← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 145

Sashe 116

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawo da kallon shi kanta yai batare daya bata amsa ba yace "ok muje part d'in Mamin" kai Aunty Fadilaty ta d'aga tana mi'kewa suka fita tare suna tafe suna hira dan sosai Asad ke son matar jinin su ya matukar had'uwa 'kanwar Mami ce ita kuma a Riyadh take aure yaranta uku mace daya ZARAH sai maza biyu.

Yasha mamaki ganinsu da yawa harda wadanda ya dad'e basu had'u ba ga larabawan 'yan mata suna rawa a gefe sun kuna wa'kar "ana ahibbu ya habibi" cikin nishad'i ganinsa yasa suka tsaya d'aya bayan d'aya ya kallesu su hud'u ne Hajir Yusriyyah Muyassara da Fujirat 'ya'yan Aunty Futuha da Aunty Aleemah sai kuma Aunty Naizarah lallai bai kyauta ba ya dad'e basu had'u ba yaushe har yaran nan suka girma haka kallon su yai suna gaidashi yace.

"Wato ku yaran nan duk abinda yazo ranku shi kuke yi ko meye abin burgewa a rawa musamman ma ke Hajir kin fi kowa kodai mawa'ki zaki aura"?.

Rufe fuska Hajir tai tana cewa "Allah a'a ni ba mawa'ki bane saurayi na ustaz ne🤣 kuma ka tambayi Aunty Fadilah ai ta sanshi kwanan baya munje gidanta dashi".

Kallon Fadilah Asad yai da alamar tambaya yace "wai haka ne Aunty Fadilaty"?.

Kai aunty Fadilah ta d'aga tana dariya tace "ba haka bane bakaga a yadda yaje gaida niba kamar ya taso daga filin kwallo".

Zaro ido Hajir tai "kai Aunty Fadilah Allah yanzu zakisa yace na rabu dashi dama wancan zuwan dayai na ma saida yace na rabu da Zayad kuma wallahi Adeel mutumin karki ne".

"Ri'ke baki Aunty Fadilah tai cikin 'yar tsokana tace "tofa Hajir babban lamari wato Adeel harya sace zuciyarki kamar haka a gabanmu kike yabonsa ah lallai kam shiyasa duk abinda yarinyar nan Zarah tai nake cewa zuwa min ziyarar da kike ne a gurin ki ta koya idan ta kama rawa da malgwad'a kamar tarwad'a abin har mamaki yake bani"

Dariya sauran suke yayin da Hajir ta fara bubbuga kafa kamar zatai kuka dan tasan maybe Asad ya sake mata iyaka da wannan Adeel din kallonta yai kamar bazai magana ba sai kuma yace "Hajir idan kin tabbata da gaske kike abinda kika fad'a zan zo Bahrain zanyi bincike a kansa".

Da sauri Hajir tace "eh Allah na yarda kuma basai ka bari na sani ba ka min bazata ta gidan Aunty Fadilah ko gidan Ummi Hadiyyah"

"Ai ba shawararki nake nema ba can you be quiet🤫 ita Muyassara bata dashi"? Ya tambaya yana kallon yadda ta zaro ido jin abin yazo kanta Caraf Hajir tace "tana dashi sunan sa Nurul-qalbih" juyawa Asad yai yana kallonta kamar mai nazari sai kuma yace "da gaske sunansa kenan ko kuma kece kikasa masa hasken zuciya"?.

Hajir kamar ita ake tambaya da sauri ta sake cewa "itace tasa masa hasken zuciyarta" rufe baki baki Muyassara tai jin 'karyar da Hajir d'in ta shirga mata tace "Allah ba nice nasa masa ba sunansa kenan" tafi Hajir tai "aiko ba sunansa kenan badan kar yace kema zaiyi bincike a kansa ne kika gigice harda komawa kalar tausayi kamar zaki kuka" harararta muyassara tai "oh to ko kukan zanyi" rausaya kai Hajir tai "oho waya sani"

"Kai kumin shiru haka bana son jin komai zan zo Bahrain din ai duk ba tsira zakuyi ba".

