← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 145

Sashe 58

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shekara d'aya tsakani da mutuwar Yusairat Asad yaje gida a lokacin khimiyyah tayi nisa sosai ta samu yanki babba cikin wannan mummunar 'kungiyar kwatsam ta fahimci asirin su yana gaf da tonuwa a daren ta cikin mirron tsafi ta kira Hudayyah ta sanar da ita abinda yake faruwa ita kuma a take tace tazo su had'u a samo mafita taje suka had'a meeting da shugabannin cewa su bazasu shigo masarautar ba akwai tsaro za'a iya samun matsala amma ita tunda anan take itace zatai musu aikin lallai ta dakatar dashi kar asirin su ya tonu tunda ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye tayi la"be tayi le'ke a ranar Asad yayi waya da Isham cewa gobe zai taso sannan ya kusa gano abinda yake nema da shirinsa cikin kayan sojoji hula ce kad'ai da takalmansu bai saba kwana yai curr yana aiki sai asuba ya fita sallah masallaci tayi amfani da wannan damar ta shiga masa d'akin sirrin sa tayi masa 'barna dalilin samunta dayai a d'akin shine hujjar dayai mata dukan hallaka sannan ya shirya batare da sanin kowa ba yabar masarautar a ranar ya koma Marshall islands.

💋MRS AL-AMEEN AHMAD CE😘.

See you next time, tanks for ur support I really appreciate it 🌹💓💯 nagode 'kwarai da gaske masoya ha'ki'ka kuna raina har bansan yadda zan kwatanta a gane ba baki bazai iya fad'a ba kalmomi bazasu tsaru ba kawai abinda zan iya cewa saidai nace ina son ku da dukkan zuciya ta 💋🤟💔💗.

YÚSRÃH MÛSÃ ÀBÚBÅKÂR
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

5608ÑG📲 F4D, J7Ñ/ÀÑ/BÖBD 67ẞ4ÀH M7ẞÀ ÀB7BÃKĀ4💻🎤 ku fito nazo💋💋💋💋💋💋💋💋💋🤗.

💎 MÉ KÃMÃR SÁRKÏ 💎

WhatsApp no:234 905 527 3614
🤙✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR 🌹.
Ba maraya😣___sai rago😪
Ba nakasashe🤨___sai kasashshe😞
Ba mai raina kad'an🙄___sai 'barawo
Ba makaho🚶____sai ma'ki gaskiya🤥
Ba munafiki😳____sai wanda ya'ki gaskiya, idan kaga abinda ba daidai ana aikatawa please yan uwa mu gyara shi👍 whoever sees a wrong thing should correct it🙏.NONE OF YOU WILL HAVE FAITH UNTIL HE WISHES FOR HIS BROTHER WHAT HE LIKE FOR HIM SELF. Removing harmful object from the road is charity.

ÀÑÑÙRÌ WRÌTÉR'S ÃSSÕÇÌÅTÍÔÑ💫
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_________________
______________________________
__________________

💫A*W*A💫
MRS ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD ÇË😘
_________________________

Mai tambarin yma dutse Jigawa state new world 🌹 new life and new style sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa.

🕌🕋🕌
May Allah bless u may Allah protect you and your household frm all calamities 🤲👏🙏.
HÃPPY JÚMÃ'ÂT MÜBÅRÄK
🍇🍉🍎🥥🍓🍌🍊🍒🍍🥝🥕🍏.

🎈Y🎉U🎈S🎉R🎈A🎉H🎈🎉🎈🎉
✨🎀M✨🎀U✨🎀S✨🎀A
🎊A🎁B🎊U🎁B🎊A🎁
🎆K🎑A🎇R🎑
🎄Y🎋M🎄
🎈A🎉
🎈

LITTLE ZARAN AUNTY 💃💃
💮🌸🌼🏵️💮🌸🌼🏵️💮🌸🌼🏵️

41~AL-JALIL
The majestic
42~AL-KARIM
The bountiful

20~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Akilinah.

🌄AVENGE ND REASSURE🌄
Episode 41&42
Asabe bata gida kwananta biyar kuma koda wasa bata fad'awa Balarabe inda taje ba amma sakamakon ta gama dashi ta shanye shi yasa baya da kata'bus bazai iya cewa ina taje ba, tana can ta sake sabo shiri ta d'ingumo masa wani asirin na cin mutumci gabadaya a duniya ya rasa dawa yake son kasancewa sai 'yarsa Indo kullum yana ha'kon ta yana neman d'an dalilin da zai fitar da Dalah anguwa ya samu abinda yake so Asabe bata auri Balarabe dan ta samu wani abu daga bangaren dukiya ba kawai wannan d'auke mata kan da yayi lokacin da taiwa Indo kyautar 'kosai da sanda ta shigo gidansa ya wulakanta ta wannan hujjar yasa ta aure shi da niyyar tarwatsa masa iyalinsa da hana shi farin ciki daga burinta ya gama cika koya saketa ko karya saketa zata tattare kayanta ta 'kara gaba ta koma Lagos tare da 'yarta Bahijjah.

Kamar yadda Balarabe yai fata hakan ne ya faru Asabe bata dawo ba Dalah ta tafi gidansu yana shigowa tana zaune tana wanke-wanke d'an gyara murya yai a firgice ta waigo domin yanzu masifar tsoron sa take ji murya na rawa tace.

