← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 145

Sashe 140

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Ajeeb yai yana cewa "kai Mami kar kisa girman kai ya kama Asad irin wannan yabo haka uhm kodan har yaji dad'i a ransa ance da albarkacinsa ake sa rai da aljannah".

"Babu ruwan ka dashi Ajeeb bana son tsokana".

"Ok shikenan Mami sorry na daina yau Allah ya kawo mu zamu fara cin girkin Amatu bari mu d'an'dana muji ko ta iya girki? Mami saka min".

"Kar ki barshi ya ta'ba Mami bazai ci wannan abincin ba".

Zaro ido Ajeeb yai yana cewa "kai wai da gaske kake? Tab Mami kiji wani black habit a gurin Asad kawai Ina jin girkin yana tashin qamshi kalli yadda Mami take yanko tsokar kifi kace wani kar a bani saika hana tunda kai ka dafa"?.

"Bakai qarya ba tunda wacce ta dafa na isa da ita".

Mi'kewa Ajeeb yai yana cewa "ok bari na dawo please Mami ki saka min ya ri'ka hucewa naga yana turiri'' yana kaiwa nan yayi waje.

Kallon Amatu Asad yai yana cewa "wato kin iya neman suna ko"?.

Da mamaki Mami tace "a'a kamar ya neman suna Asad nifa ta kawowa"?.

"No Mami ba ina maganar kiba ita kanta nake magana nine ya kamata ta fara nema amma tsabar tana gaggawar ta kawo miki kalli a yadda ta sako hijab d'in".

A tare Amatu da Mami suka kalli hijab d'in tab a baibai ta sako dariya Mami tai tana cewa "ai wannan ba komai bane jewel ki saka masa abinci".

To tace saida ta zuba komai takai masa ta aje zata mi'ke yace "me kike nufi"?.

Cikin rashin fahimta ta kalleshi tana cewa "meya faru"?.

"Oh tambaya kike? Kina nufin da kaina zanci"?.

Zaro ido Amatu tai tana d'an kwa'be fuska itafa shikenan yanxu kuma ta banu domin ta fahimci Asad mutum wani kalar ra'ayi........

"Zoki d'auke abincin ki".

Dawowa daga tunanin tayi tana kallon sa kafin ta kalli Mami taga itakam ta d'auke hankalinta daga kansu juyowa tana sake kallon sa zatai magana yace.

"Zauna".

Zama tayi akan kujerar da yake ta gefensa tana d'aukar spoon ta d'ebo abincin zata bashi yayi mata nuni da kanta kaita girgiza tana cewa.

"Nifa a 'koshe nake".

"Me kika ci"?.

"Saida na tsaya naci acan sannan na kawo mata".

"Ok qara ai kinyi tafiya ya rage nauyi".

"Na 'koshi".

"Bana son musu".

A dole yasa Amatu ta cusa abincin domin data gama saida ta tsaya taci tana yunkurin amai yace ta bari haka Mami dai batace musu komai ba har Ajeeb ya dawo ya gayyato Annur tunda yanzu Ameer babu shi a cikin lissafi yayi aure had'uwa dashi yana da wuya musamman in dare yayi kamar irin karfe tara goma ba'a ganinsa sai washe gari.

Cike da tsokana Ajeeb ya ri'ka cin abincin dan Asad yayi magana yaga ko qarasa kallonsa baiyi ba ya tsokane shima kozai kula yaga ya baiwa iska ajiyarsa har suka gama baice qala ba suka dawo kan hira da Mami Amatu tana gefe da d'an zomonta ta zuba masa farar shinkafa yana ci ita kuma tana kallonsa cike da so gashi fari tas gashin jikinsa.

