← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 145

Sashe 47

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dalah na zaune tana sa'ka mifici na saidawa da take Indo tana kefenta sai bori take mata ta'ki cin abinci wai saita bata kud'i ta sayo irin alewar bahijjah itakuma sisi bata dashi sauri take ta karasa maficin ta bata takai shagon tunda dama mai shagon yana Sara saiya saya ya bata alawar shigowar Balarabe kenan jin yadda take kuka harda shid'ewa ya daka mata tsawa "uban me akai miki zaki damu mutane da koke koke kamar gidan mutuwa"? Yaro ba hankali kuma ka saba mahaifin ka na sake maka da sauri ta tashi tayi gurin sa bataji wannan tsawar dayai mata ba da gudu taje zatai masa oyoyo tana rike shi ya tureta yana wuce ciki kifawa Indo tai tana kuka da sauri Dalah ta mi'ke tana d'ago ta tare da kad'e mata kasar jikinta ta rike mata hannu suka koma bata karasa maficin ba tsabar takaici haka ta bata cike da damuwa tace "kar'bi kije gurin Bintan gidan Habu ai kinsan gidan ko"? Kai Indo ta d'aga tana goge hawayen fuskarta tace "eh na sani" cigaba Dalah tai "maza ki bata kice wai ta baki kud'in zaki sai alewa inji ni sauri" kar'ba Indo tai zata fita Asabe data fito daga d'aki ta riski karshen zancen Dalah bata ankara ba sai jitai an rafka salati a bayanta Asabe na cewa "to sabon salo gemu a kafad'a malam fito kaji wata magana ga Dalah nan ta aiki Indo maula dan a zageka a gari ace 'ya daya ka kasa mata abinda uba yakewa 'yarsa" kamar an hankad'o Balarabe ya fito yana cewa "meya faru" nuna Indo Asabe keyi "kalli man wai mafici ta bata ta wai waye a cikin matan Habubakar tace wai ta bata abinci yanwa take ji mu bamu girka ba tun jiya kaji fa bayan d'azu ta sauke abincin dan kawai tasa a gari a zageka" kumbura sosai Balarabe yai yana huci kamar zai rufe dala da duka "oh yanzu kuma sharrin da zaki min kenan daga kin bar wannan saiki koma wannan kinje gari kin yad'a wai banai miki sutura duk kayan da kike sawa kece kike dinka abinki na shareki ban nuna miki fushina ba shine kuma yanzu zaki fara tura ta maular abinci bayan ban rageku da komai ba ke wallahi Dalah kina da ba'kin hali indai baki canza ba zan dauki mataki a kanki" juyawa kan Indo yai yana fisge maficin "kema dan ubanki bani nan shekiya munafika tun baki girma ba uwarki zata koya miki halin tsiya halin karya gwafar ubanki zakici wallahi" ya karasa maganar yana ralla mata maficin aka sannan ya jefashi a wuta ya kone dur'kusawa Indo tai a gun tana kukan azaba Dan yajin dukan har 'kwa'kwalwata nuna Dalah yai da yatsa wacce take tsaye hawaye fal idonta yace "ke kuma daga yau sai yau kinyi na farko kinyi na 'karshe kada tsautsayi yasa na kara jin kin tura gidan uban kowa maula biyar bana tauye muku hakkinku wallahi tallahi idan kika sake makamancin haka saimu kwashi dambun tsiya dake sakarya bagidajiyar mata kawai" yana fadin haka yai waje yana maganganu dariya Asabe tai tana kallon yadda Indo keta mulmula gurin daya rad'a mata maficin tace.

"Hummm ubanku zakuci daga ke har tsogalgalar uwar taki zakusan wace Asabe dan wallahi sunana kawai kuke ji wannan somin ta'bi ne ban nuna muku komai ba yanzu aka fara wasan za'a kwashi yan kallo nan gaba kuma ki jira ki gani" d'aki itama ta shige tabar Dalah tsaye kamar bishiya dukawa tai tana d'ago Indo suka koma kan tabarma ta goge mata hawaye cikin danne damuwar ta dason farantawa Indon tace "kinga kiyi shiru ki daina kuka indai akan alewa ne zan sayo miki" cike da yarinta Indo tace "baba ne zai taho min da ita"? Kallon ta Dalah tai da sauri jin furucin datai Allah sarki cikin tausayawa wato dai babu abinda ya canza harta manta da abinda yai mata yanzu amma saboda ta kwantar mata da hankali tace "eh shine zai taho miki da ita kinga d'auki abincin kici zai kawo miki" da murna fal ranta ta dauka ta fara ci Dalah ta zuba mata ido kawai ta fad'a kogin tunani.

A ta'kaice bayan wani d'an dogon matsakaicin lokaci Bara'atu ta haihu yan biyu maza Hassan da Hussain haihuwar su day wata sha biyar ta sake haihuwar mace aka saka mata Nafisa Maimuna itama ta haihu mace sunan yarinyar salmah ta sake mace da namiji amma akwai gaf sosai tsakanin su da shekaru.

