← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 145

Sashe 114

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Isham ya girgiza yana cewa "Clarah ni a nawa ra'ayin ina ganin laifinki ne kece kika 'ki mayar da hankalinki guri d'aya ki fahimci Asad ba baya son kisan familyn sa bane a'a ya riga da kun gama magana tun da dad'ewa anyi yarjejeniya tsakanin ku kinsani ya sani yace miki zai aureki sai yayi retire to miyasa da kikasan hakan bazaki dauke kanki daga garesa ba ki mayar da hankalin ki kan aikinki kina kallo sabin d'auka ma nema suke su fiki 'kwazo da himma gaskiya Clarah kisa tunanin ki guri d'aya nayi mamaki ma yadda kike da wasan nan har Asad ya amince zai aureki Kinga kin ta'ki sa'a, na fad'a miki wani abu Asad ba ruwansa da mace ko wacece ita baya kula mace baya kallon mace baya had'a tafiya da mace idan baki sani ba ki sani shiyasa nake sake jajjada miki chance ur chance before chance, chance on you kiyi amfani da damarki kafin damar tayi amfani dake tunda Asad yace miki yasan da aurenki kija baki kiyi shiru kafin ki kaishi bango ya furta miki kalmar ya fasa duk ranar daya fad'i haka tofa ko mutuwa zakiyi bazai ta'ba aurenki ba nasan Asad nasan halinsa ba tun yanzu ba shi kaifi d'aya ne sannan baya magana biyu kin gane"?.

Shiru Clarah tayi tana kallon Asad jikinta a sanyaye itakam ta kad'e ta gama yawo ace mutum kana son sa kana nuna kulawarka garesa amma shi Sam baya takai da xata iya saita ha'kura dashi saidai batajin koda duk duniya zasu taru a kanta akan ta rabu da Asad bazata iya ba saidai idan numfashin ta ne ya yanke...................

"Zaki iya tafiya".

Jin muryar Asad yasa a firgice ta dawo daga tunanin da take tana daidaita kanta tace "kayi hakuri dan Allah bazan sake ba".

Kalmar farko ya sake maimaita mata "zaki iya tafiya''.

Da mamaki tace "haba Asad ha'kuri fa nake baka ka saurare ni kafin na tafi....................

"Clarah get of my sight''.

Jin abinda yace yasa ta mi'ke tana sake kallon sa tare da jin zuciyarta kamar zata fito waje daga qirjinta tsabar zafi da turaruwar da take da zata iya ko tana da iko data fito masa da ita yaga yadda ta cika ta batse da soyayyarsa a kewaye take da muradin kasantuwa dashi tana fatan ranar da zata bud'e ido ta ganta tare da Asad matsayin couple💑 sauke ajiyar zuciya tai bata sake cewa komai ba ta fita a gurin da kallo Isham ya bita yana girgiza kai sannan ya mayar da hankalin sa kan Asad yana cewa.

"Ni kuwa Buddy ya batun abinda kake nema ka gano yarinyar ko har yanzu a'a"?.

Kai Asad ya d'aga masa ''ban ganota ba amma dai bincike ya nuna min 'yar Nigeria ce zuwa gidan da nayi tazo min a mafarki tayi min bayani sosai akan 'kungiyar kuma na yarda da abinda ta fad'a min domin dajin da suke ciki tabbas ba dajine wanda yake a bayan qasa ba dajine na siddabaru ba'a iya ganinsa kuma dole saida wata sar'ka ake iya shigarsa tace min akwai sar'kar a wuyan kowanne d'an 'kungiyar to amma Isham abinda na gagara fahimta har yau shine ita yarinyar mutum ce ko aljana idan mutum ce taya ta sani bayan tana karamar yarinya kuma ba wata babbar ma'aikaciya ba a cikin bincike na nagano bata da ala'ka da wani wanda yake neman 'kungiyar kuma batasan ana neman 'kungiyar ba sannan kullum suna cikin yi mata barazana duk ranar data fad'awa wani zasu hallaka ta amma haka bai bata tsoro ba a halin yanxu maganar da muke dakai mafi yawancin abubuwan da suke aikatawa ta sani d'ai-d'ai ne suka 6oye mata shi sai dai Isham nayi iya kokarina amma na gaza ganota na rasa inda take da kamar ace zanyi sa'a ta kunna location d'inta shine zansan inda take kai tsaye amma matukar mukaci gaba da tafiya a haka har abada bazan san komai ba".

