Sashe 94
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tun a daren suka fara shiri asubar fari bayan anfito daga sallar asuba sukaci gaba da shirya sauran kayan amma iya suturunsu banda koda cokali babu wacce ta d'auka sai kayan sawa saida gari yayi haske sosai har rana ta fito⛅ malam Habu ya dawo sannan sun gama shiri sunyi gurum a gaban d'auri d'aurin kayansu suna jiransa shi kuma yayi tunanin bai kamata koda ace Ilyah yana watsar dashi ya kyaleshi ba dole zaije ya masa sallama akan zaibar gari yau.
Guri ya samu a kofar gidansa ya zauna babu yaron dazai aika cikin gidan shiru shiru yana ta zaune ganin kada lokaci ya 'kure masa yasa ya tashi yana buga murfin kofar gidan tare da yin sallama kafin ya koma ya zauna da kamar minti biyar Ilyah ya fito yana bud'o kofa tare da le'ko kansa waje yaga waye ganin Malam Habu zaune a kofar gidan yasa ya karasa bud'e kofar yana fitowa yace.
"Lafiya zaka zo da wannan sassafen kana bugawa mutane kofa bayan ba yanzu ne lokacin tashin mu a barci ba menene kuma".
Mi'kewa tsaye malam Habu yai bai damu da yadda ya nuna masa ba kawai ya mi'kawa Ilyan hannu yana zuwa barka da asuba yaya Ilyah ina kwana"?.
Bai amsa masa ba bai kuma bashi hannu sunyi musabaha ba sai tambaya daya sake jefo masa "wai Habubakar ko 'batan kai kayi ne naga sai wani ladabi kake min bayan kai mutum ne mai tsaurin ra'ayi nasanka nasan halinka batun yau ba amma dai wani abu kazo nema a gurina ko? Ko har yanzu bashin kud'in ne baka gama biya ba saika sayar da 'yarka guda daya ka biyasu tunda yanzu kam baka komai a duniya bandasu dama sunyi ba'kin jini ba wacce take da saurayi bazasu ta'ba auruwa ba tunda sun riga sun jibge kalli fa babbar yarka Asma'u tafi su Hassan amma har yanzu tana gabanka hummm ba'kin cikin su ne zai kashe ka balle ba d'a namiji ka samuba taya idan ka tsufa wazai kula dakai sannan matsiyatan 'ya'yan naka kila tsinannu zasu aura talakawa irinka idan ma sun aurun kenan balle a son zuciyarka kayi tunanin sune zasu taimaka maka 'ya'ya maza dasu ake ado🙄 kuma dasu ake more rayuwa🤔 dasu ake nishad'i🙊 dasu ake had'a tafiya🤪 dasu ake had'a karfi da karfe😳 kuma 'ya'ya maza sune komai sukai ado ne🤐 amma ba 'ya'ya mata ba musamman 'ya'yan talaka irinka sukam babu abinda zasu amfanawa mutum banda damuwa da 'kuncin rayuwa kuma banyi qarya ba Habubakar ka duba yanzu sun saka a wani hali sune silar karyewar arzikinka idan baka fahimta ba ko ba haka bane"? Ilyah ya tambaya yana kallon shi.
'Dagowa malam Habu yai yana kallon Ilyah cikin jin takaicin maganar wulakancin da yake fad'a masa amma saiya share ya danne d'acin da yake ji a ranshi yace "niba wannan ya kawoni ba dama nazo ne nai maka sallama yau zan tashi insha Allahu zan bar gari kada na tafi babu sallama kaji jita-jita daga baya a gari babu dad'i muna uba d'aya tunda bani da wani d'an uwa na jini bayan kai komadai menene ubanmu d'aya kuma hannunka baya ru'bewa ka yake ka jefar shiyasa nazo na fad'a maka"
Dubansa Ilyah yai yana cewa "au haba yau zaka bar gari? Gudun hijira zakai kenan to a sauka lafiya ba shine abinda ya kawo ka gurina ba to ai ka fad'a min naji shikenan saika dawo idan kuma inka tafi bazaka dawo ba har abada ma had'u a lahira🙁 sannan qarya ne kace hannunka ya ru'be ka'ki yankewa ka jefar nidai zan yanke kuma na jefar ka gane"¿.
