Sashe 14
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"ASAD kayi kokarin da baza a samu wanda zai iya koda kwatan kwacin saba na jinjina maka kaidin jarumi ne sadaukin da ba tamkarsa lallai zaka iya fad'a da koma waye kaine mutum na farko daya shigo tarkon mu akai kokarin bada jininsa amma ya tsira ya haye ya tsallake rijiya da baya saidai ka sani cewa bazaka iya gano kungiyar mu ba har abada kaiwa sauran yan uwanka sojoji masu son gano mu albishir cewa sunyi kadan ba wanda ya isa jada mu a halin yanzu da nake maganar nan dakai mun hallakar da sojoji d'ari biyar masu neman wannan kungiya tamu ciki harda babban abokinka wanda kayi matukar damuwa dashi kuma baza ku kara haduwa ba har abada kaima na barka ne kawai dan ka bada labari ka fad'awa masu neman wannan kungiyar irin ka cewa su dakata kafin su rasa ransu domin kungiya ce ta matune masu had'ari zan barka kaje kayi nazari hhhhhhhhhhh ya karasa maganar yana shekewa da wata mahaukaciyar dariya.
A fusace Asad yai tsalle yana hawa kan macijiyar ya damko mutumin suka yo kasa nan dambe ya kaure tsakanin su kowa naji da 'kuwwa da karfi duk gurin ya rude kamar mutum dubu ke fad'a so mutumin yake ya kwace sakamakon da fari ya dauka yafi karfin Asad zaiyi nasara a kansa sai daga baya yaji Asad din na neman halaka shi ya samu da'kyar ya kwace daga rikon dayai masa yana tsalle ya koma saman macijiyar da matukar gudu macijiyar ta tashi sama a hanzarce Asad ya harbo macijiyar da bindiga tayo kasa kara harbinta yai itama saita zama ruwa kafin ya saitin mutumin a satin Zuciyar shi ya harbeshi shi shima kara yai sai kuma ya kama da wuta faaaa kamar an zuba masa fetur wanda yaji falon ya kaure suna cewa "Asad lafiya me kakeyi haka"?.
Da sauri Asad ya dawo cikin nutsuwar yana kallon su cikin alamar tambaya yace "me nayi"? Hararar sa Ajeeb yai yana cewa "ban sani ba tsabar rashin mutunci kagani fa yadda ka harbi TV gashi nan ta fashe me kake kallo kodan kaiba ma'abocin son wasan kwallo bane maimakon kace mu canza channel shine ka lalata TV gabadaya wato mu daina kallon kenan"? Kasa cewa komai Asad yai sai Khimiyyah daya zubawa ido gira ta dage masa tana murmushi ba tare datai magana ba Ajeeb yaci gaba "wai Asad meke damunka ne sai anyi magana kai banza da mutum ko ka kure shi da kallo kamar Wanda ya warke daga ciwon makaranta" shidai Asad rasa ta cewa yai sai kallon Khimiyyah kadai yana mamakin abubuwan daya gani yanzu kenan Khimiyyah me take nufi wannan abun da ya gani hakan na nufin tana da ala'ka da kungiyar da yake nema? Jiyai tace "prince Asad kada ka damu da abinda ka gani wannan mafari ne ba'a nuna maka komai ba saidai ana farkar dakai ana maka gargadin cewa ka fita daga sahun masu son gano wannan abar kayi shawara" harararta Ameer yai yana cewa "ke kuma me kike cewa sai wani magana kike a juye me kike nufi"? Dariya tai tana mikewa tace "babu komai prince Ameer kawai dai na fad'a ne shi yasan me nake nufi" tana fadin haka ta mike tana fita a parlon "wai ita wannan meke damunta ne? Yawancin lokuta zakaji tana magana wata kala da batai kama data masu hankali" Annur ya fad'a shima yana mikewa ya cigaba "Khimiyyah a kaf cikin mu na fahimta itace ta fita daban take wasu irin abubuwa masu wuyar fassara yarinyar nan tana da matsala a kwakwalwarta".
