← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 145

Sashe 91

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Allah Mami Asad dinne zumane dole sai an cishi da haya'ki ai nine maganinsa Mami ki 'kyale ni dashi kawai Nima bari na tafi kinga sha d'aya tayi".

Kai Mami ta d'aga "ok Ajeeb mu kwana lafiya".

Mi'kewa Ajeeb yai shima yana fita yayin da yabar Mami ita kad'ai tana dariyar diramarsu kafin itama ta tashi tana shiga bedroom.

🏕️'KAUYE🏕️
Binta tana zaune a kofar d'aki tana zubin hula Amatu ta fito daga d'aki tayi wanka kallon ta Binta tai da mamaki tana cewa "Amatu wani wuri zakije ne naga kinyi shiri haka"?.

Kai Amatu ta d'aga tana murmushi tace "Eh umma zanje gurin babah Rakiya da gidan baba Ilyah nabiyo ta gidansu Fatima kinga tunda na dawo bamu had'u da ita ba bata zoba nima banje ba rabon da muga juna harna manta".

Amatu ta karasa maganar tana shirin fita Binta ta dakatar da ita da cewa "ayya Amatu ai Fatima tayi miki nisa anyi aurenta kuma mijin nata sun tafi rani tare" da mamaki Amatu ta dakata tana cewa "aure kuma amma wa ta aura koba a garin nan bane"? Kai Binta ta d'aga "a'a d'an nan garin ne man zaki sanshi Sadam Dan gidan malam Yakubu can wajen anguwarmu kodan ba zama yake sosai a gariba ba lallai ki sanshi ba"? Dan shiru Amatu tai cikin tunani zuwa wani lokaci tace "eh gashi a raina kamar na sanshi amma naso na mantashi gaskiya saidai idan Allah yasa sun dawo na ganshi kodama ace zan tunashi amma nikam umma wai har yanxu babu mai saurayi tsakanin Aunty Asma'u da Jamila"? Kai Binta ta d'aga mata "eh Amatu babu wallahi ni abun har tsoro yake bani abun yayiwa malam yawa".

Kallo kofar d'akin Saude Amatu tai tana cewa "Amma ai ita Aisha ba naji ance Hussainin baba Ilyah yana sonta ba ko fasawa yai"?.

Kai Binta ta girgiza tana cewa "Humm Amatu kibar wannan maganar kwanan baya bakiga irin cin mutumcin da Ilyah yazo har gidan nan ya saukewa malam ba yana zaune akan tabarma kamar zai fad'a kansa ya rufeshi da duka akan yaran nan suna kawo masa d'an cefane idan sunje kasuwa harda masa gorin 'ya'ya maza waidan baida sune yasa yake son rabashi da nasa kwad'ayi da zilama ce tasa yake jansu a jiki yana musu fara'a Allah ya sauwake d'an sa ya auri Aisha dake".

Takaici ne ya kama Amatu bata sake cewa komai ba ta kama hanya ta fice daga gidan ko a hanya ma aikin tunani tayi-tayi har taje gidan baba Rakiya ta gaishe da ita sannan ta biyo ta gidan Ilyah da sallama ta shiga duk suna zazzaune a waje anata aiki domin yau mahaifan Nurain zasu zo ro'kon arziki sun sanar musu tun satin daya wuce.

Nafisa anci wanka an gyagije sai kaiwa da komowa ake daga nan ayi nan itace me toye-toye🥨🥐🍔 ance ta bari Salma tayi dan kartai 'kwaurin haya'ki amma ta'ki balle yanzu ta sake kamar da bushasha take a gidan itace ta gaban goshin Ilyah tunda ta samu Hassan da Hussaini basa nan sun koma gurin neman kud'in su a ranar da sukabar garin kowa a gidan barci yai da munshari na dad'i musamman Bara'atu da Ilyah ji suke tamkar wani qaton dutse ne aka sauke musu daga kansu kuma suna fatan Allah yasa kafin su dawo malam Habu yayi auren 'ya'yansa koda nakasassu ne masu bara😣 ko miskinai da fa'kirai sufa ko kare malam Habu zai daurawa aure da 'yar sa ya bashi basu da damuwa da haka matsalar su suga dai basa gabansa kafin tantiran nasu 'ya'yan su dawo wannan shine kwanciyar hankalin su.

Kujera maimuna ta bata tana zama bayan sun gaisa kawai tai shiru jin suna zancen kila yanzu ma ba'kin sun kusa karasowa ayi sauri a gama mamaki ne ya kamata wato ba'ki zasuyi yan birni shine suke musu wannan hidimar haka jiki na rawa kallon Bara'atu tai wacce ta dam'bare bakinta da janbaki tayi d'aurin kwalin ture kaga tsiya ansha kwalliyar atamfa mai tsada anyi sabo kitso da 'kunshi sai murgina kai take tana wa'ka sau'ke numfashi Amatu tai kafin ta mi'ke tana cewa.

"sai anjima".

