← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 145

Sashe 8

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gaba daya jikin 'yan gurin rawa yake an rasa mai kwarin gwiwar cewa komai sai salati da ake ganin yadda Kimiyyah ke wata iriyar mi'kar tana sankarewa irin na mai 'ka'karin mutuwa hankali tashe Ajeeb yace "Abba muje asibiti dan Allah karta mutu" kasa magana mai martaba yai sai mikewa kawai dayai ya bar gurin da sauri Ajeeb da Ameer suka dauketa suna fita sauran suka bi bayan su har lokacin Mami bata daina kuka ba ta kasa shiru ga jikin ta sai rawa yake kamar maijin sanyi ko mai zazzabi da'kyar ta d'ago tana kallon fuskar jarumin d'an nata da har lokacin yana cikin mood altering ganin jini duk ya bata mata jiki yasa ta kalli hannun sa zaro ido tai ganin harbi da sauri tasa hannu cikin aljihunsa ta dauko wani d'an karamin towel fari ta daure masa hannu gabadaya ta kasa nutsuwa kuma tasan ba magana zaiyi ba amma dai tace "Asad mai Kimiyyah tai maka kake kokarin kashe ta meya kawota part dinka ya naga harbi a hannunka"? Shiru yai kamar kurma kuma dama haka take tunani rike hannunta yai yana fita da ita saida ya mayarta har part dinta kafin ya dawo ya cire bullet din hannunsa ya nad'e hannu yana tattare kayayyakin daya tarwatsa domin tun daga parlor ya soma dukanta har harabar part dinsa Saida ya gama sannan ya mike yana shiga bedroom ya cire kayan jikinsa ya shigo toilet saboda sanin irin zafin Zuciyar sa yasa ba mace ko daya da take aiki a part dinsa mazan ma sai taka tsantsan suke.

Ruwa mai matukar sanyi yake kwararawa jikinsa idanuwan sa a rufe hannunsa nakan kyakkyawan pink lips dinsa ya ma rasa mai tazo yi part dinsa uban waye ya turo ta mai take nema har ta samu damar shiga d'akin sirrin sa tai amfani da na'urarsa ta tura sako ta goge masa abubawa masu mahimmanci wanda yadau tsawon shekaru yana tarawa yau daya tasa yayi losing dinsu duka bude idonsa da har lokacin babu fari ko kadan yai tare da furzar da zazzafar iska ya dunkule hannunsa ya kaiwa mirron toilet din naushi take ya tarwatse ko'ina numfashi ya sauke cikin zafin Zuciya bad temper yafi awa biyu yana tsaye shower 🚿 na zubar ruwa a kansa kafin ya daura towel ya fita zama kawai yai gaban mirror yana zubawa had'ddiyar kyakkyawar fuskarsa ido mikewa yai a gurin yana komawa kan katafaren katon bed dinsa Wanda ya 'kawatu da kwaliyar zinare kwanciya yai yana kallon sama tare da lulawa cikin tunani har ya bata lokaci a haka karfe daya da rabi tayi bai sani ba kuma a yau yake son komawa domin isham ya kirashi a waya tun jiya ya yi masa albishir cewa ya kusa gano abinda ya dade yana nema amma yau d'aya Kimiyyah ta wargaza masa tanadin dayaiwa shekaru da dama runtse ido yai da karfi tare da cusa yatsunsa cikin lallausan gashin kansa tuni yaji ransa ya kara baci fiye da da jiyake dama zai hadu da Kimiyyah yanzu babu abinda zai hana ya d'aga bindiga ya harbe ta, tashi zaune yai a tsakiyar gadon yana tan'kwashe kafafunsa kamar daga sama idanuwan shi suka sauka akan wani photo wanda ya kasance anyi shi da dadewa zai kai shekara sha takwas sau'ka gadon yai yana zuwa gaban photo yasa hannu ya dauka yana kallo ko ba'a fad'a ba shine ya dauki wata karamar yarinya a hannunsa zatai shekara biyar da uniform a jikinta yana murmushi ita kuma tana dariya kuma da gani photon a waya akayi shi ya bayar aka wanka fuskar yarinya kadai yake kallo a ranshi yana tunanin shi da ita har abada bazai sake ganinta ba domin dama bai santa ba saidai yana fatan ya sake haduwa da ita ko sau daya ne a rayuwar sa aje photon yai yana barin wurin yaje ya fara tattara kayansa yana sawa cikin trolley ya zuge kafin yayo alwala yasa kaya yai salla ya shirya cikin kayan soja anan tsantsan asalin kyansa ya kara bayyana fili 'karara gaskiya ya matukar haduwa fad'a batawa fita yai a bedroom din,
yana yin hanyar wata kofa da aka rubuta STOCKYARDS anyi masa launin golden sai haskawa yake kamar ba rana ba password ya rubuta kafin kofar ta bud'e ya shiga iya ganinka dabbobin daji ne kamar gidan zoo fili ne mai girma an kawata shi da ado kyansa baya faduwa saidai hasashe wani 'katon 'ka'k'karfan zaki na ganinsa ya nufo shi yana kukan su na zaki da matukar gudu yana zuwa gabansa ya taka wani irin burki mai burgewa dukawa Asad yai yana shafa gashin zakin cikin so can ya jiyo kukan wata 'yar karamar giwa yana dubawa yaga har tazo inda suke amma babarta tana d'an nesa dasu itama shafa jikinta yai a yau baiji sanyi a ranshi ba sai yanzu daya shigo nan mikewa yai zakin🦁 na biye dashi ya soma zagaya gurin yaga lafiyar su kafin ya fito yana fita a part din nasa gabadaya yayi tunanin zuwa gurin Mami saidai yasan ba lallai itama ta zauna ba maybe ta bisu asibiti yana tsaye a katon katafaren kofar shiga fadar mahaifin sa yasa anyi masa Kiran wani bawa wanda ya kasance duk masarautar shi kadai ne jininsu yazo daya gano Asad din tsaye yasa shi karasowa da sauri cikin girmamawa ya du'ka yana cewa.

