← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 145

Sashe 105

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Bara'atu ta d'aga da sauri gudun kada su bada ita a gaban ba'ki tana cewa "to Bari nemo muku yanzun nan" tana kaiwa nan tayi waje da sauri harda tuntu'be Ilyah kadai take so ya shigo ta sanar masa zuwansu shima yayi taka tsantsan a samu a rabu lafiya tunda yanzu su sun zama qarfen qafa masu wuyar cirewa.

Bayan sun gama haka suka fantama dasu yawo layi layi har gidan malam Habu ganin gidan babu alamarsa sai fili ga tulun qasa a gurin yasa tun a hanya kafin suzo gida suka tambaya ina ya koma akace musu bayan tafiyarsu ga abinda ya faru sannan Ilyah ne ya saye gidan kuma Malam Habu a yanxu babu wanda yasan a duniyar da yake sai Allah sun sha mamakin Ilyah duk da yana mahaifin su da suka dawo gida kuwa tsiya iri iri suka sauke masa harda ya jira wutarsa tana nan tun daga yanzu an hura masa ita tana ci jira kawai take ya mutu tabalbaleshi dad'in abun ma a kofar gida sukai masa ba a gaban yan matan nasu ba su suna cikin gidan gurin dangin Bara'atu.

Da dare yayi ganin yadda mutane akai shimfid'a a waje kowa ya kwanta dayake lokacin zafi ne yasa Hassan kiran Bara'atu gefe yana cewa.

"Wai umma a ina 'yan matan mu zasu kwanta ne dare fa yayi barci sukeji"?.

Kallon sa Bara'atu tai tana cewa "a ina kuwa zasu kwanta baga shimfid'a nan anyi ba zata wadaci kowa".

Zaro ido Hussaini yai "kai akan tabarma kuma tabdijan gaskiya bazasu kwana a kasa ba".

Baki bud'e Bara'atu tace "au a sama zasu kwana kenan"?.

"A'a ba'a sama zasu kwana ba amma dai katifa zaki basu ko taki ko ta baba".

Kai Bara'atu ta jinjina tana cewa "lallai yaran nan baku da hankali nice zan baku katifa ta tana kan gadona na fito da ita wasu 'kattin su kwanta cab hummm".

Kallonta Hassan yai yana cewa "to meye ba surukanki bane basu isa kiyi musu haka ba ba'kin naku ne fa bikin 'yarku suka xo".

Kafin Bara'atu tayi magana Hussaini yace "abin haushin ma wai harda wasu 'kattin? Kai Hussainan tawa ce 'katti"?.

Wata uwar harara Bara'atu ta sakar masa tana cewa "au bazan fad'a ba sannu ubana saika rufeni da duka saboda nacewa wasu 'katti sai naga budurwa tafi uwa ko irinku ko"?.

Kau dakai Hassan yai "nidai Umma duk ba wannan ba kisan yadda zakiyi ki nemo musu katifa suna mota fa suna jiranmu Hassana har gyangyad'i take tsakani".

Tsaki Bara'atu tana cewa "wallahi indai bazasu zo ku kwanta a inda kowa ya kwanta ba saidai su kwana a motar wai me kuke haka ga guri nan malala da yawa amma dan masifa danku d'aga min hankali kunzo kun dameni haba da Allah gafacan kuban guri" ta karasa maganar tana wucewa ta koma cikin baranta ta nemi guri kusa da yan uwanta dake ta aikin yanka alayyahu dasu albasa za'ai sabuwar miya gobe ma gagarumin biki za'ai sannan da kusan magriba amarya tad'au hanyar birni kamar yadda take fata.

"Kan bala'i Hassan kaga wata shariya a gurin Umma wai da gaske take a cikin wadannan mutanen zasu zo su kwanta haka kawai su zuba musu 'kwar'kwata a kyakkyawan gashinsu🤣.

