← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 145

Sashe 6

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Karasa ka duba"? Malam Habu ya tambaya cikin mamaki yana juyowa ya kalleta a gadarance tace "eh haka nace ko kana tunanin muna aiki akwai wanda zai tashi maka wahala bayan kai kazo nema" ran malam Habu a 'bace yace "Bara'atu kinsan abinda kike fada kuwa" wani kallo tai masa tana cewa "ni nasan abinda nake cewa domin ni a hayyaci na nake ina ci ina sha banda matsalar komai saidai azo inuwa ta a ra'bu a fake kai kuwa fa tun karayar arziki ta same ka kullum kana yawon maula a gidan kamar duk kauyen nan mune muka fi kowa arzik..................

"BARA'ATU!!!😡 Malam Habu ya fad'a cikin tsawa wanda hatta yaran dake zaune gefe suna cin nama saida suka tsorata nuna ta yake da yatsa idonsa yai ja na bacin rai yace "Bara'atu ki iya bakin ki a kaina wadatar da mijin ki yake dashi baki isa kice zaki wulakanta niba domin uban mu daya dashi baki San wahalar saba kawai kin ganshi a saurayin sa kika aure shi kuma shine kike neman zagi na"? Tabe baki tai tana cewa "eh ai isa nai" malam Habu zai magana suka jiyo muryar Ilyah na cewa "ke Bara'atu ke dawaye ne anan nake jin hayaniya haka"? Mikewa tai tana shiga d'akin sa ta dade kafin ta fito tana sake wuce su ta shiga wani wuri da alama dakin ajiyar abinci ne sai gata ta fito da daurin leda tana cewa "dama maula ce abinda ya kawo ku shi kanshi ya fahimta gashi nan garin kwaki ne yace a baka koda gishi kwa tsama kuci" ta karasa maganar tana aje masa a gaban sa kafin ta koma ta zauna.

Cikin fushi malam Habu yai bol da wannan ledar garin ya tarwatse yana huci yace "ai dama d'an talaka bai iya samun waje ba wato ke harkin manta irin ke wahalar da kika sha a gidan ku yanzu kin samu guri har kike gorantawa wani meye a gidan naku wacce tsiyar ce fad'a min" mikewa Bara'atu tai ta fara masifa ta zazzaga bala'i irir iri wanda yasa sauran yan matan gidan fitowa da sauri Nafisa ta karaso tana cewa "wanne d'an hauren ne ya ta'bo ki umma? Gaskiya mu mun gaji da wannan maula da ake zuwa mana hakan ma bai isa sai anyi cin mutunci to wallahi bazamu dauka ba"..............

Tana rufe baki taji saukar zazzafan mari a fuskar ta Wanda yasa ta fasa Kara tana durkusawa a gurin ta fashe da kuka da sauri Ilyah ya fito wanda duk abinda ake da yana ji bai fito sai yanzu da aka mari yar lelensa cikin fad'a ya soma magana.

"Wai Habubakar wanne irin wulakanci ne wannan ka zagi mata ta ka goranta mata ka shigo gidana kai tsaye ba neman izni na duk hakan bai ishe kaba saika marar mun 'ya to yanzu kam ya isa haka na gode zaka iya tafiya ba an baka abinda kazo nema ba" a fusace malam Habu yace "yaya Ilyah yau ni kake fad'awa haka a gaban matan ka da 'ya'yan ka nagode kuma ka nuna min iya matsayi na" jan hannun Amatu yai suka fita yana fita Bara'atu taja tsaki tana cewa "wallahi ko kadan bakai sa'ar dan uwa ba haba inaga da baka fito ba saidai a debi gawata yadda ya zuciya ya hauro dinnan tsaki Ilyah yaja yana huci yace "ni na rasa me yake damun sa saikace nine dora masa talaucin duk yabi ya addabe ni tunda karayar arziki ta same shi ya hana naji dad'i amma zanyi maganinsa kodan yanzu ma alhamdulillah nasan shi da zuciya watakila bazai sake zuwa gidan nan ba ni kuwa haka nake so kuyi sauri ku gyara kajin nan a dafa su in anjima zanyi manya baki wanda nake sarar kaya a hannun yan kauyukan nan nake sarar musu daga binni zasu zo dan Allah ku tsara abincin nan sosai" ya karasa maganar yana komawa d'aki ta tafar sauke Habiba amaryar Ilyah batace saidai tana mamakin bakin hali irin na Ilyah ace kana da wadata d'an uwanka baida shi Amma saidai ka wadata bare ka barshi yana yarfe gumi yana aunar abinci a shago da kasuwanni Allah ya sauwake ta fad'a a ranta tanajin takaici da nadamar aurensa haka Nafisa ta share fuskar yatsunsa kuwa d'as a fuskarta sun fito hakan yasa ta dau alkawarin daukar fansan.

Malam Habu na fita daga gidan Ilyah yai nufin zuwa gidan dayan yayan nasa Sabi'u yai sa'a kuwa ya same shi a kofar gidan sa zaune mutane sun kewaye shi irin masu neman na kayan miyar nan ganinsa cikin jama'a yasa bayan yayi sallama sun gaisa ya nemi su d'an ke'be can nisa da mutane suka tafi karkashin wata bishiyan kuka malam Habu yasan da kamar wuya amma zai gwada kokarinsa yana fatan yakai nasara "ina jinka Habubakar ya akai ne na ganka duk a hargitse"?.

Ran malam Habu a bace yace "yanzu tsakani da Allah yaya abinda matar yaya Ilyah tai min tayi daidai yanzu shi daya goya mata baya bayan yanajin irin cin fuskar datai min ya kyauta min kenan ya kyautawa Bappan mu"?.

