← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 145

Sashe 128

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'auke kai yayi daga saitin ta yana kallon Amatu wacce tai kamar bata gurin kai ya jinjina kamar zaiyi murmushi sai kuma ya ta'be baki tare da ajewa Clarah kofin da yake shan coffee d'in wanda a d'ari Amatu ta d'ago kai tana kallon sa zuciyarta na harbawa cikin fargaba da tashin hankali wanda batasan dalilinta nayin hakan ba kuma bata da amsa jikinta na rawa batasan ta saki coffee d'in hannunta ba saboda sanyin da jikinta yai.

Cire lips Clarah tai tana juyar da kanta gefe ta saki murmushin mugunta ganin tarkonta ya kama ji take kamar ta tashi ta taka rawa tsabar murna da farin ciki har annurin fuskarta ya kasa boyuwa cikin zafin nama Asad ya ri'ke kofin da Amatu ta sake ya had'a da hannunta yana kallon fuskarta da cikin idanunta ita kuma sam ta'ki d'agowa ta yarda su kalli juna kallon Clarah yai yaga fara'a fal fuskarta tana kad'a kai tace.

"kasha coffee dinka da alama malama Amatu ta 'koshi tunda har jiki yayi sanyi tana shirin zubarwa".

Jin abinda Claran tace yasa shi sake kallonta sosai oh wato saboda Amatu ne tai haka dama? nan take ya harbo jirgin domin ya fahimci tayi haka da niyya so take ta hada shi da Amatun tayi zargin wani abu ko da ala'ka mai 'karfi tsakanin su na cewa itan wife to be d'insa ce zai aureta idan yayi retire kai ya jinjina yana kallon Clarah da take ta masa murmushi tana far da ido coffeen na cikin hannun Amatu shi kuma yana ri'ke da hannun nata yace.

"Bani wannan coffee d'in da alama zaifi dad'i saboda ya riga ya huce" yana kaiwa nan ya kar'ba yana sha shiru Amatu tai batace komai ba cikin hade rai ya juya dashi zuwa saitin bakinta dan karma taga kofar yi masa gardama mamaki ne ya kama Amatu har batasan sanda tayi tagumi ta zuba masa ido ba cike da burgewa ya d'age mata gira alamar da magana ne? Humm Amatu batasan lokacin da ta saki murmushi ba tana d'an rufe fuska cikin kunya hannu yasa yana janye nata hannun kafin yace.

"Me kike rufewa fuska ko har kinji d'umi daga sanyin da jikin ki yayi"?.

Kai ta girgiza kamar zatai dariya tace "babu komai".

"Oh da gaske kin tabbata da abinda kika fad'a"?.

Kaita sake d'aga masa "ok kinyi fushi ne"?.

Zaro ido tai "ni kuma fushi a'a wallahi".

"kina so na yarda"?.

Nan ma kaita d'aga coffee d'in ya bata "sha wannan" sauke ajiyar zuciya tai tana sa hannu zata kar'ba ya mata nuni da ta bud'e bakinta ya bata bin umarninsa tayi cike da jin dad'in bai tozarta taba kamar yadda Clarah taso ta gefen ido Amatu ke kallon Clarah datai suman zaune ta kasa 'kwakkwaran motsi kaita jinjina tana fuskewa yaci gaba da bata coffeen saida suka gama zasu tafi ya kalli inda Clarah take zaune tayi fam fuskarta a had'e ya mata nuni cewa ita suke jira.

Idonta fal da hawaye tace "Asad na kasa gane maka wai me kake haka wace wannan yarinyar daga ina kazo da ita maye ala'kar dake tsakanin ku da har take kwana a gidanka wanda nima shaida ce baka barin mace taje maka ko bakin gate balle ta samu damar shiga maka cikin gida Asad shekara ta nawa dakai ban ta'ba shiga maka gidanka ba amma ita fa wannan meye hadinku wace ita mahaifanka sun san da zaman ta kuwa a'a? ada bana jin ko d'ar a kanka amma Asad yanzu kasa min shakku a cikin raina ka fad'a min gaskiyar ala'kar data had'aku ta yadda zan fahimce ka daga gidanku ka taho da ita ko mahaifanka basu san da ita ba"?.

Tab da wani irin mugun 'karfi Asad ya juyo wanda a zabure Clarah taja da baya tana huci cikin tsawa da bacin rai yace "what do you mean? Are u out of ur sense? Me kike nufi da cewa iyayena sun sani ko basu sani ba kallon fasi'ki kike min wanda ya kawo mace gida ya aje saboda more rayuwa dama shedar da zaki min kenan akan wani banzan kishi da bazai amfane ki da komai ba Clarah kinsan meyasa bazan hukuntaki akan wannan maganar da kika fad'a min ba? Saboda banyi niyya ba amma wallahi yau da sai kin yabawa aya za'kin ta sai kinyi dana sani kinsan waye ni I think 🤔basai na miki tuni ba ki farka ki tuno idan kin shiga cikin duhun baccin mantuwa ne kafin na farkar dake da azabata".

Kuka Clarah keyi sosai tana kallon sa hannunta dake faman rawar tsoro tasa ta share hawaye jin yana neman yanke ala'kar dake tsakanin su tace "kayi hakuri abinda nace maka idan ya 'bata maka rai ba zarginka nake ba Asad na yarda dakai fiye da yadda kake zato amma dan Allah ka fahimce ni ka saurare ni ka sauka daga dokin Zuciyar da ka hau ina son sani please 👏"...

