← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 145

Sashe 4

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tanko ne yace "gaskiya malam Habu baka kyauta ba dan me zaka ce masa haka kuskure aka samu" wani kallo malam Habu yai masa yasa cewa " ka jira ni kaima ban gama dakai ba akwai tsakin mu da tsakuwa dakai dan wallahi nafi karfin wulakancin kowa a cikin ku" Mudi cikin haushin gorin da malam Habu yai masa dazu yace "ah kafi karfin wulakancin kowa Kam tunda ka samu shiga yayan matarka yana binni shine yake turo maka kud'i shiyasa kakewa kowa kallon hadarin kaji" kai malam Habu ya d'aga "ai hakan ma arziki ne wani ya samu yayan matar tasa ya ri'ka turo masa kamar ni din idan zai iya na isa ne" "ka isa kuma"? Tanko yai maganar cikin 'kulewa malam Habu bai damu da tunzurar da Tanko yai ba yaci gaba "eh na isa ne harna wuce inda ake tunani kuma a gabaki dayan majalisar nan babu wanda ya isa kamo kafa ta arziki badan ruwa da yaiwa babban zakara duka ya dawo d'an tsiyako ba" cikin ba'a Mudi yace "au au ba wani ruwa daya daki babban zakara ka dawo da arzikin naka mana watakila tunkaho da gadara daka fara nuna mana ne Allah ya jarrabe ka da talauci da rariyar hannu ya kwace kudin" "wa ya fad'a maka jahili"? Malam Habu ya tambaye shi yana kallon yadda Mudi ya zuro masa ido "rai bace Mudi yace "ka fad'i komai malam Habu lokacin kane dan banyi karatu ba kake goranta min kaima ba wayon Kane ya baka ba" caraf Sadi dake gefe tun dasu yana son yai magana sai yanzu yace "wai ku dan Allah meyasa kuke haka? Matukar malam Habu yazo gurin nan baza kubar shi ya huta ba waye ne keba da talauci ko arziki?" Ganin sunyi shiru yaci gaba "gaskiya yan majalisar nan ku gyara malam Habu fa ba karamin mutum bane ba abin rainawa bane ya kamata kusa hankalinku guri daya lokacin da yake da abin hannu kullum kuna li'ke dashi kuna yan'kare masa hakori da wayon 'kauye shi kuma ba rowa yana baku kud'i kuna bushasha amma yanzu dan karaya ta same shi kuke masa dariya gaskiya kun zama bulutu masu manta kyautar jiya ku sake tunani".

Tsam Tanko ya tsomo baki "to kai Sadi indai ba munafirci da shishshigi ba meye naka a ciki waye baisan bakin talaucin malam Habu ba saifa ba'ko wanda mota ta sauke amma indai d'an gari ne haifaffan kauyen nan yasan malam Habu fa'kiri ne a fa'kiran ma shine ogon yan rashin wadatuwa da komai" dariya Mudi yai yana cewa "haka nefa Tanko kila yanzu inka latsa shi bashi da biyar tasa rabon da yaga kud'i harya manta saidai ya hango su daga nesa a hannun wani yayi fatar ina ma shine kila biyar tasa bazai kuma mallaka ba" dariya suka bushe da ita harda masu rike ciki wanda malam Habu yaji zafin dariyar amma ya danne kamar bai damu ba yace "ba dani kuke ba da wanda ya jarrabe ni kuke" "waye ya jarrabe ka" Mudi yai maganar yana kuma shekewa da dariya "ban sani ba 😠" malam Habu yace yana daure fuska.

Sadi dai da baya jin dad'in abinda ke faruwa yace "dan Allah malam Habu kayi hakuri" cikin nuna rashin damuwa malam Habu yace "ba abinda ya bata min rai kasan su ba komai suke ganewa ba" "maye bama ganewa"? Tanko ya fad'a yana dauko sigari akan farantin gaban Mudi zai kunna wuta da sauri malam Habu ya tashi tsaye zai tafi yace "kune abin tausayin amma kun kasa ganewa Allah ya ganar daku" da sauri Tanko da Mudi suka ce "Amin inda gaske kake idan kuma ka fada ne dan ace kai malami ne na Allah Zuciyar ka a wanke take nan kuwa ba'ki 'kirim take aniyarka ta bika" malam Habu dai bai kuma sauraron suba yai gaba domin sun kore shi sakamakon wannan sigari da Tanko ya kunno.

