Sashe 16
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da gudu Bahijjah ta fito daga d'aki tana cewa "ai wallahi Dalah baki isa ba kika kashe min uwa kema saina kashe ki dallacan sake mata wuya" ta karasa maganar tana jan hannun Dalah wanda Dalah cikin kunar rai tasa d'ayan hannunta ta saukewa Bahijjah mari kara Bahijjah ta saki a gigice tai baya tana kuka kokawar kwacewa Asabe ta soma tana cewa "kinsan Allah Dalah kin shiga uku kin gama yawo kwanan ki ya 'kare kuma zaki gani" "naga alkairi baki isa kimin abinda Allah baiyi min ba" Dalah ta fad'a tana wujijjiga Asabe ta dokata da kasa tabi ta turmushe ta jin da Asabe tai Dalah na neman illata ta yasa ta soma kurma ihu tana kiran ma'kota suzo su ceceta kowa naji yai burus domin dama haushinta suke ji akan gallazawar da takewa Indo yau kuma take neman agaji wanda yazo ceton ta ma ya cika 'kasurgumin munafiki haka Dalah ta luguiguita Asabe Saida ta mata dukan data tabbata ya gama ratsa jikin ta sannan ta 'kyale tana rike hannun Indo suka bar taje ta bata wani abincin kafin ta fito ta d'ora mata ruwan zafin da zata dumama jikinta Asabe kam na kwance sai zafga ihu take ba ma'kwafcin daya leko balle ya tambayi me ake.
Da dare bayan sallar Isha Binta ta shigo d'akin su Amatu ganinta zaune sauran suna kwance yasa tace "mamar gida baki bacci ba zaman me kike"? Sauke ajiyar zuciya Amatu tai tana kallon Binta tace.
"Umma na gaza yin bacci ne ina ta tunani akan goben mu" kallon mamaki Binta tai mata jin abinda tace yasa ta ce "kamar ya"? Cizon yatsa Amatu tai cikin damuwa tace "umma na sani cewa muna cikin wahala da 'kuncin rayuwa kuma kowa ya sani musamman baba Ilyah yana da wadata amma ya taimaki babanmu ya'ki ga 'yan uwa na kowa ta damu taga tayi aure amma babu saurayin dake zuwa kofar gidan nan taulauci kamar a kan mu aka fara kullum wannan abun yakan hana ni bacci duk wanda ya d'ebo cin mutuncin sa sai yazo ya sauke mana kamar mune muka dorawa kanmu talaucin kinga jiya da bakya nan kinje anguwa Kande matar me gari har tsakar gidan nan tazo bakiji irin cin mutuncin da taiwa umma Saude ba akan Buba yazo hira gurin Asma'u harda gori iri iri kwata kwata jiya raina a 'bace na wuni".
Kallon ta sosai Binta keyi gaskiya akwai matsala a gidan nan wacce dole sai sun tashi tsaye sun had'a 'karfi da 'karfe sun magance ta sake kallon Amatu tai a karo na biyu tace.
"Amatullahi kiyi hakuri ki daina saka damuwa a ranki kada kina yarinya hawan jini ya kama ki insha Allahu komai zai daidaita kinji" kai Amatu ta d'aga batare datai magana ba Binta taci gaba "Amatu dama akwai abinda nake son fad'a miki gobe idan Allah ya tashe mu da rai ki shirya zamuje gurin 'kani na Bashari".
Zaro ido Amatu tai da mamaki tace "wai baba Bashir? kenan gobe zanga su Nabilah da Maryam kai amma naji dad'i umma Allah ya kaimu tun asuba zan fara shiri" murmushi Binta tai ganin ta kawar mata da wancan damuwar dake damunta tasan yau zata samu bacci cikin kwanciyar hankali mi'kewa tai tana cewa "eh ki shirya insha Allahu da wuri zamu tafi" "to umma saida safe" mi'kewa Binta tai ta fita yayin da Amatu ta cika da murna sosai domin ta dade bataje ba ganin bacci ya'ki daukarta yasa ta mike tayi alwala ta fuskanci gabas ta fara nafila tana jerowa mahaifin ta addu'o'i na samun wadatuwa da arziki mai dorewa".
Washe gari da wuri kamar yadda Binta tace mata suka shirya itakam Amatu tun asuba ma tai wanka suna karyawa ta shiga d'akin malam Habu yana kwance ya d'aga kansa sama ga kwanon d'umamensa da aka kawo masa bai tashi yaci ba durkusawa Amatu tai tana cewa "baba ina kwana"? Tashi zaune malam Habu yai yana murmushi yace "lafiya na tashin mamana har kun gama shiri kenan yau sai kwanan birni"? 'Dan sauke kai Amatu tai tana cewa "baba dan Allah na roke ka kadaina sa damuwa a ranka in Allah yaso wata rana sai labari komai yai farko zaiyi karshe duk nisan dare gari zai waye inda jirgin sama yaje kunkuru ma za'a ce masa barka da zuwa na sani kana cikin damuwa sosai baba amma ka roki Allah shine mai badawa idan kuma ya baka babu wanda zai hana ka" ta karasa maganar da shar'bar hawaye.