Runtse ido yai cikin son baiwa zuciyarsa hakurin ta tsaya ta saurareta da sassauta fushin sa yace "me kike son sani"? Numfashinta na sar'kewa cike da kishi da 'kunan rai Clarah ke kallon Amatu muryarta na rawa tace "Asad dan girman Allah ka fad'a min gaskiya wace wannan yarinyar a gurinka maye hadinka da ita dan Allah ka fad'a min mene matsayinta cousin ko blood sister d'inka ce uwa daya uba d'aya nikam hakuri na ya 'kare nagaji wallahi bazan iyaba zuciya ta bazata iya d'aukar wadannan matsalolin ba please Asad na had'a ka da girman Allah dan son da kake wa ma'aiki ka fad'a min miye matsayin ta a gurinka"?.

Shiru yai yana tunani duk da ta sakashi a tarko ta had'ashi da girman Allah yana musulmi idan yace mata cousin d'insa ce yayi qarya idan yace mata sister d'insa nan ma ba gaskiya bane dan haka babu yadda ya iya dole ya fad'i asalin abinda baya ta'ba so ya furta kalmar yanzu saidai ya kama dole ya fad'a...........

Clarah tana shashshe'kar kuka tace "Ina sauraron ka Asad dan Allah ka sanar dani matsayin ta a gurin ka duk duniya yanzu wannan ne damuwa ta".

Batare daya kalleta ba kai tsaye yace "she's my wife🙊 ita d'in mata tace za'bin d'an uwana Ajeeb ce kuma ina girmama hakan".

Zaro ido waje Clarah tai a wannan lokacin ta kasa ri'ke hawayen ta da'kyar tace.

"wannan d'in matar kace"?.

"Eh ba tambaya kike wacece itaba mene matsayinta a gurina mene baki gane ba I will try to do my best na ganin cewa ki fahimce ni domin bana son a gaba ki sake yimin magana a kanta"?.

Shiru Clarah tai tare da zubawa Amatu ido cike da jin tsanarta da wani ba'kin kishi daya turnu'ke ta da bakin ciki idonta yana tsiyayar da baka'ken hawaye ta kuma maimaita kalmar.

"Asad really she's your wife? Is this some kind of joke dan kaga yadda zanyi ne a kanka kamin haka"?.

Asad baiyi niyyar kallonta ba saida yaji abinda tace ya d'ago kyawawan idonsa yana kallon ta fuska babu wasa dan karma taga kamar yana mata yawo da hankali ne yace "who is joking with u? Dama tunda muke dake na ta'ba fad'a miki wani abu na wasa nayi miki kama da mai wasa" shiru tai ba'kin ciki damuwa da takaici sun cika mata ciki "ki amsa min tambaya ta na ta'ba yin wani abu dake na wasa dan yawo da hankali"? Kamar da har lokacin ta kasa magana balle ta amsa masa tambayarsa tsaki yai domin ta fara fusata shi in yaci gaba da tsaiwa zai iya sharara mata mari sai kawai ya ja hannun Amatu yana bari wurin d'ora hannu Clarah tai aka tana fashewa da wani wahalallan kuka tare ta zama ta kifa kanta akan table din cikin rashin sanin madafa ko abinyi kuka take sosai tana dafe da zuciyarta dake mata rad'ad'i da zafi.

Koda suka koma gida Amatu zama tai shiru a parlor cikin damuwa tunani ya cika ranta duk da tasan qureshi Clarah tai harya furta kalmar ita matarsa amma a zahiri ba haka bane saidai dole tana son suyi magana akan Claran koba yau bane domin dama ba wani shiri suke ba gashi yau tasa an tono abinda ke rufe.

Amatu tayi matukar damuwa ba kamar Asad ba da yake komai hankalin sa kwance kamar komai bai faru ba sai magriba yayi alwala zai fita Amatu dake zaune har lokacin a parlor yazo zai fita ta sauke numfashi saboda abinda zata tambaye shi dan batasan amsar dazai bata ba tace.

"Nifa a ganina kamar Clarah tana kishi dani ne saboda tana sonka bayan batasan ba haka abin yake ba ni kawai aikina ne ya kawo ni amma yanzu kome zance mata bazata ganeba data tsaya ta fahimta ta daina wahalar da kanta a kaina saidai bazata gane ba sonka ya rufe mata ido"?.

Asad baiyi niyyar ya tsaya ko yin magana ba amma jin abinda tace yasa dole ya tsaya ya fahimtar da ita domin shifa dama Clarah bata gabansa ta karasa fice masa aka kuma zai sameta ya gargad'eta kada ta sake masa maganar aure tsakanin su ya fasa bazai iya zama da mace irinta ba gara ya qare rayuwasa haka da zama da Clarah mayar da hankalin sa kan Amatu yai yana cewa.

"Shikenan dan kawai tana sona nima saina sota? Bafa rayuwa ake kawai ba babu mace a raina har gobe".

Numfashi mai nauyi Amatu ta sauke tana cewa "Amma tana tsananin sonka fa kuma alama ya nuna tana so kuyi rayuwar aure da ita meyasa zaka ce haka"?.
Chapter 128 · 0% Book details