Sauke numfashi Isham yai yana kallon sa yace "to yanzu mafita d'aya ce mezai hana kayi mata magana kace ta bud'e location d'in''?.

"No Isham link d'in shafinta baya aiki ai basu barta banza ba sun lalata mata komai ta yadda bazata iya tura sa'ko ko a turo mata ba shiyasa suke nuna mata komai sun san daga laptop d'inta babu inda zata iya share d'insa".

Kai Isham ya jinjina yana cewa "kai amma abun baiyi dad'i ba duk da haka Asad kada ka sare kaci gaba da jajircewa kamar yadda ka saba kullum insha Allahu zaka samota".

"To Amin Isham saidai bansan ta inda zan fara binciken ba"?.

"Tunda a Nigeria take acan ne idan kaje ya kamata ka tsaya ka bincika koda ace zaka dawo".

"Ok shikenan Isham zan jarraba".

"Yauwa Asad Allah ya bada sa'a Allah yasa ka samota a wannan karon" Amin yace masa ganin lokacin sallah yayi yasa suka mi'ke suna fita daga cikin babbar rumfar barrack d'in da suke.

🏕️QAUYE🏕️
________ Yau Dauda da Indo suka sauka uhm mamaki kowa keyi musamman wasu harda masu rantsuwa ba Indo bace saidai wata matar Dauda ya aura acan masu ganin 'kwa'kwaf saida suka zo suka tabbatarwa kansu Indo d'ince da gaske nan fa akaita gulmar abinka da qaramin gari ko'ina anji harda masu zuwa sannu da dawowa dan suga meke going.

Indo tayi mamakin jin wai Dalah ta koma gidan babanta Balarabe gaskiya bata ji dad'i ba a fili qarara ta nuna rashin jin dad'inta da hakan Aliyah ta nuna Mata yanxu fa ba irin da bane Balarabe ya sauya Asabe bata da iko dashi ya dawo cikin hayyacinsa jin hakan datai yasa tad'an ji dama-dama amma duk da haka bata le'ka gidan ba a ranar sai washe gari da yake shigowar yamma sukai.

Tun safe taiwa Irfan wanka ta shirya shi itama tayi wankan bayan sun karya Dauda ya sa'ba d'ansa a kafad'a domin yanxu ya riga ya waye hakan ba komai bane suka tafi gaishe da Dalah suna shiga da sallama Dalah ta zaro ido waje tana cewa.

"Indo kune a gari"?.

Murmushi Indo tai tana kallon kofar d'akin Asabe batai magana ba ta karasa gurin Dalan sakamakon d'aki akwai zafi yasa ta d'auko musu tabarma waje zama sukai suna gaida ita fuskarta fal da fara'a ta amsa balle dama tun jiya yara suka zo suka yi mata albishir Indo ta dawo.

Kar'bar yaron tai tana kallon sa da murmushi a fuskarta tace "masha Allah Balah (Irfan) yayi girma lallai kun dad'e rabonku da gida ai jiya ina zaune Yusufa yaron gidan malam Hamza ya shigo da gudu ni harna yi zaton ko irin tsokanar nan ta yara yayo aka biyoshi na fara masa fad'an ya daina tsokanar kar wata rana ya tsokani wanda yafi karfin sa ya dakeshi sai yake cemin ba tsokana yayiba wai kune kuka dawo yazo ya fad'a min harda d'a um alhamdulillah Allah ya raya gashi babanki bai dad'e da fita waje ba ko kun had'u a hanya"?.

