Sashe 92
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jitayi yace "kina jina Asma'u cene ko wace kodan ba sanin wacece ke d'in ne damuwa taba ba wannan nake son fad'a miki ba ki bud'e kunnen ki dakyau kijini sa'ko daga ni Ilyah zuwa gurin Habubakar kice masa ba yaji yau akazo ro'kon arzikin Nafisa ba kada ya kuskura naga 'yar qafarsa a kofar gidan nan da sunan yazo kar'ba ban gayyace shiba bana yi dashi da masu kyakkyawar sutura nake sha'ani na irinsu Alhaji Gambo" ya fad'a daidai anyi sallama a kofar gidansa yace "hum kinji Niko zaki iya tafiya fatan dai basu baki kayan 'kwalamar ba dan nasa abinda ya kawo ki kenan ba wata tsiyar ba kila 'kwad'ayayyan uban naki ne ya turoki ga mai kud'in banza kuzo a baku yau ku samu abincin dare ko saboda su Hassan basa nan kun dawo gidan jiya cikin talaucinku da kwanan yunwa idan ba munafirci ba da baki zo ba sai yau? Tabd'i Allah ya sauwake kaji talaucin ko Habubakar yayi asara" ya fad'a yana kallon Amatu daidai Alhaji Gambo d'an kasuwa ya shigo domin yanzu shine babban abokinsa kaf qauyen dashi yake harqalla cigaba Ilyah yai da cewa "gara da basu baki ba naga karshen son zuciya kuma wallahi dasun baki wannan kayan ma saina kar'be domin nayi alkawari Habubakar bazai ta'ba morata daidai da naira biyar ba koda zai mutu ne saboda ba'kin ciki har abada fice ki bani gu nace shine ina magana kika tsayar da ido kina kallona har ina neman 'kwaruwa ban sani ba ko Habubakar ya sayi maita ne? domin ga alama nan kin nuna da ido kina neman tsotse min 'bango ki cinye ni😲 dalla ki barmin gida nace" yana fad'in haka ya wuce da sauri itama Amatun ta fice daga gidan sannan bata amince ta fitar da hawayen dake damun cikin idanuwanta ba kuma koda taje gida bata nuna wani abu dazai fallasa abinda yafaru ba kuma bata fad'awa malam Habu cewa ga sa'kon da Ilyah ya aikota ba kawai ta share tayi kokari ta danne abun duk da yana cin ranta ganin abun zaiyi mata illa a zuciya yasa ta tashi tana kunna laptop d'inta domin d'ebe kewa duk da ba koda yaushe take samun damar kaita caji ba dole sai an bar kauyen shiyasa sai tayi sati bata bud'e taba.
🧜🧜🧜🧚🧚🧚
Bayan wani lokaci hummm tafiya dai tafiya inji madugu wata sabuwa inji d'an caca bayan watanni shida da kar'be gonar malam HABU wadannan mutane suka kuma dawowa da baya wai kud'in gonar da akai lissafi baikai yadda zai biya su wannan kayan na buhu goma ba sannan an ta'ba kawo masa bai biya haraji ba sau biyu shima dubu dari dole ya sake ciko musu kud'i yanzu ko su tafi dashi😭..
Rasa inda zai d'ura kansa yaji dad'i a duniya malam Habu yai suna waje da mota suna jiransa wai sun bashi awa daya ya kawo musu dubu d'ari biyu🙊 idan bashi da ita ga takardar sammaci sun yanko sun taho masa da ita zaiji jiniyar yan sanda sharce gumi kawai malam habu yake yi a tsakar gida ya shiga d'aki ya fito ya juya nan ya Kalli can ga iyalai suna kuka damuwa goma da ashirin jin suna yi masa horn yasa da sauri ya fita waje ko takalmi bai d'eba tuni ya rafka tuntu'be a babban yatsarsa na qafa da wani dutse dake kafe cikin zauren gidan nasa farcensa ya d'ago jini na zuba saura kad'an farcen ya fice daga jikinsa amma tashin hankalin da yake ciki baisa yabi takan ciwon da yaji ba damuwarsa ya samu ya rabu da wadannan mutanen lafiya baya so yabar cikin ahlinsa baisan Mai zaicewa ubangiji ba tunda ya gaza sauke nauyin daya d'auka na hakkin iyalan nasa.
Yana d'ingishi ya fita wajensu murya na rawa yace "dan Allah dan Annabi kuyi min rai wallahi bani da ko naira biyar a cikin gidan nan wanda zan dauka na baku amma ayi cinikin gidan idan yakai na kud'inku saina biya dashi"
Kai wani daga cikin jami'an ya d'aga yana cewa "ok ai malam Abubakar kaga nan garin kune kai kasan inda zaka samo dillalai sai kaje ka kirasu ayi cinikin muna jiranka zamu wuce".
Jin haka yasa da sauri malam Habu ya nufi gidan Ilyah yasa akayo masa sallama dashi bayan ya fito ganin Malam Habu yasa ya had'e rai yana tamke fuska bai damu da yanayin tashin hankalin daya ganshi a ciki ba duk da yasan kwanan zancen amma yai burus sai maganar wulakanci
daya tarbeshi da ita yana cewa.