"Ka gafarce ni shugaba na ka kira ni ne"? Kallon sa Asad yai nadan mintuna kafin ya bud'e baki cikin zazza'kar muryarsa da baiyi magana da ita ba tun dazu yace "Amjadd will you work for me if I ask you"? Sake dukawa Amjad yai yana cewa "Allah ya taimake ka Allah daukaka ka zanyi kowanne irin aiki daka sani amma ranka ya dade kamin bayani da hausa dan nafi fahimta ba sosai nakejin turanci ba" ya karasa maganar muryar shi na rawa saboda tsoro domin dazu a gaban sa ya fara dukan Kimiyyah jikinsa ma rawa yake kuma yana sauraron me zaice masa can ya tsinkayo muryarsa yana cewa "batu ne akan stockyard dina ina son ka kula min dashi kafin na dawo ya zama tamkar ina nan kuma koda Ajeeb ne ban amince ya shiga wurin su ba kaji abinda nace"? Da sauri Amjad yace "eh ranka ya dade za'ai yadda kake so Allah ya tsare ka ya dawo dakai lafiya" "Amin" ya fad'a can kasa kafin cikin taku ya wuce da sauri Amjad ya mike yana jan trolley yabi bayansa har mota da wadanda zasuyi masa rakiya zuwa airport batare da sanin kowa ba ko bankwana da kowa ko tunanin halin da Kimiyyah take ya wuce airport daga nan jirgi ya d'aga dashi zuwa Marshall islands.

Ummmhh😘😘 SAFE JOURNEY ALIYU ASAD🌹🌹.

To yau kam anan zan tsaya sai idan Allah ya kaimu gobe a'a ba gobe ba sai jibi oh sorry it was a mistake ba jibi ba sai gata zaku samu typing kuyi hakuri kada ku gajiya da halina ni haka nake bani da haushin kowa😅🤣😂.

Mrs AL'AMEEN AHMAD CE 😘 ta kowa.

Sannan ga wata sanarwa idan kuna so na yi muku typing gobe tofa saina ga sama da mutum dubu sunyi comments 😂😂😂😂 idan kuwa ba haka ba nayi fushi saina huci kafin na d'ora ehe bazan fatse aiki na nayi muku typing ba ku turo min sticker 🤗😜 duk wacce ta sake turo min sticker saina debo mata yan committee ko na kaita ofishin 'yan hisba 🤣😅🤣😂😅.

Jinjina nake a gare ku masoya abokan arziki fatan samun rahmar ubangiji da amincin sa a duk inda kuke bazan ta'ba mantawa daku ba.
Naja'at Musa Abubakar
Zarah Musa d'an Adam
Hafsat Harees
Salmah Hayat
Suwaiba Yusuf
Fatima Idris
Khadija A Yusuf
Saudat Yusuf
Zainab Sunusi.

Mrs Al'ameen Ahmad ce ke gaida ku 🌹🌹💍💍🌃🌆🌃🏙️.

YUSRAHMS WE WILL MEET AGAIN 🤗.

Tofa a'a abun yayi ashe ana son posting irin wannan comment haka na wani ma ban samu damar karantawa ba sai hakuri amma maganar gaskiya kun bani mamaki ai bansan haka littafin nan keda farin jini ba ya tara masoya da yawa masu min fatan aikairi TO IDAN KINJI DAD'I KO KAJI DAD'I KAI SALATI D'ARI GA MANZON ALLAH SAW RANAR JAMA'A ZAKA SAMU WANI HASKE RANAR ALKIYAMA WANDA DA ACE ZA'A RABAWA ABIN HALITTA ZAI ISHE SU SHIGA ALJANNAH🌲.

TYPING 📲 FRI 01 March 8:18AM Yusrah Musa Abubakar na karaso kuzo kusha story.

💎ME KAMAR SARKI 💎

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY.

YUSRAH MUSA ABUBAKAR)(Maman little Zaran aunty 😘)(*).
🕌
🕌 🕌
🕌 🕌 🕌
🕌🕌🕌🕌🕌🕌
🕌 🕌
🕌 🕌
🕌🕌🕌🕌🕌🕌
📿📿📿📿📿📿
🕋🕌🕋
It's Friday don't forget to recite suratul al-khaf may Allah open the door of success for all of u may Allah accept our du'as may Allah bless nd help us Amin 👏.

Dedicated to
MR HAUSA EBOOKS 📚
📚📓📒📕📖📗📘📙📕📔
SHURAIHU USMAN CEO FAUNDER OF TASKAR NOVELS.

STORY AND WRITTEN BY
✍️Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty 😘.

07~ AL-MUHAIMINU
The dominator
08~AL-AZIZ
The almighty.

4~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Khaifina.

💎Me kamar sarki 💎
By
🌹 Yusrah Musa Abubakar Mrs Al'ameen Ahmad ce 🌹.
Chapter 8 · 0% Book details