Sashe 19
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"AMATULLAHI" taji Bashir ya fad'a wanda ya katse mata tunani muryarta na d'an rawa tace "na'am Abba" cigaba Bashir yayi "naji abinda kike so ki zama soja indai shine burinki zanyi kokarin cika miki sannan na biki da fatan alkairi da sa albarka a duk inda kika tsinci kanki ki zama mai juriya da tawakkali ki yarda da kaddara mai kyau ko akasin ta kinji" kai ta d'aga "eh Abba nagode Allah ya saka maka da alkairi ya kara arziki" "Amin yace yana mikewa shima ya fita Binta da bakinta ya'ki rufuwa tace "tofa maman masu gida ke kuma abinda kike sha'awar yi kenan soja ikon Allah babu abinda nake tsoro a rayuwa ta kamar naga soja😂 ashe wata rana zan bud'e ido naga 'yata jini na da kayan sojoji" murmushi Safiyyah tayi tana cewa "ai aunty haka al'amarin yake sai godiya kin gani dai ga Amatullahin ki tace soja take so masha Allah" huuuuuuh sauke ajiyar zuciya Binta tai tana mi'kewa tace "kinga kar zuwa miyattin nan ya shiririce min bari na tashi" katse ta Safiyyah tayi "ai aunty na ta kaina dakin barshi idan naje zance kinzo kina ma gaishe dasu" kaita girgiza "a'a barni Safiyyah dole naje mu gaisa da mahaifanki sun iya bada tarbiyyah tsakanin mu dasu sai son barka irin ahlinku ake nema a had'a jini dasu" murmushin jin dad'i Safiyyah tayi na yabon da Binta kewa mahaifanta tace "shikenan aunty mu gode sai kin dawo ni kuma Amatu tashi ki raka ni yadi gidan 'kawata" to tace tana mi'kewa Nabilah data dauko jaka tace "nima dai momy binku zanyi" hararar ta Maryam tai "baki isa ki rusa min tafiya ba tun shekaran jiya nake bin yarinyar nan ta raka ni na kar'bo dinkuna na tace sai yau kuma dan rainin hankali kice wani bazaki jeba aiko baki isa ba" had'e rai Nabilah "ina ce 'kafa tace bata mutum ba kuma nace na fasa rakiyar ko dole ne"? Kai Maryam ta jinjina tana cewa "mom kina jinta tanai min raahin kunya ko"? Cikin son raba fad'an tace "kinga Nabilah ba'a haka kin manta kome kikacewa Maryam kina so tanai miki idan har baki raka ta ba nan gaba kikaga wani abu a gurinta kina so ko kice ta baki kaza ko tayi miki kaza ni da kaina zan hana ta domin ba kece kika gina ta ba" kwa'be fuskarta Nabilah tayi "ni mom ke nake son bi" "na sani Nabilah kiyi hakuri ki raka ta meye zan taho miki dashi nasan yanzu tayo sarin kaya" Nabilah na kumbura fuska tace "takalmi da jaka sai mayafi shi nake so" "ok karki damu zan sayo miki tashi kuje ki rakata" badan ranta yaso ba tana jujjuya kai suka fita Maryam na balbale ta da masifa "wallahi Nabilah kina bani mamaki wai tsabar wulakanci in kina son abu a gurina kiyi ta min ladabin kura ga mai akuya amma babu komai bari Abbanmu ya dawo zan hada ki dashi" ita dai Nabilah shiru tai tana bin bayanta har suka fita harabar gida ta jirata taje ta dauko motar tana shawo kwana da ita sannan ta tsaya bud'e kofa Nabilah tayi ta shiga suka wuce.
