Sashe 85
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaman dirshen Asabe tayi a kasa tana fashewa da wani kukan ba'kin ciki tare da d'ora hannu aka tana kiran "shikenan nikam na shiga uku na lalace haihuwa batai min rana ba Markah wanne wacce irin yarinya tana neman kasheni lokaci na baiyi ba Wallahi tallahi bazan yarda ba yanzun nan zan tafi gurin boka shashirgi ya kashe min wannan mitsiyacin yaron idan taga baya duniya dole ta ha'kura dashi shege tsinanne mara tarbiyya yazo ya gur'bata min komai wayyo Allah na wayyo nashiga uku..................,..
Katseta Markah tai da cewa "a'a dan Allah Asabe kiyi shiru haka ki daina kiran masifa akanki tashi mu tafi gurin bokan zanyi masa bayanin komai abinda faruwa ina Mai tabbatar miki Bahijjah zata dawo gareki bazata ta'ba auren Iluh bs tashi mu tafi qawata a Bari ya huce yana kawo rashin sa'a kinga yanxu ma gashi kin koreta a gidan kuma ai kinga Baki wanke biyar ba kin bata goma tunda kinsan ko tantama Babu yanzu haka tana gurin sa".
Zabura Asabe tai ta tashi tana surar hijab tace "muje Markah mu tafi gurin boka kafin zuciyata ta buga da ba'kin cikin yarinyar nan wallahi kawai kashe shi za'ai bazan iyaba" Kai marka ta d'aga "kwarai Asabe wannan ce kad'ai mafita a kashe shin zaifi sau'ki muje" fita sukai Markah na ce mata ta goge hawayen fuskarta saboda kar mutane su gani a tsaya tambayar ba'asi.
Bahijjah Kam data samu ta fita da gudu daga gidan bata tsaya ko'ina ba sai kofar shagon Iluh yana zaune sai ganinta yai aguje tana waiwaye tana kuka mi'kewa cike da mamaki duk da yasan bazai wuce akan binsa datai garin su bane amma sae yace.
"Lafiya Bahijjah meya faru haka kiga harda jini a goshinki Babu kwali ba takalmi balle uwa uba hijabi"?.
Cikin kuka Bahijjah tace "Iluh kana sona"?.
Da sabon mamaki Iluh ya kuma kallon ta yana cewa "kamar ya wannan wacce irin tambaya ce kuma? Ina sonki mana".
Kai ta jinjina tana goge hawaye tace "zaka aure ni"?.
"Eh aurenki man zanyi".
"To Iluh indai da gasken kana sona aurena zakai ayau Iluh ka koma garin ku kazo da mahaifanka su kawo komai zuwa Nan da wata d'aya a d'aura mana aure shine abinda nake so kawai kayi min yanzu ka huce min zuciya".
Kai Iluh ya d'aga yana murmushi yace "shikenan karki damu yanxu ma kuwa zanje gobe zamu zo tare dasu karki damu ai ninace Ina sonki" jin abinda yace yasa Bahijjah goge fuskarta tana samun guri ta zauna koba komai tasan idan iyayen sa suka zo dole Asabe ta karbesu ta kuma yarda da auren idan ba haka ba saita d'ebo Mata 'yan hisba😳.
Nurain yayi waya da Nafisa ya sanar mata mahaifansa zasu zo rokon arziki tunda ya fad'a Mata take ihu har mutanen gidan sun d'auka ba qalau take ba fitowa daga d'aki tai da gudu tana cewa "
"Umma ki tayani murna yanzu Nurain yake sanar min cewa na fad'a muku a cikin watan nan mahaifansa zasu zo ro'kon arziki na garin nan"
Zaro ido Bara'atu tai tana washe baki tace "tofa 'yan binni zasu zo ashe kwanan nan zamuyi manyan Ba'ki tab bari babanki ya dawo na fad'a masa a fara tanadar kayan tararsu tun daga yau wadannan shashashun yayyin naki ma su dawo a sanar musu su kawo tasu gudun mawar kilar sunan can gidan fatararran can Habu😵...
Nafisa Kam saboda farin ciki take bata kula da zancen da Bara'atun datake Mata ba kawai Kira take "wayyo Umma wallhi harna hasko ni a binni umma na kusa zama yar gayu kun kusa fara cin shinkafa yar buhu da taliya haka zan ri'ka ciko mota ana kawo muku🤭.
Itama Bara'atu dariyar tai cike dason zuciya tace "yauwa Nafisa haka nake son ji ki tabbatar kina lalarsa kud'i masu tsoka kina turo mana zan ri'ka zuwa akai akai duk bayan sati biyu😲 Ina kar'bo komai kema kwanan nan sai kiga kin gaji ubanki a sai miki gonaki filaye da shanu da kuma awakai ko".
Kai Nafisa ta d'aga "kwarai umma meyasa tun farko Salma itama nace tacewa baba tana son d'ayan abokin Nurain amma ta'ki wai ita sai Adamu yana tafe daf da qasa kamar d'ingwai d'in kaza abu kamar tuntu'be gashi gidansu talakawa ne basu da kud'i ranar naganshi tare da babansa sun tafi 'kwadago noman kud'i gonar Mai gari sunata sauri kamar zasu kifa..........,...........
Rufe mata baki Bara'atu tai tana kallon kofar d'akin Maimuna tace "ke Dan ubanki kiyi shiru kar maimuna taji kina cin mutuncin surukinta dariya Nafisa tai tana tafa hannu Bara'atu dake le'ken ta inda Maimunan zata bullo murya ta d'aga tana cewa "Maimuh Maimuh kina nan"? Jin shiru yasa ta sake kwalla Mata Kiran da qarfi "Maimuh nace kina d'aki ne ko barci kike"?.