Shiru sukai suna kallon sa daidai ya kar'bi jaririn dake hannun Aunty Naizarah yace "wannan yaron kine dama kinyi aure"?

Kaita d'aga "Eh kusan shekara biyu ma ai kasan rabuwarmu dakai tun a rasuwar Abu Samir bamu sake had'uwa ba" kai ya jinjina daidai Ajeeb ya shigo yana waya gud'ar da su Aunty Fadilah da Aunty Aleemah suka sakar masa ne yasa Ajeeb sauke wayar da sauri yana toshe kunnensa yace.

"Kai auntis wannan ai sai kusa mutum jinsa ya d'auke na tsawon da'ki'ku irin wannan 'kara kamar ina ramin gyare duk gud'ar ta miye"?.

"Oh really zakace bakasan ta meye ba"?.

Zama Ajeeb yai kusa da Asad yana cewa "yes but I've comfirmed it bansan komai ba 😝 na miye"?.

Dariya Aleemah tai tana cewa "eh gud'ar taya ka murna ce kasan dole muyi maka gud'a gobe iwar haka ka zama ango Ajeeb kabar sahun tuzurai irin su o'o🤩".

Murmushi Ajeeb yai yana kallon Asad daya hade gira jin abinda tace Ajeeb da 'yar fara'a a fuskarsa yace "uhmmm Aunty Aleemah kenan aurena mai ganinsa saiya shirya surprise ne".

"To surprise ya wuce gobe kasha manyan kaya kuje mighty Alhussain ya kar'bo maka alkawarin ri'ke 'yar mutane cikin kima ai tayi dace baka da fad'a ba kamar Asad ba shikam matarsa Allah yasa mai ha'kuri ce idan kuma itama mai zafi ce irinsa hummm zakusha rabiyar fad'a" kai Ajeeb ya jinjina yana cewa "tabbas kinyi gaskiya Asad kamar kububuwa haka yake a tafashe zafi wane yaji in kinji ana soja marmari daga nesa shifa Asad tuwon 'kaya ne miyar allura baisan wargi ba" dariya tai "hhhh lallai kam naga alama amma duk da haka ai ya.............................

Katse musu magana Aunty Fadilah tai daidai ta fito daga bedroom din Mami ta 'karaso gurin da murmushi fal fuskarta tana cewa "Asad muga hannunka" 'Dagowa yai daga wasan da yakewa yaron hannunsa yace "miye a hannun nawa"? "Babu kaidai mu gani man" bai bata ba kawai ya tsaya ya zuba mata ido tamke gira tai tana cewa "Asad wannan kallon naka ai sai kasa mutum ya 'kwaru please bring me your hand✋" mi'ko mata yai yaga dai me zatai masa babu zato yaji ta shafa masa abu a hannu sai tashin 'kamshi yake bud'e idonsa yai akan abun yana cewa.

"Subahanallahi Aunty Fadilaty meye wannan kika shafa min" ya karasa maganar yana jin zuciyarsa na tashi kamar zaiyi amai dariya tai tana sakin gud'a tace "wannan lalle ne na shafa maka".

Had'e rai yayi "lalle? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un meye had'i na dashi kuma amfanin me yake"? "Amfanin dole a shafa maka tunda zaka zama ango".

Kai ango kuma sake had'e fuska yai "wanne irin ango? Ajeeb dai zakiwa haka ba niba kawai kin 'bata min jiki".

'Dan zaro ido Aunty Fadilah tai "oh sorry haka ne mantawa nai but tun d'azu Ajeeb aka shafa masa nasa, kodan ai ba matsala tunda kai Hussainin ango ne ko" shiru yai yana kallon Ajeeb wanda yake dariya wata uwar harara ya sakar masa wato silarsa yasa an bata masa jiki sannan tsabar iskaci yake masa dariya mi'kewa yai yana kallon Fadilah yace.

"Good night Aunty Fadilaty".

