Sashe 37
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Katse ta Ramatu tai "saurara da Allah Salamatu na gaji da wannan dogon bayanin naki aina sani nace ko" mi'kewa Salamatu tai tana cewa "a'a ba maganar kin sani bane sake tuna miki nai kada abu yazo ya cakud'e" tana gama fadin haka tai waje da harara Ramatu ta rakata daidai Ilyah zai shigo d'akin ganin Salamatu na shirin fitowa bai matsa mata ba itace tai 'ko'karin bashi hanya tare da matsawa gefe amma duk da haka Ilyah saida ya bangaje ta ya wuce mamakin tsaurin idonsa Salamatu tai saidai wannan mafari ne kadan ne daga cikin halayensa marasa tsari daya koya daga Ramatu wanda bazai kaishi ko'ina ba.
Yana shiga d'akin yaga Ramatu sai kaiwa da komowa take ganinsa yasa har tana 'kwarewa tace "yauwa Ilyah dama kai nake nema muna cikin bala'i mun shiga uku yau ranar tonon asiri tazo dole mu tashi tsaye mu kauda matsiyaciyar tsohuwar nan".
Zama Ilyah yai yana cewa "su waye meya faru"? Ramatu na huci kamar wacce tai gudu tace "Salamatu man yanzu baku had'u da ita ba tazo tayi so'ko'ko aka wai tana tuna min cewa manyan gonaki biyun da malam yake nomawa na d'anta Sabi'u ne taji ina zancen rabon gado kar nace za'a raba harda su" "to sai me dan ma yana da gonaki da yawa nasan da an raba mana zan zama me arziki ki had'a min da tumuninki na fara kasuwanci shiga da fitar kaya ina sayar da manyan hajoji masu tsada" washe baki Ramatu tai "kuma fa haka ne kaima ka iya kawo shawara yanzu dai shikenan bari a raba gadon muga iya kason mu na rantse da Allah Salamatu bata bina bashin rantsuwa idan ta kuma 'bata min rai akan maganar gonakin nan sai na shafe tarihin ta saidai ayi ba ita".
Ilyah dai na kallon Ramatu sai surfa bala'i take tana bushewa bai saike tanka mata ba ya tashi ya fice a kofar gida yaga Sabi'u da Habu sun shimfida tabarma suna zaune gabansu kwanuka tsaki yai baiko kallesu ba yazo zai wuce Sabi'u ya dakatar dashi "Ilyah tun dazu fa kai muke jira abincin har yayi sanyi bakazo ba" wata irin ba'kar harara Ilyah ya sakar masa yana cewa "dawa zakuci abincin? Amma dai bada niba na wuce ajin cin abinci da irinku" gaba yai bai saurari Sabi'u dake faman masa magana ba Habu da ransa ya gama 'baci yace "dan Allah yaya Sabi'u kaima ka 'kyale shi ai Allah ya gani mun fita hakkinsa duk wanda ya zagemu mun barshi da fitowar rana da fad'uwarta shiru Sabi'u yai cikin damuwa yace "ni bana so ne ace kanmu ba'a hade yake ba mutane a gari zasuga kamar mun ware shine amma babu komai muci kawai" sun kasance sun matukar damuwa da rashin d'a'ar da ilya yake nunawa saida ya zasuyi babu yadda suka iya.
Kamar yadda Ramatu ta bukata haka tai tsayin daka saida aka raba gadon nan kowa ya san matsayin sa nan da nan suka fara kasuwanci kamar abun gasa kudade suka fara shigowa wadata ta samu amma Sabi'u duk ya fisu samun bud'i da Ramatu ta bud'e ido taga Ilyah bai tara na kansa nan hassada ta shiga zuciyar ta da ba'kin ciki ta kasa zaune ta kasa tsaye afujajan taje gurin 'kawarta neman shawara ta kuwa samu ta kaita gurin boka wai ya baiwa Ilyah sa'a da kasuwa a sawa wadancan bakin 'kyalle da farko aikin yaci sosai daga baya yazo ya karye sun koma basuyi sa'a ba dan boka ya tashi daga dajin kuma basu san inda ya koma ba.
Hankali tashe ta samu ilyah "kai Ilyasu nifa ban gane ba anyi gabas da kare wai meya haka ne kwanan baya naga kasuwanci wada wada amma yanzu kace a sati baka rike dubu goma taka? Gaskiya ne Salamatu kwai muguwar mace wai asiri tai maka ko Sabi'u gashi nan har ya sayo shanu ya had'a amalanke amma kai ko kaza baka saya ba gashi tun daga zancen auren sa da Rakiya yar gidan na'ibi har anyi auren harda 'ya'ya biyu me kake kallo Habu ma daka girmeshi gashi nan da yake shi kasuwancin yana kai masa lokaci guda ya auro mata biyu Saude da Binta gashi shima a gidansa an samu 'karuwa Sauden ta haihu mace ansa sunan kakarku Asma'u naji Sadi ma abokinsa yayi kai kuma saboda mutuwar zuciya tun daga Bara'atu shekara kusa uku bata haihu ba kuma baka kara wani auren ba banji kace komai ba ina naka zancen da Maimuna ya kwana"? Ta'be baki Ilyah yai "yana nan man jira nake na karasa gini na kema na fitar dake daga wannan gidan ki koma guna" zaro ido tai cikin murna tace "Allah kace kwanan nan zamu fara shan romo" "umh zaki sha kam dan bijimi zan ri'ka yanka mana" rasa inda zata sa kanta Ramatu tai saboda jin dad'in abinda Ilyah yace har haskowa take tayi dumu dumu cikin mai'ko😂.
