← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 145

Sashe 80

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Malam Habu ya girgiza yana cewa "ban dace da Wanda zakuyiwa shimfid'a ba ban kasance mutum wanda zai zauna akan shimfid'a ba mena kawo muku dame na tafi na barku a wanne hali kuka tsinci kanku bayan tafiya ta daya kuke ciyar da kanku daya kuke tufatar da kanku tsawon wannan lokacin hakika yau ina matukar jin kunyar hada ido daku saboda abinda na aikata muku dan Allah ku yafe min😒🤲🙏.

Kai kowa yake girgizawa murya a sanyaye Binta tace "malam bakai mana komai ba dan Allah ka zauna".

Shima kan ya girgiza yana cewa "Binta bazan ta'ba zama ba wallahi har sai kunce kun yafeni sannan ne zuciyata zata d'an samu nutsuwa kad'an na samu qwarin gwiwar iya zama daku a yanzu saboda na gaza na kasa".

"Ayya malam baka kasa ba mun fahimce ka kuma nidai na yafeka duniya da lahira".

Kai Saude ta d'aga "Nima malam na yafeka babu abinda kai mana"..

Nanfa kowa ya dauka sun yafeshi jikin A'i ma dai yayi sanyi qalau sai ido kawai take binsa dashi sai lokacin Malam Habu ya iya zama ruwa Binta ta kawo masa sannan ta nufi murhu tana d'ora masa tukunyar ruwan zafi dan a yanzun kam sun fahimta cewa da 'yan fashi suka had'u tunda ga alama nan ya nuna jikinsa da akwai tabambuna Saude ma da sauri ta tashi tana dauko masa tuwo ta sako miya ta kawo masa kai ya girgiza mata domin a yadda yake jin jikinsa ko ruwa had'iya d'aya bazai iya shaba kawai ruwan zafi yake bu'kata su Jamila na gefe sunata aikin share hawaye sun san yau da ace Amatu tana nan hummm ba'a san ya zatai ba gara da bata nan kuma sun dau alkawarin insha Allahu bazasu ta'ba fad'a Mata ba bazata ta'ba sanin anyi wannan abun ba.

Saida malam Habu yai wanka da ruwa mai zafi sosai ya d'umama jikinsa ya gasa shi sannan ya fito yana zama cikin nutsuwa yace su saurareshi a hankali ya basu labarin duk abinda ya faru tun daga ranar da sukaje Cameroon har yau da 'yan fashi suka taresu a daji suka kar'be musu komai yana rufe baki A'i dake faman ciwon yatsa tace.

"Kai amma Allah dai ya tsine musu albarka Allah ya tarwatsa su mitsiyata tsinanu in Allah ya yarda suma kud'in bazai amfanesu ba shine ajalinsu".

Shidai malam Habu baice komai ba haka sauran babu wanda yace qala sai jimami da takaicin irin dukiyar da Malam Habun ya Tara kuma wadannan 'yan fashin suka kar'be haka kowa jiki a sanyaye sukaita zaune a gurin ba um ba um um kowa babu barci a idanunsa sai damuwa haka Binta tayi hamdala da babu Amatu a gidan da yau batasan wanne irin hali zata shiga ba ganin a yadda babanta ya shigo gida tun daga wata 'kasa ga tabon ciwon dukan 'yan fashi a jikinsa kila saita kwanta jinya".

🌃️MARSHALL ISLANDS🌃
Clarah tana zaune duk abun duniya ya isheta so take su had'u da Asad akwai abinda zata tambaye shi amma kwanan nan baya samun hutu kullum suna fita operation ne sauke numfashi tai tana d'aukar phone d'inta ta kira numbar sa amma line busy bari tai kamar mintuna biyar ta sake kira still number busy tsaki taja cikin takaici tana mi'kewa ta soma zaga gurin tare da tunani a zuciyarta shin meye ya rageta meye ya tauyeta me zatai wanda zaija hankalin Asad dame Yusairat ta fita har tayi nasara akansa meyasa ita ta har yanxu ta kasa koda samun nasarar lokacin sa? wannan tunanin ne fal ranta kullum bata aiki sai son gano me yake so ta ri'kayi wanda zata jawo ra'ayinsa da gaggawa.....,.............

