← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 145

Sashe 119

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi bazan yarda ba saina aureshi ni Asad nake so taya za'a ce yayi aure bayan zaman jiransa nake zuciyata zata fashe wayyo Allah nashiga uku ku taimake ku ce min da wasane ko mafarki ba'a gaske bane Asad yai aure innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" ta karasa maganar tana gwara kanta a bango duk ta hargitsa jikinta ta dame kwalliyar fuskarta harda yankan wu'ka a hannunta inda ta she'ka aguje ta d'auko zata da'bawa cikinta aka kar'be garin kwatar wu'kar taji ciwo.

Gurum Mami tai tana kallon ta ta kasa koda motsin kirki jin abinda Makiyyan ce cewa tabd'i subahanallahi ana wata ga wata Makiyyah ma son Asad take wai amma fa akwai gagarumar matsala a gaba Asad Asad fa? Gaskiya ta d'auki abinda bazai kaita ba Asad mijin mace hud'u ne amma d'aya ma yana rabawa biyu zaiyi ko bazai yiba ga wacce Ajeeb ya za'ba masa sannan ita Makiyyah da take 'yar gida ya za'ai kena..................................

Tunanin Mami ya katse sakamakon zuwa da Makiyyah tai ta dur'kusa a gabanta tana ri'ke kafafunta da tsananin kuka sosai tace.

"Dan Allah mami ki taimaka min kar na mutu zuciyata a yanzu haka ci take da wuta ambaliyan jini take damuwa zata kasheni bazan iya cigaba da rayuwa a masarautar nan ba ina kallon matar Asad tana zarya wallahi zuciyata bugawa zatai please Mami ki tausaya min rayuwata tana cikin garari na fad'a shafin jarabtar soyayya ha'kuri na ya gama karewa dole na fito na bayyana kowa ya sani idan na mutu son Asad ne ya kashe ni ba komai ba".

Zaro ido Mami tai jin zata d'ora mata masifa idan ta fad'a a daidai ta mutun basai a camfa ri'ka cewa son Asad d'in bane bataji dad'in maganar Makiyyan ba amma ganin bata cikin hayyacinta yasa tacewa Sultana Shafi'ah ayi mata addu'a amma ko rufe baki Mami batai ba Sultana Hadizah tace.

"Humm yo wacce addu'a ba abinda take bukata daya wuce ku aura mata Asad d'in amma saiku tanadin kayan kar'bar gaisuwa ko tunda naga ta matsu taje ma'kabarta ki rasa wanda kike so sai azzalumi gaki nan gashi ai saiki aureshi tunda mutuwa kike sha'awa kina kallo yadda ya mayar da Khimiyyah zararriya kodan ba dama ka fad'a sai aga zafinka bayan an gama cutar ka".

Had'e rai Mami tayi dan dama tasan Sultana Hadizah saita magantu amma ko kallon inda take batai ba kawai abinda ya kawota part d'in tayi ta share Makiyyan ma take ta burgima a qasan carpet tana Kiran an ceceta Asad take so saboda takaicin maganar da Sultana Hadizah take fad'a kawai ta amso Shaukiyyah ta fito daga nan aka d'auketa a mota zuwa bangaren Sultana Fatima idan sun gama abinda xa'ai zuwa Nan da sha biyun dare sai tazo ta kaita part d'in mijinta Ameer sannan ta koma part d'inta bata ko zauna ba ta zarce yankin inda tasa akai Amatu ta sameta ita kad'ai duk 'yan rakiyarta sun tafi sai 'ya'yan Aunty Futuha da kuma su Hajir da Muyassara suna zaune suna hira iya su Amma banda ita tunani tayi kada daga zuwan yarinya ta sanyata a damuwa sai kawai ta cewa su Hajir d'in su tsaya anan su kwana tare da ita ba yau za'a kaita part d'in mijinta ba sai an gama biki duka tana fad'in haka ta juya ta fita ta barsu suna cigab da hirarsu.

