← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 145

Sashe 79

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda Iluh ya furta haka ne ya faru bayan ya dawo tun a ranar ya fara zuwa kofar gidan Balarabe ana yo masa sallama da Bahijjah sai kud'i yake kashe mata kamar hauka tun Bahijjah bata kulashi har tazo yanzu ya zama duniya babu wanda taji tana so sama da Iluh hankalin Asabe yai mugun tashi tayi fad'an tayi dukan akan dole sai Bahijjah ta rabu dashi itama taja tunga tayi tsayin daka tace wallahi mutuwa ce zata rabata da Iluh har gurin bokanta Asabe taje akan wannan al'amarin ya bata magunguna tayi dan ta rabusu amma kamar wanda ta sake d'ora musu dan'kon soyayya haka kullum suna manne har shagon da yake kwana take binsa idan yai jinkiri baizo gurin ta da wuri ba daga nan su juyo su dawo kofar gidan Balarabe har kusan raba dare suke suna hira🙊 gari kwa nan ya d'auka ko'ina gulmarsu ake daba-daba mafi yawa saidai sucewa Asabe Allah ya 'kara alhakin Indo ne da Balarabe ya fara binta tun daga yanzu ta fara ganin sakayya ba'a shuka gyad'a dawa ta fito.

Yauma kamar kullum yadda suka saba suna zaune manne gaf da juna wai a hakan hira suke bakajin tashin muryar su Asabe ce ta fito daga cikin gida a fusace ko mayafi babu balle takalmi tana zuwa ta d'auke Bahijjah da mari cikin ba'kin ciki take nuna ta da yatsa muryarta na rawa tace.

"Bahijjah idan na isa dake ki shiga gida kafin naci uban daya kawoki duniya".

Juyawa tai kan Iluh tana cewa "kai kuma tsinanne la'ananne indai ka lalata min 'ya wallahi bazan yarda ba saikayi zaman gidan yari sau nawa zan fad'a maka bakai ba ita tafi karfin auren talaka matsiyaci irinka saboda kai maye ne d'an mayu jikan mayu ka nace sai naga da yadda zaka aureta da 'karfin da kake nunawa dan ko kai uwa yata maye bazan d'au Bahijjah na baka ba domin mahaukacin kare bai cije ni ba ko Bahijjah zata kare rayuwar ta babu aure wallahi tallahi baka isa ka aureta ba kaji na fad'a ma shege matsiyaci mara zuciya ana korarka kana mannewa".

Dariya Iluh yai yana mata kallon mahaukaciya yace "wai da gaske kike ban isa na aure taba tab kan bala'i lallai zaki azumin kaffara dan wallahi banga shegen🙊 daya isa hana ni auren wannan yarinyar ba ko d'an uban waye shi a garin nan kin gane😣😳 ai garama kafin kowa yaji kibi ta ruwan sanyi ki bani ita idan kuwa ba haka ba zaki bani aurenta da qarfin hatsi dan wallahi Allah ko zaki mutu saina aureta".

SUBAHANALLAHI ASABE TAKI TA SAMEKI KIN GAMU DA GAMONKI🤔🤨.

Yana rufe baki Asabe ta kaiwa Bahijjah dake tsaye kusa dashi wata irin sha'ka tana cewa "zaki wuce ki shiga gida ko saina kasheki a gurin nan"?.

Da sauri Bahijjah taja baya tana cewa "na shiga wanne gidan ni wallahi shi zanbi nabar zaman gidan nan daga rana irin ta yau idan make bazaki aura min Shiba zamuje gurin liman yakai sadaki a daura mana aurenmu".

Dafe 'kirji Asabe tai cike da rud'ewa idonta kamar zai fito waje batasan lokacin da hawaye masu zafi suka fara yi mata zarya a kuncinta ba nuna Bahijjah take da yatsa amma ta kasa magana a fusace ta fisgeta tana hakad'ata cikin gida tasa murfin kofa ta rufe tare da juyowa tana kallon Iluh wanda ya tsaya 'kerere yana kallon ta tace.

