← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 145

Sashe 75

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KANO🏙️
_____Yau ranar asabar week end ne babu aiki Nurain yana gida shi kad'ai a parlor yana waya da Nafisa Auta da Amnah sun tafi gidansu gaida momynsa Zainab na bedroom tana barci dan haka ya sake ya bararraje suke zuba hira ta soyayya😝 shida Nafisa a waya sai dariya yake bai lura da Zainab dake tsaye tun d'azu ta zuba masa ido jikinta na rawa idonta fal da hawayen tsananin kishi ba jin maganganun da suke fitowa daga bakinsa wanda hankalin ta bazai d'auka ba a guje tazo tana fisge wayar tana jifa da ita tare da fashewa da kuka tana kallonsa tace.

"My choice me nake ji haka kalaman soyayya a bakinka kana furtawa wata? Wacce tsinanniyar ce 'yar uban waye? waye ubanta me take ta'kama dashi dahar zata shigo cikin rayuwarka wallahi tallahi my choice bazan d'auka ba bazan yarda ka fad'a min wace ita" ta karasa maganar tana rikeshi tare da jijjigashi da karfi wanda da alama batasan tana yin hakan ba.

'Bam'bare hannuwanta Nurain yai a jikinsa yana fuskantar ta yace "kinga Zainab bana son shirme ki nutsu muyi magana".

A burkice Zainab tace "nutsuwa my choice taya zan nutsu bayan wannan mummunan tashin hankalin daya sameni wai me kake 'boye min ka fad'a gaskiya idan har ba cin amana ta kake ba"?.

Kai Nurain ya girgiza yana ri'kota dan yasan yanxun nan saitai hanyar kitchen tace zata kashe kanta ba hankali gareta ba idan kishinta ya tashi yace "ni ban ta'ba cin amanarki ba ban kasance mai zaluntarki ba saboda ina son ki".

Fusge jikinta Zainab tai tana cewa "idan har kasan baka cin amanata kana da gaskiya ka fad'a min wacece wannan yarinyar sannan meye ala'kar ka da ita"?.

'Dan shiru yai yana kallon ta kamar bazai magana ba sai kuma ya sauke numfashi yana cewa "kinsan 'kauyen da Dad yake tura ni 'karbo kayayyakin da ake kaiwa gidan marayu a gurin wani mai kud'i a 'kauyen"?.

Tsayawa Zainab tai da kukan tana kallon sa tace "shine ya baka 'yarsa"?.

Kai ya girgiza mata "no ba shine ya bani ba nine naganta naji ina son ta".

Zaro ido waje tai tana dafe kirji zatai magana ta 'kwaru ta soma tari da ruwa a kusa dashi ya zuba a cup yana bata maimakon data kar'ba tasha saikawai ta watsa masa shi a jiki tana sake fashewa da kuka mai ta'ba 'kwa'kwalwa muryarta na rawa tace.

"Kai kace kana son ta aurenta zakai my choice"?.

"Eh aurenta zanyi saboda inada dalili idan ban auri yarinyar nan ba akwai matsala ba 'yar kamara ba shiyasa nake so ki tsaya ki saurare ni zan miki bayani yadda zaki fahimta".

Yana rufe baki ta tashi da gudu ta shige bedroom da kallo ya bita cikin mamaki saidai yasan wace Zainab yadda take masa mahaucin so dama abune mai wuya ta iya kwantar da hankalinta ya auro wata mace amma hakan shine mafita gareshi dole ya auri Nafisa kodan tsira da mutuncin sa yana cikin tunani yaji ta sake fitowa da kukanta bai ankara ba yaga ta bud'e kofar parlor ta fice da sauri ya tashi yana bin bayanta mota yaga ta dauka tsaye yai yana hard'e hannunsa yasan ba wannan 'kauyen zataje ba tunda batasan hanya ba bazai wuce gidansu zata ba shi kuwa hakan ma zai taimaka masa wajen warware matsalar sa juyawa yai yana komawa parlon ya d'au wayarsa amma harta fasa masa screen bai damu ba ya zauna yana sake danna kiran wayar Nafisan domin hakan ma yana rage masa wani zafin😳.