Tsaki Hassan yai yana cewa "wallahi bazasu kwana a kasa ba muje d'aki shegiyar amaryar ba bikinta suka zoba ta d'aga tata katifar ta basu ko naci ubanta" yana rufe baki sukai d'akin Nafisa a kwance suka sameta har tayi barci wani duka Hassan ya sauke mata wanda a firgice ta tashi cikin gigin barci ganin basawa tsaye a kanta yasa tace.

"Meya faru"?.

Harararta Hussaini yai yana cewa "ubanki ne d'aga mana katifa yan matan mu zasu kwanta".

Jin abinda yace yasa Nafisa tace "kai dan Allah Hussaini daga yau nima fa shikenan nayi bankwana da katifar kuma a kasa zan kwana"?.

Dundu Hassan yai mata yana cewa "a bola zaki kwana dan uwarki ba kasa ba har ana magana kina mayarwa mutane wato ke ga amarya ko rainin amarci ya shigeki wallahi so kike yanzu nan na karya miki qafa sai naga gaggawar zuwa gidan mijin shegiya 'kwartuwa🙈 zakici ubanki da qafafunki zaki nemi hanyar qauyenku ki gudu idan kikaji maza🙉.

SUBAHANALLAHI WADANNE IRIN YAYU NE WANNAN😂.

Tsayawa Nafisa tai tana kallon sa cikin tsawa yace "zaki d'aga ko saina hautsinar dake".

Ba arziki da gudu Nafisa ta d'aga tana ficewa d'aga d'akin tsaki Hussaini yai yana cewa "idan ba jaraba bama wannan yarinyar ina ta isa aure kaga fa yan matan mu dame muka fisu amma a hakan iyayensu sunce mana yara ne mud'an kara jira hummm zata ci ubanta ne kama muje" d'aukar katifar sukai waje.

Da gudu Nafisa ta karasa gurin Bara'atu tana kuka tace "Umma Kinga su Hassan sunje ina barci na suka daddake ni sannan suka qwace min katifa ta wai yan matansu ne zasu kwanta".

Dafe kai Bara'atu tai tana kallon ta tace "Kinga Nafisa daina kuka iya yau ne zaluntar taki gobe iyanzu koda kud'i bazasu ganki ba balle su zalunce kin saidai su zalunci kansu tashi kije d'akina ki kwanta" mi'kewa Nafisa tai tana shiga d'aki.

Bara'atu kuma ta tashi tana zuwa kofar d'akin su Hassan harsun shimfid'a katifar sun sa bargo su d'ame sun d'auko fulo guda biyu sun jera suna kafa 'kusa zasu daura musu net tabi Bara'atu ta ri'ke tana cewa.

"Yanzu ku kun kyauta kenan yarinyar tana barci tsabar ba'kar mugunta kuje ku daketa hakan bai isheku kuka murgineta kuka kar'be katifar yayi muku kyau".

Daina kafa 'kusar Hassan yai yana cewa ''to Umma tsakani da Allah kuma fa ba haka akeyi ba taya zamuzo da ba'ki tun daga wata 'kasar ku kasa tarbarsu da abun arziki alhali hadisi ne guda cewa "wanda ya bada gaskiya da Allah da ranar alkiyama ya girmama ba'konsa" kodan kuba sani kukai ba gashi yanzu na sanar daku gobe saiku tashi da wuri ku nema musu kayan kari na Alfarma don baza suci abincin biki ba sannan a ragunan baba a yanka musu daya ko a bamu kaji biyar gobe mu kaisu masu suya su sayo musu kuma naga wannan shegiyar yarinyar anyi mata gara to wallahi kar mu tashi tafiya ace ba'a d'iba musu ba tunda muna da mota har Kanon zamu bita muje mu d'ebo musu".

Sauke numfashi Bara'atu tai jin zai mayar da ita sokuwa ya d'ora mata ciwon kai bata biyewa maganar saba ta juya tana cewa.

"Allah ya shirye ku".