"Habubakar me kuma ya kawo ka gurina bayan akanka da 'ya'yan ka babu irin cin mutumcin da Hassan basuyi mini ba a cikin garin nan"?.
Sauke numfashi Malam Habu yai yana cewa "dan Allah yaya Ilyah ka saurare ni ba wannan ce ta kawo niba xuwa nayi idan zaka sayi gidana kazo muje ayi ciniki ba'kin nan aka sake turo min wai akwai wasu kud'ad'en da ake bina a kasa dubu d'ari biyu idan ba haka ba saidai su tafi Dani ni kuma bana so na tafi nabar iyalai na cikin wani hali dan Allah ka taimaka min idan ma bazaka saya ba ka ara min na biyasu daga baya zanyi aiki tu'kuru na biyaka nidai damuwa ta na fita daga hannunsu".
Wani kallo Ilyah yai masa yana cewa "au haba to su tafi dakai d'in man Ina ruwana meye damuwa ta nine kake cewa zan d'auki bashin kud'i har naira dubu d'ari biyu na baka? Hum lallai kayi kuskure tun wuri ka farka daga wannan banzan tunanin da talauci ya d'ora maka kai harka manta irin abubuwan daka jawo min dasu Hassan akan tsinannun yaranka Ina kud'in da suke kai maka na zancen? kodan Ina za'a samesu duk sun qone tunda duk na haram ne dana Allah ya isa kaci kaida mitsiyatan matan naka da 'ya'yan naka wallahi tallahi Habubakar ko bindiga yanzu aka saitaka da Alan wannan kud'in bazan ara maka ba kuma bazan sayi gidan ba saidai a harbe ka uban me zanyi da kayan daya fito daga hannunka naje na gogi masifa da talauci dan haka ka barmin qofar gida"..
Kai Malam Habu ya girgiza duk da yaji mugun ciwon maganganun da Ilyan ya fad'a masa amma bai ha'kura ba marar abu baya zuciya qara qar dakai yai yana cewa "nidai yaya Ilyah duk ba wannan ba dan Allah ka taimake ni ka saya karsu tafi dani😭.
Tsaki Ilyah yaja yana kallon yadda yatsar qafar Malam Habun ke fitar da jini amma tsabar rashin tausayi ya d'ago yana kallon cikin idanunshi dayai ja saboda 'bacin rai yana cewa "wallahi Habubakar saidai su tafi dakai amma bazan saya ba koda ace idan sun tafi dakai d'in shikenan har abada bazasu dawo dakai ba bai dameni ba meye had'ina dakai iye fad'a min Baffah ne kuma baya nan koda ace yana nan bazan fasa na sauka daga abinda nace ba balle baya duniya bani da wani had'i dakai daga yau bani bakai kajiko dan haka yanxun nan kabar min kofar gida na kafin nasa wadancan almajiran suyi ma atule da qairayi"ya fad'a yana kallon almajiran dake zaune a karkashin wata bishiya zasuyi su goma sha biyu suna tulawa.
Bud'a baki Malam Habu yai zaiyi magana amma Ilyah ya katseshi cikin tsawa yace "ka 'bace min da gani nace shashasha wato talauci yasa ka zama dabba ko sai aita maimaita maka magana baka fahimta ba"?.
Ran malam Habu a mugun 'bace ya juya da sauri cikin fushi yabar kofar gidan idonsa a rufe sun cika da hawaye da'kyar yake ganin hanya bai koma gida ba haka ya sake shan kwana ya tafi d'ayar anguwar dake kusa dasu da akwai wani mutum shima d'an kasuwa ne sosai yake harka saidai yaje a akasi daya tura yaro cikin gidan sai akace baya nan ya tafi ziyara d'azu garin danginsa kuma bayau zai dawo ba iya tashin hankali malam Habu ya shiga haka yayita yawo a layuka kamar mara hankali babu takalmi karshe ya dawo gida jami'an suna nan a inda ya barsu a yadda suka ganshi ya dawo sun san kila bai samu mai sayan gidan ba dan haka suka yita da wajewa zasu kar'bi gidan a madadin kud'in su sun saya dubu d'ari biyu da hamsin a take suka bashi dubu hamsin d'in kan sannan sukace masa nan da sati ya zauna cikin shiri zasu zo su rushe gidan su mayar dashi gidan gona su zuba kajin turai🐤 a ciki duk abinda yasan nasa ne a gidan ya d'ebe kafin su dawo domin da mota zasu zo su ni'ke gidan ya d'ebe 'kasar sa ya basu filinsu😭🙊 dole haka ya amince babu yadda ya iya yana ji yana gani yanzu baida komai.
Bayan tafiyarsu haka zazza'bi mai zafi ya rufe malam Habu a ranar babu wanda ya iya had'iyar koda ruwa ne a gidan haka suka wuni suka kwana cikin fargaba da nadama Rakiya matar Malam Sabi'u yayan Malam Habu haka da labari yaje mata tazo gidan tana kuka sosai tace wallahi bata sani ba bata nan tayi tafiya da ko tumuninta na gado saita siyar ta biyawa Malam Habu kud'in nan amma yanxu ma nan da satin idan suka dawo Asma'u taje ta fad'a Mata zatazo idan sun yarda su kar'bi gonarta su barwa Malam Habu gidansa😞😥.