Haka a bangaren Habu ma A'i ta haihu mace sunan yarinyar Jamila tsakani shekara biyu da Binta itama ta haihu mace Habu yasa sunan mahaifiyarsa Hauwa (Amatullah) watan Amatu goma sha daya Saude ma ta sake haihuwar mace Aisha daga nan nefa rayuwa ta soma bun'kasa ahli yayi yawa saidai babu wani kyakkyawan zumunci tsakanin su da Ilyah baya sauraron su ko kadan kamar baisan da zaman suba abun ya damu Habu dan haka ya samu Sabi'u sukaje gurin malam Zayyanu aminin Baffah tare da zayyane masa komai akan ya kira Ilyah ya masa nasiha amma da Ilyah yazo bayan ya gama sauraron dalilin kiran bud'ar bakinsa cewa yai shifa kar a takura masa baida wasu yan uwa bayan matansa da 'ya'yansa da kuma dukiyar sa wannan abinda ya fad'a ya matukar 'kona musu rai babu irin shan kan da wa'azi wanda malam Zayyanu baiyi masa ba amma karshe mikewa yai ba magana ya karkad'e musu 'kura yai gaba duk binsa sukai da kallo ransu a 'bace musamman habu da yake jin kamar ya she'ka aguje ya sha'ke masa wuya hakuri da magana mai dad'i malam Zayyanu ya ri'ka musu da nuna musu cewa zai dawo kan hanya zai shiryu kuma suma suna yi masa fatan hakan kafin lokaci ya'kure masa.

Bayan d'agowar yaransu sun kasance babu makaranta ta zamani basu santa ba basayi saida aka zowa mai gari da takarda daga 'karamar hukumar da take mulkarsu dan haka tun jami'an basu tafi ba mai gari yasa aka tara magidanta na garin suyi musu bayani yadda zasu gane karshe bayan su tafi mai gari yasa akai shela nan fa gari ya dauka harda masu zagi wai za'a toshe musu hanyar samun kud'i haka kawai za'a 'kir'kiro makaranta wai ita boko wasu suna ce wallahi yaransu bazasuyi ba kaf 'kauyen baifi mutum biyar ne suka yarda da abinda ba'kin suka zo dashi ba ba'a garin 'karamar hukumar tai makarantar ba a wani babban kauye ne kusa dasu saidai garin nada girma sosai amma dai 'kauye ne bayan an kammala a gari tsirarun mutane ne suka shigar da yaransu wannan makaranta wadanda basu amince ba sunfi yawa suna yi musu kallon wawaye ganin babu yara sosai a makarantar ga malamai 'kwararru yasa suka kai kukan su cewa babu d'alibai wakili ya sake turowa aka sake yin shela ana bi gida gida ana daukar sunan yara da basu uniform da littafai da jaka da sandals kyauta ga motar yan makaranta school bus 🚌 wacce zata ri'ka fitowa dasu tana kawo su idan an tashi driver ya mayar dasu amma duk da haka a banza wannan baiyi aiki ba dan wasu iyayen har 'boye 'ya'yansu suke dan a 'bangaren Ilyah ma cewa yai Allah ya sauwake makarantar 'karyace da yaudara kila nan gaba su sace yara su gudu babu wanda zaiyi a yayansa kadan ne a garin ke zuwa amma habu dai babu wanda aka bari cikin yaransa kowa na zuwa shi baya jiran motar daukar d'aliban ma a tasa yake d'iban su yakai yawan zuwa da yake har tasa malaman sukai sabo dashi suka sanshi sosai sune silar da aka dawo kiransa da malam Habu yan gari na masa isgili wai kodai yana cusa kaine dan su d'auke shi koyarwa.

A wannan garin kuma da akwai wani mahauci ana kiransa 'kwalisa yara suka samasa sunan sakamakon idan yaje rafi yayi wanka duk sai jikinsa yai farin ta'bo da farar kasa kuma idan ya dawo gari saiya ri'ka tafiya irin ta yan gayu yana doro yara suna tsokanarsa kullum idan d'aliban sun tashi shi kuma nan ne gurin zaman sa wata ranar har kwana yake kuma gashi a lokacin sanyi ne yana kwance da dare sanyi ya dameshi ya kasa barci sai juyi yake yana ma'kyar'kyata tashi yai akwai wani guri ta bayan makarantar da aka jibge kara da yawa kawai yaje abinka da mahaukaci ba hankali ya dauko ashana a aljihunshi ya kunnawa karan wuta dan ya samu yaji d'umi tun wutar tana ci kad'an kadan hartai karfi yadda shima ta dameshi gashi dare yayi babu mutane jin zafi a jikinsa yasa shi matsawa daga gurin yana dariya yace "ina yara kuzo muyi 'kwalisa na kunna haske kun ganshi yana yawa kuzo muyi 'kwalisa na iya had'a haske" ya karasa maganar yana rawa da tafi shi kadai sai shirmensa yake yayin da wuta taci gaba da tsiri har farfatsi take haka ta fara kama makarantar nan ga gidajen garin kusan duk dangan kara yafi yawa ga iska da ake mai karfi watsuwar da wutar take yasa ta fara kama ko'ina gidanjen kusa da gurin farkawar wani mutum ganin hasken daya sa'ba hankali yasa ya fito da sauri daga d'aki zaro ido yai yana raraka wani uban ihu.

"Subahanallahi innalillahi wayyo Allah jama'a ku tashi wuta ta kama shikenan tamu ta 'kare" da gudu yayo waje yana kara zunduma wani ihun "ihuuuuh jama'a ku tashi gobara ta kama kara dan Allah ku farka" nan da nan mutane suka fara tittid'owa suna fitowa gari ya rud'e da salati kowa ya rasa inda zaisa kansa sai ruwa suke de'bowa suna watsawa amma kamar basa zubawa sai kara tsiri take kamar zata ta'bo sama ruwan gidaje ruwan rafi ruwan rijiyoyi haka suka ri'ka kwararawa da'kyar suka samu wutar ta mutu bayan tayi musu mummunan ta'adi duk ta kone gidajen dake makotaka da gurin babu abinda ya tsira sai mutanen gidan da yan kayan da suka samu nasarar fitowa dashi.
Chapter 47 · 0% Book details