Sashe 123
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi mamakin jin tambayar da yayi mata amma sakamakon tun farko yace idan ta sani kawai tace ta sani in bata sani ba tace bata sani ba tuna hakan yasa tace.
"Eh na sani, nasan wata 'kungiya guda d'aya".
Numfashi ya sau'ke yana cewa "Menene sunanta"?.
"Overcrowded potency association".
Tana rufe baki ya rubuta sannan yace me kika sani game dasu a ina suke sun ta'ba nuna miki yadda suke cutar da mutane a wanne wurin suke da wacce alama ake iya zuwa gurin su"?.
Shiru Amatu tai tana nazari zuwa wani lokaci ta d'ago ganin kallonta yake yasa ta d'an kau dakai cike da fargaba tuna cewa idan ta fad'a sunce zatasha mamaki amma me ko dukkan mutanen dake kungiyar ne zasu taru a kanta hakan bazai hana ta fad'a ba kodan a kawo karshen zaluncin su.......
"Ina jinki".
Sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa "nasan wani abu a kansu mutane ne marasa imani da tausayi suna hallakar da mutane a 'kalla d'ari a rana batare da sun damu ba sannan inda suke ba'a iya zuwa sakamakon dajine na tsafi ba'a bayan qasa yake ba yana ma'kale a wani gurin siffar sa yanayin kumbo su kad'ai ne suka san inda yake sannan a tsakaninsu a hannun kowannen su a tare dasu akwai wata ba'kar sar'ka ta tsafi wacce da iya ita ake iya shiga dajin a kullum suna zama suyi meeting sau biyu safe da yamma akan yadda zasu kara qarfafa kungiyar tasu su bun'kasata su cikata da mutane zasu bazu a baya kasa zasuyi fito na fito da mutane musamman sojoji wajen ganin sun ya'ke su sunyi magana akan wani soja wai shi kad'ai ne ya gagaresu ya zama barazana garesu basu san ta yadda zasu 6ullo masa ba banda shi babu wanda ya sake firgita su saini, shine sukace min amma na sani duk jarumtaka ta bazan kai labari ba zasu ya'keni dani dashi domin mu biyun nan ne zamu iya tarwatsa qullun su da qungiyar su amma bana jin hakan a raina tunda ni abinda nake fatan zama ban zama ba".
Tunda ta fara magana Asad yake rubuta duk abinda tace har takai aya jin abinda tace a qarshen maganarta yasa ya d'ago yayi mata kallon mintuna biyu kafin yace.
"Me kike son zama"?.
"Soja".
Asad baiyi tsammanin abinda zatace kenan ba ya dauka wani abune can dabam ba shiri ya zuba mata ido cike da mamakin abinda ta fad'a wato soja take son zama hummm lallai fad'uwa tazo daidai da zama yana maraba da wannan muradin nata zaiyi amfani da wannan damar ya cika burinsa itama ya cika mata nata zai sanyata a 'bangaren sa zai tabbatar ya gama had'a komai abin nemansa.
Kan Amatu na sunkuye tana kallon qasan carpet taji yace.
"Aikin soja kike nufi"?.
Kai ta d'aga yaci gaba "kina son zama soja ne wannan shine burinki"?.
Nan kaita d'aga tana cewa "eh dukkan karatun danai akan haka ne Ina so nayi aikin soja wannan shine burina a rayuwa".
"Ok Ina zuwa" yana fad'in haka ya mi'ke yana shiga bedroom shiru Amatu tai tana kallon zakin dake kwance yana barci tai mamaki tab shi kuma harda zaki yake rayuw...........
Bata karasa maganar ba ta d'ago da sauri ganin zakin yayi mi'ka yana tashi tsaye tare dayin wata kalar girgiza gashin jikinsa yana she'ki taga ya xuro mata ido yana d'an gyara kofa mi'kewa tai da sauri tayi hanyar fita aiko taji yayi kukan zakuna da gudu ta karasa fita ya rufa mata baya😳 ganin ya biyota yasa ta zubar da takalman kafarta da yake masu santsi ne haka ta she'ka da gudu hankalinta a tashe kamar zata kifa tana haki ta shiga parlon Mami ganin Mamin zaune yasa ta fasa ihu tana 'boyewa a bayanta kafin Mami tayi magana sai ganin shirgegen zaki tayi ya shigo yana tafiyar kasaita irin yadda zakuna suke yi saida yazo tsakiyar falon sannan ya tsaya yana sake kukan zaki.
Zaro ido Mami tai da sauri tad'au waya zata danna kiran Asad d'in sai gashi ya shigo zakin na ganinsa ya tafi gurinsa murmushi Asad yai yana kallon Mami wacce ta sakar masa harara tana cewa.
"Asad me kayi wannan dama kace taje part d'inka ne dan kasa zaki ya cinyeta kasan Allah duk ranar da zakin nan ya ci mutum a masarautar nan sai kayi zaman gidan yari fatan ka jini dakyau"?.
Shafa gashin zakin Asad keyi cikin son da yake masa yace "Mami komai nakeyi ina sane har abada zakin nan bazai ta'ba koda cizo bane balle har yaci mutum an riga an cire masa dukkan wani dafi babu abinda zai iya yi haka sauran animals d'in babu mai fad'a a cikinsu babu wani abu dazai faru" ya karasa maganar yana mayar da hankalin sa kan Amatu wacce ke le'ko zakin tana daga bayan mami yace.