Washe gari su Aunty Fadilah duka suka tafi gida har airport Mami tayi musu rakiya suka sake bankwana tana bada sa'kon gaisuwarta zuwa gurin sauran 'yan uwa sannan ta dawo gida tana shigowa falonta taga AJEEB zaune shi kad'ai yana breakfast kai ta jinjina tana murmushi batace komai ba ta karaso tana zama d'agowa yai yana kallonta ganin murmushi a fuskarta yace.

"Mami barka da safiya kin tashi lafiya"?.

"Lapia kalau Ajeeb ya jikin naka"?.

Da d'an mamaki Ajeeb yace "jikin me kuma Mami"?.

"Oh harka manta kenan ai Asad baya masarautar nan a jiya ya koma domin Amjadd ya fad'a"?.

Dariya Ajeeb yai yana cewa "humm Mami ki bar batun Asad d'in nan na rantse miki da Allah ko wuya ya huce ya dawo zakiga yadda za'ai dashi akan yarinyar duk qarya ce da yake cewa sai yayi retire zaiyi aure yawan cika min bakin daW yake da nuna ban isa nayi wani abu a kansa ba yasa ni kuma nasa kansa yad'au caji na hukunta shi ta nan gaba ko ance yai min bazai ba".

Kai Mami ta girgiza tana cewa "kamar dai ka manta waye Asad kake cewa haka shine zai huce akan lokaci hum kawai kadai ka kyale bari nazo" mi'kewa tai tana shiga part d'in da tasa aka kai Amatu zuwa wani lokaci ta fito Amatun na biye da ita a baya tazo ta zauna a qasan carpet domin itakam batasan komai ba duk abinda akeyi batasan ma Ajeeb su 'yan biyu bane kuma kamarsu d'aya.

Kallonta Ajeeb yai yana cewa "Amatullahi dan Allah kafin nace miki komai zan fara da neman yafiyar ki akan abinda na aikata miki nasan ban kyauta ba banyi daidai ba amma ba nayi haka dan na cutar dake bane dan Allah ki fahimce ni zan fad'a miki komai yadda zaki gane ki yarda dani".

Cike da mamaki Amatu ta d'ago tana kallon sa me yake nufi kamar ya yafiyar ta tame yake nema Kuma.............................

Ji tayi Mami tace "a'a Ajeeb kayi shiru zanyi magana da ita"?.

"Ok Mami" Ajeeb ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya cikin tausayawa Amatu da rashin jin dad'in abinda yayi mata batare data sani ba yanzu baisan wanne irin kallo zatai masa ba?.

Dukka hankalinta Mami ta mayar kan Amatu tana cewa" Hauwa'u Amatullahi sunanki ko takwara tace ke lallai kam Asad bai sani ba¿ Sake qare mata kallo Mami tai gaskiya ta Ajeeb d'in fa yarinyar akwai nutsuwa da gani babu tambaya ko ba'a fad'a ba.

"Amatullahi ki saurare ni dakyau ki fahimci abinda dazan fad'a miki Ajeeb tunda yake zuwa gurin ki ya ta'ba fad'a miki shi d'an biyu ne kuma kamarsu d'aya ba'a bambance su''?.

Kai Amatu ta girgiza jiki a sanyaye tace "a'a bai fad'a min ba".

