← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 145

Sashe 95

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batun su malam Habu kam sunyi tafiya iya tafiya kawai daji suka yanka har dare yayi musu dole suka tsaya a cikin wata rugar fulani suka ro'kesu kwana d'aya kafin wayewar gari kuma sukai sa'a suka samu yan arziki kamar sun sansu haka sukai maraba dasu sukai musu hidima duk da a gajiye suke amma sakamakon mutanen masu fara'a ne yasa malam Habu dasu Binta zama tare sukaita hira harda dariya wacce malam Habu rabon da yayi dariya su gani harsun manta yaushe ne haka suka raba dare sosai sunata musayar magana sannan kowa yaje ya kwanta washe gari saida rana ta fito sannan sukai shiri sukayi musu sallama sukaci gaba da tafiya kamar yadda suka fara basu samu hanyar bi su fita daga dajin ba dole da wani daren ya riskesu a hanya sukai kokarin tsayawa su kwana a dajin saidai wannan karon babu gidan fulani ko d'aya daga daji sai burtali babu kuma d'an abinda zasu kafa tanti su kwana kafin wayewar gari hakan yasa malam Habu yace musu kowa ta gyara d'an wani guri ta shimfid'a zaninta ta kwanta shi kuma yaje ya 'ballo wani babban itace ya dawo yayi tsaye a kansu yana gadinsu ta inda ya samu sau'ki ma akwai hasken farin wata yakan duba kowacce idan an d'auki lokaci saboda gudun kada abu Mai cutarwa ya samesu irin su miciji kunama ko wani mugun 'kwarin da danginsu haka ya kwana tsaye a kansu har asuba sannan suka tashi idonsa kuwa yayi ja sosai ya kumbura karkad'e zannuwan sukai suna mayarwa cikin kayansu yace musu suyi gaba su nemi ruwa ayi sallah tafiya suka cigaba dayi gari ya fara haske suka samu wata rijiya a dajin da guga a kafe anan suka tsaya da gugan wasu sukai alwala saboda lokaci na neman 'kurewa wasu kuma sukai da gora bayan sun idar suka d'ora tafiya dama babu wanda yasa rai da abinci a wannan dajin dan haka ma yunwa bata damesu ba basu daina tafiya ba kuma basu tsaya hutawa ba saida suka daidaici lokacin sallar Azhar sannan suka tsaya da ruwan gorunan da suka d'uro sukai alwala sukai sallah a karkashin wasu bishiyoyin goba ayaba🍌 mangoro kashu sun nuna matuka sunyi ja sosai tun suna sama domin a daji suke ba wajajen mutane bane balle a yagesu amma suna kallo Malam Habu ya hanasu su ta'ba yace musu idan sunci maishi bai sani ba sunci haram domin na wani ne a cikin gona suke kuma zasu biyashi a lahira kawai suyi ha'kuri su rike yunwarsu Allah zai basu halak a gaba haka suka mi'ke cikin 'kwarin gwiwa sukai gaba sun d'anyi tafiya suka had'u da wani gida 'kwal shi d'aya a dajin sai shanu masu yawa gasu nan sunata kiwo wasu suna kwance da alama dai gidan fulani ne tsayawa sukai a waje sukai sallama da Mai gidan bayan ya fito Malam Habu ya tambaye dan Allah ko zasu samu kindirmo na sayarwa su matafiya ne daga gari kaza suke kuma sun kwana a dajin nan sun wuni amma basu samu abinci sunci ba cikin tausaya musu d'an fulanin ya musu izinin shiga ciki sannan kuma babu dafaffan kindirmo sai d'anye ya tatso musu suna zaune matarsa ta kawo musu ruwa suka sha shi kuma ya aje musu yana daukar kwando ya fita daga gidan.

Zuwa wani lokaci ya dawo d'auke da kwandon a kansa fal kayan marmari ya sauke yasa matar ta d'ebo ruwa ta wanke ya kawo musu yace suci kafin a 'kare abinci sunyi mamaki wato dai wannan gonar kayan ta wadannan fulanin ne malam Habu yayi gaskiya da yace suyi ha'kuri zasu samu halak a gaba gashi kuwa da sukai ha'kurin sunci halak d'in mai abun da kansa ya basu duk da sanda ya hanasu tsinka kowa ransa ya biya.

A gidan suka karasa wuni har bayan sallar la'asar ganin kada lokaci ya 'kure musu suba masana daji ba basu San karshensa ba yasa malam Habu yaiwa fulanin sallama yace zasu d'ora tafiya tambayarsa sukai inda zaije daga yace shima bai sani ba yana son fita dai daga dajin ya samu hanya ne dan haka sukace masa ya tsaya ya kwana gaskiya yanzu idan yace zai fita a dajin dare zaiyi masa saidai gobe da safe su sashi a hanyar inda ya kamata yabi godiya ya musu sosai kuma yayi farin ciki da karamcin da suka nuna masa dashi da Iyalansa.

Washe gari da safe bayan sun karya sukai wanka a gidan domin tunda suka baro gida yau kwana uku babu wanda jikinsa yaga ruwa inba na alwala ba bayan sun gama shiri haka d'an fulanin ya wuce gaba domin ya fitar dasu a dajin harda matarsa suka tafi saida suka kaisu ga'bar dajin suka sasu a hanya sukayi musu kyakkyawan kwantance inda ya kamata subi sannan sukai bankwana harda basu dubu goma d'an fulanin yayi yace malam Habu yai 'karin guzurin tafiya Allah ya tsare ya kaisu lafiya duk inda suka nufa ya saukesu cikin sa'a godiya sosai Malam Habu yayi musu har saida sukace masa ya isa babu komai kafin suka sake gaisawa da sallama suka wuce su kuma fulanin suka juya zuwa gida.