Sai dare kusan karfe sha d'aya Asad yace su tashi su tafi domin yaga Amatun ta fara gyangyad'i anan suka bar su Ajeeb sakamakon barcin daya fara kamata suna tafe tana had'a hanya dole zomon ma sai Asad d'in ne ya ri'ke mata suna shiga ta wuce bedroom harta kwanta zomonta ya fad'o mata arai da sauri ta tashi tana bud'e kofa ta fito tsaye tayi a kofar shiga bedroom d'in Asad tana 'kwan'kwasawa izini ya bata ta shiga domin bai rufe kofar ba tunda tashi kwanciya ba laptop ce a gabansa yana aiki shiga tai tana kalle kallan inda zataga zomon ganin bata ganshi ba yasa tace.

"Ina zomon nan"?.

Da hannu ya nuna Mata kan d'an wani abu kamar table anyi masa a an zagaye shi da flowers masu clours yana kama da gadon yara

"Ok sorry I was going in gently
Suna tare dasu Ajeeb ya baro su ya dawo part dinsa amma har lokacin Amatu bata dawo kiran wayarta yai sai kuma yaji wayar na ringtone a kusa dashi ba da ita ta tafi ba.
Yana kwance a tsakiyar gado da waya a hannunsa Amatu ta shigo dawowarta kenan daga gurin Mami d'ago kai yayi yana kallon ta murmushi tai masa tana karasowa bakin gadon yana daga kwancen da yake ya mi'ko mata hannu ri'kewa tai tana hawa ta kwanta a gaban shi tana matsawa kusa dashi sosai ta kifa fuskarta a kirjinshi da yake cike da ba'kin gyararran gashi wanda ya kwanta lif-lif shima rungumota yayi sosai a jikinsa yana cewa.

"Wato shine kika barni ni kad'ai ko? Kinyi tafiyarki gurin Mami".

'Dan murmushi tai tana kallon shi cike da so da burgewa tace "eh Mami tayi ba'ki ne yan uwanku na Bahrain sunzo shiyasa ban dawo da wuri ba na tsaya a gurin su ne".

"Wai kina nufin su Aunty Fadilaty sun sauka? Kuma shine ko tai kirana ta sanar dani" kallonsa Amatu tai "ai baka sani ba ko zata zo ne ku gaisa" "eh na sani man zata zo part d'ina koni banje ba but ko tazo yanzu bani da lokacin gaisawa da ita yanzu lokacin mata tane" dariya Amatu tai da sauri ta mi'ke zata sauka a gadon ya dawo da ita yana rungumeta ya d'ago fuskarta yana ri'kewa da hannu biyu yace.

"Ina zakije"? Itama kallon cikin kyakkyawan idanunsa take wanda suka cika suka batse da tsantsan soyayyar ta cikin murmushi da nuna kulawa tace "zan had'a musu wani abu ne kafin su shigo mana" "wani abu kamar me kenan me zaki had'a musu sufa larabawa ne kinsan kalolin abincin sune ko sai kin tambayi mijinki🤗"? d'an d'aga kai Amatu tai cikin tunani tace "mekasan Aunty Fadilah naso"? Shima shiru yai yana kallon ta zuwa wani lokaci yace "indai abinda take so zaki mata da wahala and ni kuma duk abinda zai wahalar min dake bana 'kaunarsa kawai ki 'kyale".

"Ai kuma kaga babu dad'i ta shigo ban tareta dako drinks ba" tashi zaune yayi yana cewa "shikenan muje ki rakani" mi'kewa tai tana sauka a gadon ta d'auko dogon hijab har kasa tasa kallonta ya tsaya yi kamar mai nazari kafin yace "kinyi kyau sosai amma wannan fuskan naki bana son kowa ya ganta kisa facemask" to tace tana daukowa tasa shikuma ya d'auki key din motarsa daidai ta d'auko masa riga ta sa masa suka fito hango Ajeeb da yayi ne suna tsaye da wani abokinsa akwai maganar da yake so suyi amma ganin bashi kad'ai bane yasa kawai suka wuce shima Ajeeb d'in ya ganshi kuma yaso tsaida shi saidai da yaga harda Amatu yasan maybe zasuje anguwa ne shiyasa baiyi magana ba.