Tunanin tane ya katse jin wayanta na 'kara ga sunan Asad da manya ba'ki da sauri ta d'auka jikinta har rawa yake cikeda shau'kin so tace.

"Hello Asad kana jina"?.

Daga can 'bangaren Asad dake zaune gaban laptop hankalinsa nakan wani abun da yake so ya kashesa da mamaki yace.

"Eh Ina aiki ne meya faru kike kirana"?.

Sake kashe murya Clarah tai tana cewa "am Asad inason zamuyi magana ne" tambaya ya jefo mata.

"Yanzu"?.

Da sauri tace "eh a Ina zan sameka"?.

"A'm at home".

Zaro ido Clarah tai jin abinda take fata ya samu tana so ya bata damar da zata shiga gidansa koda sau d'aya ne a rayuwa taga yadda 'kawatar gidan yake domin Tasha tambayar Isham ya tsarinsa yake shikuwa ya bata amsa cewa a 'kawace yake sannan bazai kwatantu ba saboda yakai makura wajen had'uwa har kwaruwa take wajen cewa 🤔.

"Ok nazo na sameka"?😳.

"No karki zo min gida"🤥.

Sak tai jiki a sanyaye tace "meyasa ne Asad baka so na ra'be ka"?.

"Saboda ni sam ban cika son mace tana zuwa gidana inda nake ba".

"Saboda kar mutane su zargeka"?.

"A'a ina ruwana da mutane saboda kare mutunci na kin gane"?.

"Ok ok na gane to dan Allah ka fito muyi magana".

"Bazaki iya fad'a min a waya ba dole saimun had'u"?.

'Dan shiru tai sai kuma tace "a'a zan iya amma nafi so saigani gaka kamar zaka fi fahimta ta yadda ya kamata"?.

"Ok ki bari zuwa nan da dare idan na samu lokaci zamuyi magana kuma saina nemeki" yana fad'in haka taji d'itttt ya kashe wayarsa hawaye ne masu zafi suka zubo mata 'kafafunta na rawa da'kyar ta samu ta zauna tare da kifa kanta akan cinya ta soma kuka zuciyarta na rad'ad'i tabbas idan Asad bai tsaya ya saurareta ba ya juyo da hankalin sa kanta ba tofa rayuwar ta tana cikin had'ari dan matukar sukaci gaba da tafiya a haka gara ta rataye kanta ta huta da wannan 'kunci da damuwar da take fuskanta kullum.

A 'bangaren Asad kuwa bayan ya kashe waya da sauri ya tattara dukkan nutsuwa da kulawarsa akan laptop d'in gabansa ganin cewa an samu wanda ya gano 'kungiyar kuma alama ta nuna mace ce saidai babu ta yadda za'ai ka gane wacece ba suna ba photo ba location ba information empty file d'inta yake a list d'in unknown shiru yai yana kallon rubutun dazai kaishi shafinta na website kafin ya danna link d'in amma yana shiga babu komai a shafin zero d'an rufe ido yai yana sake kallon laptop d'in zuciyarsa na tambayar sa wace ita a ina take taya zan sameta awane yankin 'kasa ko gari take a duniya ta Ina zan fara shin sojace ita ko 'kanwar soja ko 'yar gidan soja shin a familyn su akwai soja tasan ana neman 'kungiyar ko a'a akwai wanda takewa aiki ko kawai a bincikenta ta gano? Mi'kewa yai batare daya rufe laptop d'in ba ya soma zaga gurin cikin nazari da yadda zai 'bullowa al'amarin kafin kamar wanda aka tsikare shi ya sake zama yana jawo laptop d'in yaci gaba da aiki ko zai dace ya samu wata 'yar alama.