Kai Indo ta girgiza "a'a bamu had'u ba".

Dalah nayiwa Irfan rawa tace "to ta yuwu ko nisa yayi amma tunda anan zaki wuni harya dawo ku gaisa".

Tana rufe baki Balarabe yayi sallama da kaya a hannunsa ganin wadanda suke zaune yasa ya karaso yana cewa "Indo kece ko kuma ido nane"?.

Sauke ajiyar zuciya Indo tai itama tana kallon shi tace "nice baba ina kwana"?.

Zama Balarabe yai da fara'a yace "lafiya kalau fatan sun sauka lafiya"?.

Kaita d'aga ''lafiya alhamdulillah".

"To madallah" mayar da hankalin sa kan Dauda wanda ke gaidashi ya amsa yana cewa "Allah yayi maka albarka Dauda Allah ya baku zaman lafiya da zuriya dayyiba" Amin Dauda yace yana mi'kewa ya fita a gidan kar'bar d'an shima yayi sai kallonsa yake xuwa wani lokaci ya d'ago yana kallon Indo da suke zance da Dalah yace.

"Am Indo dan Allah kiyi ha'kuri ki yafe min kuskuren dana aikata miki a baya wallahi bansan meya sameni ba nake irin wadannan abubuwan na sani kinyi ha'kuri a gidan nan kin sha wahala amma yanzu ga ribar ha'kurin nan kina gani Allah ya miki babban arziki kina zaune lafiya a d'akin mijinki ido ba mudu ba amma yasan kima Indo ko ba'a fad'a ba ansan kinajin dad'i a hannun yaron nan Dauda ya rikeki da amana Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa sannan bazan gajiya ba da neman gafararki ba dan Allah Indo ki yafe min kuskuren dana aikata miki a baya"?.

Kai Indo ta girgiza tana cewa "a'a baba bakai min komai ba na yafe maka albarkarka nake nema".

"Allah ya albarkaci rayuwar ki Indo" Amin tace cikin jin dad'i tana kallonsa rabon da ta zauna wai Balarabe ya fad'a mata magana mai kyau ta ruwan sanyi harta manta wannan lokacin.

Tashin Asabe kenan daga barci jin maganganu yasa ta fitowa ganin wadanda suke zaune ga Indo da gaske kamar yadda labari yazo mata cewa sun dawo harda d'a tayi ki'ba ta kara kyau Asabe batasan lokacin data sake murje ido ba ganin da gaske dai Indon ce yasa tace.

"Indo Indo wai dama da gaske yara suke jiya da naji anzo ana cewa Dalah kin dawo harda d'a"?.

Kallonta Indo tai batare da ta kawo komai daya faru a baya ba tace.

"Eh nice baba Asabe ina kwana"?.

Kamar Asabe zata fasa ihu da'kyar tana had'a ba'ki tace "la la lafiya kin dawo lafiya"?.

"Lafiya kalau ina Bahijjah"?.

Shiru Asabe tai bata iya ce mata komai ba zuwa wani lokaci tace "ta mutu" tana fad'in haka ta koma daki zaro ido Indo tai tana kallon Dalah tace.

"Innalillahi Bahijjah ta mutu"?.

Kai Dalah ta girgiza tana cewa "a'a bata mutu ba tayi aure ta auri wannan yaron Iluh d'an garuwa wanda farko yace yana sonki har sun kawo rokon arziki aka fasa sakamakon zuwa gurin mai gari da akai to shine ya aureta saidai da yake Asaben bata so inaga shiyasa tace miki ta mutu".

Indo bata sake cewa komai ba har Asabe ta sako hijab tazo tana cewa Balarabe "na shiga gidan Markah"?.

"Sai kin dawo".

Tana ji ya fad'i haka ta fice da sauri tana tafe kamar zata kifa harta qarasa gidan tun daga zaure take kwala Kira.
Chapter 114 · 0% Book details