A zaune Malam Habu yake a cikin d'akinsa ya zuba wani uban tagumi mai ban tausayi yayi zurfi cikin tunanin rayuwarsu ta baya tun daga tasawarsu har zuwa yanxu da yake shan wannan ba'kar wahala da quncin rayuwa baisan hawaye yana ta zuba a idonsa ba ko motsi baiyi tsabar nisan dayai da duniyar mutane ya fad'a duniyar tunani da tuna baya yadda rayuwarsu ta kasance kifa kai yai yana rufe ido kawai ya soma kuka sosai kamar qaramin yaro saboda tuno mahaifansu kawai ya zurfafa da tunanin da.
TUNA BAYA🤔.
AYYA ALLAH SARKI MALAM HABU😣😞😔😢.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘😘😘
Sai mun sake haduwa idan Allah ya kaimu gobe darai da lafiya zakuji asalin tushen tarihin labarin su🤔.
Reader's baku tambaye niba shin ya akai malam Habu ya talauce 😔?
Meye asalinsu🙃?
Wanne kalar 'kalubale ya fuskanta a baya😭?
Me ya jawo silar tauyar arzikin sa?
Domin samun amsoshin wadannan tambayoyin ku kasance tare dani👇.
+2348160983083
YUSRAH MUSA ABUBAKAR MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY💃💃💃.
We will meet again.
🎹🎺🎷💃💃🎶🎵🎻 Ranar kuce masoya maza kada kuyi sanya muyi rausaya 'yan uwa mu taho da baya baya mune muke shagali 😘 ranar mu tayi haske 🌃.
TYPING 📲 TUE, MAR 5 /24 8:10AM🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈.
💎ME KAMAR SARKI 💎
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY.
Story and written by
📚✍️Mrs al'ameen Ahmad ce 😘.
Tnk u masoya godiya sosai sosai godiya💖💕.
Always be watchful don't take risk don't try to get lost try to protect your life 🌌 always 🌹.
Be good be helpful everybody will like u to be a happy child like my daughter Fatima Ilham 👌 then people will like u.
Ayi hakuri idan an samu typing error matsalar keyboard ne.
🤔Think before you do 🚨
15~AL-KAHHARU
The subduer
16~AL-WAHHAB
The bestover.
8~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Hamidina.
📚✍️YUSRAHMS💞🌹💃👌.
🌄 REMEMBER ND STRUGGLE 🌄
Episode 15&16
Asalin su duka 'yan wani 'karamin 'kauye ne wanda ya shahara da mutane ba'ki 'yan garin d'ai d'ai ne mahaifin malam Habu ya kasance a wannan garin matan sa uku Salamatu itace uwar gida danta daya Sabi'u sai 'yar tsakiya Ramatu ita ce mai yara biyu Ilyah da 'kanwarsa Lami sai kuma amarya Kulu wato Hauwa amma ta rasu d'anta daya Habubakar suna wata kalar rayuwa a hagunce wacce babu girmamawa ga wanda ka fi hakan kuma ya samo asali ne a wurin 'yar tsakiya Ramatu sam bata da kirki kuma bata da kara batasan meye mutunci ba Baffa mijin su kullum yana nusar da ita yayi yayi ta gane amma ta'ki ta kauda kai.
Zaune suke a tsakar gida kowa na harkar gaban shi wata yarinya ta shigo dauke da farantin talla a kanta tana kuka wiwi kamar ranta zai fita da gudu Ramatu ta fito daga d'aki tana cewa "ke Lami me akai miki kike kuka keda waye wanne d'an iskan ne la'ananne fad'a min yanzu nan naje gidan uwarsa na tsige mata gashin albarka tassss".
Har lokacin kuka Lami keyi ta kasa magana "ki fad'a min uban me akai miki ko shashancin naki ne ya mitsa dama yau naga ba'a son ranki kika fita tallar nan ba".
Kai Lami ta girgiza tana cewa "a'a Innah ba haka bane yaran gidan su Abu ne suke ce wai banyi karatu ba ni jahila ce jaka dakikiya bansan komai ba sai daukar kaya kamar 'yar dako".
Cikin masifa Ramatu tace "kuturun uban can lallai yaran nan akwai matsiyata ba kece jahila ubanninsu ne kwashashshu masu kai duk 'kwar'kwata".
