Sashe 40
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata karasa fad'ar abinda take son fad'a ba Ramatu ta fito daga d'aki da gudu tana zuwa inda suke cikin kalan fitina tace "me naji kina cewa kamar a taimakawa da mayunwatan iyayen ki abinci? Amma ba abincin gidan nan ba? Haram giya a gidan liman bazai yiwu ba idan Ilyasu yaci gaba da zama dake zaki talauta shi yau saidai ki kwanan gidan ku maza dauko gyalen ki ku tafi tare da shegiyar 'kanwartaki sakin uwar miji ma sakine dan haka kije na sake ki😂 yanzun nan ki kwashi kayan ki kibar gidan nan kafin na shiga d'aki na fito" komawa d'aki Ramatu tai Lawisa dake ri'ke da baki tace "tabdijan yaya Barah kedin dama irin wannan zaman 'kuncin kike a gidan amma bakije gida kin fad'a an dau mataki ba gara da akai a gabana na gani muna zuwa gida zan zayyanewa baba baza ki dawo gidan Ilyah" tari dabai kama Bara'atu ba batai ba tana tsaye a guri daya ganin ta'ki dauko gyalen su tafi yasa Lawisa shiga ta dauko mata tana cewa "yau zaki barci cikin salama muje" kai Bara'atu ta girgiza cikin damuwa tace "Lawisa ki fahimta ba Ilyah ne ya sake ni ba bashine yace na bar masa gidan saba dan haka babu inda zanje domin shine yake aurena dan shi nake zaune".
Tun kafin Lawisa tai magana Ramatu tayo waje wuf tana cewa "au bazaki tafi ba naji kince ko? Yau kuwa zan nuna miki kalar nawa tsaurin idon" tana gama fadin haka tayi wajen turmi tare da dauko ta'barya tayo gurin su tana cewa "wallahi saina 'bare miki kai da ita" da gudu Bara'atu da Lawisa sukai waje yayin da Ramatu tabi bayansu har tsakar gidansu tana rafka kiran.
"Kandiya ke kande fito yau sainaci dambun uban 'ya'yanki".
Da sauri kandiya ta fito tana cewa "subahanallahi lafiya Ramatu na ganki da ta'barya ko takalmi babu balle mayafi".
Ramatu na haki take nuna Lawisa da yatse tace "yau saina ci uban daya haife ki zakisan wace Ramatu ke kuma nace na sake ki babu ke babu d'ana har abada idan kunne yaji jiki ya tsira matsiyaciya mara zuciya ana korarki kina mannewa saboda kinga kud'i ke kuma kandiya ya rage naki kiwa yarki fad'a ta rabu min da d'a idan ba haka ba sai munyi 'batacciya daku wallahi" tana fadin haka tai waje da ta'baryar ta a hannu kamar sabuwar kamu.
Mamaki ne ya kama kandiya tana kallon Bara'atu dake kuka tace "wai meya hada kune harda biyoki da ta'barya kuma"?.
Share hawaye Bara'atu tai tana cewa "babah kinsan halin matar nan ko ba'a fad'a miki dama da ya akai auren balle nayi shekara uku ban haihu ba akan haka tana goranta min da tsine min tace Ilyah ya karo aure wai ya auri Maimunan gidan san 'kira yar gidan malam Sa'idu to yau kuma sai ya shigo da kifi nasa a abinci ta kwace kifin ita kadai hakan bai isa ta zage ni ta hana na karasa dafa abincin ta goranta min sannan tace wai kina kaimin rubutu ina dafa musu abinci dashi ana haka Lawisa taje kawai dan taji muna zance shine tace wai kin aika a kar'bo miki abinci dan haka ta gaji sakin uwar miji ma saki ne naje ta sakeni".
Dafe kirji kandiya tai "kai jama'a mun shiga uku kinji wata masifar ko? Ni dama tun farko shiyasa ban goyi bayan auren nan naki da Ilyasu ba saboda nasan halin Ramatu koba dad'e koba jima sai wani tashin hankali ya shigo dacan ma maye balle yanzu kun dawo zama gida daya ni gara da haka ta faru ma ya sake ki yafi alkairi da wannan zaman damuwar da kike da mahaifiyarsa mu ri'ke talaucin mu bazaisa ki rasa wani mijin auren ba".
Tsaki Lawisa tai tana cewa "kinsan Allah innarmu da ace nice nake auren Ilyah wallahi Ramatu bata isa min haka ba koda taga Barah ba magana ce ta dameta ba da ace nice hummm da an d'ebi yan kallo".
Harararta kandiya tai "ke da Allah rufawa mutane baki sakarya kawai idan da ked'in cema me zaki iya yi wallahi a tsiwar ki yadda Ramatu bata da mutunci da yanzu ta dad'e da karya miki 'kafa tana daidai da zamaninki".
Ta'be baki Lawisa tai tana shigewa d'aki a ranta tana jin da fa ace itace bazata dauka d'in ba kamar yadda ta fada, kallon Bara'atu kandiya tai tana cewa "kinga Barah kiyi hakuri kinji shiga d'aki Allah yasa haka ne mafificin alkairi" Amin Bara'atu tace tana bin bayan Lawisa yayin da Kandiya tai zaman dirshan cikin jimami da damuwar tsiya da suka gayyatowa kansu na auren Bara'atun da Ilyah.
Har dare Ilyah bai dawo gida ba dan haka baisan me ake ba Ramatu kuwa tabarma ta dauko tana zama a waje ta kasa ta tsare tana jiran shigowar sa amma shiru har ta fara gyangyad'i sai dare sosai haka taji tafiyarsa da sauri ta bud'e ido ganin ya nufi kofar shiga d'aki tace.