"Ke kuma ina jiranki zamu karasa magana ki kawo min takardunki".
"To tace tana yin hanyar shiga part d'in da take zaune Mami batai magana ba duk da taji abinda Asad d'in yace amma bata nemi qarin bayani ba bata tambaye shi me zaiyi da takardun Amatun ba tunda wannan magana ce tsakanin su ba abune wanda ya shafeta ba.
Fitowa Amatu tai tana bashi ya kar'ba yana dubawa zuwa wani lokaci ya d'ago yayi mata kallon minti d'aya sannan yace..
"Ki same ni a part d'ina kizo min da laptop d'inki" yana kaiwa nan ya juya ya fita zakin na biye dashi.
Tsoro ne ya kama Amatu jin da gaske part d'insa zata sake komawa gurin wancan 'katon zakin karfa taje ya cinyet...........
"Jewel kije man ku kasara maganar" Mami ta fad'a tana kallon yanayin ta mi'kewa Amatu tai cikin ladabi tana shiga ta d'auko laptop d'in ta fita daga part d'in Mami ta koma tana kalle kallan inda zataga zakin amma babu shi babu alamarsa iya Asad d'in ne kuma shima waya yake bai nuna mata ta zauna ba saida ya gama ya juyo yana cewa.
"Bani laptop d'in".
Mi'kewa masa tayi daidai ya sake jefo mata wata tambayar.
"Kin shirya zaki iya aikin soja shekarun ki nawa".
Kan Amatu na qasa tace "ashirin da shida".
"Ok zaki iya training d'in soja ko bazaki iya ba"?.
"Zan iya".
"Bana son wasa kin tabbata da abinda kika fad'a"?.
"Eh".
"Alright kin shirya"?.
"Eh na shirya".
"Ok bani minti d'aya daga yau zaki fara" ya fad'a yana mi'kewa ya shiga bedroom tana ta tsaye ya dad'e bai fito ba harta d'auka ya manta da shafinta sai kuma taga ya fito yana bata wani abu yace "ki shiga nan ki fito ina jiranki banda sanyin jiki da zafi zaki ri'ka yin komai".
Kar'ba tayi tana shiga inda ya nuna mata cikin mamaki data bud'e abun riga da wando ne jesi amma wandon dogo ne ta gani kai meyake nufi kenan shi zatasa mizai mata shiru tai tana sake kallon kayan daga baya kuma ta cire hijab d'in jikinta a ranta tana tunanin taya zata sa riga da wando dai tuna yana jiranta kuma karta 'bata masa lokaci yace komai ta ri'ka yinsa da zafi yasa dole ta cire atamfar jikinta tasa jesin saidai sun mata yawa musamman wandon domin dama kayansa ne dur'kusawa tai ta nad'e kafafun wandon gashi ba hula balle tasa kawai saita mayar d'an kwalinta sannan ta fita.
Yana tsaye bai matsa daga inda yake ba karasowa tai tana tsayawa d'an nesa dashi kad'an.
"Cire wannan abun kan naki ki ajeshi".
Taji saukar muryarsa yace haka babu musu ta cire d'an kwalin dole tunda ba yadda ta iya gashi kanta babu kitso yana taje dad'in abun ma tayi parking d'insa da ribom.
"Fallow me".
Yana fad'in haka ya nufi wata kofa da sauri tabi bayansa ganin inda yake sa password zasu shiga yasa taji hankalinta ya tashi a ranta tace.
"Na shiga uku wato kawo ni zaiyi su cinye ni kenan dama harda bani kaya nasa stockyards wayyo Allah na...............
"Me kika ce"?.
Jin tambayar dayai mata yasa tayi saita nutsuwarta karfa ace a fili tayi maganar.
"Idan naga dama ne zan kawo ki su cinye ki ai da yanzu sun gama sun sha ruwa ke wato Ajeeb ya gama min sharri a gunki ko cewa kiyi taka tsantsan dani bani da hankali rights"?.
Da sauri Amatu ta girgiza masa kai bai sake cemata komai ba har suka shiga gurin tayi mamakin girma gurin da kyau ga tsaruwa gini ne na zallar qarfe mai kyau akai musu ga dabobin daji nan giwa da sauransu kaita jinjina tana kallon ikon Allah har suka bar yankin su suka shiga wani wurin shima fili ne mai girma yana da fad'i yanayin sa kamar filin ball⚽ tsaf dashi sai 'karafinan motsa jiki a gurin masu tarin yawa ga igiyoyi a d'add'aure suma masu yawa da Abubuwan training kaita jinjina a ranta.
"Tofa yau ake yinta wannan duk kayan training ne? Caf amma fa na kad'e"............
"Zaki fara training daga yau? Ina so ki san komai ki iya komai cikin wata d'aya zaki iya"?.
"Eh zan iya".
"Ok gud bismilllah" ya fad'a yana nuna mata wani qarfe yace "fara da wannan qaramin ki ri'ka d'agashi sama sosai kina saukewa banda tsayawa kuma da sauri.
Kallon qarfen Amatu a iya idon ma ganinsa bala'i ne balle ace ka cira uhm matsawa tai tana dur'kusawa da'kyar ta runtse ta d'aga shi yana kallon dama yasan tunda bata ta'ba ba zaiyi mata wuyar d'agawa shiyasa ya bata qarami nan gaba da hannu d'aya ma zata iya d'agashi inta riga training d'in ya ratsa jikinta