Dariya Hassan yai yana cewa "Amin Umma addu'a ce mai kyau kikai mana kai Hussaini jeka shigo dasu Allah yasa basuyi barci a cikin motar ba aiduk laifin umma ne kaga fa mu yadda suke mana acan ga mahaifansu na sonmu in munje suyita hidima damu amma nan sunxo gurin kwanciya mai kyau ma ya gagara haba" fita Hussaini yai yana shigowa dasu suka zo suka kwanta su kuma sukai waje domin ba sosai dare yayi ba.

Washe gari ranar yinin biki amarya an'ki zama guri d'aya ayi yu ayi nan fuuu sai sallama takewa mutane kamar bazata sake dawowa garin ba har abada bakinta har kunne yau zatai kwanan birni la'asar nayi motocin d'aukar amarya suka fara jerowa harsu biyar ras amma sakamakon yanayin dawowa saboda idan sun kaita acan zasu kwana su d'anyi mata gyare gyare sai su taho shiyasa aka za'bi mutum shida kadai motar amarya ita kad'ai sai Maimuna sannan sauran motar mutum had'un suka shiga aka dau hanyar birni dan tsabar d'oki da'kyar Nafisa ta tsaya aka d'anyi mata nasiha sai mi'kewa tsaye take ana dur'kusarta🤔 a haka aka gama fad'an ba lallai nasihar ta shiga kunnen ta bama hankalin ta ya kad'a gaba haka ta tafi tabar su Bara'atu da Ilyah cikin farin ciki da murna 'ya ta koma rayuwar city🏙️.

🏙️KANO🏙️
________Uhm Allah yayi amarya Nafisa a gidan Nurain yaudai mafarki ya zama gaskiya buri ya cika anzo birni za'a bararraje a gwangwaje a d'ebi nishad'i balle wadanda suka rakota ba yawane dasu ba daga mutum biyu ta bangaren Ramatu sai dangin Bara'atu suma su biyu sai kuma Maimuna da Salma suna zaune a part d'in da aka baiwa Nafisa sai zizzilla ido suke suna santin gidan Nafisa tazo aljannar duniya haka Nurain ya kawo musu kayan abinci da abun sha iri iri na alfarma masu tsada wanda basu ta'ba ganin irinsa ba wani tsoro sukaji kar suci ya jawo musu matsala sannan yace su tsaya su kwana saboda dare yayi musu gobe da safe sai yasa a mayar dasu aiko dad'i ne ya rufesu jin zasuyi kwanan daula.

Har Nafisa na tambayar Salma "amma dai Salma badake zasu koma ba? ki tsaya kimin sati tunda bikinki sai watan gobe zansa Nurain ya miki sayayya sannan ya kaiki har gida da kansa".

Zaro ido waje Salma tai tana kallon Nafisa dake wani fari da gwalli irin na amare kafin tayi dariya tana cewa "ni yar ubana rufa min asiri ban shirya zaman birni ba wallahi tare dasu zamu koma ba zaman da zan kimaji na fad'a miki dan kada ma kisa rai ehe bazan zauna ba".

Marairaice Nafisa tayi "haba ke kuwa Salma yanxu in kuka tafi bansan ranar had'uwar muba idan ba garin nazo ba dan Allah ki tsaya kiyi min sati"?.

Kai Salma ta girgiza tana cewa "kefa wallahi bazan zauna ba ko kwana d'aya ne yadda muka zo tare dasu tare zamu koma garama kibar ro'ko na".

Kallon maimuna Nafisa tai tace "dan Allah umma Maimuh kisa mana baki a zancen nan ko Salma zata yarda ta zauna min zansa Nurain ya mayar da ita".

Itama Maimunan da yake bata goyon bayan zaman Salman bataga me zata zauna tayi ba a yanxu dan haka cikin zillewa da wayancewa tace "a'a ni ba ruwana da safgarku ta shirme ku daina sani a ciki kuyi iyaku" ta fad'a tana kau dakai Salman ma ta kafe bazata zauna ba dole haka Nafisa ta ha'kura da niyyar idan Nurain ya shigo zata fad'a masa ya lallmi Salman ta zauna tayi satin.
Chapter 105 · 0% Book details