Tace "yauwa d'an albarka kace yanzu zamuyi rayuwa me yanci da muna zaune a bushe a 'kai'kashe kamar kilishi kullum murna nake fata nake ina jiran wannan lokaci na bayan ran malam domin samu dukiyar gado dan haka maza ka shirya yanzun nan akwai wani guri da nake son muje idan mun samu abinda muke so matsalar mu ta zamo she'kak'kiya".
"Ina ne wanne wurin ne me zamuyo"?.
Ramatu na kokarin daukar gyale tace "kai dai tazo man ka gani ko bayan raina ka rike wannan ka huta yace sai dare ya raba zamuje yana cikin daji" "daji kuma amma mutumin arziki ne zaiyi rayuwa a daji"? "Yo Ilyah taya dama wanda yasan me yake zai bar zaman cikin jama'a ya koma daji boka ne fa".
"Boka kuma amma me ye had'i na da boka mezai bani"?.
"Me zai baka kake tambaya? Tab lallai Ilyah bansan asirin da sukai maka ka lalace haka ba har boka kake cewa wai me zai baka"? Zama Ilyah yayi yana jan wani kwano dake rufe ya bud'e ganin shinkafa yasa ya fara ci wani kallo Ramatu ta masa tana cewa "yau nake ganin sakarai sauna Iliyasu anya Habu da Sabi'u basu je gurin yan bori sun kashe maka zuciya ba gaskiya bazan yarda ba saina je gurin boka na naji komai" Ilyah bai sake ce mata 'kala ba haushi ne ya kama Ramatu ta soma balbale shi da masifa amma yai banza Saida ya gama ya mike yana kallon ta yace "karki damu nan da sati biyu zaki bud'e ido kiga surukar ki nima biyun zan aura Bara'atu da Maimuna domin ina matukar kishi da habu har bansan yadda zan kwatanta miki ba" cikin farin ciki Ramatu tace "yauwa d'an albarka haka nake son ji sai yanzu naji zuciya ta tayi sanyi na fasa zuwa gurin bokan yau sai wani lokacin" Ilyah na shirin fita yace "in an jima zansa a kawo miki nama" zaro ido Ramatu tai baki washe tace "kai kai kai kace yau zanyi bacci da mafarki ina jiranka dan albarka" sa kai Ilyah yai ya fita a gidan yayin da yabar Ramatu sai rawa take a d'aki tana shewa.
Alpha tunda ya fara jinyar rasuwar Lami ake fama dashi lafiya ta'ki samuwa saidai yanzun ba kamar da ba ya samu sauki jikinsa ya warware amma har lokacin nutsuwar sa bata dawo ba saidai da sauki tunda yana magana zaune yake a parlon gidan su Naja'atu wanda yanzu zuwa gurin ta na d'ebo masa kewa tsawon lokaci baiyi magana ba dan Naja'atu har ta fidda rai da zaice wani abu sai kuma taji yace.
"Naja'atu wai dan Allah da gaske shikenan Lami ta rasu bazan sake ganin taba har abada taya zan manta da ita"? Sauke ajiyar zuciya Naja'atu tayi tare da dan rufe ido tana tuno rayuwar da sukai a baya cikin son boye hawayen ta tace "Alpha kayi hakuri dan Allah tabbas Lami ta rasu bata duniya ta tafi ta barmu da kewarta babu yadda muka iya sai addu'a abinda ya rage tsakanin mu da ita bansan ta yadda zan fara kwatanta maka yadda na damu da Lami da halin dana shiga a kanta ba Alpha na sani kana tsananin son ta nice mutum ta farko dazan bada sheda akan haka dan Allah kayi hakuri ka dauka rayuwar da kukai a baya kamar mafarki ne" kai Alpha ya jinjina "lallai kowanne lokaci da irin nasa salon dole ya nemi taimako dan tunanin ta na gaf da rusa masa rayuwa Zuciyar sa ta kusa bugawa kallon Naja'atu yai kafin ya mi'ke yana cewa "shikenan Najat na gode zan tafi ki gaida min mama" mi'kewa Najat tayi suna fita tare tayi masa rakiya ya tafi bayan rasuwar Lami tana so ta fad'a masa tana son sa ta kasa kawai tana matukar tausaya masa ne daga haka abu ya zarce kullum idan suna waya tana shawarar fad'a masa ta kasa balle su had'u face to face saidai tana adda'ar Allah yasa shima yaji wani abu a kanta.
Zaune Balarabe yana shan fura yake gefensa Dalah tana tankad'en garin masara d'agowa yayi yana cewa "nikam ina Indo ne har yanzu ban ganta ba tunda na shigo gidan nan"? 'Dan murmushi Dalah tayi tana cewa "ai tun d'azu ta fita nidai tace min gurin Adama zataje kuma ban sani ba ko ta biyo ta wani gun" kallon ta Balarabe yai "amma me nace miki bance ki daina barinta tana fita koda yaushe saboda ina ji da ita bani da wata 'yar ita kadai ce jini na gashi ba wani girma tai ba ina tsoron kada wadannan yan iskan da suke lalata yara cin zalin nasu ya biyo ta kaina" sauke ajiyar zuciya Dalah tayi daidai ta mi'ke zata je gaban murhu tace "insha Allahu malam babu abinda zai same ta" shiru Balarabe yai hankalin sa jin bai kwanta ba mi'kewa yai yana cewa "bari na bi bayanta gaskiya na taho da 'yata" yana fadin haka yai waje da kallo Dalah ta bishi cikin jin dad'in nuna kulawarsa ga 'yar tasu guda tal kamar rai da yake.