'KAUYE🏕️
____A babban dandalin garin inda yake cike da samari da 'yan mata kowa da abinda yake sayarwa Indo tana zaune a gaban kayan sayarwata tayi tagumi naban tausayi hankalin ta baikan kowa tayi zurfi a duniyar data fad'a na tunanin wannan baud'dd'iyar rayuwa da take karasowar Dauda kenan ganinta da abin sayarwa yasa yaje inda take yana cewa.

"Indo".

Da sauri Indo ta d'ago a razane tana kallon sa fuskarsa murtuk lullu'be da 'bacin rai yace "amma me nace dake jiya? bance karna sake ganinki da kayan tallar wannan matar ba wato taurin kai ya hana kiji magana ta ko"?.

Sunkuyar dakai Indo tai tana goge hawaye muryarta na rawa tace "kayi hakuri dan Allah yaya Dauda wallahi ba laifina bane idan banzo ba duka na zatai".

"Ta dake ki tayi hauka ne"? ya fad'a a tsawace har saida Indon ta tsorata da sauri tad'an matsaya baya tana fashewa da kukan tashin hankali da damuwa tace "kayi hakuri" mi'kewa yai yana cewa "shikenan tashi muje gidan" jiki a sanyaye ta mike tana d'aukar kayan suka tafi jikinta sai tsuma yake tasan yau kam ta shiga uku ta lalace kila kasheta ne kawai Asabe bazatai ba a gidan nan yau hakan ma dan tasan tana morarta da babu abinda take mata tasan yau saidai tai kwanan kabari mus zata kasheta har lahira kuma ubanta baida farcen sosa baida ikon cewa 'kala ta kashe banza suna shiga Asabe tana shirin kulle kofar d'aki zata fita anguwa ganinsu yasa taja ta tsaya tana cewa.

"Malam lafiya zaka shigowa mutane gida kai tsaye ba neman izini"?.

Bai kula Asabe ba sai juyawa dayai yana kallon Indo wacce ta ra'be acan baya jikin katanga ga alamar firgici bayyane a fuskarta yace "ke zonan" karasowa Indo tai da sassarfa tana tsayawa a bayansa kad'an saboda tsoro cikin tsawa yace "jeki aje mata kayanta a gabanta" matsawa Indo tai jiki na 'kyarma take kokarin sau'ke katon bahon tallar abincin dake kanta rawar da hannunta keyi yasa bazata iya ri'kewa dakyau ta sauke ba a tsautsayi ya su'buce ji kake tassss baho ya fad'o abincin ya zube miyar ta zube sannan bahon ya tsage zaro ido Asabe tai tana cewa "kan bala'i amma yaron nan da 'karfin hali kake to wallahi bari kaji saika biyani dan ko uwarka Aliyah bata isa jadani ba balle kai karamin alhaki d'an marar kunya fitsararre bashi kaci saika biyani bazan d'au asara ba" bai ko kalli inda take ba ya juya yana cewa Indo "muje" da gudu Indo ta fita a gidan tana kuka sannan ya kalli Asabe yana cewa "ke kuma ki kuka da kanki na rantse da Allah kafin nabar garin nan saina saita miki zama zanyi maganinki tunda ke ba mutuniyar arziki bace"

"Aliyah da Balah neba mutanen arziki ba d'an marar kunya".

A fusace ya nunata da yatsa yana cewa "kada ki kuskura ki sake zagarmin mahaifana wallahi zanyi 'kasa 'kasa dake a gun nan"🙊.

"Inka fasa yin 'kasa 'kasa dani baka haifu d'an halak ba".

Shigowar Balarabe ganin Dauda ga Asabe tsaye sai huruwa take yace "a'a lafiya waye wannan haka ba Dauda bane d'an gidan Malam Balah mene haka meyake faruwa?

