Sashe 130
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mene kuka d'auko a cikin wadannan jakunan ku d'aga hannu ku matsa daga garesu yanzu" ta fad'a batare da jin ko d'ar ba kuma babu makami a hannunta.
Cikin mamaki suke kallon fuskar juna jin abinda tace tana mace har take da qwarin gwiwar cewa su d'aga mata hannuwansu sama................
"Nace ku d'aga hannunku sama ku matsa daga gurin kayan nan bakwa jin hausa ne"?.
Cikin fushi wani ba'kin kato dashi ya shafe fuskarsa da ba'ki kallonta yai kafin ya kwarara wata uwar dariya yana cewa "kai lallai ma boss kaji yarinyar nan me take cewa 'yar karama da ita baifi na murtsuke ta da kafafuna ba da alama batai shekara talatiin ba har ta samu kwarin gwiwar tararmu dan tana soja"?.
Kallonsa amatu tai babu alamar tsoro tace "kai sakarai bari na fahimtar dakai domin naga ga dukkan alamu kwakwalwar ka ta dod'e bankai shekara talatiin ba amma ina da karfi da zarra dazan cusa tsoro a 'kirazan magauta na ina da zafi fiye da na tsohon jarumi dan shekara sittin bana gudu saidai a gudun min kuyi abinda nace ku d'aga hannunku kafin kuji azaba"?.
D'aure musu kai tayi da maganganunta da alama dai da Shirin ta tazo musu kallon ta babban cikinsu yai yana hura hanci yace.
"Waye ya kawoki nan bakisan kinzo mahallaka bane mu kikewa barazana yarinya"?.
Murmushi Amatu tai tana cewa "tambayi kanka abinda ya kawo ni kafin ka tambaye ni kuma kaine abin tuhuma meya kawoka nan ka bani amsa ka huta domin shine kad'ai zai tseratar daku daga hannu na"?.
Cikin tsawa d'aya daga cikin su yace "keee kin kuwa san me kike fad'a kinsan su waye mu da zaki tare mu gaba da gaba"?.
Wani kallo Amatu tayi masa tana cewa "kai kuma ka rufe min baki domin da cikakkun maza nake magana ba lusari irinka ba".
Tana rufe baki sauran suka kware da dariya jin wani rainin hankali datai ma shi kuma kallon kansa yai ya tabbata shi siriri ne bashi da ki'ba amma wannan yarinyar ta raina masa hankali ransa a mugun 'bace ya d'ago yana kallon ta ganin irin kallon da take watso masa yasa shi yai kukan kura tare da jefar wu'kar dake hannunsa ya nufota da gudu gyara tsaiwa Amatu tai tana hard'e hannuwanta a 'kirji ta zuba masa ido bata ko motsa ba Asad na tsaye inda yake boye yana kallon ta da yadda ta fuskaci wannan saurayin amma shima baiji ko d'ar ba ya tabbata zata ceci kanta koda ace babu shi.
Gyara tsayuwa Amatu tai daidai ya iso inda take yai tsalle yana kawo mata naushi gogewa tai ya daki iska tare da yin tangal tangal zai fad'i ya samu dai ya tsaya da'kyar yana huci gira Amatu ta d'aga "yadai kar kace min harka gaji naga kana haki da alama dai banyi 'karya ba lusarin ne right"?.
Wow tamkar ta watsa masa wuta a jiki haka ya zabura yana sake yowa kanta yana zaro wata wukar dake soke a jikinsa ya kawo mata yanka caraf ta ri'ke hannun tana murd'ewa 'kara ya saki yana jefar da wu'kar wani sirrintaccen salon duka💪 da Asad ya koya mata ta sauke masa a wuya sai gashi ya zube kasa sharkaf ganin abinda ya samesa sauran abokan tafiyarsa yasa suma suka zaro wu'ka'ke su hud'u suna nufota cikin kuwwa hannuwa Asad yasa cikin aljihun wandon sa yana zaro bindiga pistol🔫 guda biyu ya jefawa Amatu wani irin tsalle tai cike da 'kwarewa da burgewa ta cafesu tare da saita na farko ta harbeshi a kafa yana fad'uwa tayi saurin harbin na bayansa sauran biyun zasu juya da gudu ba zato sukaga Asad ya dira a gabansu tare da damkarsu ya wujijjiga ya watsar gefe yana nufar inda manyan jakankunan guda uku suke Kowacce anyi mata shiri na musamman an datseta da key kallon Amatu yai wacce itama ta d'ago tana kallon shi da nuna cewa ya zasuyi dan shiru yai zuwa wani lokaci yace "zakije ki dauko mana motar ds kika zo da it's ko zaki jira naje na dauko"? Kallon sa tayi kafin ta mayar da kallonta kan 'kattin da suke kwance suna juyi cikin azaba kaita jinjina tana cewa.
"jeka dauko ni ina nan din".
Yayi mamaki baiyi tunanin zatace haka ba ya dauka zatace itace zata dauko motar sai kuma yaji amsa sa'banin yadda yaso ji amma kuma baida shakku akan Amatun sa ya tabbata jaruma ce yana da babban ya'kini a kanta babu wani abu da bazata iya ji dashi ba.
"ok ki jira ni".
