← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 145

Sashe 124

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma tad'an basa mamaki domin tayi kokari yadda yake zato ba haka ya gani ba dan tana farawa yaga ta dage maimakon tayi sanyi dakatar ta yayi ya sauya mata wani wanda yadan fi na farkon girma zuwa wani lokaci yace tabar wanan suka koma 6angaren igiyoyi banda ta'ba kasa daga wanda ta ri'ko wannan ta saki wannan haka tai tayi suka koma gurin gudu wuri ne mai tsaho tun daga farko ta fara idan tazo gurin da ya aje mata wani abu sai tayo tsalle ta haure shi wani wurin karfen ma da tsayi kamar katanga amma a hakan zatai tsalle ta ri'ko karshensa ta haure tunda suka fara bata tsaya ba saida lokacin sallar Azhar yayi sannan yace taje tayi amma bata koma part din Mami ba a nasa tayi shi kuma yaje masallaci yana dawowa suka d'ora inda suka tsaya basu sake dakatawa ba sai sallar la'asar.

D'aga nan komai ya canza aka d'auki wani salon sabon training d'in mai wahala shima ko duba da cewa yau ta fara Asad baiyi kawai shikam iya qarfin sa da qwarin gwiwa yake nuna mata komai domin baya so a gaba taji shakka ko tsoron abokin gaba musamman daya fahimci itace yarinyar da ya dad'e yana nema itace sirrin wannan 'kungiyar ke hannunta da taimakon ta zai cika nasa burin to itama dole ya cika mata nata zai mayar da ita jarumar soja wacce za'ayi mamakinta wannan kawai shine abinda ya d'auka a tsakaninsu amma bayan haka babu wata ala'ka da yake jin ta had'a su.

Bai barta ta samu hutu ko na sakan d'aya ba saida akai kiran sallar magriba sannan yace taje ta koma part d'in Mami shikenan sai gobe basai yaje ya nemota ba tana yin sallar asuba ta fito suci gaba amma masa tai tana fita a gurin duk ta hargitse tsabar wuya ribom din kanta ya fad'i gashin duk ya barbaje amma ba tashi take ba hijab kawai ta saka kayanta ta debesu a hannu ta fita daga part d'in Amjadd yana zaune yana kallon ta har ta fita mamaki ne fal a ransa to wannan d'in wace ita yasan dai Asad bai kula mata baya safgarsu to ita kuma wannan fa? Kodai itace matar da d'an uwansa Ajeeb ya aura masa? Ya fad'a a ransa cikin tunani ''eh tabbas babu shakka ita ce domin babu wacce ta isa tunkarar Asad haka a zauna lafiya.

A matukar gajiye Amatu ta shiga part d'in Mami tayi sa'a kuwa bata parlor dan haka kawai ta wuce part d'inta da ruwa me zafi tayi wanka ta d'auro alwala tazo tayi sallah bata fito falor ba saida akai isha sannan ta shirya ta lokacin data fito Ajeeb da Asad dukka suna tare da Mami kamar zata koma sai kuma ta fasa ta karaso da sallama tana dur'kusawa ta gaida Mami.

Amsawa Mami tai da murmushi tana kallon ta kafin ta kalli Asad tana girgiza kai tace "jewel ina kika tsaya ne d'azu naga baki dawo ba ina ta jiranki.

D'agowa Amatu tai tad'an kallo Asad kafin tace "Ina can".

"Kina can kamar ya me kika tsaya yi"?.

"Mami zan shiga aikin soja ne".

Amatu na rufe baki Mami da Ajeeb suka zaro ido suna kallon Asad da sauri Ajeeb yace.

"A'a wallahi bazai yuwu ba bamu amince ba wanne irin aikin soja kuma kina mace kece kika ce zakiyi ko tilasta miki yayi fad'a min yanzun nan na 6ata masa ransa"? Ajeeb ya karasa maganar yana hararar Asad wanda yayi masa wani kallo.

Kai Amatu ta d'aga "eh nice".

"A'a jewel ki fad'a min gaskiya idan Asad ya saki dole kiyi min bayani aita Ajeeb d'in wanne irin aikin soja kina mace gaskiya baza kiyi ba".

Sauke numfashi Amatu tai tana cewa "dan Allah Mami karku hana wallahi dama ni tun tuni zamowa soja burina ne ba shine ya tilasta niba nice nace Ina so dan Allah Mami ku bari na cika burina''?.

Kai Mami ta jinjina tana cewa "ai shikenan fad'uwa tazo daidai da zama Allah yasa ki fara lafiya ni bazan hana ki cika burinki ba tunda abinda kike so ne amma iyayen ki fa sun san da haka ne"?.

"Eh Mami sun sani mahaifina har tambaya yake akan wanda zan samu yamin hanyar aikin ba'a samu ba shiyasa na ha'kura yanzu kuma na samu ina son nayi aikin soja".

Sauke ajiyar zuciya Mami tai tana kallon ta tace "to jewel Allah ya taimaka Allah yasa ki fara a sa'a Allah ya tsare ki".

"Amin Mami na gode" Amatu ta fad'a cikin farin ciki fuskarta ta bayyanar da murnar hanatan da Mamin batai ba.

Gyara zama Ajeeb yai yana kallon Amatu yace "gaskiya baza kiyi aikin soja ba Amatullahi muma muna maza akai mana tayi muka 'ki balle ke mace kinga ki d'auke hankalinki daga nan idan aiki ne zan biya miki kiyi karatun likitanci ki zama 'kwararriyar doctor ki shahara kiyi suna kina taimakon al'umma amma babu inda zakije'' Ajeeb yana rufe baki Asad yace.