Ba'kin ciki ya gama cika Asabe ganin yadda Dauda ya jawo mata asara ta kalli Balarabe tana cewa "wallahi bazan yarda ba gurin mai gari zanje yanxu nakai kararsa a mana iyaka haka kawai zai shigo min gida kai tsaye ya zageni yasa wannan matsiyaciyar yarinyar Indo ta xubar min da abinci ta fasa min baho sannan ya ri'ka fad'a min magana son ransa".

Kallon Dauda Balarabe yai yana cewa "kaga jeka abinka Dauda kyale kawai".

A masife Asabe tace "ya 'kyale kawai meye kake nufi a barshi ya tafi kaine zaka biyani"?.

Kai Balarabe ya d'aga "eh zan biya ki Dauda jeka".

Dauda yaso magana amma ya share kawai ya fice a gidan yana jan tsaki mai karfi wata uwar harara Asabe ta sakarwa Balarabe tana cewa

Kace ya tafi ko saboda bakai yaiwa asara ba to wallahi bari kaji yau saika biyani sannan tunda ka goyi bayansa duk wata wahala da Indo take yi a gidan nan kaine zaga ka dawo yi ka gane"?.

Jikin Balarabe yana rawa yace zanyi komaye kinsan yaron nan da zuciya badan Allah yasa naxo ba kikai kuskuren masa wani abu saiya nad'a miki duka babu ruwansa".

"Uban wa zai nad'awa dukan aiko yau da yaga hauka ganin idonsa dan wallahi saiyài kwanan bayan kanta kuma hakan ma ba ha'kura naiba bari naje gidan Aliyan itama wata tsinanniyar nasan itace ta turoshi yazo yaci min mutunci".

Dakatar da ita balance yai da cewa "Asabe karki je gidan mutane da rana tsaka ki kyale xanyi aiyukan da Indo d'in takeyi da".

Tsayawa Asabe tai tana juyowa tace "ai wallahi Balarabe sai naje na kaddamar mata da nima bani da mutunci ba'a ta'ba ni na barta ta kwana lafiya sannan kafin na dawo ka share gidan ka wanke wadancan kwanuka ka kyara gurin da shegiyar 'yar taka ta xubar min abincin ka sakewa raguna na igiya🙊 ka xuba musu dusa ka d'ora min sabon girki" tana fadin haka tai waje fuuuuu sauke ajiyar zuciya Balarabe yai yana kallon abincin dake zube a kasa kafin ya fara tattarawa.

Sauri Asabe keyi kamar zata tashi sama haka ta afka gidan malam Balah babu sallama suna zaune harda Dalah ga Indo tana kuka Dauda yana musu bayanin abinda yake faruwa tana xuwa babu wanda ya lura da ita ta sha'ki Indo tana cewa .

"Kee taso min nan mu tafi dan gwafar ubanki matsiyaciya munafika kukan uban me kike yau saikin biyani asarar da kika jamin".

Duk d'agowa sukai suna kallon Asabe wacce ta kama Indo da karfin tsiya tana janta harda mari ba zato taji itama wani lafiyayyan mari ya sauka a kuncinta a gigice ta saki Indo tana dawurwuri domin Dauda akwai zafin hannu marin ya tsarata ihu ta saki tana cewa.

"Wayyo Allah shikenan ya makanta ni na daina gani ruwan idanuna ya tsiyaye na shiga uku wallahi bazan yarda ba saina had'aka da hukama yau sai an mana iyaka".

Ba wanda ya kula iskarta saida marin ya saketa ta dawo daidai ta kalli Aliyah tana cewa.

"Aliyah kinyi asarar haihuwa Dauda ba d'an halak bane cikin shegensa kikai tsinanne ne kuma wallahi bari kiji ku jira sammaci saina d'auko muku 'yan sanda".

Dariya Aliyah tai tana kallon yadda Asabe ke huci tace "maza sauri ki d'ebo bataliyar sojoji ba 'yan sanda ba mutuniyar banza kawai ki jira karshen ki ai Daudan ne daidai dake wofantacciya kawai".
Chapter 75 · 0% Book details