Share hawaye Lami tayi tana cewa "dan Allah Innah na gaji da wannan gorin da ake min ki taimaka ki barni na ri'ka zuwa makaranta ko sau biyu ne a sati".
Zaro ido waje Ramatu tai kamar an fad'a mata abu mai muni har tana make Lamin cikin fad'a tace "uban karatu zaki kinsan Allah Lami indai ina raye bakiyi makarantar boko ba zaki 'kari maitarki ki barni domin tallar da kike yafi min da ubanki zan saya miki kayan d'akin? Dama hakan ne yasa ki dawowa gida da kuka tashi ki koma ko kija abinda zanyi miki tsinannan dukan da sai kin kasa tashi".
Mi'kewa Lami tai cikin ladabi ta sake daukar farantin ta fita Allah ya d'igawa yarinyar hakuri na kwatance kome za'ai mata bata fushi bata nuna gajiyawa.
Daidai zata fita Baffa ya shawo kwanar gida gida suka had'u a zaure ganinsa yasa da sauri ta goge sauran hawayen fuskarta tana cewa "sannu Baffa kawo tabarmar na kai maka" murmushi ya mata yana matukar kaunar yarinyar domin tana da cikakken hankali tun kafin ta mallaki hankalin kanta sake kallon ta yai karo na biyu kafin yace.
"A'a jeki tallar ki kinji zan 'karasa Allah ya miki albarka" "Amin Baffa ta fad'a tana juyawa ta fita shi kuma ya shiga cikin gidan ko bari ya karasa sallama Ramatu batai ba ta soma babbaka fad'a "malam yanzu haka rayuwa take wai 'yan iskan yaran nan gidan can harda tare Lami a waje suna ce mata jahila uban wa aka haifa da sani dama jiran ka nake ka shigo na dauki mayafina naje gidan saina yiwa Jummai tass zagi na tsamar nama domin banga dalilin da 'ya'yan ta zasu hana tawa zaman lafiya".
Ganin ta yayimo gyale daga jikin igiya tana shirin fita Baffa ya katseta Ramatu ina zaki je babu neman izini na" bata saurara ba tace "yo malam ai kaji inda nace zanje indai ba son maimaita magana ba dole na 'kwatawa 'yata yanci cikin 'kawayen ta domin ni ban haifi jahila ba".
"Ban baki izinin fita ba Ramatu ki dawo ai basuyi karya abinda suka fad'a ina jin lokacin da suke fad'an har mutane na cewa kaji gorin da akewa 'yarka tsabar kunya na kasa magana ji nayi kamar nayi nutso cikin 'kasa".
Tabe baki Ramatu tai "yo malam ai ka nutse a cikin 'kasar hakan ma da kyau nikam zuwa zanyi naja musu kunne akan 'yata bazan dauka ba" zata fita ya kuma dakatar da ita da cewa "Ramatu kada kije gidan mutanen nan kiyi musu wani abu Allah ya la'anci mai tashin fitana kibi a sannu idan kinsan farkon sa baki san karshen saba" bata fasa ba tace "wallahi malam saina je saina tabbatar musu na amayar abinda ke cin raina tunda kai bazaka iya ba" tana fadin haka fuuuuu tai waje kai malam ya girgiza batare daya kalli sauran matan nasa ya shiga d'aki cikin tausayawa suka bishi da kallo domin a zahirance Ramatu tana matukar wahalar dashi da halinta.
Mayafi a kafad'a Ramatu ta shiga gidan ganin yaran ta 'yan mata su biyu kawai ta fad'a musu da duka babu neman dalili ko tsayawa tambaya tana masifa "ina tsinannun gidan nan ku fito naci uwar ku dan dambun ubanku jahilci akai ya Jummai da Mamman matsiyata 'ya'yan Allah bani mu huta gori kina ina ba'kar munafika fito nace".