🏙️DUTSE MOPAL-BASE🏙️
Amatu tana zaune ita kad'ai a bedroom da laptop a gabanta sai bincike take ta shiga nan ta fita nan wani assignment zatai mai matukar wuya da had'ari tafi awa biyu tana bincike ta shiga nan ta fita duk ta hargitse tad'au zafi ga abinda take nema bata samu ba gashi Maryam ta mata maganar ta shirya zasuje gano amaryar yayansu Ahmad kwasam taci karo da tashin hankali abun d'imuwa dasa a gigice a firgice a fita hayyacin wato dai taga wani abu da wani 'bangare da 'yan 'kananan bayanai game da wannan ba'kar mummunar azababbiyar 'kungiyar wacce gwaraza da hazi'kan sadaukan maya'kan sojoji suke son sani da mafarkin samu ta kowanne hali.

Abun ya firgita mata tunani daga farko har batasan lokacin data rufe laptop d'in ba jikinta na rawa kamar maijin sanyi lokaci guda taji wani irin 'karfin zuciya da tsikewa ya dirar mata kamar wacce aka 'kara mata kuzari haka ta mi'ke daga kwancen da take tana yaye bargon data lullu'ba ta sake bud'e laptop d'in tana kunnata taci gaba da bincike saidai sa'banin na d'azu dan yanxu zallar rubutu ne take karantashi wanda dama already an turo ne dan ita ana mai mata gargad'in ta kame bakinta idan kuma ba haka ba zata hallaka ta'be baki Amatu tai bayan ta gama karantawa tace.

"Ji wani jahilci su waye kuma wadannan mutanen a wanne gari suke 'kungiyar meye wannan d'in jini yake ambaliya haka kamar ruwa ga wani irin ba'kin daji" mutttttsss ni harsun bani haushi ma aikin banza uban me zanyi da 'kungiyar su harda gargad'ina wani karna fad'awa kowa wanda ya damu da kasuwa shiyake bada sautu" Amatu na rufe baki Maryam ta shigo tana cewa.

"Surutun me kike ke kuma koda Nabilah ne"?.

Kai Amatu ta girgiza tana rufe laptop d'in tace "a'a kawai Ina duba abu ne".

"Ok kiyi wankan mana ko kin fasa zuwa gidan ya Ahmad d'in ne"?.

Mi'kewa Amatu tai tana cewa "oh sorry wallahi sha'afa nai amma yanzu zan shirya ku jirani" ok Dan Allah da sauri kinga yazo tare zamu tafi dashi tunda nikam bansan gidan ba garama keda Nabilah kunje sau d'aya".

Dariya Amatu tai tana cewa "humm ai kema rashin kirki ya hana ki zuwa Allah yasa idan mukaje yau ya Ahmad d'in ya hanaki tahowa saikin musu weekend naga tasan zillewa".

Ta'be baki Maryam tai tana cewa "tab wallahi bazan zauna ba haka kawai na zama yar shara da wanke wanke suna d'aki sun 'kule ni ina waje Ina shan aiki umm daina fad'a ma karkisa na fasa".

"A'a indai danna fad'i haka ne zaki fasa dama dai baki da niyyar zuwa fad'ar hakan ne zaisa ki fasa"?.

"Eh man sauri ki shirya muna falor" ok ganinan yanzu" bathroom ta wuce Maryam kuma ta fita duk suna falor harda Alhaji Bashir da yake yau ba ranar aiki bace ganinta ita kad'ai yasa Ahmad cewa "ke maye haka ina soldier🤗 d'in take"?.

'Yar dariya Maryam tai tana d'aukar handbag d'inta tace "yanxu zata fito wanka take".

"Oh sai yanxu ma ta shiga wanka dama an fad'a mata sojoji haka suke da sanya komai a zafafe sukeyi anya kuwa zata iya aikin nan kawai bari ta fito na bata shawara ta koma 'bangaren doctor ta barwa maza soldier d'in nan"?.
Chapter 80 · 0% Book details