Cigaba Mami tai "ok yayi miki laifi sosai gaskiya Ajeeb su 'yan biyune akwai d'an uwansa sunan Asad dashi aka d'aura miki aure bada Ajeeb ba duk zuwa gurin ki da Ajeeb yake yi domin d'an uwansa yake badan kansa ba kuma baiyi haka dan ya 'bata miki raiba a'a yayi haka ne abisa kyakkyawar zuciya da kyakkyawar niyya da kuma kyakkyawar manufa fatan zaki fahimce shi sannan jin ba dashi akai auren ba kada ki tada hankalin ki wannan ba komai bane ki qaddara dama can ba Ajeeb d'in ne mijinki ba Asad ne kuma kada kiyi ba'kin ciki insha Allahu kinyi dace Asad na qwarai ne Ina fad'a miki haka a matsayina na uwa gareki bawai matsayin mahaifiyar Asad ba Amatullahi nice na haifi Asad na raineshi har ya girma dan haka nafi kowa sanin dukkan halayyarsa yana da zafi da saurin fusata sannan shi murd'add'an mutum ne wanda ba'a gane masa amma fa a cikin hakan idan kika bi wasu matakai ina tabbatar miki da Asad zai dube ki na farko ko maye zai faru kada ki kuskura a gabansa ki nuna raki kada ki nuna gajiyawa da karaya ko sarewa karki nuna kina jin tsoron magauci karki nuna masa bakida zafi karki nuna ke raguwa ce ki ri'ka nuna jarumtarki a fili koda a gabansa kada idan yayi magana ki razana ko ki firgita ki tsaya tsam ki saurareshi kuma ki fuskanceshi ki nuna masa cewa zaki iya ji da komai Amatullahi indai kika bi wadannan hanyoyi iya wannan kad'an d'in dana fad'a miki kina zaune Asad zai nemeki da kansa a lokacin da baki ta'ba tsammani ba abu na qarshe shine zanci gaba da 6oyeki anan bazan ta'ba nunawa Asad kina cikin masarautar nan ba koda ya dawo zanga zai nemeki ko zanyi min magana a kanki ki kwantar da hankalin ki kisa tunaninki guri d'aya kiyi rayuwa cikin farin ciki ina tare dake fatan kin fahimci duk wani abu dana fad'a miki"?.

Kai Amatu ta d'aga tana sau'ke numfashi a hankali tace "eh Mami na fahimta sosai kuma nagode Allah ya saka da alkhairi sannan Ajeeb yabar neman yafiyata babu abinda yai min na fahimce shi insha Allahu Mami zaki sameni mai ladabi da biyayya zanyi dukkan abinda kika umarce ni fatana Allah ya dafa min".

Cikin jin dad'i Mami tace "Amin takwara ta Allah ya miki albarka Allah ya baki nasara Allah yasa kece silar canzawar Asad".

Tun Amatu batai magana ba Ajeeb yace "Amin Mami saidai wani hanzari ba gudu ba Amatu na manta ban fad'a miki abu guda ba shi Asad ba doctor bane irina sannan baya d'aukar wargi abu 'kalilan zakiyi yanzun nan ki fusata shi soja ne shi" ya karasa maganar yana mata alamar harbi da bindiga.

Kallon Ajeeb Amatu tayi lokaci guda taji wata muguwar fad'uwar gaba ta sameta har tana d'an dafe 'kirji tare da cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un".

Dariya Ajeeb yai wanda Mami ta harareshi tana cewa "ya haka Ajeeb meye na tsorata ta dan soja ne sai akai ya? Kinga Amatu share shi kinji babu wani abu Asad yana da sau'ki sosai idan ka tsaya ka fahimce shi Ajeeb ya fad'i haka ne da wasa kada ma ki dama tunaninki a kansa kinji".

Kai Amatu ta d'aga "to Mami na gode".

"Ok takwara ta wanne sunan zan ri'ka kiranshi dashi ne domin gaskiya kin d'auko babban suna"? Mami ta tambaya tana kallon ta da murmushi.

"Ai kawai Mami ki ri'ka ce mata takwarar ma yayi idan Asad ya dawo yaji haka sunanki ne da ita maybe ya sau'ko da wuri".

"A'a Ajeeb ba takwara zance mata ba ni jewel✨ zance ai yayi"?.

"Wow jewel? Tab lallai kice ke Amatu kinzo a sa'a kiji sunan da Mami zata ri'ka kiranki dashi uhm mu kuwa daga Ajeeb sai Asad babu wanda ta saurayawa suna".

Murmushi Mami tai tana cewa "ai kuma ba sunan ku Ajeeb da Asad ba ko"?.
Chapter 119 · 0% Book details