Jitayi daga wajen kofar kewayen shanunsu ance "a'a kin ganni nan Ina baiwa raguna dusa ne Bari nazo".
"Oh na d'auka kina cikin d'aki ai"Bara'atu ta fad'a tana kallon Salma data shigo tun kafin tayi magana Nafisa tace "Salma ki taya ni da na kusa tafiya binni a watan nan mahaifan Nurain zasu zo maganar auren mu".
Murmushi Salma tai cikin tausayawa Nafisan haka nan taji jikinta yayi sanyi hankalinta bai kwanta da auren Nafisa da Nurain ba amma dan kar suce ba'kin ciki take Mata yasa tace.
"Alhamdulillah na taya ki da murna sosai Nafisa Allah ya sanya alkairi kice kwanan nan zamu shiga cikin Kano muga yadda take"? Ta karasa maganar da yar dariya.
Cikin zumud'i Nafisa ta fara ido tana cewa "kwarai Salma ki tanadi Kaya masu kyau kafin na fitar da anko ki fad'awa Adamu ya d'inka miki kamar kala biyar domin ke acan za'a baro ki sai kinyi min sati biyu ko wata d'aya kafin nasa Nurain ya dawo dake".
Zaro ido Salma tai tana kallon Nafisa da mamaki take "niii kaza mijina zakara rufa min asiri ban shirya zaman binni ba ki barni a kauye na inda nafi wayo naci abinda nake dashi nasha ruwan rafi dana rijiya zanfi zama lafiya".
Nafisa zatai magana maimuna ta karaso gurin tana cewa" gani in kaji Kira an samu amma banda kiran Dan sanda lafiya miya faru tun d'azu naji sai dariya kuke"?.
Ai tun kafin Bara'atu tai magana Nafisa tai wuf tace "umma Maimuh ki taya ni murna mahaifan Nurain zasu zo ro'kon arziki na na kusa tafiya binni"🤔.
Ba Umma Maimuh ba hatta Bara'atu saida ta zaro ido ganin yadda Nafisa ke fad'ar magana kai tsaye Lallai kam zasu Sha kallo dariya Maimuh tai tana cewa "to kice mu shirya kar'bar ba'ki Allah ya kawo su lafiya".
"Amin umma Maimuh Wallahi harna hasko ni a binni".
Kai maimuna ta jinjina tana cewa "Allah dai ya kaimu lokacin Nafisa yasa ayi a sa'a sannan Allah yasa gidan zama ne".
Amin suka ce Nafisa daketa faman sambatu tace "umma a idon zuciyata har haskoni nake a binni wai".
Murmushi Bara'atu tai tana cewa harkin hasko ki a binni Kona haskoni saboda idan kikai aure naje miki ziyara sai nayi wata dazan dawo gida saina huta😮.
UMM INJI MAI CIWON BAKI.
Baki maimuna ta bud'e tana kallon Bara'atu tace "haba dai wata fa sai kace a garin ga'ba-ga'ba kije gidan mijin 'yarki kiyi wata ana zaune lafiya"?.
"To meye a ciki maimuna Dan nayi wata ko shekara zanyi nasan yadda wannan yaron yake da kud'i bazai gajiya da yimin hidima ba dan haka wallahi zuwa zan ri'ka yi akai akai Ina kwaso Mana kayan dad'i".
Kai maimuna ta jinjina tana cewa "to shikenan Allah ya kaimu lokacin Allah yasa ayi a sa'a shine fatan mu" Amin Bara'atu tace yayin da Nafisa ta mi'ke tana d'auko hijab tace Salma wai ta rakata gidan kakanunta "gidansu Bara'atu) ta fad'o musu Salma Kam tace bazataje a dawo lafiya fita Nafisa tai Wanda umma Maimuh taji mamaki da taga Bara'atu bata hanata ba ta d'auka zatai Mata magana sai taga tayi burus har wani bin Nafisan take da kallon burgewa wai tana abun wayayyu.
Yau kam gidan malam Habu a cike yake da murna Amatu ta dawo gida na dindindin Dutse saidai taje da sunan ziyara musamman Malam Habu kamar ya mayar da ita ciki haka yasata a gaba kawai yake ta kallonta har hawaye yana zuba a idonsa batare daya sani ba muryar Amatun ce ta dawo dashi daga tunani.
"Baba Dan Allah ka daina kukan haka zan shiga damuwa".
Murmushi Malam Habu yai cikin sauri ya goge hawayen fuskarsa yana cewa "mamana hawayen farin cikin ganinki ne saboda wata irin kewa da naji tana kama ni bansan taya zan kwatanta miki ki fahimta ba mamana dukanku Asma'u Jamilah Aisha dake yarana ne kuma ina tsananin sonku amma maganar ke kin fita dabam acikin su arai nake jinki mamana fatana Allah ya d'aga darajarki Allah ya d'aukaka minke7 ya kaiki matsayin da ban ta'ba zato ba mamana................
Kukan da Amatu tasaka masane ya hanashi karasa abinda yake son cewa sai kawai yayi murmushi yana cewa kada ki damu kinji mamana insha Allahu albakata tana tare dake a koda yaushe kece nutsuwa ta bana so kiyi nisa dani saidai na sani dole wata rana zan bud'e ido na rasa ki a gidana tunda zaki aure Allah yasa wanda zaki aura mamana ya mutunta minke ya rikeki ya soki ya kyautata miki ya baki kulawa wacce bamuyi zato ba saboda da gudun kada a wahalarmun dake nake jin a raina kamar bazan iya bada aurenki ba mamana amma ya zama dole, murmushi yai yana kallon ta yace.