"Saika hanata na gani idan kana da iko da ita"?...

Zaro ido Ajeeb yai yana kallon Asad da mamakin wato yana nuna masa shine mai iko da ita saboda yana son tayi aikin soja shiyasa zaice haka amma da maganar ita matarsa ce zaice inaaa, tab sake kallonsa yai yana cewa ''oh Asad me kake son cewa ne kamar ya idan ina da iko da ita me kake nufi"?.

"Ban sani ba".

Dariya Ajeeb yai yana cewa "kan bala'i haba Asad karka bada maza man Ina jarumtakar taka tun ba'a je ko'ina ba bari kaji gaskiyar magana Amatu bazatai wani aikin soja ba ka gane"?.

"Shine nace saika hana idan kana da iko da ita, ko mahaifin ta bazai hanata cika burinta ba tunda ya amince mata kaga kuwa kai banza Ajeeb baka isa ba aiki ne kuma sai tayi".

"Aiko Asad baza tayi ba"?.

"Ok ka hana idan ka isa"?.

"Na isa harna wuce inda kake zato na bazata sake zuwa part d'inka koyon wani shirmen training ba daga gobe zan fara koya mata practical" Ajeeb ya karasa maganar yana kau dakai dan kada Asad yaga dariya yake.

"Uban practical zaka koya mata".

"Ko kuma kai nace uban training zaka koya mata ba kalli iya yau d'aya yadda kasa 'yar mutane ta gigice gaskiya Asad bansan cewa kai malam zalumu bane sai yau''.

Banza Asad yayi masa ganin haka yasa Ajeeb ya kalli Mami yana cewa "Mami kina jinmu dashi fa please ki hanashi wannan abun da yake kokarin yi ba daidai bane"?.

Kai Mami ta girgiza tana cewa "a'a Ajeeb babu ruwanka a lamarinsu sunfi kusa wannan tsakaninsu ne bakaji ba me jewel din tace dama can zama soja burinta ne kaga ai itama tana so kawai ka bisu da fatana alkhairi".

Kai Ajeeb ya d'aga "to shikenan Mami Allah ya taimaka Allah ya tsare yasa a gama lafiya juyawa yai yana kallon Amatu yace.

"To jewel d'in Mami tunda kece kike son aikin soldier d'in mukan baba abunda zamuce saidai Allah ya taimaka dama haka o'o yake so kenan kuma ya samu mace jaruma ba uhm? Mami daga baya zakiga yadda za'ai drama dashi kuma nina fad'a miki muna nan sai maganata ta zama gaskiya"..

Kai Mami ta d'aga tana cewa "to naji abar maganar haka jewel tashi kije kici abinci inaga tun breakfast d'in safe da kikai ko"?.

Zaro ido Ajeeb yai yana kallon Asad yace "kan bala'i tun safe tsabar kai ba'kin mugune Asad gaskiya Mami ki dakatar dashi kinga ya nuna alamar kasheta yake shirin yi".

Kai Mami ta girgiza tana cewa "a'a Ajeeb ba haka yake nufi ba kayi shiru wannan ba shafinka bane abu ne tsakanin mace da mijinta😳" ta karasa maganar da murmushi tana kallon Asad wanda shima da sauri ya d'ago yana kallon ta jin abinda ta fad'a kafin ya girgiza kai.

'Yar dariya Mami tayi dama ta fad'i hakan ne taga ya yanayin Asad d'in ya zai kasance kuma sai taga abinda take zato mayar da hankalin ta kan Amatu tai tana cewa "jewel je kici abinci'' to Amatu tace tana mi'kewa ta fara tafiya kenan taji muryar Asad yace.

"Kar kici mai nauyi".

Ba iya Amatu ba hatta su Mami saida suka kalleshi da mamaki jin wata sabuwar takurar kuma Mami tace.

"Asad kamar ya kar taci abinci me nauyi mekake nufi"?.

"Mami dare yayi zai takura mata sannan nace tana yin sallar asuba taje ta sameni domin ni ba zama nazo ba".

Harararsa Ajeeb yai yana cewa "humm kinji ko Mami? Ashe dan kansa ya hanata to wallahi baka isa ka hanata rayuwa Mai kyau ba ka gane kuma naji kana maganar ba zama kazo ba badai kana nufin tare da ita zaka tafi ba kaje ka gana mata azaba ko hum babu inda zataje? Juyawa yai kan Amatu yaci gaba "Amatullahi kici abinda ranki yake so idan ma nauyinsa yakai nauyin dutse ai ba cikin mutum bane naki ne babu Mai matsa miki lamba indai ina nan bazaki abinda ranki baya soba".

Itakam Amatu batai magana kawai tayi murmushi tana mamakin tsokana irin ta Ajeeb da kalan magana, Asad bai kulashi ya mi'ke yanaiwa Mami saida safe ya fita Ajeeb ne dai ya dad'e sosai dan Amatu ma shiga bedroom tai ta barshi sai kusan karfe sha biyu ya tafi shima Mami ta mi'ke tana kulle kofa ta shiga part d'inta tunda yau Mai Martaba a 6angaren Sultana Fatima yake.

***
Washe gari kamar yadda Asad yace mata tanayin sallar asuba ta gaisar da Mami daidai ya shigo shima suka gaisa da Mamin sannan yace ta biyoshi fita sukai tare tana bin bayansa har part d'insa gurin jiya haka yauma wuni guda tayi yana bata horo tasha wahala kuwa har yafi na jiya haka ta gala'baita amma zuciyarta bata kasa ba.
Chapter 124 · 0% Book details