"Meya faru ne Habu meya hada ku me kaje yi gidan"?.

A hankali cikin nutsuwa malam Habu yai masa bayanin komai kai Sabi'u ya jinjina yana cewa "ai indai Bara'atu zatai yafi haka ba kirki gareta ba ta maganar kane dan talaka bai iya samun waje ba amma babu komai karka damu za'a biya mana ina maman namu take nawa ne kudin ai na fad'a maka duk wata matsalar ka idan ta tashi ka rika zuwa kana fad'a min ka kyale Ilyah indai ba harkar zumunci bane yanzu ka wannan maza da sauri kaje ka biya mata" karba malam Habu yai cikin jin dad'i da kaunar yayan nasa Wanda yake share masa kuka a duk sanda ya kawo korafin sa bai ta'ba nuna gajiwa ba ya mike yana sake masa godiya da fatan alkairi kafin yaje ya rike hannun Amatu suka wuce da kwarin gwiwa ya mayar da it's makarantar ya biya mata komai sannan ya shiga cikin gari dayake makarantar ba a garinsu take ba kusa da kauyen sune saida aka tashi ya biya ya dauketa suka tafi gida.

Sauke ajiyar zuciya Amatu tai tare share hawayen fuskarta bayan ta dawo daga tunanin da take ta sani mahaifin ta mutum ne na 'kwarai mai kyawawan halaye sannan ya na son farantawa ahlin sa amma babu ta gama mamaye shi sauke kanta kasa tai ganin Binta ta zo wuce wa dan kada taga cewa kuka take, Amma me tuni ta hango ta tun daga nesa Saida tazo saitin ta tace "Amatullahi me akai miki kike kuka"? Jin tambayar datai mata yasa wasu sabbin hawayen sake gangarowa da sauri tasa hannu ta goge bude baki tai kamar zatai magana ganin Bintan na tsaye a kanta tana jiran amsa sai kuma ta kasa cewa komai a karo na biyu Binta tace "mamar gida tambayan ki fa nake me akai miki kike kuka"?.

Kai Amatu ke girgizawa da'kyar tace "umma shin bazan iya taimakon baba ba"? Da mamaki Binta tace "kamar ya"? Cigaba Amatu tai da cewa "umma zan koma gurin su Abba Bashir 'kanin ki na fara kasuwanci domin na taimaki baba wannan damuwar dake damunsa na gaji da gani bazan iya ba a iyasani na mahaifi na mutum ne me annurin fuska amma yanzu koda yaushe baya ciki walwala ki tuna yadda ya ri'ka kula dani ya taso dani a cikin gata ya bani komai da nake bukata a rayuwa idan na zuba ido yaci gaba da zama a haka na yaudari kaina na cuci kaina bazan iya yafewa kaina ba umma ina bukatar taimako" ta karasa maganar cikin kuka sosai wanda ke fitowa daga asalin ainishin cikin Zuciyar ta".

"Kinga mamar masu gida kiyi hakuri haka kinji karki jawo hankalin mutan gidan a kanmu" rufe bakin umma keda wuya caraf sukaji A'i na cewa "aikin banza kenan rigar bayan salla meyi ake cewa tai shiru kar muji za'a boye mana ko saurayi tayi ko kuma wani laifin tai ba'a so mu sani iye a fad'a min domin idan baku fad'a ba kun barni cikin zulumi" juyawa Binta tai tana kallon A'i dake wanke kwanuka batare datai magana ba tace "Amatu tashi ki koma kinji ina zuwa" mikewa Amatu tai tana shiga kamar yadda umman ta umarce ta.

Tabe baki A'i tai tana cewa "oh ni Indo yanzu Binta abin har yakai ga haka kin fara hurewa yarki kunne dan ta raina ni ina matsayin matar ubanta saboda kina kishi dani".

Kallon ta sosai Binta keyi cikin mamaki wato ta fahimci A'i ba 'yar neman zaman lafiya bace wa ya sako da ita har zata dauka..........

Katse mata tunani A'i tai "dake fa nake Binta"? Wani kallon umma ta kuma aika mata dashi batare datai magana ta wuce uzurinta dariya A'i tai tana cewa "ahahaha hayye kai ni yar gidan baba gaskiya akwai tantirai a gidan malam Habu gashi kuwa sun fara bayyana Allah ya tonu asirin su suna shirye shiryen zuwa gurin boka to naji ku sai ku sake shiri ku taka a sannu idan ba haka ba yanzun nan na garzaya na sanar da mai gari" ko kula iskar ta umma batai ba balle tasa ran ta mayar da ita mutum kawai aikin gabanta take.

🥀🌻MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘 MAI TAMBARIN YMA DUTSE 🏞️''YAR MUSA JIKAR ABUBAKAR MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY 💃.

Mrs Al'ameen Ahmad ce mai tambarin yma dutse sabuwar duniya 🌍new world new life 🌌 and new style 👌.

🌹 Yusrah Musa Abubakar ta kowa ce kuma ni I have no girman kai if you are fushi dani tofa you are just 'batawa kan k lokaci 🕐.

Manzon Allah mai Makkah mai birni da 'kauyuka.

A gaskiya naji dad'in comments dinku yan uwa matukar jin dad'i da yadda kuka gwada kauna ga littafin nan hakan da kukai ya faranta min kuma na sake samun sabon confident na gwarin gwiwa daga gare ku kuma albishirn ku insha Allah zan dage kamar yadda kuka bukata naga kullum nayi muku posting koda kadan ne ngd da yabawa💖💕👏.
Chapter 6 · 0% Book details