"Ai Annur ba kai kadai ne ka fahimci hakan ba nima na gani sau tarin wasu abubuwan ta akwai abun duba da tambaya amma koma maye mu sa mata ido matsayin mu na yan uwanta muna da hakkin kula da duk wani motsin ta mu dawo da ita kan hanya" Ajeeb yai maganar yana mikewa shima zai fita har yakai kofar palon ya juyo yana kallon Asad yace "Asad kai kasan me Khimiyyah take nufi tunda dakai take sai ka fara tunani kayi nazarin ta mu hada gwiwa muna kula da komai nata" yana gama fadin haka yai waje tsaki Ameer yai yana cewa "waye zai tsaya bata lokacin sa akanta Khimiyyah ta fara zarce inda ake zaton ta a iya sani na banda makaranta daya zama dole babu inda ake barinsu su fita amma idan tayi wani abu zaka rantse irin wadannan tantiran yan matan club din nan ne" "eh kaima kace wani abu anan amma ai ni banga hujjar da zamu zauna muna binciken ta da sa mata ido ba kawai su Abba zamu sanarwa" kai Ameer ya girgiza "a'a Annur idan su Abba suka sani akwai matsala zamu lalata zaman jin dad'i na wani lokaci kawai ka 'kyale mu samo hujjoji da kanmu kafin mu sanar musu" "ok shikenan hakan ya kamata muyi" Asad ya kalla yana cewa "Babyn Mami muje lokacin sallah yayi" mikewa Asad yai yana rufe laptop din da sauri Makiyyah tace "prince Asad kawo na aje kuje masallacin" "no thanks I don't want" ya fad'a yana ficewa dariya Shaukiyyah tai tana cewa "kai gaskiya iska tana wahalar da mai kayan kara ina son shi yana zamewa" a fusace Makiyyah tace "ki dakata malama fatan ba dani kike ba"? Zaro ido Shaukiyyah tai tana shirin sakin wata dariyar tace "da nace miki me? Yau nake ganin isa da mallaka sharri zaki min Makiyyah"? Hararar ta Makiyyah tai cikin takaici tace "jarrabawa ce kema baki fi karfin a jarrabe kiba so haka yake fad'i da babbar murya ki 'kara ina matukar son Asad so mai tsanani ma kuwa" cikin tsokana Shaukiyyah tace "au haba so fa mai tsanani kika ce? Tab lallai kina da aiki wallahi prince Asad babu yan mata a gaban shi balle soyayya karma ki nemi dorawa kanki hawan jini" caraf Khaldiyyah tace "haka kike gani amma tunda taji tana son sa zata iya daukar duk wata damuwa mukan namu ido ne tunda mutum ya fad'a ruwa sai muga da yadda zai fito" nuna ta Makiyyah tai da yatsa tana cewa "ki dakata haka ki daina yi dani tun farko soyayya Asad a jini na take ta riga da ta zama kwalliya ta kuma bazan daina ba ko ku taya ni son abinda nake so ko ku zuba min ido nai gwagwarmaya ta da kaina na nemi soyayya ta" "to shikenan Mrs prince Asad Allah ya baki shi musha biki" Shaukiyyah tai maganar tana kau dakai dan kada Makiyyah taga dariya take mata mikewa Makiyyah tai tana cewa "amin inda gaske kike" fuuuu ta fice ta bar iya su biyu sauke ajiyar zuciya Khaldiyyah tai tana cewa "wallahi ina tausaya mana nida Makiyyah dukka hankalin zaratan namu ba'a kan mu yake ba" tabe baki Shaukiyyah tai tace "nikam shiyasa tun farko ban dorawa kaina wahala ba farko na harbu dason Ameer da naga kawai zan bata lokaci na kawai na share abun kuma da haka kukai ina tunanin zaifi domin ni gashi na zauna lafiya" kai Khaldiyyah tai girgiza cikin damuwa tace "bazan iya Shaukeey kawai zanci gaba da hakuri har ranar da prince Annur zai ce yana sona" kai Shaukiyyah ta kad'a "shikenan Allah ya kaimu wannan ranar" "Amin ya kamata muje muyi sallah kinga har lokaci ya fita" mikewa sukai Shaukiyyah na cewa "oh haka ne fa to sai muyi sauri".
Lokacin da Asad ya dawo daga tunanin kallon Isham yai tare da jinjina kai yace "Isham I believe what you said tabbas Khimiyyah tasan wani abu akan kungiyar nan domin ta ta'ba nuna min alama a bayyane" "oho ka gani ko dama na fad'a maka sai ka tsaya kayi nazari zaka sake gano komai, yanzu wanne irin mataki zaka dauka"? Shiru Asad yai zuwa lokaci mai tsawo kafin yace "sai nayi nazari" kai Isham ya d'aga "ok shikenan buddy amma ka taso muje ka kwanta dan Allah ka samu nutsuwa ka saba zama ka kwana ido biyu kana tunani da ayyuka bakai komai ba please let go" mi'kewa yai batare daya sake magana suka shiga bedroom.
Mrs al'ameen Ahmad ce 😘.
Yau ba dogon bayani kawai Allah ya tashe mu lafiya mu d'ora inda muka tsaya yau kaina na min ciwo😒.
11~AL-KHALIQU
The creator
12~AL-BARI
The Designer
6~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Taibina.
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
🎉🎉🎉🎉🎉
🎉🎉🎉
🎉🎉
🎉
🌄 REVENGE ND WREAK🌄
Episode 11&12
*'KAUYE*
Asubar fari tun ba'a shiga masallaci ba Asabe ta fito daga d'akin ta jin yadda ake kad'a iska mai sanyi yasa ta koma d'aki tana dauko hijab sannan ta fito ta bud'e randa ta soma kamfatar ruwa tana zubawa a bokati Saida ta cika ta kinkima ta shiga d'akin su Indo kwance ta ganta tana bacci can dayan 'bangaren Bahijjah ce itama a tata shimfidar cike da mugunta Asabe ta d'aga bokitin ruwan sanyin ta kwarewa Indo a kanta a firgice Indo ta farka tare da fasa 'kara jikin ta na ma'kyarkyata tsawa Asabe ta daka mata tana cewa.
"Ke dallacan munafika mitsiyaciya ki rufe min baki dama yanzu lokacin hutu ne tashi ki fito ki tafi debo min ruwa me nace miki jiya ban ce kika bari na sake zuwa tashin ki saina fasa miki baki ba"? Shiru ido tai ta kasa magana sakamakon kakkarwa da bakinta yake wani irin duka Asabe ta sauke mata tana finciko ta kiiiii ta wurga ta waje tana daukar ice ta soma jinka mata tana cewa "ke dan uwarki nice zanyi miki magana ki tsaya kina kallo na da idonki kamar na mayu tsinanniya makira mai halin mujiya zaki tashi ki debo min ko saina farfasa miki jiki"?.