"Allah ya tsinewa uwa da uban da suka haifeka shege tsinanne talakan banza wallahi karya kake Bahijjah tafi qarfin auren d'an garuwa irinka tun wuri kaje ka nemi daidai dakai" tana fad'in haka ta bud'e kofa ta fad'a gida kai Iluh ya jinjina yana cewa "lallai matar nan baki sanni ba amma babu damuwa zan nuna miki iyakarki indai ni d'an halak ne na cika sunana Ibrahim wallahi tallahi wallahi tallahi saina auri yarinyar nan kuma zaki gani" yana fad'in haka shima ya juya yabar gurin haka Asabe taiwa Bahijjah tsinannan duka a cikin gida bayan shigarsu harda fasa mata baki tayi mata jina jina saboda irin ciwon da takejin zuciyarta nayi.

🌴 CAMEROON 🌴
Sakamakon ganin irin ri'kon amanar da su malam Habu suke dashi yasa Alhaji Idrisu ya saki jiki dasu yake musu duk abinda suke so ya d'auke nauyinmu komai shi yake musu suma haka suka zage karfin su suna kyautata masa da d'an abubuwan da baza'a rasa ba kuma hakan saiya zame musu gamda katar domin sun ninka da samun kud'i albashi kusan ninki biyu yake biyansu akan nada ga ihsani da sutura akai akai tuni sukai 'kiba dakyau suka mayar da jikinsu babu rama saidai malam Habu kullum yadda yaga rana haka zaiga dare baya samun barci tunanin iyalansa yake ya a wanne hall suke ya taho bai bar musu sisi ba.

Suna zaune a wajen gate d'in kofar Alhajin Sadi na masa hira amma ba sosai yake amsawa ba saidai yace masa umm umm saboda tunani dayai masa yawa kallonsa Sadi yai yana cewa "lafiya kuwa nifa naga kamar kana cikin damuw ko baka da lafiya ne"?

Kai malam Habu ya girgiza "a'a ina lafiya Sadi hankali nane ya juya izuwa gida idan ba zuwa nai na ganosu ba bazan mayar da hankalina akan aiki ba".

"To babbar magana yanzu ya kake so ayi"?.

"Alhaji nake jira ya dawo nayi masa magana idan ya amince saimu tattara muje gida ko sati biyu muyi mu dawo idan ma kai kana ganin baza kaje ba saika bani sakon da zankaiwa matarka ko"?.

Kai Sadi ya girgiza yana cewa "a'a nima zanje basai mu dawo tare ba ai inaga tunda Alhaji yana gari ma dayya dawo mu sanar masa gobe kawai sai tafiya ko ya kace"?.

Kai Malam Habu ya d'aga "eh haka ne gaskiya na damu naje gida dan haka insha Allahu gobe iyanzu mun sauka bari ya dawo daga ofishinsu zan sameshi naji me zaice Allah yasa kar yace mu d'an kara zama wallahi haka kawai naji lokaci guda garin nan ya isheni gida nake so".

"Humm malam Habu kenan dama ai haka ne suma kuma na gidan suna can suna kewarka saboda wasa-wasa fa mun dad'e anan amma zamuje mu yiwa hajiya mammah mai abinci sallama ko"?.

"Eh zamuje bari ya dawo tukuna mu fara sanar masa kar muyi gaggawa duk da nasan bazai hana ba domin munyi muguwar dad'ewa a garin nan shekara da kusan watanni hud'u kamar wanda aka rufe mana bakin mu koma gida".

Da dare bayan Alhaji ya dawo suka sameshi da bukatarsu ta zuwa gida akan nan da sati kamar biyu zuwa uku idan sukaga ahlinsu zasu dawo ya amince harma ya musu alheri irin wanda basa zato dasu da matansu yadika da atamfofi ga kud'i kamar dama ajiya suke bashi sunyi murna qwarai da gaske sukai masa godiya da addu'a mai kyau washe gari tun asubar fari sukai shiri ana fitowa daga masallaci d'auko hanyar gida.