Sayayya mai yawa suka yowa Aunty Fadilaty hanyar su ta dawowa Amatu ta kalli Asad ganin hankalinsa na kanta baya kallon titi yasa tace "na tambaye ka"? Gira ya d'age alamar what murmushi tai tana sake kallon yadda yake kasada dasu a kan hanya kamar masu rai goma ga motoci sai wucewa suke tace "meyasa lokuta da dama idan kana tu'kin mota baka ri'ke sityari kuma baka cika kallon gaban kaba baka tsoron wata rana mu fad'i"? Kallon ta yai dakyau yana murmushi kuma har lokacin ba titi yake kallo ba yace" 'kwarewa ce ta kawo haka sannan motana mai saiti ce idan na riga na saita ta inda zanje har bacci zanyi abina itace take sarrafa kanta kalli ki gani ba nine nake sarrafa taba shiyasa kikaga ban cika kallon gaban nawa madam" yar dariya tai daidai an bud'e musu kofar babban gate d'in masarautar sun shiga Ajeeb kuma ya fita da mota suna parking Amjadd ya taho da gudu yana durkusawa yace.

"Barka da dawowa ubangida na" kallonsa Asad yai yana cewa "Amjadd ka d'ebo kayan motar nan ka kawo min" to ranka ya dad'e" Amjadd ya fad'a yana tashi da azama ya fara de'bowa suna tafe ganin yana yin hanyar part dinsu yasa tace "ina part d'in Mami zamuje" kai tsaye ya bata amsa "eh amma ba yanzu ba saimun koma part d'inmu" suna shiga suka zarce bedroom Amatu na cire hijab d'in ta aje tana yin hanyar toilet ri'ko hannun ta Asad yai "ina zakije"? "Wanka zanyi" kai ya girgiza "ba yanzu ya kamata kiyi wanka ba sai anjima inada bukatar ki😍" kallonsa tai "kace Aunty Fadilah tana shigowa part dinka kuma idan tazo muna ciki bata jimu bafa"? "Saita juya" ya kara maganar yana zuge zif d'in rigarta ya d'auketa sukai kan bed abinsu d'onono tsarki da romo😂😂😂😂.

Kusan san Amjadd biyar sai jido kaya yake yana kawowa parlor saida ya gama sannan ya fita had'uwa sukai da Aunty Fadilah da 'yarta zarah zatai shekara ashirin da kuma Aunty Aleemah da ma'asumah sun shigo part din ganinsa yasa Aunty Fadilah tace "Asad na ciki ne"? Cikin girmamawa yace "eh ranki ya dad'e yana nan" kaita d'aga "ok shikenan jeka" wucewa Amjadd yai yana sake waigowa ya kallesu larabawa kyawawa madarar kyau iya kyau shiga sukai amma parlon shiru babu kowa zama sukai Aunty Fadilah nacewa "maybe basa nan naji shirun yayi yawa kamar ba halitta a part d'in"? Aunty Aleemah dake gefe tana shafa waya tace "ko kuma suna bedroom ba" itadai zarah yar gidan Aunty Fadilah dama bata zauna ba tana tsaye tace "Ummi ni tafiya zanyi gurin su Aunty Naizarah zan koma" kallonta Aunty Fadilah tai tasan akan Asad ne ta rasa meke damun zarah meyasa take masifar jin tsoron sa zarah kam hanyar fita ta nufa dakatar da ita Aunty Fadilah tai "wai zarah meyasa kike tsoron Asad ne"? Tsayawa tai tana juyowa kamar zatai kuka tace "Allah ni tsoron sa nake" kai Aunty Fadilah ta d'aga tana cewa "to dawo bana san shirmen banza" dawowa tai ta zauna a bisa dole dan ba yadda zatai suna ta hira amma itakam tayi shiru addu'a take a ranta Allah yasa karya fito harsu gaji da jira su koma part Mami gajiya Aunty Fadilah tai ta mi'ke tana zuwa kofar bedroom din tadan 'kwan'kwasa kafin ta koma ta zauna.
Chapter 140 · 0% Book details