Yana fadin haka ya wuce Amatu na tsaye a kansu babbansu dake kwance ba kafar gudu cikin takaici yace "ke wato har kinajin kanki jar wuya ko saboda kina da karfin wannan sojan"? Wata uwar harara Amatu ta sakar masa tana cewa "a'a ka manta bakace koriyar wuya ba wanne soja kake magana akai?🤔 kodashi ko babushi dama nima ba sa'ar wasa yan jagaliya irinku bace domin nafi 'karfin kanku a tafashe nake" yunkurawa yake yana son tashi ya kasa murmushi Amatu tai tana cewa "ayya sorry rago d'an wannan harbin kakewa raki anya kai namiji ne ba mata maza ba dan harbi a kafa kawai humm an harbeni a ciki ma amma ban karaya ba kuma zuciyata bata kasa ba jarumtakata bata raunana ba kuma ban ta'ba dana sani ko 'kasa a gwiwa ba saikai"? Juyi ya kumayi tare da d'agowa yana mata kallon barazana yace "na rantse da wanda numfashi na yake a hannunsa kunci bashi matukar ina da rai koni ko ku" 'yar dariya mai cike da burgewa Amatu tai tana masa kallon wanda zafin ciwo ya gigita saidai a masa uziri daidai Asad ya parker mota ya fito Isham ya biyo bayansa cike da mamaki yace.
"Kai buddy wai kana nufin anan ka tafi ka barta da wadannan 'kattin"?.
Kallon Amatu Asad yai yana cewa "to miye dan na barta anan"?.
"Babu amma kaine ya kamata ka tsaya ita taje".
"Humm Isham kenan har yanzu baka fahimci wacece ita ba wannan yarinyar! wannan yarinyar!! 'kyale kawai" ya karasa maganar yana sa hannu ya dam'ko kwalar rigar babban cikin su ya jefashi a mota kafin sauran ma ya cillasu tare da jakanku nan sannan suka shiga suna barin gurin kiran daya shigo wayar Asad ne yasa shi sassauta gudun da yake tare da d'agawa daga can 'bangaren Clarah tace.
"Hello Asad kana ina yanzu"?.
Kallon Isham yai da shima yake kallon sa bai bata amsa ba yaci gaba da tu'ki saida ta sake magana yace "naje wani wuri ne miya faru"?.
"Maimakon ta bashi amsa saita sake jefo masa wata tambayar "wanne irin guri bashi da suna ko baka bukatar na sani"?.
"Eh" shine abinda kawai yace ya katse kiran yana kallon sun kusa fita daga dajin.
"Asad na tambaye ka"? Isham yai maganar yana kallon screen din wayar Asad din da sunan Clarah ya fito 'baro 'baro tana sake kira amma yai banza kamar baiji ba Asad bai amsa masa ba dan haka yaci gaba.
"Clarah kwana biyu ta'ki maida hankalin ta kan aikinta gabadaya ba sosai ma nake ganinta ba yanzu amma naga ka share baka tambaye taba"? Kamar Asad bazai tanka ba sai kuma yace "akan mezan tambaye ta bayan tana da hankali da akwai abinda yake damunta ai zata sameni tamin bayani inda tasan ciwon kanta ni banason shashanci".
Numfasawa Isham yai "amma Asad Clarah ta lalace da yawa bakaga irin ramar datai ba ya kamata ka aje komai ka dubata ka tambaye ta" "waye zai tambaye ta amma ba Dani kake ba"? Murmushi Isham yai yana girgiza kai yace "dakai nake man Buddy maganar seriously nake maka fa" d'an tsuka Asad yai "Isham kabar 'bata bakinka dan indai akan Clarah ne ba sati ko wata ba zai d'auke mu tsawon shekara guda ban fahimce ka ba ka gane"?.
Huuuuuh Isham ya sauke ajiyar zuciya yana kallon sa sai kuma yayi dariya yana cewa "Mrs Aliyu Asad gaskiya mijin nan naki sai a hankali baya sauraron abinda bai ga dama ba" murmushi kawai Amatu tai batace komai ba amma tayi mamakin jin yadda Isham d'in yace wannan mijin nata dama ya yarda ita matarsa ce harya fad'a masa ya amince da auren ne koko a'a ba shine yace aikinsa yasa a gaba d'agowa tayi tana kallon Asad da hankalinsa ke kan tu'ki daidai yayi parking Clarah ta fito tare da wannan sojan na ranar Sir. David Jason shima d'an Germany ne qasarsu daya da Claran.
Tsayawa tai tare da zuba musu ido da kuma ganin abinda sukai wato so yake dai Amatu ta fita matsayi shiyasa duk wata harka da yasan zata d'aukaka zai ta gaba sam ya daina nemanta a komai sai lokaci zuwa lokaci humm amma ita tana zaune photo decoration tana gayyar tunani har suka wuce bata farga ba saida sir David ya mata magana sannan ta dawo cikin hankalin ta da alamar tambaya yace...
"Me kike kallo"?.
Jin tambayar dayai mata yasa taji wasu zafafan hawaye sharrrr suna zuba a idonta da mamaki ya sake jefa mata tambaya "meyasa kike kuka"? Har lokacin kasa magana tai sai shashshe'ka da take zuba mata idonsa wanda ya cika shi fal da ba'kin ciki tana sharcewa Sir David yana tsaye yana kallon ta kamar ya samu TV zuwa wani lokaci yace "kina bukatar nutsuwa ne"? Kai ta d'aga masa "kina bukatar taimako na? Ko kina bukatar mai agaji a kusa dake"? Bata da bakin masa magana kawai da kai ta bashi amsa murmushi yai dan ya ganeta tun ba yanzu ba tana matukar son Asad kamar yadda shima yake matukar sonta saidai ta'ki amince masa saboda son Asad ya gama cika mata zuciya da 'kwakwalwa amma kwanan nan zai jawota jikinsa ya ri'ka rage zafi da ita tunda ta'ki amince ya aureta.
Tofa ji wani asararre🤔 kamar shi bai haifa ba hummmm rayauwa ce indai kaiwa d'an wani rashin da'a za'ai wa naka🤨.