Kamar yadda sukai musu kwatance haka suka ri'ka bi sannu a hankali duk wata alama da fulanin suka fad'a musu zasu gani sun gani har suka samu suka fito daga dajin sai gasu a wani karamin gari wanda ba mutane da yawa wani mutum da suka fara had'uwa dashi Malam Habu ya tambayeshi dan Allah nan wanne gari ne ya fad'a masa sunan garin yayi masa godiya sukai gaba a wannan garin ko zama basuyi ba suka tari 'yan mashina malam Habu yace su kaisu bakin titi inda zasu samu mota.

'Daukarsu sukai a jere bayan an gama ciniki suka fita dasu daga garin suka kaisu bakin titi wajen 'yan yuniyan masu tsare mota biyansu hakkinsu malam Habu yai sannan yaje gurin yan yuniyal d'in yace musu Kano zaije to sukace masa amma ya jira kafin a samu mota komawa yai ya zauna zuwa wani lokaci da aka samu mota kamara ce ma taxi🚗 babu kowa a ciki suka tare masa ita aka saka musu kayan a but sannan suka shiga bayan direban ya sallami 'yan yuniyal d'in ya shiga suka tafi.

A hanya yake tambayar su wacce anguwar za'a kaisu malam Habu yace shi baisan sunan anguwanin Kano sosai ba idan badan yanajin radio ana fad'ar wasu ba murmushi driver yai yana cewa "nima kuwa kaga ba d'an Kano bane daga yola na taso na dawo nan farko bakaga irin wahalar danasha ba kafin na zama d'an gari a farawa nafara zama ina haya mai gidan ya tashe ni ya zuba wasu tsabar wulakanci ba laifin tsaye bana zaune ba hanashi kud'in hayarsa nake ba amma ya tozarta ni daga nan na tashi na dawo d'orayi a nan ma mukai fad'a da Alhajin da nake hayar a gurin sa nan shima dai ya koreni yanzu maganar da nake maka Ina anguwar kabuga jan bulo na samu wani d'an arziki tunda na kama hayar gidansa ko banida kud'i yana d'aga min kafa kusan shekara goma maganar da nake maka a yanzu idan za'a kar'bi kud'ad'en hayar gidajensa ni yake wakiltawa ya yarda dani fiye da yadda kake tunani ko wannan motar da kake gani shine ya saya min nake haya kuma kwata-kwata a wata cewa yayi na ri'ka bashi dubu goma ai kafin a samu irinsu Alhaji Abubakar masu kyawawan zuciya za'a tona suna wuya a yanxu Malam humm".

Shiru Malam Habu yai cikin tunani ko yai nasa magana idan zai hadashi da Alhajin? Eh kawai ka tambayeshi tunda bakasan inda zaka samu sa'a ba jin zuciyarsa ta bashi shawara yasa ya d'ago yana cewa "a wata nawa kuke biya kud'in hayar"?.

Kai driver ya jinjina har malam Habu ya tsorata ya d'auka kud'ad'e za'a fad'o masa sai yaji yace "ba wata wata ake biya ba yanayin yadda ka kama gidan dakuna biyu da toilet da kitchen dubu d'ari ne a shekara".

Sauke ajiyar zuciya malam Habu jin sai shekara ma ba duk wata ake biya ba yace "ko zaka had'ani dashi idan munje kano d'in Nima dama bansan inda zanje ba banida kowa bansan kowa ba kawai daka na taho neman kud'i".

Kai driver ya d'aga masa yana cewa ''ok ba matsala amma gaskiya yanzu baya gari yayi tafiya zuwa wata 'kasar sannan indai ba yana da wasu gidajen a wasu anguwanin ba bana tunanin akwai sauran wanda suke empty ba mutane a ciki gaskiya ba lallai ku samu ba yanzu wacce anguwa zan kaiku"?.

Shiru Malam Habu yai jikinsa yayi sanyi har saida ya sake tambayar sa sannan yace "kaimu can anguwar da kake meye ma sunanta"?.

"Jan bulu" driver ya fad'a yana kallon sa.

"To ka kaimu can Allah ya dafa mana🤲" Amin driver yace🙏 daidai sun shiga Kano ya tsaya yasha mai kafin ya tashi mota ya d'ora tafiya zuwa wani lokaci ya shiga anguwar saida ya samu inda ya kamata ace ya saukesu gurin da ba fuskar mutane ba inda yake da wani kango sannan ya tsaida mota suka fiffito ya bud'e but ya sau'ke musu kayansu Malam Habu ya biyashi yayi masa godiya sannan drivan yace masa karya damu zaiyi waya da Alhajin zai tambaya masa idan akwai zuwa Nan da karfe goma na dare zai ganshi ya dawo gurinsu to malam Habu yace masa ya sake masa godiya.

Bayan driver ya tafi suna nan zaune kamar marayu umartarsu Malam Habu yai cewa su tashi su shiga cikin wannan kangon suyi sallah amma karsu shiga da kayansu tunda ba tambayar meshi sukai ba ya sayo musu ledar pure water guda biyu ya kawo musu kowa ta d'auka tai alwala sukai sallah yana tsaye yana jire musu kayansu saida suka fito shima yayi tasa alwalar a matsayinsa na ba'ko baisan ko'ina ya tafi neman masallaci daka ya samu akusa yayo sallah ya dawo sai kuma yunwa da take damun kowanne nan kuma birni ba qauye bane balle ace za'aga masu abincin saidawa a layi suna yawo dashi nan saidai restaurants ko masu saidawa a shaguna.

Sunata zaune zaman jiran tsammani har wani yaro yazo wucewa da bokiti a hannunsa tambayar sa malam Habu yai.
Chapter 95 · 0% Book details