Amma me tafiya batai kyau ba domin a hanya sun had'u da 'yan fashi🙊 haka suka taresu a daji sukaiwa wasu duka bayan sun yashe musu komai na motar karshen wulakanci hatta kayan jikinsu basu bar musu ba saida sukai musu tikk sannan suka korasu cikin mota suka gudu wadanda basusan qaddara ba harda kuka haka malam Habu ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi na takaici bayan lokaci mai tsawo daya d'auka baya gida yau ya dawo da qwarin gwiwa zai kawowa iyalansa abunda da dad'e yana mafarkin samu yaga ya wadatasu amma tsinannun sunyi musu bankad'a sai bayan sallar isha sosai suka sauka a 'kauyen kusa dasu daga nan ko kud'in mashi basu dashi sai a qasa suka d'auko hanyar gida sanda suka iso sai mutane d'ai d'ai dare ya fara kowa ya shiga gida da'kyar Malam Habu yacewa Sadi saida safe wanda Sadin shima da'kyar yace masa Allah ya tashemu lafiya jiki babu armashi a sa'bule kowa ya nufi gida da yake Malam Habu yafi kusa Sadi yana anguwar gabas a gurin suka rabu shiya wuce gida shi kuma ya qara gaba.

Malam Habu da'kyar yake d'aga kafarsa da babu takalmi yake takawa zuwa cikin gidansa jiki a mugun sanyaye cike da tunanin me zaice musu da wacce fuska zai kallesu tsawon wannan lokacin me suke ci daya suke rayuwa waye yake kula dasu sauke ajiyar zuciya yai yana shiga gidan da sakaliyar sallama😥 a bakinsa duk suna zaune a tsakar gida cikin hasken farin wata tarr daya haske ko'ina.

Cike da mamaki suka zuba masa ido suna kallonsa domin a yadda yai sallama da muryar daba tashi ba basu saba jinsa da ita ba duk tunanin su ko wannan mahaucin ne 'kwalisa tunda yake shigowa qauyen kuma basu rufe gida ba a razane kowa ya tashi Aisha da tafi kowa tsoro da gudu tai hanyar d'akinsu tana cewa.

"Wallahi 'kwalisa ne ku tashi yanzu ya fara duka jiya ma ya mari Habiba a dandali".

Jin haka yasa kowa ya mi'ke a firgice zasu gudu muryar malam Habu da tsantsan damuwa yace "ku dawo kufa nine ba wani ba yanzu na dawo".

Duk tsayawa sukai sak A'i dake ri'ke da fitila ta haskesa ganin da gaske Malam Habun ne yasa tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un mun shiga uku malam me zan gani haka"? Ta karasa maganar tana sake haska fitilar da sauri suka matso gurin sa Aisha ma dake d'aki jin abinda A'in tace yasa da gudu ta fito kaii da gaske shine duk salati suka saki Asma'u kam da yake tafi kowa saurin kuka haka ta fashe dashi tana dur'kusawa a gun domin kowa yaga a yadda malam Habu yake yasan tafiya batai kyau ba.

"Malam meya faru dakai haka daga ina lokaci mai tsawo shiru muna sa rai zaka dawo mana gida fal da Abubuwan arziki sai muga haka" A'i ta fad'a tana sake kare masa kallo.

Saude dai ta kasa magana Binta ce ta danyi qoqarin cewa "sannu da dawowa Malam bari na kawo maka tabarma" ta karasa maganar tana juyawa zuwa d'aki tare da share 'kwalar data zubo mata ta dauko tana shimfid'a masa kasa zama yai yana tsaye kamar an dasa shi.

"Malam dan Allah ka zauna nasan a gajiye kake"?.
Chapter 79 · 0% Book details