"Ilyasu me zakai anan dama jiranka nake gidan uban wa ka tafi kayi dare haka baka dawo ba"?.
'Dan juyowa yai yana kallonta zuwa wani lokaci ya shige d'akin batare daya bata amsa ba dariya tai tana sake mi'ke 'kafa tace "zanji me zaka ce na karasa sauke ma damin bala'in dana dauko".
Wuf ta ganshi a kanta kamar wanda aka jefo shi cikin alamun tambaya yace "ina Bara'atu taje"?.
Wata uwar harara Ramatu ta zafga masa tana cewa "sannu ubana to matse ni saina fad'a maka inace duka na kazo yi dan irin wannan 'kerere da kayi a kaina duka kawai nake jira".
'Kara hade rai yai jin abinda tace shifa uwarsa ce amma harga Allah ta fara isar sa lamarin ta ya gama cika masa ciki...............
"Dan ubanka me kake kallo tunanin wa kake amma dai ba wannan tsinanniyar 'kai'kasashshiyar matar taka ba?.
"Wai dan Allah baba me kike yi haka ne"? Ilyah yai maganar ransa a mugun 'bace cikin fad'a Ramatu tace "dambun ubanka nake yi haka, wato dama akan shegiya matarka bankad'add'iya zaka gaya min magana? A lallai Ilyasu wuyanka ya isa yanka".
Takaici ne ya cika Ilyah shi ya rasa gane kan Ramatu kodai ta fara samu zarewa ne bai sani ba dan yaga abun nata yana neman wuce gona da iri amma bari ya bita a sannu tsuntsu me wayo ta wuya ake kamashi zama yai yana cewa "kiyi hakuri nifa dama ba akan wani abu na tambaye kiba mubar maganar d'azu bayan na fita alhaji Munniru yai Kira na akan zai sayar da wata gonar sa kozan saya saidai kafin mu gama ciniki kawai shegen nan Habubakar yaxo ya sayeta da filin kusa da gidan Buba haka mafa kwanan baya gidan me doki wanda ya rasu 'ya'yansa da suka d'aga zasu sayar shine ya saye ga gonar wajen gabar inda yake noman shinkafa kiga girman ta duk shekara saiya d'inke kusan buhu d'ari a bai samu da yawa ba ya samu buhu saba'in ko tanin komai aka d'aga a garin nan za'a sayar shi zai saya na rasa a ina yake samun kud'in sai kace me kud'in ganye ko matsafi kuma fa akwai haihuwa a gabansa amma tsabar had'ama alhaji Munniru ya kara masa kud'i shima da yake mitsiyaci ne ya sayar masa".
Zaro ido Ramatu tai tana cewa "kace da haihuwa a gabansa waye me ciki Saude ko Binta"?.
"Eh Binta ce harya tsufa kuma kwanan nan zai sake auren A'in gidan su me guga har ankai ro'kon arziki".
Dafe 'kirji Ramatu tai "au kuma shine tsabar hassada Salamatu bata zo ta gayyace niba aiko wallahi zan rama har ayi bikinka da Maimuna bazasu sani ba mitsiyatan mutane kawai duk sun asirceka ka'ki abun arziki amma na samo hanyar tarwatsa su kada ka damu Ilyah Bara'atu tayi gida nice na saketa domin bata haihuwa gara ka kara aure".
Kai ya d'aga cikin so kwantar mata da hankali yace "shikenan zan kara amma dan Allah ki bari na dawo da ita nifa ina son mata ta".
Shiru Ramatu tai tana kallon sa kamar me tunani zuwa wani lokaci tace "to shikenan ka dawo da ita amma ba yauba ba gobeba ba jibi ba sai an gama komai na maganar aurenka da Maimuna an tsayar da rana tukuna idan ma zan yarda ka dawo da itan kenan".
"A'a zaki yarda man na fad'a miki nifa ina son mata ta" hararar sa tai "sannu d'an masoya na gama magana matukar kana son sake bud'e ido kaga barakatu ko Bara'atu sunan nata? Indai kana son sake ganin ta matsayin matarka tofa saika kara aure".
Mi'kewa yai yana cewa "to shikenan zan 'kara saida safe" Ramatu data bishi da kallo tace "kowa ya kwana lafiya shi yaso😁" a'a kai jama'a wannan wacce irin uwace shidai tari da bai kama shiba bai sake yi ya shige d'aki.
Zunbur Ramatu ta mike tare da dauko maganin data kar'bo d'azu ta dauki bokiti da ruwa da sand'a tai waje tana yin hanyar daji ga ihun karnuka ya cika gari domin dare ya yi sosai yadda aka bata umarni haka ta aikata haka ta fara zuba magani cikin ruwan bokitin tayi wanka dashi kafin ta dauki gatarin da aka bata ta soma sara tana kiran Salamatu bayan ta tona tasa maganin ta rufe sannan ta dawo gida a bayan d'akinta nan ma tayi kamar yadda tai a dajin sai waige waige take kada Ilyah ya fito ta shiga uku tana gama tai wuf a guje ta fad'a d'aki tana gumi tare dayin dariya tace "haba malam sai yanzu naji daidai hankali na ya kwanta da wani ya kamani bansan me zai faru ba bari na kwanta mu jira wayewar gari muji me zai samu Salamatu"☹️😧 ta karasa maganar tana kwanciya akan katifarta da Ilyah ya sayo mata.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘
Maman little Zaran aunty sai Allah ya kaimu gobe da nisan kwana😣 da rahmarsa garemu ina yiwa kowa da kowa fatan alkairi.
Yau typing d'in ba yawa sai hakuri.