← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 145

Sashe 129

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amatu ta karasa maganar cikin d'ar da tunanin irin amsar dazai bata jitai yace "dan kawai tana tsananin sona sai ya zama dole na aureta bazan iya zama da Clarah matsayin mata taba bana hango nasara a tare dani matukar naci gaba da ala'ka da ita kodacan na fad'a mata bazan aureta ba amma gani take kamar wasa nake mata a zahirin gaskiya Clarah bata cikin irin matan da nake so na aura nayi rayuwa dasu amma badon haka ba da yanzu muna da yara kusan uku ko hud'u ni da ita bar batun bana son ta zuciya tama tana gargad'ina akanta kullum cewa nayi baya baya da ita karna yarda da ita d'an Adam bashi da tabbas".

Ajiyar zuciya Amatu tai tana cewa "amma ni a nawa tunanin bazata ta'ba cutar dakai ba saboda tana sonka"?.

D'AN juyo dakai Asad yai yana kallon Amatu jin abinda tace sai kuma yai murmushi yana ri'ko hannun ta ya mikar da ita tsaye kamar yadda yake yana sunkuyo da fuskarsa daidai tsayinta yace "ke yarinya ce mai hankali shiyasa tun farko naji zan iya had'a tafiya dake Clarah ta girme ki da kusan shekara bakwai amma na tabbata kin fita nutsuwa hankalin ra'kuma gareta babu sonta a zuciyata babu ita a cikin tsarin rayuwa ta bazan iya zama da ita ba".

A damuwance Amatu tace "ni bana so taga kamar nice na shiga tsakanin ku na raba ku saboda kafin zuwa na kuna tare".

"Hum akan me zata fad'i haka dan kawai tana kishi dake ne manta da ita lokacin sallah yayi kije kiyi" kaita d'aga masa bata sake magana ba ta shige bedroom shi kuma ya fita zuwa masallaci.

Clarah bata dawo gida ba sai kusan karfe sha biyu na dare tayi wa Sir David waya yasa azo a dauketa sai gashi da kansa yaje daukarta tayi mamaki mutumin da saidai a bud'e masa mota ya shika a tu'ka shi yau shine yake tu'ki da kansa saboda ita daidai ya fito daga gurin hutawar ta kalleshi da mamaki a fuskarta tace "oga David da kanka"? Murmushi ya mata tare da rage girman idonsa a kanta yace "eh kece fa ba wata ba aikinsan dole nazo da kaina kin manta ne ina sonki" d'an hade rai tai tana kauda kai gefe jin abinda yace bata sake magana ba sai shine ya cikata da surutu bayan ta shiga motar suka bar gurin sai zance yake mata ba kai ba kafofinsu ganin zai zarce da ita yasa tace.

"Sir tsaya na sauka" bai tsaya ba bai kuma kalleta ba yace "ki sauka zuwa ina" takaici ne ya kama ta ji wani rainin hankali tace "na sauka zuwa gida karka wuce dani" murmushi yai "oh madam wato har yanzu babu yarda tsakanin mu ko"? Shiru ta masa yaci gaba "a tunani na Clarah zaki iya yarda dani 'kasar mu d'aya yaren mu d'aya amma kin tattara dukkan kulawar kin d'ora akan wancan Asad din da bai damu dake ba bai damu da damuwar kiba idan ba haka ba bazai ta'ba tafiya ya barki a wancan gurin ba" da mamaki a fuskar Clarah tace "oh dama kasan tare muka fita"? Gira ya d'aga mata "yes na sani kuma ba wani ne ya fad'a minba da idona na gani har kika jefar da wayar ki ta lalace right"? Shiru ta masa cikin takaici tuna cewa jiya ta sai wayar kuma waccan wayar ma shine silar fashewarta bata ankara ba ta gansu a gidan sir David yana bud'e mata kofa yace "fito".

Had'e rai tai "na fita zuwa ina please oga David ka barni na tafi gidana"?.

Kafad'a ya d'aga "ok zaki tafi Clarah amma fa maganar gaskiya ba yauba sai gobe ki tsaya ki taya ni kwana" zaro ido tai "me na taya ka kwana kamar wata matarka ina Mom Juliana take ba tazo maka ziyara ba da yaranku biyu ma ance" murmushi ya buga mata "eh tazo satin ta biyu nace ta koma nima karshe wannan watan zanje gidan dan haka kawai ki taho muje zan baki komai kike so" kai Clarah ta girgiza tare da ja da baya zata gudu caraf ya ri'ke ta yana daukarta yasa a kafad'a domin 'katon gaske ne yai ciki da ita tana dukan sa a baya akan ya sauketa amma ko sauraron tabaiyi ba Saida ya kaita har bedroom kafin ya direta akan bed a firgice ta mi'ke zata sauka yayi kanta yana fad'awa a jikinta tare da rungumota yasa ha'kori yana yage maballin dake gaban rigarta zatai ihu ya hanata ya toshe mata baki da nasa yana tura ta tai baya binta yai ya danne yana ci gaba kissing d'in ta.

A zauce Clarah take kokawa dashi sosai amma ta kasa 'kwatar kanta saida ya gaji da bata kiss dan kansa ya 'kyale ta yana sake rungumeta sosai a jikinsa yace "sorry for what I did bana so ki ri'ka min gardama ina son ki aurenki zanyi ki gane man"?.