"Mu kwana lafiya Asad" ta fad'a da fara'a ajewa Naizarah jaririnta yai yana fita shima Ajeeb bai jima ba ya musu sallama yabi bayansa a bedroom ya samu Asad yana tsaye jikin window daga shi sai 3Quarter da singlet fara iskar waje mai sanyi na shigowa ta windon tana kad'a gashin kansa dake she'ki jin motsi a bayansa yasa ya juyo suna had'a ido da Ajeeb ya sake d'aure fuska yana cewa.

"Wato dan wulakanci Ajeeb gashi nan kasa a dalilinka jikina sai warin lalle yake".

Shima Ajeeb din hade rai yai yana d'auke kai ya karasa bakin gado ya zauna ya kalli yadda lallen ya 'bata masa farar rigar jikinsa yace "da nai maka me? Dama nace Aunty Fadilah ta shafa maka lalle ne uban yan sharri".

"Eh ai silar Kane kaita nufo dashi kasa ta ya'ba min ni meye hadina dashi nine ango ko kai fad'a min"?.

Kallon sa sosai Ajeeb yai sai kuma yasa dariya yana cewa "dama yau ba muyi ba tun safe na lura dakai kana takala ta fad'a ina share ka domin ni ango ne bazan biyewa tuzuru irinka ba shiyasa yanzu daga laifin daba nawa ba kake neman d'ora min dan ni akazo shafawa ya sameka a tunani na ai duk daya ne Asad babu bambanci tsakani na dakai kaine muke uwa daya uban daya dukkan yarda ta Asad tana gareka na amince dakai fiye da yadda kake tunani banida wani wanda ya kaika balle har na kalleshi naji dad'i a raina inai maka wani irin so wanda baki bazai iya musaltashi ba kuma zanci gaba da sonka matukar raina indai ina numfashi,.

'Dan dakatawa yai tare dayin shiru yana kallon Asad sai kuma ya ri'ko hannun sa batare da ya sake cewa komai ba suka zauna a bakin gado hannunsa na cikin nasa ya ri'ke sosai yaci gaba.

"Asad dan Allah komai zai faru gobe karka tada hankalinka ka d'auka cewa kaddara ce kuma kada kayi ba'kin ciki nasara tana tare dakai duk da zakaga abubuwa sa'banin fahimtar ka a matsayina na d'an uwanka ina gargad'in ka cewa kabi gaskiya Asad ka tsaya akan daidai dan Allah Asad gobe karka tada husuma a gidan nan ina fata zakayi min wannan alfarmar"? Ajeeb ya karasa maganar da serious face yana kallon Asad wanda shima shi yake kallo duk jikinsa ya saki da maganganun Ajeeb d'in saiya samu kansa cikin fargaba da shiga tunani iri iri meya faru meyasa Ajeeb yace masa haka a irin wannan lokacin shidai ya a iya sanin sa tunda suke dashi bai ta'ba fad'a masa magana irin haka ba sai yau meyasa? Katse masa tunani Ajeeb yai.

"Asad baka ce komai ba please 🗣️say something ️".

Kasa cewa komai Asad yai sai kallon Ajeeb da yake yana sake jujjuya maganar daya gama fad'a yanzu ya kasa gane me Ajeeb ke nufi ina ya dosa to meya kawo wadannan maganganun? Girgiza shi Ajeeb yai yana cewa "Asad are u ok? Kana lafiya kuwa"?.

Kai ya d'aga masa da'kyar yace "eh" kallon sa sosai Ajeeb yake yace "to amma ina ta magana kayi shiru kamar kurma meyasa naga ka canza yanayi daga yaune fa na final zaman karshe a bedroom tare ni dakai da sunan kwana saidai dan nishad'i shikenan gobe iwar haka bazaka ganni ba koda kud'i inacan kana nan".

Tabdijan wai tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Asad ji yayi hankalin sa ya 'kara mugun tashi fiye da da hajijiya na d'ibansa kansa har ciwo yake ya d'au zafi sosai yake kallon Ajeeb da shikam harkar gabansa kawai yake kamar dai bai fad'i komai ba ganin zai sake magana yasa Asad cewa.
Chapter 116 · 0% Book details