Sadi daya bi malam Habu da kallo harya 'bacewa ganin sa yace "kai jama'a rayuwa a gaskiya ina tausayawa mutumin ace kullum rayuwar ka ba sauyi kome a ta'ba kamar me bakin iyaye saiya narke" tsaki Mudi yai yana cewa "kai dallacan wa ya fad'a maka malam Habu abin tausayi ne? Ai talauci da rariyar hannu yanzu ya fara gani ba ya nace saiya iya rike gidan saba muje zuwa waye mai nasara" cikin mamaki Sadi yace "ban gane meye abinda kake cewa ba kamar akwai abinda ka sani game dashi"? Murmushi Mudi yai mai ma'ana yana sake kure Sadi da kallo yace "karka damu haka malam Habu zai Kare rayuwar sa kamar 'beran masallaci bazai ta'ba samun wadata ba" "wai me kake cewa ne Mudi lafazin ka ya nuna da akwai wani abu da kake shiryawa" dariya Tanko yai yana cewa "malam Sadi karka damu wannan ba shafin ka bane mu tsaya iya haka kada ka sake neman binciken wani abu gare mu" shiru Sadi yai duk hankalinsa bai kwanta ba yace "amma da akwai wani abu da kuke boye min"? Har hada baki sukai wajen cewa "karka damu damu" sauke numfashi Sadi yai yana cewa "to meyasa bakwa so na sani"? A zafafe Mudi yace "to kai munafikin banza me kake so ka sani bayan wanda ka sani"? Sadi bai damu da zagin mudi ba ya kalli Tanko yana cewa "to me kuke boyewa" kafada Tanko ya d'aga "babu abinda muke boyewa kaga abu sa'banin hankali ne a tattare damu"? Kai Sadi ya jinjina yana cewa "kwarai ba abu daya ba da yawa kuke boyewa kuji tsoron Allah idan da hannun ku akan bawan Allahn nan ku kyale shi yaji dad'in rayuwar sa dan Allah" harararsa Tanko yai yana fadin "ka damu da kanka kaima ka kashe wutar dake gabanka kafin kai kokarin kashe ta wani" mikewa Sadi yai yana cewa "indai kune silar durkushewar malam Habu gaskiya kun cika azzalumai makiya a garesa amma ba damuwa akwai Allah zai saka masa" Sadi zaibar wajen caraf Tanko ya rike masa riga yana cewa "to ba kaji sirrin mu ba kada ka fad'awa kowa idan tsautsayi yasa ka fitar da zancen nan zakaga yadda ake wasan tsutsa a rana" cikin takaici Sadi ya fisge daga rikon da Tanko yai masa yana jan tsaki yabar gurin aka barsu iya su kadai sai zu'kar hayaki suke kallo d'aya zakai musu kasan su 'kware a wannan fannin.

Balarabe na zuwa cikin gidan shi ya bankad'a labule yana cewa "munafika ina kike fito yau asirin ya tonu kin gama yawa mitsiyaciya mai farar 'kafar dama zaman hakuri nake dake komai nawa a sace hakan bai ishe kiba harsai kin fad'awa duniya hali na bankadaddiya mai hana zaman lafiya da ke nake mai idon d'inya kina ina ko saina shigo d'akin na cillo waje dake zakifi fahimtar abinda nake fad'a".

Shiru yaji ba'a amsa ba a hargitse yace "Dalah ke Dalah kina jina kikai banza saboda ga d'an iska yazo yana magana ko"? Da sauri Asabe ta fito daga dayan dakin cikin munafirci tace "ayya malami na ango na uban yayana meya faru ne bansanka da fushi ba" Balarabe na jijjiga kamar mace yana huci yace "ina Dalah take"? Dad'i fal ran Asabe tace "ai bata taje anguwa ba" "anguwa uban wa ta tambaya har ta samu damar fita"? Kar dakai Asabe tai tana dariyar cin nasara zata hada bom yau a gidan tace "au wai dama bata fad'a maka ba ta fita? Ganin bai magana ba ta d'ora "gaskiya malam bakai dacen mace ba ashe dama ba tambayar ka take ba Amma kullum saita fita" "kullum ina take zuwa"? Balarabe ya fad'a bud'e baki Asabe tai zatai magana Dala ta shigo da sallama da kwano a hannun ta Wanda da sauri Asabe tace "ka gani ko maula taje anguwa ta na nunawa mutane kasawar ka cewa baka iya rike mu baka iya ciyar damu gaskiya malam kai maganin ta kullum fa haka take wannan yawon kamar taci kafar kare".

Bai saurari Asabe ba sai Dala daya zubawa na mujiya kafin a tsawace yace "Dala uban waye ya fasa a gari na nemi Indo har yanzu aka goranta min a majalisar zaman mu ki fad'a min"? Da mamaki sosai Dala tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un malam wallahi ba sani ba" a hasale yace " baki sani ba? Karki maida ni wani gailo man an fad'a miki cewa duk wani siddabu da kike a gidan nan da asirce asirce ban sani ba zuba miki ido nai dake da matsiyaciyar 'yar taki naki domin gadon ki tayo gadon tsiya da bakin hali ina Indo din itama dan kambun ubanta? Ke Indo kina ina"?.

Da gudu Indo ta fito daga d'aki tana sharar hawaye ta tsuguna a gabansa jiki na rawa wanda asabe a nata 'bangaren ji take kamar ta taka rawa dan murna burinta ya cika lallai Marka aikinta mai kyau zata sake dagewa harsai ta fitar da Dalah daga cikin wannan gidan ya zama daga ita sai yayanta ta wanda biyar ta tsoma goma....................
Chapter 4 · 0% Book details