Cike da mamaki malam Habu ya tsaya kawai yana kallonsa ya tabbata yanzu kam Ilyah yayi nisa ya wuce inda yake zato yasan babu imani a tattare dashi ko d'igo tunda har yake zazzaga masa maganganu marasa dad'i haka bayan yasan halin da yake ciki kad'a kai Malam Habu yai yana cewa "shikenan yaya Ilyah zan tafi Allah ya sadamu da alkhairi shine fatana sai wata rana".
Ta'be baki Ilyah yai yana bin bayansa da kallo kafin yace "to to d'an gudun hijira agaida nagaba aida na d'auka zaka tsaya ayi bikin shalele dakai kodan uwar me zaka bani ban gayyace kaba da masu nauyin aljihu ake harka bada talakawa ba".
Shidai malam Habu bai sake ce masa 'kala ba yayi tafiyarsa yanajin 'bacin ran wannan maganar da Ilyan ya fad'a masa amma ba komai lokacin sane wata rana sai labari yana zuwa gida ko zama baiyi ba yaiwa Rakiya sallama yace su fito da kaya waje haka kowa ta dau kaya aka suka fita a gidan abun gwanin ban tausayi inka gansu a wannan lokacin mutane a layi sai binsu ake da kallo Malam Habu yana gaba da Ghana must go a kansa su kuma suna biye dashi kowa suma da kaya suna cikin tafiya sun kusa fita daga qauyen sukaji ana 'kwalla kira.
"Malam Habu Malam Habubakar ka tsaya".
Dakatawa yai tare da waigawa bayansa can nesa ya hango Sadi sai cin gudu yake har ya karaso inda suke yana haki yace.
"Haba malam Habu ina zaka je haka dan Allah ka dawo kar kabar garin nan yanzu Ina kasan zaka nufa komai yai zafi maganinsa Allah kada ka yanke hukunci lokacin da kake cikin fushi na rokeka daka sauke kayan nan ka taho mu koma gida karkaje ko'ina".😞
Kai Malam Habu ya girgiza yana kallon Sadi yace "wallahi Sadi bazan dawo garin ba a yaudai na barshi kuma babu mai dakatar dani najishi bawai dan cin mutuncin da yaya Ilyah yayi min ba a'a kawai garin ya fita min arai kuma bazan fasa barinsa ba saidai idan Baffah ne ya dawo yace na ha'kura kaga kuwa abinda bazai yuwu ba kenan domin wanda ya mutu ya mutu Sadi kayi hakuri dan Allah bawai banji shawarar daka bani bane a'a nagode da nuna kaunarka gareni domin abinda kaimin wallahi ko yaya Ilyah da muke uba d'aya baiyi min abinda kaimin ba a rayuwa Allah ya saka maka da alkairi Allah ya kaddara saduwarmu saina dawo" kallon iyalan nasa dake tsaye suna sauraren su yai yace "kai ku muje sai wata rana Sadi bazan gajiya da ce maka nagode bs domin duk garin nan babu wanda ya damu dani koya damu da barina daga garin daga kai sai Rakiya matar yaya Sabi'u bazan ta'ba mantawa daku ba a rayuwata" ya kasara maganar hawaye na zuba masa tuna d'an uwansa ya tabbata da ace Sabi'u yana da rai duk haka bazata faru ba bazai ta'ba shiga damuwa da tozarci ba koda na minti daya babu yadda Sadi ya iya yana tsaye yana kallo malam Habu ya juya sukaci gaba da tafi kamar ya d'ora hannu aka ya rusa kuka dan ba'kin cikin tafiyar malam Habun haka yake ji da yana da gida da gona wallahi daya hanashi tafiya ya bashi yana tsaye tun yana hangosu har ya daina ganinsu hawaye ne kawai yaji yana zuba masa shar shar daga idonsa jiki a sanyaye da'kyar ya d'aga kafarsa ya fara tafiya ya koma gida cikin tarin damuwar inda malam Habu ya nufa yanzu.