"sannu baba" ta karasa maganar a d'ari-d'ari a mamakin sai taga ba kamar kullum ba ya saki fuska harda murmushi yace "yauwa me kike anan"? 'kara d'agowa tai tana kallon sa jin me yake cewa anya babanta ne mutumin da baya kulata ya tsaneta rabon da tai masa magana ya amsa mata a sake harta manta jin ya sake cewa "Indo ba dake nake ba nace meye kikeyi anan"?.

A zabure tace "ina wanke kwanuka ne" kallon kofar d'akin Dalah yai ganin ba takalminta yace "ina Dalah"? Cikin sanyi Indo tace "taje gidan babah Aliyah tace zata biyo ta gida su gaisa da Innah" kai ya jinjina "to to shikenan zonan yanzu" yana fad'in haka wuff ya fad'a d'aki mi'kewa Indo tai jikinta na rawa ta bishi d'aki tana shiga ya banko kofa🙊.

Shigowar Dalah ganin ba Indo a gurin wanke wanken kuma ga takalmanta dana Balarabe a kofar d'akinsa yasa da sauri taje tura kofar tayi sa'a baisa sakata ba abinda ta gani ne yasa hankalin ta yai mugun tashi zuciyarta na bugawa ta rafka wani uban salati dafe 'kirji tace "na shiga uku na lalace malam mezan gani haka? Wacce irin ba'kar rana ce wannan"? Jin maganar Dalah yasa a firgice Balarabe ya saki Indo dake kuka tana ta kokawar 'kwacewa daga jikinsa jin ya saketa da sauri ta mi'ke da gudu ta fita daga d'akin tana kuka dan ma Allah ya rufa asiri babu abinda yai mata binta Dalah itama tayi da sauri dan batasan inda zata nufa ba shima Balaraben biyo bayansu yayi sai muzurai yake cikin takaici Dalah tace "Malam wacce masifa ce ta sameka ace 'yar daka haifa kake kokarin lalata da ita meya sameka haka ya akai ka canza rayuwa"? Daidai Asabe zata shigo taji abinda Dalah ke cewa dan haka a hankali cikin sand'a ta koma da baya ta la'be tana murmushi wato ha'konta ya cimma ruwa.

Tsawa Balarabe ya daka mata cikin borin kunya yace "ke dalla gafara matsa min anan danai me mekike nufi dan kawai nace ta shiga d'akina tamin shara shine ke kuma saboda gidahuma ce har kika fassara hakan da wata tsiyar" kai jimin mutum kallon sa Dalah tai hawaye na taruwa mata a ido ta ce " yanzu tsakanin ka da Allah Malam ko kunya bakaji ba kake kokarin lalata mata rayuwa gaskiya nagaji bazan iya ba wallahi kawai ka canza hali" a masife yace "bazan canza d'in ba da nace bazan canza d'in ba kinga Dalah ki kiyaye zanci mutunci fa mekike nufi da zan lalata mata rayuwa iye? Saboda ga 'kwarto jikan 'kwarata ko? To nayi maza kisa lasafika garin nan da kewayensa kowa ya sani na nemi Indo wallahi duk ranar da tsautsayi yasa kika tona min asiri naji wannan labarin ya fita waje sai kinga yadda zanyi dake shashashar banza mahaukaciyar wofi" yana kaiwa nan yayi waje yana surutai iri iri na borin kunya da gudu Asabe ta fice a gidan dan karya ganta sauri take kamar zata tashi sama daidai anyi kiran sallar magriba suka had'u da 'kawarta Markah da sauri ta tareta.

"Ke Markah ina zuwa haka? gurin ki fa na taho".

"Tofa 'kawar arziki ince dai lafiya ko asirin ne ya karye muku fito rana bankad'a ta same mu"?.

Kai Asabe ta girgiza "ke a'a waya fad'a miki ai kinsan nace miki na tafi gurin boka ko? To zuwa nai aka sake bani sabon sihiri nasa boka ya cusawa Balarabe son kasancewa da Indo aiko sai gashi d'azu gida ba kowa sai ita kad'ai Dalah bata nan ya lallameta yasata a d'akinsa humm naso yayi 'barna ya aikata abun kunyar dazai bar abin fad'a har jikokinsa amma shegiyar Dalah ta dawo ta katse min hanzari yauwa kuma sannan ya gargad'eta kada ta kuskura wannan labarin wani ya sani basu san ina ra'be ina jiba shiyasa na garzayo na fad'a miki dan kema in kinyi gaba ki yad'a so nake zancen ya bazu ko'ina".

Dariya Markah tai "kai amma wallahi 'kawata baki da mutunci kin iya tsiya ya kamata ki barshi haka ai kin rama yanzu saiki 'kyale shi ki fita rayuwar sa ki barshi ya huta".

"Ta'be baki Asabe tai "humm naki wasa ne tabd'ijan waya fad'a miki na gama ramawa ina dai kan hanya har yanzu nasan komai ya lafa bari na koma gidan naje nayi 'kirmishishi kamar bansan komai ba sai anjima kawata" "to shikenan 'kawar dama gulma ce ta kawo ki kuma kin fad'a min hankalinki ya kwanta nima bari na koma gidana, toni dama ina zanje ne mema na fito yi a waje? Dan tsaki taja tuna had'uwar da sukai da Asaben yasa ta manta kawai ta juya gida, duk abinda suke tattaunawa Malam Habu yana zaune 'kar'kashin wata bishiya yana jinsu ya danji mamakin Balarabe daya nemi 'yarsa Indo subahanallahi kai jama'a Allah ya kiyaye 'bacin rana.
Chapter 58 · 0% Book details