data fad'a jin tace "Gadoji bakice komai kisa baki cikin maganar mu".

"Kai Gadoji ta girgiza "a'a bazan shiga ba Deluh bari na fad'a miki gaskiya Jamila nice nace bazata sake zaman aure da Tanko ba domin ni 'yata me tarbiyyace bazai bata min halayenta ba babu sauran ala'ka tsakanin Tanko da Jamila saki ne ya rage dan haka duk ranar da kikaje gano shi kice ya baki sakinta tunda ba mutumin arziki bane wa zaiso hada zuri'a dashi ya gama gur'bata rayuwar sa da banzayen d'abi'u marasa kyau gaskiya kawai kiyi hakuri".

Kuka sosai Delu keyi tana wa Gadoji magiya "dan Allah Gadoji ki taimaka kada ki duba halin Tanko ya dubeni ki bari mu tafi da Jamila".

Sauke ajiyar zuciya Gadoji tana cewa "gaskiya bazan iya ba taimako d'aya zan miki shine kawai kiyi hakuri ki dauki danga dan bazan bar Jamila taje ko'ina ba magiyar ya isa dan Allah ki fahimta".

Gadoji dan Allah kiyi hakur.................

Katse ta Gadoji "kinga Deluwa dan Allah karki sake ro'ko na na riga na fad'a miki gaskiyar lamari".

Goge hawaye Delu tai da gefen mayafinta tana mi'kewa zuciyarta na tafasa tace "shikenan nagode sai anjima".

Kai Gadoji ta d'aga "to Allah ya bamu alkairi".

Haka Delu ta koma gida hajijiya na dibanta ko gabanta bata gani haka zazzabi ya rufe harda amai gabadaya Tanko yasa rayuwarta a tsaka me wuya.

Baffah na zaune a kofar d'akinsa Sabi'u ya fito daga d'akin hatsi hankali tashe yana cewa "Baffah babu hatsi fa a d'akin nan".

Cikin mamaki Baffah ya dube shi "kamar ya ba hatsi kuma Sabi'u"?.

A rud'e Sabi'u yace "babu kusan rabi an sace".

"An sace kuma Sabi'u? Sake dubawa dai".
Chapter 34 · 0% Book details