Har lokacin murmushi malam Habu keyi yana mai matukar farin ciki da godiya ga Allah da samun Amatu dayai matsayin 'ya a gareshi duk sanda ya shiga kunci ko damu ita ke fada masa kyawawan kalamai tayi amfani da sansanyan lafazi koda yaji bazai iya jurewa data fad'a masa zai ji ransa yayi sanyi kallon ta yana cewa "mamana kada ki damu share hawayen ki Allah ya miki albarka ya tsare min ke a duk inda kika tsinci kanki ya baki miji na gari wanda zai rike min ke da mutunci ya kyautata ki ya faranta miki kamar yadda kike faranta min" Amatu na shashshekar kuka tace "amin baba na gode da adduar ka gareni" "kada ki damu mamana Allah ya kiyaye hanya saikun dawo" mikewa tai ta fita yayin da malam Habu ya bita da kallo ji yake kamar da ransa zata tafi baya so tai nisa dashi ko kadan saidai ya danne bai nuna ba domin matukar Amatu ta sani baza taje ko'ina ba bude murfin kwanon yai ya soma cin tuwon a bisa jin yunwa badan yana so ba dawa tazo gida baida kudin dazai saya yaje wajen mutane da dama ya roke su ya basu gero su bashi dawa sun'ki.
Amatu na fitowa taga su Aisha sun dauki kaya zasuyi musu rakiya Binta kuma ta shiga d'akin malam Habu sallama taiwa su Saude kafin tai jin Bintan ta fito suka tafi saida suka hau mashin sannan su Aisha suka juya gida cikin rashin jin dad'in tafiyar Amatun.
'karfe daya na rana suka sauka a Dutse round na farko tare da 'yar jakar kayansu anan suka sake tarar d'an mashin sukai masa kwatancin anguwar da zai kaisu.
Bashir 'kanin Binta ne uwa daya uba daya shima dan asalin 'kauyen ne karatu ne ya fara kawo shi cikin dutse bayan ya kammala ya fita da kyakkyawan result wanda yai sa'ar wani mutum da suke hayar gida a gurin sa ya musu hanya su biyar aka dauke su aiki nan da nan ya samu abun hannu har yana iya taimakawa yan uwansa daga karshe ya sayi fili yai katon gida ya auri wata mace mai suna Safiyyah yar babban mutum ce kuma Allah ya azurta su da yara uku Ahmad shine babba sai Maryam da Nabilah suna zaune a mopal Base (mofalbes).
Mashin na sauke su Binta daidai an bud'e kofar gate din gidan mota ta fito biyan d'an mashin kudinsa tai Amatu ta dau jakar suka karasa sauke glass din motar akai matar Bashir ce da alama gurin aiki zataje fuskarta da mamaki ta dan zaro ido tana cewa "wata sabon gani anya ba 'batan kai kuka yi ba wa naka gani kamar aunty na ta kaina"?.
Murmushi Binta tai domin inda sabo ta saba da tsokanar Safiyyah indai tazo cikin wasa Binta tace "eh 'batan kai mukai shine muke tambayar gidan wani Bashir ko kin sanshi"? Dariya suka sa gabadaya banda Amatu dake murmushin jin dad'in ganin yadda safiyyah tai ba nuna wulakancin yan kauye sun zo.
Mayar motar da baya Safiyyah tai tana cewa "mai gadi amso kayan su ka kawo parlor" da gudu mai gadi yace "to hajiya" kallon su tai fuskarta fal da fara'a tace "mu karasa ciki" katseta Binta tai "ba wani gurin zakije ba kada ki makara mu yan gida ne har zaki dawo" kai Safiyyah ta girgiza "eh office zanje amma babu damuwa zan kira na sanar dasu yau bazan samu bulla ba ku shigo ina zanyi wannan manyan ba'kin na tafi wani gun ah ku shigo muje ku huta kun shawo rana" shiga katon falon gidan sukai babu kowa bayan sun zauna ta bud'e fridge tana dauko musu ruwa mai sanyi da drinks ta aje musu tana cewa" sannun ku da zuwa ya hanya da gajiya"? "Lafiya kalau ya muka sameku ina yaran ne banga ko daya ba"? "Sunje makaranta Najeeb kuma yana hospital wajen practical, bari nasa a kawo muku abinci" ta fad'a tana mikewa ta shiga wata kofa.
Sauke ajiyar zuciya Amatu tai tare dayin tsam tai shiru bata sha ko ruwa ba kallonta Binta tai tana cewa "Amatullahi meke damunki"? D'agowa Amatu tai idonta fal da hawaye tace "umma na tuna baba ne yanzu ko a wanne hali yake ya samu abinci yaci ko baici ba" kai Binta ta girgiza cikin kwantar mata da hankali tace "ki daina kuka yana halin lafiya cikin 'koshi domin dazu da zamu taho bayan na shiga d'akin na bashi dubu biyar nace ko d'an wani abu ya saya dan haka ki daina sa damuwa a ranki" sansanyan numfashi Amatu ta sauke kafin fuskarta da annuri ta dau ruwa tasha wanda Binta taji dad'in ganin sakin ran da Amatu tai.
Empire masarauta
Tun asuba su Ameer suka koma hospital domin sake jin me doctors zasu ce akan case din Khimiyyah a wanne hali take kuma jiya iyau babu wani labari mai dad'i.
Mami ta samu zazzabin ya sauka taji sauki saidai tayi kiran Asad bai d'aga ba tayi tunanin ko yayi fushi ne a zahirin gaskiya kuwa baya kusa da wayarsa mi'kewa tai tana fita ta shiga gurin me martaba tayi tare da neman izini ta zauna cikin nuna alamar damuwa tace.
"Ranka ya dade kayi hakuri abinda ya faru na sani babyn Mami yayi kuskure ina nema masa afuwarka".
Shiru taga mai martaba yayi bai d'ago ba bai kuma ce komai ba tasan lallai Asad ya fusata shi sosai kuma batasan da yadda zata bashi hakuri ba ko ta taushi Zuciyar sa a wannan lokacin, sake kallon sa tayi yana kallon kasa sauke numfashi tai tana nazarin sa cikin zurfafa tunani tace.
"Allah ya baka nasara magana nake".