Sashe 136
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Numfashi Amatu ta sauke tana cewa "amma meyasa ka kasheta daka bari saina warke na tambaye ta me nayi mata a rayuwa take son ganin bayana".
"Amatu bazan iya jira saikin warke ina kallon Clarah da wannan mummunan aikin datai ba babu wanda zai ta'ba ki na barshi ya huta babu wanda zai yunqurin kasheki na barsa da nasa ran ke amana ce gareni sannan ke garkuwa ce gareni dukkan duniyata tana wajenki taya zanbar wanda yake wasa da rayuwar ki ya rayu humm impossible".
Shiru Amatu tai kamar me tunani sai kuma ta d'ago tana cewa "yaushe za'a bani sallama"?.
"Sai kin warke sosai".
"Ni na warke ai".
"No baki warke ba ki bari ki sake jin dad'in jikin ki".
"Ina jin dad'in jikina yanzu ma".
Kallonta Asad yai kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa yana mi'kewa yace "ina zuwa bari nayi magana da doctor abinda yace shi za'ai idan yace saikin sake warwarewa dole ki zauna" yana fad'in haka ya fita ya bar Isham dake tsaye a bakin kofa yana jiran dawowar sa yayin da Amatu ta gyara zama tana d'aukar yogurt d'in dake kusa da ita ta fara sha har sanyinta ya huce.
Doctor bai baiwa Amatu sallama ba a ranar kamar yadda take so sai da ta sake kwanaki ta gama warkewa tas sannan ya rubuta mata sallama suka koma gida batafi kwana biyar da barin asibiti ba ta koma bakin aikinta kuma ko kadan bata yiwa Asad maganar gida hankalinta duk ta tattara shi ga aikinta har mamaki take bashi shekara biyu da rabi amma babu ruwanta da qorafi ko neman pass tace tana son gida shine ma yayi tunanin zai kaita ta gano gidan tayi 'yan kwanaki su dawo abinda ya bashi mamaki daya fad'a Mata zai kaita gida sai yaga tana murna ashe dama tana so dannewa take humm ya yarda Amatullahi jaruma ce sosai wacce za'ai kwatance yana jin yanzu kam zai iya zama tare da ita zai kar'beta matsayin matarsa domin ta cancanta duk wani abu da yake so jarumta rashin nuna tsoro hankali natsuwa rikon addini ilmi sanin girma na gaba ta qware ta wannan fannin to meyake jira babu ba shida wani sauran jayayya ko tirjiya wannan yarinyar itace irin macen da ya kamata ya aura dama ya zauna da ita kuma ya kar'beta zai ri'keta da daraja amma bazai sanar mata ba yafi so sai sun koma gida ya sami Mami yayi mata magana akan haka tunda matsayin qanwa ya taho da ita bayan haka itama tasan cewa babu maganar aure a tsakanin su aiki ne yasa ya jata a jikinsa sosai yake ji da ita ya bata kulawa sukai sabo da sha'kuwa har haka.
Tana zaune a parlor ya shigo yana waya da Mami tana jin Mami tana tambayarsa ina jewel ta d'auka zai bata sai taji yace.
"Jewel d'inki tayi barci".
"Ayya har tayi barci yanxu Asad kodai yau ta gaji ne''?.
"No Mami bamu fita operation ba ita ce dai taje checking point da safe".
"Ok Asad yaushe kace zaku taho"?.
"Jibi ranar Monday".
"To shikenan Asad Allah ya kawo ku lafiya ka gaishe min da jewel d'in idan ta tashi".
"Ok Mami zata ji sai anjima" yana katse kiran Amatu ta ture laptop d'in gabanta tana d'an bubbuga kafa kamar zatai kuka.
"What"?.
Jin abinda ya tambaye ta yasa shagwa'be tace "kuma nifa na dad'e ban gaisa da Mami ba".
"Oh wai akan haka ne meyasa kika 6atar da taki wayar"?.
"Allah ni ba 6atarwa nayi ba bansan inda ta fad'i ba sai ka saimun wata".
"Waye zai sai miki wata"?.
"Kaine".
"Haba dai"?.
"Allah".
"Ni bazan sai miki waya ba kuma kema bazaki saya da kud'in kiba laptop ma ta ishe ki"?.
"Saboda me"?.
"Saboda ina kishi".
Cikin rashin fahimta Amatu tace "kishin me"?.
"Kishin na kira Mami kema ki kirata sai naji kamar na zubda hawaye saboda kishi".
Dariyar da ba shiri Amatu ta saki tana kallonsa tace "da naga hawayenka wanne kala ne".
"Oh a hawayen harda kaloli"?.
"Eh akwai".
"To fad'a min kala biyu wanda kika sani"?.
Gyara zama tai tana ri'ke yatsarta alamar zata lissafa masa tace "na farko shine hawaye masu araha wanda abinda bakai ya kawo ba mutum zaita zub dasu a banza kamar yadda Clarah take yi na biyu sune hawaye irin naku killatattu masu tsada da wiyar fitowa duk ranar da aka ga hawaye a fuskar irinka tofa ranar gaskiya mummunar rana ce bama fatan zuwanta kaji kalolin hawaye"?.
Murmushi ya mata yana girgiza kai yace "naji shikenan to nabar kishin tunda kema 'yar gidan Mami ce tashi muje kiyi mata shopping tare da babies d'in Ameer Shaukiyyah ta haifi yara biyu maza an sanya musu Hassan da Hussaini sunan Abba da Daddy kema daga nan sai ki sayi abinda kike so''.