Banza tayi masa ba'kin ciki kamar zai kasheta ta fisge jikinta tana mi'kewa gashi ya yaga mata riga sauka tai a gadon yana kallon ta tayi hanyar fita a d'akin ta fice daga gidan gabadaya tana tafe ta kakkare rigar sakamakon ko'ina da haske wanda ya santa zai iya ganinta kuma iska ake rigar sai budewa take haka ta karasa barrack gabadaya ranta a dagule bata lura da abinda Sir David yayi mata damuwarta Asad ne ko kadan a ranar bata samu barci mai kyau har gari ya waye tana zaune tayi tagumi ko sanin inda kanta yake batai ba.

Bayan wata biyu da faruwar haka Clarah ta sauke kamar gaske ta d'auke kanta akan kishin da Amatu sai wani sabon salon shishshigi ma da take nuna Mata harda kiranta qawar take yi ta nemi suyi exchange d'in number Asad ya hana tayi tamkar bata damu ta share yanzu bata nuna fushinta kome zai faru tana had'iyewa ta barshi a ranta.

A 'yan kwanakin ne aka gano cewa an sake wasu kayan aiki na sojoji wanda ake tunanin da sa hannun wasu a ciki kuma kayan fad'a ne da makamai masu kyau da tasiri shiyasa aka ce a fita neman wad'anda suka d'iba farko Asad ba guri d'aya zasuyi da Amatu ba shida Isham da sauran soldiers zasuyi wani bangaren suma Clarah suyi wani bangaren ko za'a kama barayin kayan.

Tare suka fito waje inda jiragen ya'ki guda biyu suke fake ana jiran had'uwar masu zuwa murmushi Clarah tai tana cewa Amatu.

"Ok qawata jirgin mu d'aya muje".

Kai Amatu ta d'aga mata sun juya sun fara tafiya Asad yace "Amatullahi".

Juyowa tai tana kallon sa shi kuma Clarah yake kallo wacce ta zubo masa ido tana son jin miyasa ya dakatar dasu Amatu ya kalla yana cewa.

"Don't allow anyone to harm you".

Murmushi Amatu tana cewa "ok tanks" kai Asad ya jinjina mata bai sake kallon yanayin Clarar ba wacce takaici ya gama rufeta me yake nufi da cewa kada ta yarda kowa ya cuceta yawancin lokuta idan ba tare dashi Amatu zata fita ba tanaji yana fad'a Mata wannan kalma hummm mtswww tsaki taja tana bin bayan Amatu wanda already ta shiga jirgin helicopter ne mai tambarin army a jikinsa gabadaya.

Lokaci guda jiragen suka tashi kowanne da inda yayi daji sosai suka shiga bincike wanda suna cikin tafiya ba zato suka ji an bud'e musu wuce da sauri kowa ya kwanta da ruf da ciki suke tafiya sunayi suna d'agowa ana fafatawa har sukai nasara suka kashe wajen mutum sha biyar irin yan dabar dajin nan wanda su kuma sojojin su mutum uku arm bush (ambush) d'in ya samu harbi ya shiga jikinsu dan haka sukace tunda sun gama bincike ba wannan dajin bane su sauya wani wayar dake ma'kale jikin Amatu aka Kira d'agawa tai tana cewa.

"Hello".

Daga can bangaren Asad yace su tafi taho asalin wancan dajin inda suke maybe 6arayin makaman suna cikin tunda sunga alama .

Sanarwa da kowa Amatu tai amma Clarah saita nuna ai su bai shafesu ba sun gama nasu operation d'in miyahada su da wancan dajin wai garama tayi shiru karsu fad'awa kowa su tattara su koma Amatu taji mamaki amma ta share batacewa kowa komai ba saida aka koma ta d'auki motar da suke fita da ita wacce bullet baya ratsa ta bom baya tashi da ita ta sake sabon shiri ta Kira Asad ta tambaye shi daji da suke yace mata sun rarrabu ne amma ta aje motar a bakin shigowa dajin ta shigo da kafa.

To tace masa tana zuwa ta tsayar da motar tana fita da sauri ta kirashi a wayarsu irin ta aiki tana cewa.

"Hello ta wajen ina zan sameka"?.

Kwatance yayi mata a hankali taje har inda yake ta sameshi magana yayi mata akan ba yace sauran su taho ba tace eh ta fad'a musu sai Clarah tace babu Mai zuwa ba wannan ne dajin da aka basu ba sun gama operation d'insu shiyasa ita ta taho ita kad'ai bai sake tambayar ta wani abu ba dama yasan za'ai haka tun da dad'ewa ya fahimci Clarah b aiki ya kawota amma yana daidai da ita.

Barin gurin sukai ita dashi suka sake nutsawa cikin dajin can nesa dasu suke jiyo maganganu a hankali cikin sand'a suka karasa suji mai suke cewa aiko wadanda ake nema ne 6arayin da suka sace makaman ne suna maganar su goma sha biyu ne amma yanxun su biyar ne bakwai sune aka kashe a d'aya dajin.

Bud'e jakankunan suke suna fito da makaman su dukka masu tasiri ne kafin suka mammayar suka sake padlock suka kulle jakunan suna maganar a Kira daya a cikin bakwai din da aka kashe musu batare da sun saniba.

Kallon Amatu Asad yai yana cewa "zaki iya fita ki tunkare su"?.

Kaita d'aga cike da jarumta tace "eh".

"Ok jeki amma ki kula sosai kada ki nuna tsoro ko ki nuna kina tare da wani ki nuna musu ke kadaice zaki iya ja dasu".

To Amatu tace tana mi'kewa tsaye daga inda suke 6oye ta bayansu batare da sun sani ba sai muryarta sukaji.
Chapter 129 · 0% Book details