Babu wanda ya kulata domin maimuna ta shiga d'aki sai Salma data shigo gidan yanzu ganinta yasa da fara'a tace "a'a hajiya Amatullahi yar boko yaushe a gari kinga yadda kikai kyau wallahi da kinyi zamanki acan kiyi aurenki kawai dan samarin qauyen nan namu sai a hankali idan kika cire irin Adamu saurayi na dan shikam gaskiya ba laifi kuma gidansu ma mutanen kirki ne humm Amatu kike to ya bokon kin gama ne kika dawo ko zaki koma"?.

'Dan murmushi Amatu tai zatai magana Bara'atu data ta'be baki tana bin Amatun da wani irin kallo tace "yan boko ko 'yan bokoko🤪 ina boko anan duk gayyar yunwa da talauci anyi asarar kud'i dai amma wanne karatu tai karatun da baza'a amfana dashi ba tunda inma kwad'ayin aikin gwamnati suke dan su samu kud'i sunsan baza'a dauketa aiki ba koda na share share ne indai a ofihi ne😐 da mai kud'i mai dukiya attajiri ake harka bada matsiyaci ba😭🙊" ta karasa maganar tana tofar da yawu😠.

Wani iri Salma tai da fuskarta jin abinda Bara'atun tace wanda yasa ran Amatu yai mugun 'baci kamar Salman zata bud'e baki ta laftawa Bara'atun magana sai kuma ta fasa tunda ba sa'ar yinta bace matar ubanta ce yadda bazata bud'i baki ta mayarwa maimuna magana haka Bara'atun ma bazata mayar mata ba duk da yanzun tasan ita ta jawa Amatun ba batace komai ba har mummunan furuci da ba'kar magana bazai fito daga bakin Bara'atu ba ko kunya tana fad'awa yar cikin ta magana jikin Salma a sanyaye ta kalli Amatu tana cewa "laifi nane dan Allah Amatu kiyi hakuri da banyi magana komai bazai faru ba kuma ban fad'a miki yar boko da sunan isgili ko na fad'a da wata manufa ba".

Kai Amatu ta girgiza kamar abun bai 'bata mata zuciya ba tace "no vex🤷 karki damu Salma babu komai ni wucewa ma xanyi sai anjima" tana rufe baki maimuna data fito daga d'aki tace.

"A'a Amatu tafiya kuma? dan Allah ki tsaya na sauke abinci kici kinji yanzu zai sauka na kusa gamawa".

Da sauri Amatu ta sake girgiza kai tana cewa "a'a wallahi nagode dama ni ziyara nazo muku sai anjima".

Tsaki Nafisa taja tana kallon Amatu tace "jimin karyar banza kinzo ziyara ko kinzo zilama😳 duk da baki zo ziyarar ba saida kika daidaici ranar da idan kinzo zaki samuwa ko? to wallahi wadannan kayan 'kwalelan ki na masu hannu da shuni ne bana masu hannu a 'kai'kashe ba".

Wata uwar harara Salma ta wurgawa Nafisan cikin son huce haushin abinda Bara'atu ta fad'awa Amatun yanzu tace "Nafisa ki iya bakin fa''zanyi mugun 'bata miki ranki yanzun nan wanda hatta ba'kin da zasu zo sai sun fahimta kin gane?.

A masife Nafisa tace "bazan iya bakin nawa zokisa nayi shiru yar iya Ina ruwanki da wannan da jinin talaucin nake wanda a haka rayuwar su zata qare ban sauko dake ba kin gane"?.

Itama Salam rai 'bace tace ban gane ba saiki sake ganar dani aikin banza kawai wacce batasan abinda takeyi ba mtswww".

Jin tayi mata tsaki yasa Nafisa a fusace ta aje abin da take ta taso da sauri tayo wajen Salman dakatar da ita Bara'atu tai da cewa "ke Nafisa kyaleta kada kije inda take nasan ko yanzu kasuwa ta watse d'an koli yaci riba zaki fita zakka ki koma rayuwa a birni na dindindin ba zaman d'and'ani haukaci irin na wasu ba aje a zauna sannan lokaci guda a tattaro tsummokara a dawo gida" ta karasa maganar tana hararar Amatu tuna irin wulakancin dasu Hassan sukai musu a kanta ita da Aisha tari Amatu batai ba Salma ma bata sake magana ba maimuna ce tasa leda tana daurawa Amatu kayan cinye cinyen da ake toyawa ta bata.

Kai ta girgiza tana cewa "a'a na gode sai anjima" tana gama fad'in haka tai hanyar fita daidai Ilyah ya shigo ga ba'ki biye dashi da alama sun karaso har qasa Amatu ta dur'kusa tana gaidashi bai amsa ba sai Bara'atu da yaiwa nuni akan ta shiga da ba'ki ciki yana so zaiyi wata magana saida yaga sun shiga daga d'aki sannan ya mayar da hankalin sa kan Amatu dake dur'kushe a gabansa yana cewa.

"Ke tashi zan fad'a miki sa'ko zuwa gurin ubanki".

Mi'kewa Amatu tai zuciyarta na dukan uku da tara tana tunanin Allah yasa ba sa'kon rashin mutunci bane...............
Chapter 91 · 0% Book details