To tace tana mi'kewa ta shiga bedroom ta sauyo doguwar riga fara tas kai adon ba'kin stone tana da yafinta duk da ba wani babba bane ta rufa shi tana fitowa ya mi'ke suka tafi saida ya fara kaita guraren daya kamata kafin ya rakata tayo shopping mai yawa harda Umman ta da babanta kuma da kud'in albashinta dama da ATM taje saida ya bari ta gama nata sayayyar sannan shima yayi tasa ya dad'a mata akan nata yace ta baiwa duk wanda ya cancanta idan sun koma sannan ya saya mata sabuwar waya godiya kuwa sosai tayi masa da jin dad'i suka dawo gida.
Washe gari ma ranar lahadi basu wuni a gida ba suna bakin ruwa gurin hutawa sai dare suka dawo a ranar yace kada tayi barci ta shirya komai jirginsu na asuba ne bata kwanta ba saida ta tabbatar ta kimtsa komai sannan tayi wanka ta kwanta asubar fari yayi kiranta a waya yace ta tashi tashi wanka da anyi sallah zasu tafi shiryawa tayi tsaf farin ciki fal ranta zata koma Nigeria bayan shekara biyu da rabi.
Isham ne ya kaisu airport yana tsokanar Amatu wai ko bazata dawo Marshalls islands ba taji tsoro dan yaga murnar tafiya take tace masa a'a Marshalls islands ko yau taje gida gobe akace ana neman ta zata dawo bankwana sukai jirgin su ya taso zuwa Nigeria already masu tararsu sun jima a airport d'in dama saukarsu ake jira suna sauka kuwa ba batun tsaye tsaye suka wuto masarauta wanda su Mami tsabar zumud'i kasa ha'kuri sukai suka fito tararsu a tare suka fito Amatu data manta wayarta cikin mota ta waiga zata d'auko a akasi bakinta ya ta'ba na Asad da sauri ta matsa baya wanda idon Ajeeb nakai sai kare musu kallo yake yana jiran su Mami su wuce yayi tsokana kuma yaji mamaki wato Asad bazai canza ba wallahi duk d'aukarsa zaiga sun dawo da baby wanda suka haifa hum Asad Asad!! Idan ya tsaya akan abu sai ha'kuri Ajeeb yana ganin su Mami sunbar gun daga shi sai Asad ya matso.
Cikin tsokana ya d'an daki kafad'ar Asad yana cewa "mutumina kana wuta fa irin wannan tsiyayar da soyayya haka har a titi🤓 ah lallai abu yayi kyau tunda ka iya kissing d'in ta a gabansu Mami nasan wallahi zakayi abinda yafi haka a gabanmu zan fad'awa su Ameer idan kuna guri saidai mu ri'ka rufe ido karkasa mu makance muna zaune lafiya kasa mu koma yawo da sanda kuma Bari na tuna maka ka manta ba matsayin mata ka tafi da ita ba matsayin 'kanwane? Ka dai tabbata babu wani abu daya faru ko"? Wani kallo Asad ya watso masa jin abinda yake cewa tare dajan tsuka mai karfi zai wuce.
Dariya Ajeeb yai yana cewa "kai d'an rainin hankali magana nake maka kodan bai shafeni ba bari na barka da mamin Naga da yadda zaka ceci kanka domin kayi mata alkawarin zaka dawo da ita yadda ka tafi da ita amma fa ni doctor ne naga wani abu a tare da ita Asad ciki ne da yarinyar nan"? Ajeeb ya karasa maganar yana kauda kai yana dariya kasa kasa dan da wasa yake so yake yaga yadda Asad din zaiyi.
A zabure Asad ya juyo yana kallonshi yace "Ajeeb maimaita abinda kake cewa kanka daya kuwa AMATU ce mai cikin ko wata dabam kake magana"? Harararsa Ajeeb yai kamar gaske ya had'e rai yana cewa "kwarai malam ciki gareta inaga ma yakai wata uku kwanan nan zaka zama Daddy amma kai kuna tare baka fahimta? Lallai Asad ashe kaima da akwai inda za'a 'kureka" zazzafan numfashi Asad ya fitar yana dunkule hannunsa yace.
"Ajeeb is this some kind of joke"?.
Mazewa Ajeeb yai yana cewa "kaifa ba da wasa nake ba malam just daina pretending kamar baka san komai ba inace kai ka d'irko mata cikin daga can🙊" Ajeeb na karasa magana cikin saurin azama da 'kakkarfan taku Asad yai ciki wanda Ajeeb ya kuma washewa da dariya yana cewa "tab Asad dama so nake na 'kure ka idan da lallami na bika ta ruwan sanyi baza ka fad'a min ba amma gaskiya da yake a tafashe kake ina bi ta ruwan zafi harna gano ka bari naje hospital din na dawo muyi wacce zamui" juyawa yai yana shiga mota.
Cikin sauri Asad ya shiga part dinsa ganin ba Amatu yasan tana bangaren Mami a zauce yayi can kamar an jefoshi mami ta ganshi suna zaune tasa Amatu gaba tana yi mata barka da sauka kawai sai ganinsa sukai har huci yake cike da mamaki mami tace.
"Asad meya faru kaifa ba wuya a fusata ka waye ya ta'bo ka daga dawowa ko hutawa bakai ba kodai Ajeeb ne dan nasan sai shi".
Bai baiwa Mami amsa ba sai Amatu da yake ta kallo sama da kasa ya zuba mata ido yana tunani baisan yanayin mace ba idan tana ciki amma Amatu normal take babu wani alama a jikinta.........
Katse masa tunani Mami tai "Asad wai lafiyar ka kuwa"?.
Sake bud'e idanunshi yai sosai akan Amatun yana cewa "eh Mami ina lafiya magana nake so muyi da Amatu".